Showing 30001 words to 33000 words out of 49839 words
Chapter 11 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
nasamu sauƙi".
Bata yarda da abinda yace ba amma sai ta kyaleshi tace, "tau Allah ya ƙara lafiya, amma katashi kaci wani abu".
"A'a Aunty yanzu zan koma sokoto dan gobe nake son na koma gida dan har yanzu ban koma ba"......kafin ya rufe baki tace, "mi kazoyi abuja yanzu?".
Yace, "wani aiki ya kawuni nida abokina kuma koda nazo har ya wuce Indian "..... tace, "to duk da haka sai kaci wani abu kafin katafi.
Ba musu ya tashi ya ɗanci kaɗan kana yayi mata sallama ya wuce warsa.
filin jirgi ya isa, ciki ikon Allah ya samu jirgi ya shiga ya dawo da shi sokoto, gidansa ya isa koda yaje ga baki ɗaya garin yaji yayi masa zafi dan haka lokaci ɗaya ya fara haɗa kayansa kamar wani ma haukwaci, dan gaskiya bazai iya bacci a cikin garin ba, gara yabar garin ko yaji sauki abinda yake ji aransa.
Tunda aka nemi Hafsat ba a ganta ba Baban Safiyya ya daina kula kowa a gidansa, ba yadda Mamar Safiyya batayi ya haƙura ba amma yaƙi, sose suka shiga damuwa na rashin kulasu da Baban Safiyya ya daina.
Shiko Abbas Yayan Safiyya wani tashin hankali ya shiga wanda lokaci ɗaya har kwanci yayi kuma duk ba komai ya jawu haka ba sai rashi ganin Hafsat, dan yanzu shi kaɗai yasan ya yakeji na rashin Hafsat, dan ko ba afaɗa masa ba yasan ya kamu da son ta, kuma so bana wasa ba, dan ji yake a ransa duk inda take sai ya nemuta,dan a halin yanzu ji yake bazai iya rayuwa ba inba ita.
Safiyya ma duk tabi ta ƙare dan yanzu ko abinci da ƙyar take samun ci, ga school duk bata jin daɗin zuwa kuma gashi sun kusa fara jarabawa amma komai ta daina ganewa saboda rashi ƴar uwata.l
Tunda safe Umma ta fara shirin tafiya garinsu, ta haɗa duk wani abin buƙatar ta, tana cikin shirin tafiya sai ga Abban Hafsat ya shigo ɗakin ciki da tashin hankali, da sauri ya ƙaraso gareta yana faɗi, "haba Fatima miyayi zafi haka, dan Allah ki tausayamin wallahi ina cikin tashin hankali, kuma dan Allah ina son ki tsaya ki saurareni kona minti ɗaya ne Fatima".....yana faɗa amma kamar ya durƙusa mata sabida kaɗuwa.
Ba abinda tace dashi, kuma bata fasa haɗa kayanta ba dan ta tafi.
Daya ga ba alamun wasa acikin lamarin ta dan haka ya ƙarɓe jikar da take koƙarin fita da ita yana faɗin, "Fatima bari kiji duk son da kikewa Hafsat nafiki sonta nesa ba kusa, kuma bazan hanaki zuwa gida ba, amma kibari gobe insha Allah zan kai ki da kaina, kuma kisani fa Hafsat ba ko ina tajeba sai wajan karatu"....nan dai ya faɗa mata duk abinda ya sani game da Hafsat.
Sose Mama tayi kukan rashin ƴarta, amma duk da haka tace sai taje ganin iyayenta, ba yadda ya iya haka ya kaita tashir mota tashiga mota ta tafi garin su tabar Abba cike da kewarsu.
Awa ɗaya ta kaita tashar garin dange, napep ta hawa ya kaita cikin garin, tunda tashiga garin gabanta sai famar dukan uku-uku yake, bakin wata ƙofar gida mai napep ya ajeta, tunda ya ajita gabanta ya ƙara tsananta faɗuwa, sallamar mai napep tayi kana ta ɗau kayan ta dan ta ƙarasa cikin gidan, gab da zata shiga gida taga wani ɗan tsoho kwance da alamu ma bashi da lafiya, har zata wuce shi sai kuma ta ƙara kallonsa, gabanta ne ya bada dummmm ai basan lokacin da tasake kayanta ba ta ƙarasa gareshi tana faɗin Baba! Baba! lafiya kuwa na ganka haka?".....tafaɗi haka tana mai sanya kuka.
Kafin ya buɗa baki yayi magana sai ga wata mata ta kurnu kai dan taga wake kuka.
Ita kuma Umma mutsin da taje ne yasa ta ɗago kanta, ɗagowar da zatayi aikuwa sai ganin wata mata tayi tsaye tana kallon ta, suna haɗa ido ta zabura da ƙarfi ta tashi tana sun tayi magana amma takasa, bawani ɓata lokaci sai gashi ta faɗi ƙasa sume.
******
Sose Hafsat ke jin daɗin zama da Aunty Shemah, kuma tana jin daɗin karatu ba kamar da tana najeria ba, dan yanzu idan kaga Hafsat kamar ba ita ba, sose kyauta ya ƙara fita kamar wata balara ba.
Yau ma kamar kullum tana ɗaki kwance tana duba wusu books ɗinta sai jin wayar ta tayi tana ƙara, kamar baza ɗauka ba kuma sai ta ɗauka, suna Sulaiman taga ya bayyana, ba ɓata lokaci ta danna picking ,kafin ta ɓuɗa baki tayi magana yace, "ki samemu muna parlour muna jiranki".
Kafin tayi magana har ya datse kiran.
Cikin tsanaki ta tashi ta gyara jikinta kana ta sanya hijab ɗinta tafito falon gidan.
Ahankali take tafiya cikin natsuwa har ta kawo cikin parlour haɗi da sallama abakinta, izini sukayi mata da tashigo, tana buɗe labulen ɗaki sukayi ido huɗu da Sulaiman, murmushi yayi mata, itama ta mayar masa da martani haɗi gashe da su, amsawa sukayi da nuna faricikin ganinta afuskar su.
Bayan sun gaisa Sulaiman yace, "Aunty wai me kike ba ƙanwar taki ta koma kalar indian"......ya faɗa haka yana kallon Hafsat yana murmushi.
Sai Aunty Shemah tace, "kodai ka ƙyasa".
kafin yayi magana abukin tafiyar su Lukuman yace, "Hafsat shikenan kin bar mu tunda kin samu Aunty gashi ko a school baki neman mu".
Murmushi tayi tace, "a'a wallahi ba haka ba, lokaci ne babu amma naso na kai muku ziyara wannan satin".
Sai Sulaiman yace, "bawani nan ke dai kin samu Aunty kin manta damu"....haka dai suka sha firarsu, daga bisani kuma sukayi musu sallama suka tafiyar su, amma ako da yaushe Sulaiman na kirata yana tambayar ta koda tana buƙatar wani abu, watarana ko bata buƙata yakan yumata aiki, sose take jin daɗi yadda yake kula da ita, amma awani gyafe tsoro takeji.
Yau Monday tunda sassafe tashirya dumin taje makaranta, parlour ta fita ta same Aunty zaune tana jiran fitowar ta, Aunty Shemah na ganin ta fito murmushi ya bayyana afuskar ta kana tace, "Hafsat ki ƙaraso muyi breakfast muwuce school dan ƙarfe 8:00 zan shiga lecture kuma saura ƙan ɗan lokaci ya cika".
A gurguje sukayi beark suka fito suka wuce makaranta, koda suka isa saura kaɗan Aunty Shemah ta makara, dan haka suna shiga tayi parking ta fito batare ma da ta kashe mota ba ta bar ma Hafsat kye ta wuce warta.
Mota ta kashe haɗi da zare kye ɗin motar ta fito ta rufe, juyuwar da zatayi sai tayi arba da ƙawar ta Zeenatu, wadda suka haɗu da ita a nan kuma class ɗinsu ɗaya, kuma itama ƴar najeria ce, murmushi suka sakar ma junasu suka gaisa kana suka kama hanyar class ɗinsu, suna cikin tafiya sai jikin Hafsat ya bata kamar ana kallonta, juyuwar da zata yi sukayi ido huɗu da Sulaiman, murmushi tayi masa kana ta gaisheshi, magana yayi mata yace idan tagama lecture yana neman ta, tace tom sai ta fito.
Gaba ki ɗaya Anwar ya kasa zama ya kasa tsaye ba shiri ya kama hanyar kaduna cikin dare dan shi kam bazai iya zama garin sokoto ba Hafsat ba.
ƙarfe biyun dare ya isa garin kaduna, koda ya isa gida ko part ɗin iyayensa ba shigaba ya wuce part ɗinsa, ciki da damuwa .....
*Bani da bakin magana gareku, ku ƙara haƙuri pls, abubuwane sukayi min yawa, dan Allah ina baran addu'a gareku pls*🙏
*#Vote*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
~~WattpadSummy M Na'ige~
*SHAFI NA 23📑*
*__________*📖 da hanzari matar da ke ƙofar gidan tayi saurin ƙarasowa gareta tana faɗin, "Fati kitashi kinji"....tana faɗa ta ɗauku ruwa ta shafa mata a fuska.
Ba ɓata lokaci sai numfashin ta ya fara dawowa dai-dai, cikin hanzari Ummar Hafsat ta tashi tana riƙi Mama tana kuka mai cin zuciya tana faɗin, "Mama dan Allah kuyafemin".
Kafin tayi maga Baban ta dake kwance yana jin ance Fati ya tashi daga kwanciyar da yake, bakin sa na karkarwa yace, "wa na keji kamar muryar Fatina, koda gizo ne takemin ko mafarkin da na saba ne?".
Mama ta ɓuɗa baki cikin sanyi jiki tace, "eh Malam Fati itace"..tun bata rufe baki ba ya fara wa Allah hamdala kana yace, "Fati ƙaraso gareni kinji".
Ba musu ta ƙaraso gareshi tana faɗin, "dan Allah Baba kuyafemin nasan niyi kuskura amma dan Allah ina neman afuwarku".
Yace, "ba komai Fati, na yafemiki har a wajan Allah, kuma naji daɗin ganinki ina yaraye bam mutuba, sai dai dan Allah abinda nakeso dake shine Fati kuriƙa zumunci ko bayan raina kada kiyar da ki katse zumuncinki da ƴan uwanki,amma yanzu idan an kwana biyu ki shirya kije duk inda ɗan uwanki yake ki sada zumunci"....nasiha yayi mata sose akan tariƙa zumunci, daga baya suka tashi suka ƙarasa cikin gida.
Bayan kwana biyu da zuwan Ummar Hafsat gidan iyayenta ta kwashe duk abinda ke damun ta na ɓatan Hafsat har cikin da Hafsat tayi ta gaya musu, sose hankalin su ya tashi da suka ji wannan labarin, Malam da Mama faɗa sukayi mata sose kana suka nuna mata ba abinda yaje mata haka face katse zumuncin da tayi, bayan komai ya lafa suka bata magana mai sanyi kuma sukayi mata alƙawarin za su taya ta addu'a Allah ya bayyana ta duk inda take.
Mamar ta tace, 'ke Fati ke da mijinki bansa wanda yafi wani laifi ba, ace ka kwashe shekaru kana cikin garin sokoto amma kakasa leƙa ƴan uwanka, dan mi Allah bazai jarabe ku ba, ke kin kama waje kin zauna baki damu da kowa ba shima haka, wallahi kuntafka kuskure babba, amma muna ƙara godiya ga Allah da har ya nuna muku dai-dai".
Kuka Ummar Hafsat keyi kamar ranta zaifita.
Kwanta uku cin garin sai ga Abban Hafsat ya zo, aikuwa shima kansa yasha faɗa a wajan iyayenshi daga baya suka haƙura suka karɓeshi, bayan komai ya lafa shima ya faɗama ƴan uwansa abinda ke faruwa, sose mahaifinshi yayi masa faɗa kana yace ba komai ya ja masa haka ba sai katse zumunci da sukayi.
Da yake garin su ɗaya da Umma, bayan komai ya ɗan dai-dai ta tsakanin shi da iyayenshi kana yaje can wajan iyayen Ummar Hafsat suma suka ɗura daga wajan da iyayenshi suka tsaya.
Bayan kwana biyu da zuwan sa sun ɗan huta shida Ummar Hafsat duk ida wani ɗan uwa yake sai da sukaje, haka da yayi ne Ummar Hafsat ta ɗan ji sanyi har ta fara saki jikin ta dashi, satin su uku garin dange sannan suka dawo cikin garin sokoto.
Gari na waye wa Anwar ya shirya ya isa part ɗin iyayensa, koda yaje suna parlour zaune suna fira, sallamar Anwar da sukaji ne ta katse musu fira, da sauri iyayen nasa suka ɗago kai suka kallesa haɗi da mamaki a fuskukin su.
Kafin suyi magana ya ƙaraso garesu yana faɗin, "Daddy , Mumy barka da safiya".....yana faɗa yana kwanciya saman cinyar mahaifiyar sa.
Daddy ne ya buɗe baki yace, "Son saukar yaushe? haka akazo ko ka faɗa mana sai kayimana bazata?".
Sosa ƙyar kansa ya fara kana yace, "afuwan Daddy , garin ne naji ya isheni yasa nazo tun cikin dare".
Da sauri Mumy tace, "au kace tun cikin dare ka dawo".
Yace, "eh Mumy, amma kuyi haƙuri gajiya nayi da garin shiyasa na dawo"....kafin ya rufe bakinsa sai Daddy yace,
"Ai na ɗauka danaga ka jima acan ka samo muna sirika".
Murmushi Anwar yayi amma bai ce dasu komai ba, sai can yace, "Mumy yaunwa nakeji haďamin breakfast".
Tace, "tau autana taso muje dining kayi beark ɗin".
Daddy yace, "tashi muje har ni muyi beark ɗin....haka sukaje dining Mumy ce tayi serving ɗin su suka fara ci.
Kowa naci abinda ke gabansa amma ban da Anwar da ke jujjuya spoon ɗin dake hannusa.
Mumy ce ta kula da haka dan haka tace, "auta na, mike dumunka naga komai baka ciba sai juya spoon ke yi".
murmushi ya ƙaƙalo kana ya buɗa baki yace, "ba komai Mumy"....kafin ya rufe baki Daddy yace, "Son bana son karya kafaɗa muna abinda ke damunka dan tunda ka shigo na fahince akwai abinda ke damunka".
Ƙyyar kansa ya fara sosa kana ya sadda kansa ƙasa yace, "Daddy ba komai, kwai wani abuki nane da bashi da lafiya kuma nake son naje dubinsa amma ina gudun kuce yawon yayi yawa bazan jeba".
Kallon sa Daddy yayi yace, "hmm kai dai auta faɗi gaskiya, ai bazan ce haka ba, zaka iya zuwa dubinsa aduk lokacin da ka gadama".
Murmushi yayi haɗi da godiya ga mahaifin nasa kana yace, "Daddy ba fa nan yake ba india yake".
Sai Daddy yace, "a'a ba komai "dubiyace Allah dai ya baka ladar zuwa, amma dai ba jimawa zakayi ba autan Hajiya".
Da ameen ya amsa kana yace, "au Daddy ba da kai ba kenan"....ya faɗa haka ashagwaɓan ce, kana ya ƙara da cewa "next week insha Allah zanje".....fatar ahairi sukayi masa haɗi da sama ɗan nasu albarka.
Suna fitowa lecture ita da ƙawar ta Zeenatu, bayan sunyi ma juna sallama ita takama hanyar da za su haɗu da Aunty Shemah ita ko Zeenatu ta kama hanyar hostel.
Wajan da sukayi parking ɗin mota ta nufa dan ita gabaki ɗaya ta manta da maganar da sukayi da Sulaiman da yace idan ta fito lecture yana nemanta.
Tunda ta fito yake kallon ta tana tafiya cikin natsowa, a hankali take taka ƙafar ta har takowa gab dashi, bata ma lura da mutum ba har tazo zata wuceshi, da yaga alamun bata ganshi ba dan haka ya ɗauku waya ya danna kiran ta, tana tafiya taji wayar ta tafara ƙara, wayar dake hannuta ta duba taga wake kiranta, dan ita atunanin ta ko Aunty Shema ce? dubawar da zatayi sai taga sunan Sulaiman na yawo saman screen ɗin wayar ta, tunawa tayi da abinda yace mata, ɗagowar da zatayi sai sukayi ido huɗu dashi, zaune yake sai aikamata da wani ƙayataccin murmushi yake, wanda ke ƙarama fuskar sa kyau da annuri.
Akalar tafiyar ta ta juya zuwa wajan da yake, shiko sai famar kallon ta yake kamar yau ya saba ganin ta, kallon da yake mata ne bata so, shiyasa sai famar tura baki takeyi waje, shiko hakan da take ba ƙaramin kyau yake ganin tayi ba, haka dai taci gaba da tafiya har ta ƙarasa wajan da yake.
Kujera dake kusa dashi ya nuna mata yace ta zauna, kamar ba zata zauna ba sai kuma ta zauna, littafin dake hannta ya ƙarɓa ya fara dubawa har ya kammala kana ya ɗago kansa ya kalleta yace, "ba ko gaisuwa".
Murmushi tayi haɗi da buɗa baki tace, "ina wuni Yaya Sulaiman".....bata kai da rufe baki ba yace, "waye yayanki hala? mama kiriƙe gaisuwar ki bana so tunda sai da na ruƙa".
Murmushi tayi haɗi da faɗi, "kai mana".
Yace, "a'a nikam kije kinemu Yayanki ba dai niba".
Alamun kuka tayi tace, "tau shikenan bari natafi tunda kai ɗin ba yayana kaki ba".
Ido ya zuba mata yana kallonta, dan yadda take magana yana masifar burgeshi, lokaci ɗaya yaji wata gogowar sonta ta ƙara laulayi zuciyar sa.
Mayafinta ya riƙe yana faɗin, "sorry My kanwa, kallonta yayi yace haka yayi miki ko?".
Bakinta ta cinnu gaba alamun yayi mata.
har ya buɗa baki zaiyi magana sai ga Aunty Shemah ta ƙarso tana faɗin, "au nan kake tsayar min da ita kana hana ta shiga lecture ko?".
Kafin yayi magana tace, "Hafsat tashi muje, idan kana son ganinta kazo gida amma adaina tsayar min da ƙanwa makaranta".
Murmushi yayi haɗi da haɗi hannayi sa waje ɗaya yace, "tuba nake Aunty, insha Allah bazan koma ba, amma akowane lokaci zanzo gidan naku".
Tace, "naji tana" faɗar haka suka fara tafiya.
Har suka shiga mota suka tafi gida Aunty Shemah ba tace da Hafsat komai ba, bayan tayi wanka ta shirya ta fito parlour dan tayi ma Aunty magana idan akwai abinda tayi mata ya ɓata mata rai ta yafe mata, dan taga kamar fushi take da ita.
Tun bata ƙarasa parlour ba sai ga Affan ɗan Aunty Shemah ya zo da gudun sa yana faɗin, "oyoyo Aunty".
Hannayita ta ware shiko ya shige yana murnar ganinta.
Ɗaukar sa tayi suka ƙarasa falo, zaune suka sameta tana duba wasu books ɗinta, a hankali ta zo ta zauna kusa da ita, bayan ta zauna ta gaisheta, bayan ta amsa suka ɗan jama kaɗan amma ba wanda yace ma ɗan uwansa komai, Hafsat ce ta katse shuru da faɗin, "Aunty ".
Kanta ta ɗago ta kalle Hafsat tayi mata kallon ya dai.
Sai da ta sadda kanta ƙasa kana tace, "Aunty dan Allah in akwai abinda nayi miki kiya femin, naga kamar fushi kikeyi dani".
Sai da Aunty Shemah ta haɗi fuska kana tace, "abinda naga kinayi ɗazo shine bamin daɗi ba, ace tun yanzu har kin fara rashin shiga class, to bari kiji muddin kina son tamu tazo ɗaya sai kin aje komai ki kama karatu, bana son kiriƙa tsaye da wani makaranta da sunan wani zance, ban yadda da wanna ba koda ace Sulaiman ne ƙanena, kuma aganina karatu kika zo ba wata shiririta ba, dan haka nake haɗaki da Allah ki dana tsayi kina zance makaranta, in ma mutum yace yana sonki zaki iya bashi dama yazo nan ya sameki amma ni a makarnta bana so gaskiya, dan ko iyayenki ne baza su barki ba, kuma ni har ga Allah tunda na ganke jin kin shiga raina".
Sai da ta kai ƙarshe zanci Hafsat ta ɗago da kanta tace, "kiyi haƙuri Aunty, kuma insha Allah bazan koma ba, duk da sai dana fito class ne, amma bazan sake ba koda ma can ba ra'ayi na ba ne".
Nan dai suka cigaba da firar su shiko Affan sai gwalamniya yake musu kamar yana jin miso ke faɗa.
Bayan kwana uku da dawowar Anwar ya fara shiri-shirin zuwa india.
Tunani ya fara to idan yaje india wace makaranta Hafsat take, da yaga abin zai bashi walaha ya fara tunanin kiran Hajara dan yasan ita ce zata samu masa address ɗin duk inda take.
Kwance take tana tunani Anwar da koma yadda zai shigo hannuta lokaci ɗaya, sai ji tayi wayar ta na ƙara, wayar ta ɗauka ta duba screen ɗin wayar , sunan da tagani ne yasa tayi picking bata shirya ba.
A kunne ta kara wayar amma bata yi magana ba sai da ta tsaya fitar da numfashi a hankali, dan ita kanta tasan tana son Anwar so bana wasa ba.
Da yaji batayi magana ba yasa ya buɗe baki yace, Hajara kin