Header Ads
Showing 177001 words to 180000 words out of 204612 words

Chapter 60 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

3101

Ads at the middle of Article

★Gaba ɗaya Raudha jitake kamar ta nutse dan kunya. Kanta a kasa ta risina ta gaida Anne da Bappi. Zata zauna kusa da Bilkisu dake tare da su yaja mata kujerar kusa da shi tare da kamo hanunta yanda su Bappi bazasu gani ba. Sai dai ya makaro sun gani ɗin. A kuma kallo ɗaya Anne ta fahimci wayo yaje yayma Raudha, sai dai addu'arta ALLAH yasa bai aikata abinda zai cutar da itaba tunda ɗinkin jikinta bai gama warkewaba. Tunda tazo ɗaki taga babu su tai niyyar kiransa a waya Bappi ya hanata. Acewarsa yasan Ramadhan na cikin hankalinsa bazai sake yarda ya aikata abinda zai cutar da Raudha ba. Gara su barsu su sasanta kansu da wuri kodan su Gimbiya Su'adah ma.
Bilkisu ce ta zuba musu abincin, dan Raudha dai ta kasa motsin kirki. Gani take kamar su Anne sun fahimci abinda duk ya faru tunda har abu yakai ga canja kaya. Kowa nacin abincinsa hankali kwance amma banda ita. Tsakura kawai take kaɗan-kaɗan.
“ALLAH in bakici abincin nan ba zan tonaki yanzu su Anne susan mikika aikato a ciki da hujja”.
Wani irin ƙululu cikinta ya bada. Harta kasa daurewa saida ta ɗan dubesa. Gira ɗaya ya ɗage mata da sakin wani munafukin murmushi daya tilastata maida kanta ƙasa da hanzari. Duk abinda suke su Anne na lure da su, sai dai kowa ya ɗauke kansa kamar bai san anaiba.
Farfesun kan rago Ramadhan yace Bilkisu ta zuba masa. Kamar jira tana buɗe bowl ɗin Raudha tai saurin toshe hanci da rike numfashinta. Babu wanda ya lura da hakan Bilkisu ta fara zubawa, kasancewar kusa da shi take tuni ƙamshin ya ƙara karfi a kusa da ita. Har takai amai na yunƙuro mata. Ta mike zaram zata bar wajen ya rikota.
“Lafiya kuwa?”.
Kanta ta shiga girgiza masa da nuna masa ya saketa amma yaƙi. Anne ce ta fahimci abinda ya ɗaga hankalin Raudhan da sauri tace, “Ramadhan saketa”. Tai maganar tana mikewa.
Sam ya kasa fahimta, a zatonsa wani abune daban, ina kafin ya samu damar cewa wani abu ta kasa daurewa ta fisgi hanunta da ƙarfi. Sai dai kafin takai toilet na bayin ta saki aman a waje. Gaba ɗayansu sukayi kanta har Bappi, dama Ramadhan tunda ta fisge ya bita. Amai sosai takeyi a wahale. Shiko gaba ɗaya ya cimimiyota jikinsa duk a ruɗe. Sai tambayarta yake mike damunta?.
“Ramadhan ka barta taji da abinda ya dameta mana Please”.
Anne ta faɗa cike da tausayin Raudha. Sai da ya tabbatar ta gama ya ɗagata cak ya nufi sashensa da ita. Anne zata bisu Bappi ya riƙo hanunta yana girgiza mata kai da murmushi a fuskarsa. “Barshi shi daya jawo yay aikin”.
Murmushi kawai tai da girgiza kai tana mintsininsa da nuna masa Bilkiau da ido. Yay karamar dariya da ita kawai tajisa. Mai aikin Anne ce tazo ta gyara wajen. Su kuma suka koma kan table suna karasa cin abincinsu kowa da tausayin Raudha a ransa


Bayan kamar mintuna goma sha biyar Ramadhan ya fito, a lokacin sun bar dining sun koma falo.
“Yaya jikin nata?”.
Bappi ya tambaya cike da kulawa. Cikin damuwa Ramadhan daya koma duk wani kalar tausayi yace, “Bappi na barota kwance zan sama mata wani abincin a kuma kira Momyn Jabeer”.
“No kiran Mommyn Jabeer ba shine mafitaba ai. Da alama kamshin naman kan canne bataso. Taci abinci saita kwanta ta huta ALLAH ya raba lafiya”.
Wani irin yarrr yaji har saman kansa. Cikin rawar harshe yace, “Anne ban gane ba?”.
Hannu Bappi ya mika masa da faɗin, “Ajiye goro na ganar da kai”.
Ganin Bappi a serious sosai Ramadhan yay ƴar dariya yana shafa aljihu. Sai dai babu komai a ciki, hatta wayoyinsa na ɗaki. “Bappi na maka alƙawarin baka koma mi kakeso faɗi dan ALLAH”.
“Tabb ai an daina aikin banza a NAYA kai dai ajiye kasha labaru”.
Rasa mima zaiyi yay, sai kawai ya kwanto agogon hanunsa ya ɗora a hanun Bappin. Bappi ya ɗan juya agogon, sai kuma ya taɓe baki. “Ba laifi mai nauyine ai. Bilkisu bashi yasha”.
Bilkisu dake dariya cike da ɗoki ta nufi Yayan nata tayi ɗan hugging nashi, sai kuma ta sakeshi. “Yaya na kusa zama Mummyne fa, Aunty nada cikin wata biyu da kwanaki....”
“What?!!!”.
Ai kafinma ta ƙarasa bayani ya juya da sauri ya bar wajen zuwa sashensa. “Na yafe miki sauran labarin”. Ya faɗa yana ɗago hannu sanda yake gab da shiga.
Mi su Anne zasuyi inba dariya ba. Pa dake tsaye tun ɗazu batare da sun sani ba yay murmushi kawai yana girgiza kansa. Ɗansa kenan abin alfaharinsa. Murɗaɗɗen mai wahalar fahimta ga wanda ke nesa da shi. Da yawan mutane akace musu Ramadhan mai sauƙin kaine a cikin gida zasu karyata. Domin shi mutumne mai yanyin mutanen da ake kira da girman kai kai tsaye. Dan kuwa tabbas magana ma sai yaso da wanda yay niyya yakeyinta. Dariya ko mutane da yawa kance basu taɓa gani daga garesa ba. Dan akan jima baiyi hakan ba sai a inda yaso. Sai dai ga wanda yaso kuma ya aminta shi mai sauƙin kaine da iya mu'amula matuƙa.


Cikin ɗan barcin daya fara figarta kawai taji an rungumeta. Tare da fara bata zafafan kiss's tako ina da ina a jikinta.
“Ya Ramadhan lafiya?”.
Raudha ta faɗa a kasalance dan da gaske barci ya fara ɗaukarta. Bai bata amsa ba. Sai rungumeta da yay tsam a jikinsa yana jero addu'ar nan ga wanda abin farin ciki ya sama.
*الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .*
*_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._*
_Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._
*اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.*
*_Alhamdulillahi ala kulli halin_*
_Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._
Rigar dake jikinta ya ɗaga nanma yana sumbatar cikinta. Kafin ya kwantar da kansa akai wasu hawaye na tuna Haseenah na sakko masa. Ashe bayan Haseenah yana da rabon sake haihuwar ƙanen a duniya. Ɗagowa yay ya sake sumbatar cikin, sai kuma ya fara karanto addu'ar nemawa ƴaƴa tsari (iyaye dan ALLAH a dingayi, kai ko yaron cikine dake karanta ki shafe cikinki kafin ya fito ki ɗora dayi masa a zahiri😘😢. Domin kuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar: ).
*أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.*
*_O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah._*
_Ina neman muku tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa_.
Raudha dake murmushi takai hannu ta shafa kansa. “Irin wannan security ba ɗaga ƙafa haka?”.
Tasowa yay gareta shima fuskar tasa da murmushi, ya kwanta kusa da ita tare da tokare kansa da hanunsa ya lakace mata hanci. “Uhmm barni gara na tofe abina tun yanzu kodan masu ƙarancin tsoron ALLAH. Yanzu nan Baby Luv kinsan da wannan abin farin cikin tun ɗazu kikaƙi sanarmin? Anya kuwa kina sona?”.
Dariya tayi tana mai saka tafukan hanunta ta rufe fuska. “Kai Ya Ramadhan kawai kuma saina kama faɗama inada cikin ɗan fari dan banda kunya”.
“Lallaima yarinyar nan”.
Ya faɗa shima yana dariya da son zame hanunta. Ƙin yarda tayi, sai ma juyowa datai da sauri ta sinne kanta a ƙirjinsa. Idanu ya lumshe a hankali tare da rungumota ya kanƙame ta shima. ji yake kamar ya haɗiyeta kawai ya huta. “I love you sweetheart”.
“I love you too Noorullah”.
“Nice name dear I love more. Na huta an daina kaƙabamin Yaya babu dangin gabas babu na yamma. Dolene yau nayi celebrations biyu kenan”.
Siririyar dariya ta saki tana mai ɗagowa ta sumbaci lips nasa ta sake maida kanta ta kudindine a jikinsa.
“Hummm wlhy yarinya ki bani kwana uku kacal saina maidaki mara kunya ta bugawa a jaridar duniya”. Yay maganar yana mai rungumeta sosai a jikinsa murmushi yaki barin fuskarsa.
Babu wanda ya karajin ɗuriyar Ramadhan da Raudha a gidan, kuma babu wanda ya nemesu. Garama ya kira Bilkisu daga baya ta kawoma Raudha sabon abinci taci ya busar mata da gashinta daga nan sukai kwanciyarsu............✍






*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*






*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*




*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_


*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_


*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_


*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_


*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_






Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k




*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_09032345899_*




*KATIN MTN*👇👇


09166221261
__________________


*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*






Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F




*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼


+227 95 16 61 77






*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*


_____________________




*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*




Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.




*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3




Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*




*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*


+234 903 177 4742




_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*














*_Episode 67-68_*




...........*_WASHE GARI_*


Washe gari babu kunya Gimbiya Su'adah tazo har sashen su Anne ta tuntuɓesu batun auren Aynah da Ramadhan. Dan Pa yaƙi bata haɗin kai kwata-kwata. Ramadhan ko taki cemasa komai duk da tasan yana cikin gidan. Hasalima har zuwa yay ya gaisheta. Yanda bata ɗaga masa maganar abinda ya faru ba a jiya shima baice komai ba. Yau ma bayan ya dawo sallar asuba yaje ya gaishetan. Nanma bataceba shima kumai bai ceba.
Koda Bappi ya gama saurarenta cewa yay taje zataji komi da suka yanke shi da su mai-martaba. Ranta ya ɓaci, amma ta danne ta tafi. Duk yanda sukai da Bappin ta kira Adda Asmah ta sanar mata. Itako daga can gurgun tunaninta bata yay aikin boka ya tabbata kenan. dan dama yace zai rufe bakin kowa ai. Shi kansa Ramadhan bai isa yin ko tari ba akan batun.


Hhh ALLAH sarki Addah Asmah. Batasan a yanzu matar Ramadhan da kakaninsa tsaye suke kansa ba. Dan a yau yini Raudha tai aikin karanta addu'oin warware sihiri dana kariyar ALLAH ita da Ramadhan suna tofawa a ruwa kamar yanda musulinci ya koyar damu. Suka kuma ajiye matsayin ruwan shansu. Yini guda suna a sashensu. Hatta abinci nan ake kawo musu. Yayinda Anne ta zaunar da shi ta sanar masa dokar Doctor akan Raudha na bedrest. Ya tabbatar mata babu damuwa zaiyi ƙoƙarinsa na kare hakan. Taji daɗi sosai tai masa nasiha ita da Bappi tare da addu'ar ALLAH ya kiyaye gaba.


Washe gari gida ya cika da baƙi taf tako ina. Bakajin komai sai hayaniya. Sai dai duk wannan hayaniya da gidan ya dauka babu mai ganin shugaban ƙasa da first lady. Dan suna can sashensu suna baje kolin shafukan soyayya kamar su kaɗaine a duniyar. Basu da aiki sai zaman garden ɗinsa dake matuƙar ɗaukar hankalin Raudha takeji kamar a wata sabuwar duniyar take. Abu mafi ɗaukar hankalinta tsuntsaye da ake kiwo a wajen da ruwan da aka kawata mai bulɓulowa cikin dutse kai kace ba tsarawa akai ba. Sau ɗaya ya barta ta shiga sukai wanka a pool ɗin wai bayaso Unborn ɗinsa ya ɗauka mura tun yanzun. Ita dai dariyama yake bata. Dan baida aiki saita idan ta haihu babynsa kaza kaza. Kokuma ya kwanta a cinyarta yayta hira da cikin da ko a jikinta bai nuna akwaishiba dan cikin a shafe yake kamar babu hanji balle ɗa.
A ɓangaren su Adda Asmah hankalinsu a tashe yake babu ango babu dalilinsa. Gashi har an fara event yau a cikin ukun kawai da mai-martaba ya basu izininyi tun a waccan ranar. Koda Fulani ta iso tasa a kira mata Ramadhan anƙi ganinsa. Gashi Bappi ya sashi kashe wayoyinsa duka sai mai muhimmanci kawai. Yo banda abin Fulani ma ganin shugaban ƙasa guda wasane kamar wani ganin Bilyn Abdull haka😏.
Aiko ta shaƙa. Tazo har sashen Anne amma ƙofar sashensa a rufe. Hakan yasata tunanin koma dai raina musu hankali ake baya gidan aka ajiye waɗanan zaratan securitys ɗin zagaye da anguwa kamar masu gadin wuta. to komadai miye Shugaban kasa Ramadhan ya zama gwal ma ya fisa arhar gani a garesu.
Dan ko kunshi da yace bilkisu ta kawo mai yiwa matarsa a sashen akai mata cikin garden, yayinda shi yake acan falon hutawarsa zaune shi da Ibrahim da A.J da sukazo biki suna shan hirarsu, dan Gimbiya Su'adah ta gama turama abokansa invitation kaf ta waya akan zaiyi amarya. Koda suka zo kuma baice da kowa komai ba akan hakan.


Koda aka kammala ƙunshin ya gani yayta santi. Kaɗan-kaɗan ya kamo ya sumbata. Harda labarta mata yanda ya dinga satar kallon kafafunta da hannayenta lokacin da akai mata na bikinsu. Aiko mi zatai inba dariya ba har saida ya ƙulu. Tako shiga masa gwalo da kiransa gulmamme.
Gyaran kai kam shi ya wanke mata da kansa ya gyara mata shi tsaf har taita mamaki. Yako tabbatar mata tsabar son da yakema gashine kawai ya sashi koya a wajen Anne. Harda cewa wataran zai mata kitso da sai tasha mamaki.



*_RANA BATA ƘARYA......_*


Lallai wannan zance haka yake. Dan kuwa a yau juma'a bayan sakkowa masallaci aka ɗaura aurarrakin yaran Taura Family har su biyar. Sai dai wanda suka kasa kunne suji da Ramadhan a ciki sukaji tsit. Sai da aka kammala a karshe aka ɗaura na Ayna'u Musaddiq da angonta Aminullahi Ashiru. Ɗa ga tsohon gwamnan jihar TANDAZA, ya jima yana sonta tana masa ikkanci, dan har kuɗi sun taɓa kawowa ta bijire. Da yake uban baida fus a gidan haka ya hakura duk da kuwa bokine garesa Alhaji Laminu Tandaza. Sai dai kuma masu iya magana sunce matar mutum kabarinsa. Gashi kuwa UBANGIJI ya tabbatar da hakan.


Gagarumar ƙurace ta tashi a gidan Adda Asmah jin sunan ango a bakin ƴan ɗaurin aure da ba haka suka saniba tun farko. A cikin kanƙanin lokaci ta hargitsa kowa. Zata taho Taura House ayi wacce za'ai ita da gimbiya Su'adah da take tunanin ta munafinceta Abban Aynah ya tabbatar mata ko gate ta tsallaka a bakin aurenta. Wannan tashin hankali ya saka Fulani hana Adda Asmah fita. Dan kowa yanda yaga Alhaji Musaddiq yau babu makawa zai tabbatar da abinda ya faɗa ɗin.
Amarya Aynah kuwa suma tayi a take sai da aka nemi likitan ceto ranta.


A Taura house kam babu wanda yasan mi ake ciki. Dan kuwa koda anguna suka shigo gaisuwa babu wanda yaji wani sabon abu da babu shugaban ƙasa Ramadhan da ganinsa dama bai zama lallai a idon kowanba. Dan yanda ya fita tare da Bappi da mai-martaba wajen daurin aure haka suka dawo a mota ɗaya. Yana shigowa kuma ta ƙofar baya yabi zuwa sashensa dan ya tabbatarma Raudha kartaje ko'ina ana ɗaura aure gida zai dawo.
Duk da dai taji gargaɗinsa. Anne tazo da kanta ta tafi da ita ta gaisa da wasu aminanta na amana dan ba wani ganin Raudhan sukai sosai ba lokacin nasu auren. Komai cikin dauriya Raudha keyinsa. Amma jikinta a matukar sanyaye yake tunda tasan yau mijinta zai zama nasune su biyu. A kwanakin nan duka kullum sai ta buya tasha kukanta. Kuma tsaf Ramadhan na lure da ita batare data sani ba. Sai dai bai taɓa nuna mataba ya barta da lokaci kawai. Zai daibi duk hanyar data

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads