Header Ads
Showing 69001 words to 72000 words out of 204612 words

Chapter 24 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

3084

Ads at the middle of Article

Hameed Taura ya faɗa lokacin da yake fitowa daga toilet ɗin bedroom ɗin nasa da Anne ke zaune. Cikin sake ɓata fuska tace, “Da jikanka nake mana”.
“Oh-oh mi yayi ɗan bawan ALLAH ”.
“Kaface haka mana. Yanzu Mariya ta kirani wai a tura musu likita. Yaje ya farma ƴar mutane babu tausayi balle duban ƙarancin shekarunta. Bai kuma tsaya neman mai taimakonta ba ya tsallake ya fita sabgar gabansa shi a dole ga shugaban ƙasa”.
Murmushi mai faɗi Alhaji Hameed yayi yana kaiwa zaune kusa da matar tasa ƴar daru. Ya kamo hanunta cikin nasa idanunsa na yawo a fuskarta. “To amana afuwa dan ALLAH. Insha ALLAH bazamu sake ba”.
“Ko jikina kunne ne ba yarda zan bazaku sake ba. Amma ina gargaɗinku da ku kiyayeni”.
Tai maganar tana tashi da cire hanunta cikin nashi dan ta ɗakko ɗayar wayarta a ɗaki ta kira Doctor. Binta yay da kallo yana dariya ƙasa-ƙasa. Banda dai daru irin nata mutum da matarsa sai a hanashi yin yanda yaso. Shekarar Ramadhan nawa babu aure, kuma shi shaidane Ramadhan baya neman mata tun yana saurayi balle yanzun. Dole kuwa ya damƙi mace a samu matsala.
Bata daɗe da fitaba ta dawo tana sabuwar mitar ƙin samun Doctor Hauwa'u, dan haka ta sake kiran Aunty Mariya taji yaya.
Koda aunty Mariya ta ɗaga saita ce tama kwantar da hankalinta an samu doctor da tazo zata dubata. dan aunty Hannah ta kira wata ƙawarta dake nan kusa da fadar shugaban ƙasar.





Duk da aunty Hannah ta lura zazzaɓi ne kawai da damuwa ke damun Raudha babu wani taɓata da ango yayi saita zaɓi yi musu ƙarya da zaunar dasu akan hasashensu na cewar ai ta gasa Raudha a ruwan zafi, dama batayi bane da ƙyau shiyyasa. Shi kuma shugaban ƙasa yana sauri yaje office bai sake taimka mata ta shiga ba da safen nan.
Kalamanta sun sake baƙanta ran su Safina har Aina'u najan tsaki da hura hanci, zuciyarta kam kamar ta ɓallo ƙirji ta fito dan takaici. Aunty Hannah najin za'a kira doctor daga Taura house tai ruwa tai tsaki akan akwai ƙawarta anan kusa zata kirata basai an saka kowa wahala ba. Ilaiko haka akai, Doctor Farhat tazo ta duba Raudha, ta kuma bata magungunan zazzaɓi harda allura da ledar ruwa ɗaya. Sai suka haɗa baki koda su aunty Mariya suka shigo nuna musu sukai dai har ciwo shugaban ƙasa Ramadhan ya jima Raudha, amma basai anyi ɗinki ba zai warke.
Sosai mamaki ya kashe Raudha a kwance, dan kuwa tanajin lokacin da suke ƙulla zancen a toilet da suka shige, ita kuma ta bisu ta laɓe dan ca take allurar mutuwa zasu mata ma tunda yanzu aunty Hannah ba'abar yarda bace ba. Sai matuƙar kunya ta hanata iya buɗe ido ta kalli kowa a cikinsu duk da addu'oin da suke jera mata na samun lafiya da albarka. Ga wani takaicin aunty Hannah da mamakinta. To miye nayin ƙaryar dan ALLAH anan? Koda ma hakance ta faru sai an fallasata ma duniya da dangin miji.

Har suka bar gidan ran adda Asmah da su Safina a ɓace yake. Aina'u kam ai ba'a magana. Dama can batazo bikin ba jiya ta iso Bingo saboda bikin rantsar da shugaban ƙasa. Yau ko tazo ne danta gansa duk da akwai shakkar hakan tare da ita a dalilin wasan ɓuya da sukeyi ita da shi game da wani al'amari daya faru a america kusan shekara huɗu kenan. Lokacin yana farko-farkon shiga ruɗanin rasa Amnah da Haseenah.


Bayan wucewar su aunty Mariya, Aunty Hannah da aunty Halima suka buɗe akwatunan lefen suka gani. Har cikin rai sai da aunty Hannah taji hassada ta soketa, dan ko ita data ɗauka tsahon shekaru tana kutsetseniya cikin manyan mutane bata taɓa ɗaura wani zanin ba. Kayane masu tsada da ƙyau. Ita kanta gimbiya Su'adah da wannan takaicin masu kawo lefen suka barota. Aunty Halima dai daɗi taji ta kumayi addu'a, dan koba komai uwarsu ɗaya ubansu ɗaya da Asabe. Ballema ita mace ce mai zafi da sauƙi, tana da kirki kuma da son dangi. Gata ƴar gaskiya da gaskiya. Dan tun bayan auren Asabe itama ta fahimci aure shine mutuncin ƴa mace ba rayuwar da mahaifiyarsu ta ɗorasu a kaiba. Batai shawara da kowaba ta nutsu ta tuba, wanda ta tuba dominsa kuma sai ya kawo mata mijin aure cikin sauƙi bisa rahamarsa.
Duk yanda aunty Halima ta hana karsu ɗauki komai aunty Hannah bata saurareta ba. Kowa a gidansu sai da aka ɗaukar masa wani abu a lefen sannan suka wuce bayan sun damƙa Raudha hannun Tambaya wai ta kula da ita idan ta tashi a barci. Aunty halima dai ba haka taso ba, taso suyi haƙuri har Raudha ta farka suji ko tanada buƙatar wani abu, amma babu yanda ta iya tunda aunty Hannah na gaba da ita.


*_TAURA HOUSE_*


A Taura house kuwa sabuwar fitina su Adda Asmah suka sake kunna gimbiya Su'adah. Wani irin zogi takeji a ƙirjinta da jin mai rabata da Ramadhan sai ALLAH......
“Wlhy Ramadhan yaban mamaki, banyi zatoba daga garesa, bansan mi yarinyarnan ta mallaka ba da har ya ruɗesa da kusantar ta....”
A hasale Fulani dake shirye-shiryen komawa masarauta saboda kiran da mai-martaba ya mata tazo ta tare gidan surukai ta katse Adda Asmah mai maganar a hasale. “Aiko yayi na farko yayi na ƙarshe dan ubansa. Bandama namiji duk inda yake maye ne (ba ni na faɗaba fulani ce😱) har miye a jikin yarinyarnan na bibiya. Yayta wani ɗaga kai da izzar banza a waje ashe shashasha ne”.
Cikin taɓe baki Addah Asmah tace,
“Ammy shiyyasa tun jiya nace a fara bata maganin nan na hana ɗaukar ciki ai, shima muyi masa gargaɗin karya raɓu yarinyarnan dan nidai nasan yanda Ramadhan ya jima babu mace koda bai son yarinyarnan zaiyi ruwan kashe gobara da ita. Amma sai kukace babu abinda zaiyi da ita. A tunaninku yanda take ƙyaƙyƙyawa ɗin nan zai iya kauda kansa gareta tunda ma ba tabbacin baya sontane damu ba......”
Gimbiya Su'adah ta haɗiye wasu hawayen baƙin ciki dake neman zubo mata. Cikin kaushin murya da jin tsananin sakejin sabuwar tsanar Raudha ta katse yayar tata, “Aiko zaiyi aman abinda ya taɓo dan ubansa. Itako sai na maida rayuwarta abin tausayi a ƙasarnan itada karuwan dangin uwarta da faƙiran dangin ubanta. Shiko zaiyi nadamar haɗa shimfiɗa da ita da yay, zaizo ya sameni ai”.
Kuka Aina'u ta sake fashewa da shi dan duk suna zaune a falon ita da su Safina. Basma da Bilkisu ne kawai babu. Lubnah dake bima Safina kam tafi kowa ɗaukar zafi, dan halinta kaf irin na gimbiya Su'adah ne dama. Rashin son Raudha ya hanata zuwa fadar shugaban ƙasar tun jiya.
Cikin takaici Munirah dake bima Bilkisu ta harari Aina'u. “Wlhy aunty Aina kina bada mata. Miye abin kuka dan Yaya Ramadhan ya kwanta da waccan wawuyar yarinyar. Nifa kune kuke ganin laifinsa Maa. Karfa ku manta jinin karuwaice, wama ya sani ko itace taja ra'ayinsa ga hakan tunda iyayenta sun koya mata. Kuma koba komai ya mora sadakinsa da wahalar da aka sakashi yakeyi na yawon zuwa ƙauye da kisan kuɗi. Ni dama ya farka shegiya yanda bazata ɗinku ba mtsoww!!”.
Duk da kasancewar Muneera ƙaramar yarinya a cikinsu sai maganarta tai musu daɗi, dan daga Yusrah sai auta Basma a ɗakin Gimbiya Su'adah, a yanzu hakan shekarun Muneera gaba ɗaya bai wuce ashirin da ɗaya ba zuwa da biyu. Amma har take iya waɗannan zantukan.
Safina ta ɗanyi dariya, “ALLAH kumafa zancen Muneera haka yake, baima kamata muga laifin Brother ba. Dan haka kibarma fushi da shi Maah. Yarinyar zamu cima ƙaniya kawai. A kuma ɗorata akan maganin hana daukar cikin nan da lalata mahaifarta. Sannan tunda Muneera ta kammala karatunta ta koma can da zama ita da Lubnah, sune zasuci mana ubanta cikin sauƙi kuma suna kawo miki abinda duk ke faruwa a gidan.”
“Shawararki yayi dai-dai Safina”. Fulani ta faɗa cike da isa da ƙasaita. batare da ta basu damar cewa wani abuba ta cigaba da faɗin, “Harma da Aina'u. Tsakanin Bilkisu da Basma ma wata taje su haɗu su zauna”.
Adda Asmah tace, “Eh hakan yayi Ammy. Sai dai kinsan Halin Ramadhan zai iya cewa sunyi yawa. Kodai su Bilkisun su zauna su”.
“Aiba lokaci ɗaya zasu tafi ba, da daɗɗaya kodan waɗan can tsoffin suma da basa iya gani su ƙyale. Amma zuwa Basma ko Bilkisu nada nasa amfanin. Su nuna suna sonta suke, zatafi sakin jiki da su har su san komai nata. Su kuma su Lubnah ta hanyarsu zasu dinga sanin wasu abubuwan ai ko”.
Cikin gamsuwa suke jinjinama Fulani kawunansu. Banda gimbiya Su'adah da har yanzu zuciyarta ke a matuƙar ƙuntace. Dan ko magana bata iya sakeyi ba.


____________________


A can bangaren su Aunty Hannah ma suna zuwa rabon ganima aka fara, sai dai banda Asabe da tausayin ɗiyarta ya rufeta game da labarin da aunty Halima ta bata dan itama batasan ba gaskiya bane tunda aunty Hannah bata sanar mata ba. Taji inama Raudha nada waya yau data kira taji ko muryartane taji sanyi. Dan rabonta da ita tun randa aka ɗakkota da ga Hutawa. Ita nan gida tayo dama ita da hajiyar birni. Su aunty Halima ne kawai suka je kai amarya.........✍






*_Hummm🚶🏻_*




________________________




Duk wacce batayi anfani da sabulunnan ba anbarta abaya acan karshen bayama kuwa duk Mai tantama akan sabulai nagyaranjiki cewa basa Aiki toh yacire mg's domin kankat ne insha Allah babu Wanda yayi anfani dasabulunmu yace baiyi ba koyaushe mg's sai sanbarka amare da uwargidaye hardama yanmata kuhanzarta kusamu naku ba karya domin bama cika Baki kugwada kubada labari da bakunanku sabulu daya tamkar dubu wadandama basasan using cream sabulun mg's herbal whitening black soap yawadacemuku jikinku zaiyi kyau koyaushe kukasance clean cikin kamshi Kuna glowing koda bakusa turare ba🤗


Kayanmu bana bleaching bn organic ne sunagyarajiki fiye da tsammaninku zaifiddomuku da ainihin natural beauty dinkine Wanda yagwada shi zaitabbar amare kuyi kokari kumallaki mg's domin baruwanku da zuwa adirjemuku jiki zakuga yanda fatarku zata dinga walwali
Ina masu pimples
Tabo(spot)
Sunburn dama dukwani matsalar fata kuyi kokari kunemi soap dinnan before 2weeks zaisharemuku hawaye kuzama abun kwatance
Sister's masu nankarwa kuma kunemi soap dinnan Yana rage nankarwa sosai🧖🏻‍♀️duk me shakku tayi kokari tagwada mg's insha Allah bazakiso rabuwa dashi ba


Akwai maisa haske Amma kayanmu nafada bana bleaching bn zaifiddomiki d ainihin halittarkine yagoge dukkan dattin jiki


Akwai Kuma Wanda zaimiki maintaining skin dinki yasaki fresh fatanki tazama kalar hutu


Pls bamacika Baki you HV to try it and see for yourself
100%tested nd trusted


Soap price:3k
Location:kaduna buh munaturawa ko Ina Amma delivery is not free


Maiso kindly message 08062991549
07046881166
Call 08064532391


Note:Babu inda zakusami mg's herbal whitening black soap sai a number dinnan bairiga yakai market b inyakai we will let you know buh as for now wnn numbern ne kawai🙏


Maiso yahanzarta before yaji sold out akwaisu available now insunkare you HV to wait akawo so maiso yahanzarta🙏adade anayi sai gsky🤭🤝


Mg's skincare


_________________________




*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*




*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_


*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_


*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_


*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_


*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_






Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k




*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_09032345899_*




*KATIN MTN*👇👇


09166221261
__________________


*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*






Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F




*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼


+227 95 16 61 77






*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*


_____________________




*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*




Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.




*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3




Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*




*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*


+234 903 177 4742




_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*














*_Episode 27_*




*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKK👇🏻_*


https://arewabooks.com/chapter?id=62aa07dd3992cc4a44aaa7a4


________________________




Assalamualaikum lovely brothers and sisters. Please support our YouTube channel *sudais kura* for Allah sake our channel is all about Qur'an recitation and other Islamic studies 🙏🏼 I am not perfect, but I'm a mother who love to see kids Recite Qur'an. I'm trying my best with the little I know to install the love of the holy Qur'an into sudais heart at this young age. Please support our journey by subscribing to *Sudais kura* YouTube channel 🙏we are planning to start some simple craft and art work too on the same channel insha Allah. Just subscribe and you will not regret❤️ the channel link 👇🏻
https://youtu.be/g6BGEBv-X8Y


________________________




...........*_GOVERNMENT HOUSE_*


Barci sosai tayi har taji babu daɗi. A kowanne motainta Tambaya kan leƙa ta tabbatar tana lafiya. Bata farkaba sai bayan la'asar. Taji daɗin jikinta sosai dan magunguna masu kyau Dr Farhat ta bata. Wanka ta farayi mama tambaya ta gyara mata ɗakin tunda dama aikinta ne. Bata tambayeta wacece ita ba tunda tasan a irin wannan gidan dama dole a samu ma'aikata. Bayan ta gasa jikinta da ƙyau ya sake warwarewa tayo alwala ta fito. Ɗakin ya sake komawa tsaf sai ƙamshi yake. Batabi takan komai ba ta gabatar da sallolin dake a kanta sannan ta miƙe ta buɗe akwatinan da aka zube matan. Cikin sa'a ta samu ɗinkakkun kaya kala kusan biyar da sai daga baya aka amso a wajen tela dan bai kammala mata na fitar biki ba da a aka kai wancan ranar. Riga ne da skirt na atanfa less Onion color. Sai ratsin milk kaɗan a jiki da stones da aka kawata ɗinkin da shi. Kayan sun mata ƙyau da fiddo kalar fatarta musamman data ɗan rame kwana biyun nan.
Duk wanda ya ganta yaga amarya kodan gyaran jikin da tasha na nagartattun kayan *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* da duk amaryar da akaima gyara da su dole tazama abar kallo. (Amare dama mata ƴan ƙwalisa dake buƙatar kayan gyaran jiki na musamman, tun daga kan ƙamshi na turarurrukan gida dana jiki, har zuwa gyaran fata da kayan mata ingantattu ku garzayo ga *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* domin samun naku kuma. Masu iya magana kance siyen nagari maida kuɗi gida😘😋🤗), ga lallin ƙafarta da hanunta raɗam tamkar bazai fita ba. Mama tambaya ce tazo ta sanar mata an shirya mata sabon abinci tunda breakfast ya huce, anma fiddashi tuni. Ta amsa cikin mutuntawa ga mama Tambaya dan koba komai zata iyama jika da ita.
Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake, amma tanajin yunwa. Dan haka tai dauriyar fitowa falon saman inda mama tambaya ta saka kuku ya shirya abincin. Sosai mamaki ya cikata ganin table ɗin a cike, dan babu wani zancen ƙauyencin gidan ko tsarin abubuwansu tattare da ita kasancewar an mata lectures na koma kafin ta shigo. hasalima ta shigo ɗin tun kafin a kawota matsayin matar gidan. “Mama wannan abinci duk suwaye zasu cisa haka?”.
Kan mama Tambaya dake tsaye a ƙasa tai murmushi. “Ranki ya daɗe ke da shugaban ƙasa ne kawai, duk da bamu da tabbacin shigiwarsa gida a yanzun”.
Mamaki da takaici ya kume Raudha a rai. dan kai tsaye ta danganta hakan da almazarancine kawai. Talakawa nawane suke wahala babu ko ruwan kunu da zasu sha a yau, amma an shirya abinci fin kala huɗu a dining ɗin gidan shugaban ƙasa wai dan shi kawai da matarsa. Tabbas ta sake yarda mulki BAƘAR INUWA ne kawai. Dan hakkin mutane kawai aka barka da shi ka shiga uku. Ta rumtse idanu da haɗiye ɓacin ranta, cikin saisaita murya tace, “Mama yayi yawa ai, ya kamata a dinga dafa iya wanda za'a iya ci kawai ya wadatar. Dan ALLAH daga yanzu a dingayin dai-dai misali. Idan kuma ansan ma shugaban ƙasa bazai dawo yaci ba adaina girkawa da shi har sai idan shine ya bukaci hakan”.
“Amma ranki ya daɗe haka tsarin yake tun a wancan shugaban kasar mai sauka dana sani nidai.”
“To mama inaso a canja yanzu danni dai bana buƙata sam”.
“Insha ALLAHU za'a gyara ranki ya daɗe, dan dama dai tun ɗazun duk ma'aikatan gidan nan suka gama taruwa domin gabatar da kansu gareki”.
Duk da gaban Raudha sai da ya tsinke

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads