Header Ads
Showing 39001 words to 42000 words out of 49839 words

Chapter 14 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt

Ads the beginning of article before Image

23 Jun 2024

479

Ads at the middle of Article

jikinsa.

Bawani ɓata lokaci suka wuce da ita hospital.

Wata hospital ce ta mata wadda yataɓa aiki a can suka wuce da ita, suna isa da ita likitoci suka karɓeta suka wuce da ita ciki ɗakin bincike, sai da suka kammala komai sannan suka fito sukace yasamesu office.

Suna isa office ɗin nasu bayan sun gaisa da yake sun sanshi sose, sabida wancan lokacin yayi aiki a hospital ɗin kuma sose suka ji daɗin zama dashi dan ba yadda basuyi ya zauna yaci gaba da aiki dasu ba yace a'a shima zaije ya taimakawa ƙasarshi.

Duban doctor yayi yace, "ya mai jikin ina fatar tasamu sauki".

Sai da doctor ya gyara zaman sa yace, "eh ta samu sauƙi sose kuma idan takiyaye dukukin da zamu bata kuma ta kiyaye shan magani to zata sauma sauƙi dan haka sai ankula sose".

Aunty ta dube doctor tace, "mike damunt?".

Sulaiman yace, "a'a Aunty ai ba sai munji ba kawai mu barsu suyi aikinsu".

Aunty tace, "a'a gwara muji inyaso akiyaye gaba".

Tace, "Doctor inajinka".

Doctor yace, "dama bawani abu babba bane lokacin dai datayi miscarriage ba awani bata kula sose ba, kuma gashi tana buƙatar haka dan yanzu idan ba kulaba aka aji wannan abun da ya tushe mata mahaifa yakan iya zama sanadiyar haka bazata sake ɗaukar ciki ba".

Wata ajiyar zuciya Aunty ta sauke mai ƙarfi kana tace, "ayi mata duk abinda yakama doctor".
Tana faɗar haka bata tsaya komai ba ta fito daga office ɗin ranta aɓace.

Irin yadda Sulaiman yaga ta fito jikinsa duk sai yayi sanyi dan shi bai so doctor yayi bayani akan matsalar Hafsat ba, da yasan zatace ayi mata bayani wallahi da bai bari ta shigo office ɗin ba, tunanin yaga bazai ƙareba, dan haka ya tashi yabita yaji mi zata ce.

Tunda Anwar ya bar gidan gabansa ke famar faɗuwa har inda yazo masaukin sa ya haɗa duk wani abun buƙatar shi yayi sallama da abukinsa sannan yarakashi filin jirigi.

Shidda na yamma Anwar yabar ƙasar india zuwa ƙasar sa ta haihuwa wato nigeria.

Koda yaje har tashiga mota shi kadai take jira, dan da ace makulin motar na hannuta da tuni tajima da bari hospital ɗin.

Yana ƙarasowa yashiga motar yaja suka tafi gida, har suka isa ba wanda yayiwa ɗan uwansa magana.

Yana yin parking ta buɗe mota tafito zuciyar ta na ƙuna sabida wani baƙinciki da ya rufe ta.

Bayan ya kashe motar ya bi bayan ta, parlour yasame ta sai safa da marwa take cikin parlour.

Ɗayan kujera ya zauna kana ya dube ta yace, "Aunty"......kafin ya kai ƙarshe tace, "dakata Sulamain! bana son jin komai daga bakin ka, wato ni kamai da wawuya marar hankali shiyasa har za ka ɗauku budurwar dakake tare da ita ka kawomin gida matsayin ƴar makaranta wai ita mai kamun kai ko! kuma har kana iƙirarin auren ta, to kasani daga yau ba kai ba ita dan haka kar ka kuskura kadowo da ita gidannan kuma yanzu zan kira su Abba na gaya musu abinda ake ciki, ni kodama nayi mamakin abin da ya maidaka ƙasar nan da sunan karatu ashe kai kadai kasan karatun da zakayi".

Haka taci faɗanta har ta gama bai ce da ita komai ba, sai da aka ɗau lokaci yana zaune kana ya buɗe baki yace,

"Haba Aunty wallahi bansanki da haka ba, ni nasan Aunty na mai tausayi ce da kuma haƙuri kuma nasan Aunty na bata zartar da hukunci har sai tayi bincike akai, dan haka nake ruƙunki dan Allah ki tsaya ki saurareni plees".

Dubanta yayi yaji miza tace amma sai yaji bata ce komai ba, irin yadda yaga tabada natsuwar ta yasan zata saurareshi.

"kamar yadda kika sani ina son Hafsat so bana wasa ba dan tun lokacin da na fara haɗuwa da ita makaranta nakamu da sonta, amma itako alokacin ba soyayya ce gabanta ba kartu shine gabanta shiyasa ko saurarena bata tsayayi ba, ban jima da haɗuwa da itaba ne nazo ƙasaranan dan na yi phd, sai dai duk wani mutsi nata idan tayi sai nasani koda kuwa bani tare da ita, kuma dakika ce Hafsat yarinya tace wallahi ko ɗaya, ni banta sanin Hafsat ƴa mace ba, ke ba itaba duk wata mace babu ta inba Maryam matata ba, Aunty, Hafsat daki ka gani wata ƙaddara ce ta afka akanta, wadda duk wani musulmi mai imani ya tausaya mata, data na nigeria Allah ya haɗata da wani sheɗanin saurayi wanda ya illata mata rayuwa kuma duk da haka bai bar ta ta huta ba yaƙi ya rabu da ita, nikuma lokacin dana samu labarin haka shine nayi shige da fice har tasamu scholarship na tafiya waje karatu ko zai rabu da ita, to nayi nasar rabasu amma yanzu haka yananan yana neman ta ruwa ajallo, danshi na hanata fita makaranta kwana biyu wannda ke da ita baku san dalilil haka ba".

Dubanta yayi yace, "Aunty labarin Hsfsat nada tsayi amma kiyi haƙuri sabida duk lokacin dana tuna sai nayi ƙwalla, amma wani lokaci zan baki insha Allah".

Kallonsa tayi da kyau kana ta buɗa baki tace, "yanzu har kasan yadda take amma kake ƙoƙarin kajefa kanka aciki, to bari kaji koda zan yarda taci gaba da zama gidannan to bazan yarda ka aureta ba, dan da alamu ba ajinka bace, dan haka nake baka shawara tun wuri kaciri wannan so dakake mata dan gaskiya bazamu barka ka aure yarinyar da bata da kamunka ba".

Yace, "Aunty kuyi haƙuri dan inaji ajikina rasa Hafsat dai-dai yake da rasa raina, Aunty bansaki da haka ba, kuma ki gayamin gaskiya, zaman da Hafsat tayi agidannan akwai abinda tayi wannda zai nuna rashin kamun kanta?".

Kai ta girgiza masa alamar a'a.

"Kingani dan haka Aunty kirufamin asiri karki bari kowa yaji wannan maganar kuma kitaya ni da addu'a".

Sassanyar ajiyar zuciya ta sauke kana tace, "na fahince ka, kuma insha Allah ba maijin wannan zance".

Yace, "yauwa Aunty na, na gode sose".

Murmushi tayi kana tace, "yaushe zaka zo muje muga yadda jikin nata yake?".

"Sai gobe, sabida ina tunanin idan muka tafi tare da ita zamu dawo inyaso taciga da shan maganinta".

Tace, "to haka yayi".

Sallama yayi mata yatafi da sunan gobe zai dawo.

*******
Safiyya ce kwanci ɗakinta ita kadai, ba abinda take sai aikin tunanin ƴar uwata Hafsat, tayi kuka har tagaji na rashinta, gashi har yanzu ko waya basu taɓayi ba, kuma ga Babanta har yau fushi yake dasu, duk abu yazo ya haɗe mata waje ɗaya, dan yanzu maganar da ake Baban ta yace wata biyu ya bata ta kawo masa miji dan aure zaiyi mata, kuma ita duk cikin masu sonta bataji wanda ya kwanta mata araiba, tana ciki haka taji Yayan ta Abbas na kiranta, da sauri ta tashi ta fita.

Zaune ta samesu shida Mama zaune, ƙarasowa tayi ta zauna kusa da Mama tana faɗin, "gani Yaya".

Wata leda dake gabansa yace, "gashi kije ki kawa Umma, kice ina gaisheta anjima zanzo".

Karɓa tayi tace tau bari nasa hijab ɗina".
Tana sawa ta ɗauka tafice Mama tace tana gaisheta....

*#VOTE COMMENT SHARE*
*SHAFI NA 28📑*

*__________📖* Koda taje gidan su Hafsat, sose Umma taji daɗin ganin ta tace, "Umma gashi inji Yaya yace na kawo miki yana gasheki kuma anjima zai zo".

Sai da Umma ta karɓa tace, "to mungode, ai yanzu bashi ba ko ke kin daina zuwa, yanzu nida Mamarku kaɗai ke zumunci, amma kema dan ƴar uwarki bata nanne, nasan da kinzo".

Sai da Safiyya ta sadda kanta ƙasa kana tace, "a'a Umma yanzu ba ko ina nake zuwa ba sabida bana jin daɗin fitar".
Ta kai ƙarshin zanci kamar tayi kuka.

Dubanta Umma tayi da alamun tausayawa tace, "wai Safiyya har yanzu baki samu ko number wayar taba? wallahi yanzu haka sabida baƙincikin rashin ta har na kamu da matsalar ido, dan yanzu ba komai nake gani sose ba, Safiyya dan Allah ki ƙara bincika muna koda mai number ta yabamu, dan kwannan ina yawan mafarkinta tana kuka".
Magana take amma hawaye na zuba a idonta.

Safiyya ma da taga Umma na kuka itama bata san lokacin da yazo mata ba, cikin kuka tace, "Umma insha Allah gobe zanje makaranta na ƙara bincike koda Allah zai sa musamu number ta".

Godiya Umma tayi mata haɗi da sanya mata albarka.

Safiyya tashi tayi ta taya Umma sauran aikace-aikacin gida daga baya tayi tafiyar ta.

*******
Saida su Hajara sukayi kwana biyu police station sannan akafito dasu dumin atambaye su daga ina suke?.

Wani ɗan ƙaramin ɗakine mai kama da akurkin kaji wannda ko mutum ɗaya yace ya zauna sai ya wahala bare mutum biyu, shi aka buɗe suka fito daga ciki kamar wasu ƴa yunwa, sabida kwana biyun da sukayi har sun fara zanja kala.

Gaban DpO aka tisasu, sai da yagama yimusu kallon tsaf kana yace, "watu kune ke fitowa dan kulalata muna ƙasa ko?".

A wahalce, "Hajara ta buɗa baki tace, "wallahi a'a asali mu ƴan makarantane".

DpO yace, "wace alama zangani wadda zata tabbatar min ku ƴan makaran tane".

Jiki na karkarwa ta buɗe jika ta ɗauku l. D card ɗinta na makaranta ta nuna masa.

Karɓa yaya kana ya duba yace, "to mi yafitar duku cikin dare?".

Rasa mizata ce tayi sai can tace, "Kakatace kuma ita kaɗai ta ragemin aka bugu min waya akaci ta rasu shine na ce sai naje ita kuma ƙwata tace nabiri da safe muje nace a'a to shine tace zata rakani, muna fitowa muka samu ɗan acaɓa to yana shigowa damu cikin garin sai yatusamu wajan da kuka ganmu".

Takai karshin maganar tana kuka sose.

Bayan dpo yagama ƴan rubuce² sa ya sallamesu tare da jamusu kunne sose, kana suka kama hanyar fita.

Bayan sun fito kallon-kallon suka farayi tsakanin su sai Zahara ta buɗa baki tace, "to yanzu ina zamuje?".

Sai Hajara tace, "muƙarasa wajan gidan Malam, dan wallahi wannan uwar wahalar da muka sha bazata tashi abanza ba sai munɗau fansa akan Anwar da Hafsat".

Sai zahara tace, "da muntafi gida zai fi".

Hajara tace, a'a gaskiya ni ba inda zanje, sai inke zaki tafi na tarar miki napep kije".

Tace, "a'a tare muka zo kuma tare zamu koma, haka suka ƙarasa cikin garin da Malamin yake, wani gida suka yadda zango kuma suka ruƙesu nan zasu zauna har lokaci da zasu je wajan Malam yacika, bamusu ko suka yardar musu har lakaci ya cika.

Ƙarfe ukun dare nayi suka fito suka tafi wajan Malamin can saman wani dutsi, kuma koda suka je wajan cike yake da mutane duk wannda ke wajan burisa ya ƙarasa wajan bokan nasu.

Sai wajan ƙarfe huɗu su Hajara suka samu shiga, bayan sun shiga basu wani jama ba suka fito ɗauke da murmushi afusakar su, waje suka samu suka zauna har inda gari yayi haske sannan suka kamu hanyar gida ciki da farin ciki a zukatansu.

Hafsat tana hospital kwance tana bacci, kanata take gargizawa tana so ta tashi amma takasa, sai can ta samu ta buɗa baki ta ambace sunan Allah, aikuwa tana faɗin haka ta farka cikin razana sai haki take kamar wanda tayi tsarar gudu.

Ba ɓata lokaci ta tashi tashga toilet ɗin dake cikin ɗakin, alwala ta ɗuru tazo ta tada sallar nafila.

Haka ce ta faru wajan Ummar Hafsat itama wani mugun mafarki tayi kuma akan Hafsat, ba ɓata lokaci taje ta ɗuru alwala ta tada sallah tana kai kukanta wajan Allah.

Hafsat tana gama sallah ta ɗauku wayar ta ƙur'ani dake kan wayar ta ta buɗe ta fara karatu, sai datayi karatu sose tafara koro addu'oi tana kuka tana faɗin,

_Lailahailla anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin._
_Hasbiyal lahu lailaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul arshil azeem._

Haka take ta mai-mai tawa tana kuka sose, dan baƙaramin tashin hankali tashigaba gami da wannan mafarki, tana kan sallaya har akayi kiran sallah ta gabatar da sallah tana cikin tasbihi bacci mai nauyi ya ɗauke ta.

Gyafin Umma ma haka ta kasance.

Kusan ƙarfe goma sai ga sulaiman yazo wajan Aunty Shemah dan su yake suje suga ya jikin nata.

Bai jima da tahuwa ba sukaje wannan karum har da Affan.

Koda suka isa wajanta sai bacci take, mutsin da tajine shi ya farkar da ita daga baccin da take, ahankali ta buɗe idonta, wayar dake kusa da ita ne ta ɗauku ta duba lokaci, sose tayi mamakin wannan baccin da tayi, kuma yanzu wasai take jin jikinta kamar bata taɓa ciyo ba,juyawar da zatayi sai ganin Aunty da Sulaiman tayi suna mata murmushi, martanin murmushin ta mayar musu kana tace, "Aunty ku ƙaraso".

Affan ne ya antayo da gudu ya faɗa jikinta yana faɗi, "missing you Aunty na".

Murmushi tayi kana tace, "missing too Affan".

Tana faɗa tana jan kuma tunsa.

Har zai sake magana Aunty tace, "kada kacika mu da surutu nan ba gida mukeba hospital muke".

Murmushi Hafsat tayi haɗi da gaishesu.

Amsawa sukayi sannan sukayi mata yajiki?.

Tace, "gaskiya ni yanzu ba abinda ke damuna, ni kwai mu koma gida".

Sulaiman yace, "bari naje naji mi zasu ce idan suntabbatar da kin ji sauƙi sai muwuce gida.

Bai jima da fitar sa sai gashi ya dawo tare da faɗin, "Aunty sunce zamu iya tafiya dan duk wani bincike sun mata kuma sunce yanzu bawani matsala sai dai takiyaye shan magani".

Aunty tace, "insha Allahu zata kiyaye".

Daga haka suka juyo zuwa gidan Aunty Shemah.

*****

Tunda ya tashi bacci yaji sabon al'amari ajikinsa, dan jiyake kamar bashi ba, ya kasa tsaye ya kasa zaune, shidai burinsa yaganshi a sokoto yanzu.

Wayar sa ya ɗauka ya dan yakirata kuzai samu natsuwar abinda yakeji....

*#VOTE COMMENT SHERA*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*

*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*

~~WattpadSummy M Na'ige~

*SHAFI NA 28📑*

*__________📖* Koda taje gidan su Hafsat, sosai Umma taji daɗin ganin ta tace, "Umma gashi inji Yaya yace na kawo miki yana gasheki kuma anjima zai zo".

Sai da Umma ta karɓa tace, "to mungode, ai yanzu bashi ba ko ke kin daina zuwa, yanzu ni da Mamarku kaɗai ke zumunci, amma kema dan ƴar uwarki bata nan ne, nasan da kin zo".

Sai da Safiyya ta sadda kanta ƙasa kana tace, "a'a Umma yanzu ba ko ina nake zuwa ba sabida bana jin daɗin fitar".
Ta kai ƙarshin zanci kamar tayi kuka.

Dubanta Umma tayi da alamun tausayawa tace, "wai Safiyya har yanzu baki samu ko number wayar taba? wallahi yanzu haka sabida baƙin cikin rashin ta har na kamu da matsalar ido, dan yanzu ba komai nake gani sosai ba, Safiyya dan Allah ki ƙara bin cika muna koda mai number ta yabamu, dan kwannan ina yawan mafarkinta tana kuka".
Magana ta ke amma hawaye na zuba a idonta.

Safiyya ma da ta ga Umma na kuka itama bata san lokacin da yazo mata ba, cikin kuka tace, "Umma insha Allah gobe zanje makaranta na ƙara bin cike koda Allah zai sa musamu number ta".

Godiya Umma tayi mata haɗi da sanya mata albarka.

Safiyya tashi tayi ta taya Umma sauran aikace-aikacin gida daga baya tayi tafiyar ta.

*******
Saida su Hajara sukayi kwana biyu police station sannan akafito dasu dumin atambaye su daga ina suke?.

Wani ɗan ƙaramin ɗakine mai kama da akurkin kaji wannda ko mutum ɗaya yace ya zauna sai ya wahala bare mutum biyu, shi aka buɗe suka fito daga ciki kamar wasu ƴa yunwa, sabida kwana biyun da sukayi har sun fara zanja kala.

Gaban DpO aka tisasu, sai da yagama yimusu kallon tsaf kana yace, "watu kune ke fitowa dan kulalata muna ƙasa ko?".

A wahalce, "Hajara ta buɗa baki tace, "wallahi a'a asali mu ƴan makarantane".

DpO yace, "wace alama zangani wadda zata tabbatar min ku ƴan makaran tane".

Jiki na karkarwa ta buɗe jika ta ɗauku l. D card ɗinta na makaranta ta nuna masa.

Karɓa yaya kana ya duba yace, "to mi yafitar duku cikin dare?".

Rasa mizata ce tayi sai can tace, "Kakatace kuma ita kaɗai ta ragemin aka bugu min waya akaci ta rasu shine na ce sai naje ita kuma ƙwata tace nabiri da safe muje nace a'a to shine tace zata rakani, muna fitowa muka samu ɗan acaɓa to yana shigowa damu cikin garin sai yatusamu wajan da kuka ganmu".

Takai karshin maganar tana kuka sose.

Bayan dpo yagama ƴan rubuce² sa ya sallamesu tare da jamusu kunne sose, kana suka kama hanyar fita.

Bayan sun fito kallon-kallon suka farayi tsakanin su sai Zahara ta buɗa baki tace, "to yanzu ina zamuje?".

Sai Hajara tace, "muƙarasa wajan gidan Malam, dan wallahi wannan uwar wahalar da muka sha bazata tashi abanza ba sai munɗau fansa akan Anwar da Hafsat".

Sai zahara tace, "da muntafi gida zai fi".

Hajara tace, a'a gaskiya ni ba inda zanje, sai inke zaki tafi na tarar miki napep kije".

Tace, "a'a tare muka zo kuma tare zamu koma, haka suka ƙarasa cikin garin da Malamin yake, wani gida suka yadda zango kuma suka ruƙesu nan zasu zauna har lokaci da zasu je wajan Malam yacika, bamusu ko suka yardar musu har lakaci ya cika.

Ƙarfe ukun dare nayi suka fito suka tafi wajan Malamin can saman wani dutsi, kuma koda suka je wajan cike yake da mutane duk wannda ke wajan burisa ya ƙarasa wajan bokan nasu.

Sai wajan ƙarfe huɗu su Hajara suka samu shiga, bayan sun shiga basu wani jama ba suka fito ɗauke da murmushi afusakar su, waje suka samu suka zauna har inda gari yayi haske sannan suka kamu hanyar gida ciki da farin ciki a zukatansu.

Hafsat tana hospital kwance tana bacci, kanata take gargizawa tana so ta tashi amma takasa, sai can ta samu ta buɗa baki ta ambace sunan Allah, aikuwa tana faɗin haka ta farka cikin razana sai haki take kamar wanda tayi tsarar gudu.

Ba ɓata lokaci ta tashi tashga toilet ɗin dake cikin ɗakin, alwala ta ɗuru tazo ta tada sallar nafila.

Haka ce ta faru wajan Ummar Hafsat itama wani mugun mafarki tayi kuma akan Hafsat, ba ɓata lokaci taje ta ɗuru alwala ta tada sallah tana kai kukanta wajan Allah.

Hafsat tana gama sallah ta ɗauku wayar ta ƙur'ani dake kan wayar ta ta buɗe ta fara karatu, sai datayi karatu sose tafara koro addu'oi tana kuka tana faɗin,

_Lailahailla anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin._
_Hasbiyal lahu lailaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa Rabbul arshil azeem._

Haka take ta mai-mai tawa tana kuka sose, dan baƙaramin tashin hankali tashigaba gami da wannan mafarki, tana kan sallaya har akayi kiran sallah ta gabatar da sallah tana cikin tasbihi bacci mai nauyi ya ɗauke

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads