Showing 180001 words to 183000 words out of 204612 words
Chapter 61 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt
dace ya mantar da ita idan suna tare kafin ta sake samun dama.
Kasa ɗagowa tai ta kallesa lokacin daya shigo tana zaune ita da Basma da Rumaisa da Fadila a falo. Yayi kyau matuka cikin ɗanyar shadda data wadatu da jiƙaƙen ɗinki. Sai maiƙo da ɗaukar ido take gamai kallo. Gashi sosai babbar riga ke kawata adonsa da maidashi wani babban mutum. Sannu da zuwa su Basma sukai masa suna mikewa. Dama Anne ce tace suzo su ɗebe mata kewa kafin ya dawo tunda tasan babu mai shiga sashen nan da sunan yazo biki.
Bayan ficewarsu ya tako a hankali zuwa gabanta yakai dukunne. Hannayenta ya kamo cikin nasa tare da saka ɗayan ya ɗago habarta. Itama tayi ƙyau matuƙa cikin wani lass mai azabar kyau da nauyin kuɗi. Ga ɗinkin ya zauna mata ɗas a jiki saboda kibar da tayi da ƙara haske da fresh. Taci kayan ado na ɗan kunne da sarka da zabba da awarwaraye ga ɗauri daya amsa sunansa ɗauri kai kace itace amaryar.
Kukan da taketa riƙewa tun ɗazun ta sakar masa. Lumshe idanunsa yayi tare da mikewa ya ɗagata cak ya rungume a jikinsa yana murmushi.
“Haba ƴar aljanna. Kwantar min da hankalinki Ramadhan B. Hameed Taura na Ameenatu Dawood Hutawa ne ita jaɗai insha ALLAH. Badan bazan iya karawaba wataran idan kaddarar hakan ta shigo, sai dai ina fatan rayuwa dake ke ɗaya dan tun asali zama da mace ɗaya ne tsarin Ramadhan. Sai dai tsarin ALLAH yana gaba da nawa Ameenatu. Amma a yanzu nakine ke ɗaya babu wadda aka ɗaurama Ramadhan aure da ita”.
Ƙanƙamesa tai da sake fashewa da kukan da batasan na farin ciki bane kokuwa na minene. “I love you Noorullah”. Ta faɗa da ɗagowa lokaci ɗaya ta manne lips nata da nashi.
Tab humm, batasan kuka ta kawo gidan mutuwa ba. Dan kuwa bawan ALLAH caraf ya cafke tare da ɗaukarta cak sukai bedroom. Yako shiga yamutsata son ransa. Yama manta da wata kwalliyar biki. Sai da labarin ya canja salo kuma ta ruɗe. Sai dai batasan dama haƙuri yake yana ɗaga kafa ba dan dole. Aiko tilas ta bari ya rage zafi yanda ya kamata. Da ga karshe dole aka sake nemo su Basma suka kawo mai sake kwalliyar biki.
Uhhm andai ji kunya😣😮🚶🏻.
★Bayan sallar la'asar sai ga Aunty Hannah mata ga vice president da tawagarta sun iso gidan bikin. A ciki kuwa harda Asabe da Hajiyar Birni dasu Fatisa. Wayyo dadi kamar zai halaka Raudha. Ta rasa inda zata saka kanta taji daɗi. Ga Anne ta saka an musu kyaƙyƙyawan karamci da tarba ta musamman ta abinci. Su aunty Hannah anata faman ɗaga kai da hura hanci ana yatsine-yatsine kai kace itace ma firt lady ɗin tsabar yanda guards ke dogare a bayanta da mata ƴan siyasa.
Ina Raudha bata ita takeba. Farin cikin ganin Mummynta ya rufe mata ido ruff. Ko Hajiyar Birni da Hajiya mama sai da sukai mata tsogumi ta gaishesu. Anan suka kasance har bayan magrib. Da zasu wuce Anne ta haɗa musu shatara ta arziki musamman su Fatisa da sukaji kamar karsu rabu da ƴar uwarsu. Dan suma dai yanzu Alhmdllhi har sun kawo mazan aure ana shirin zuwa hutawa gaida Alhaji baba Dauda mai zamani surukin Mr president na ƙasar NAYA. Yaso zuwa daurin aure Inna ta tashi da amai da gudawa aka kwasheta asibiti a rikice tana can ana kara mata ruwa dole ya hakura. amma yasha takaici wai kallo ya wucesa daga shi har M. Gambo amininsa da shima ya gama saye zuciyar asabe batare data san shiɗin bane har yanzun. Dan yace bazai bayyana mata kansa ba sai ta yarda ya turo iyayensa. Itako tace su ba yaraba bata yarda da wannan ganganciba yazo gareta kawai su sasanta. To yanzu dai yace zaizo ɗin amma bai tsaida rana ba.
Bayan wucewar tasu ma zazzaɓi ne ya rufe Raudha. Koda aketa shirin tafiya dinner ita tana can duƙunkune a bargo. Dama kuma bata saka ran zuwan ba tunda tasan Ramadhan dai bazaije ba. Kuma babu tabbas zai barta taje itama.
★Kafin a tafi dinner gimbiya Su'adah ta cigaba da neman number Fulani da Addah Asmah kamar yanda taketa fama tun bayan dawowar ƴan ɗaurin aure hakan baiyu ba. Dan duk kashe wayoyinsu sukai. Taso su Safina su leƙa gidan suyi ALLAH ya sanya alkairi hakan bata yuwuba dan Taura house yayi matukar cika kasancewar duka matan gidan uku sun aurar da yara.
Ta turama Ramadhan gargaɗi sosai akan ya tabbatar yaje dinner ɗin nan amma sai dai baima gani ba dan yau yayi busy da yawa. Babu wanda yasan ainahin abinda ya faru sai fa da aka isa wajen dinner sai su Bilkisu Amare kawai da angunansu amma babu Aynah babu Ramadhan babu duk wani wanda ya shafi masarautar Bina dake a gidan Addah Asmah dan dama biyu aka rabu. Wasu sukayo nan Taura House wasu can gidan a cewarsu duk za'a haɗe wajen dinner da walima dakai amare.
A sannan gimbiya Su'adah takejin mummunan labarin cewa ai kiɗa ya canja bada Ramadhan aka ɗaura aure ba. Ta matuƙar gigicewa a haukace ta shiga neman number Ramadhan amma har sannan switch up. Ta nufi sashen Pa ta iskesa da baƙinsa da basu wuce ba. Tsabar yasan miya kawota kuma yay kememe yaki tasowa. Haka ta wayance ta fito. Maida akalar kiranta tai ga Mai-martaba, shikam ta samesa. Sai dai yaja mata gargaɗi akan idan har tace wani abu yana cikin Taura house sai ya mata hukunci mai muni, tabar koma minene za'a tattauna bayan biki.
Wannan al'amari ya matuƙar sake rikita gimbiya Su'adah, dan kuwa a daren nan jininta ba karamin hawa yayiba har sai da Safina ta taimaka mata da maganin barci.
★Wajen dinner kam bidirinsu suka sha kamar babu gobe. Dan gaba ɗaya anan aka haɗe amare da angwayen. An raƙashe an kwalle anci ansha sai dai Bily taji inama Raudha na wajen. Amma dai su Basma sun ɗauka komai a waya duk da anyi vedio recording. Su Ibrahim ne suka halarci wajen bisa wakilcin babban yayan amare shugaban ƙasa Ramadhan tare da cos. Hakama manyan mutane matan gwamnoni da ministers da ƴaƴansu duk sun halarta. Dan hatta da yaran su Alhaji yaro glass na nan anyi komai da su kamar babu wata a ƙasa. Karfe ɗaya aka tashi amare da tawagar jama'a yan biki sukayo gida. Masu gidaje a cikin Bingo suka nufi nasu muhalli anama angwaye da amare fatan alkairi da zaman lafiya da zuri'a masu albarka.........✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Episode 69-70_*
............Washe gari Raudha ta tashi batajin daɗi sosai. Dan har saida Dr Hauwa ta shigo ta dubata har dasu karin ruwa. Sai hankalin Ramadhan ya rabu biyu ga meeting da za'a zauna duk da dai babu Raudha a ciki. Ga jikinta kuma.
Itako Gimbiya Su'adah tana can sun fice a sace ita da Safina zuwa gidan Addah Asmah, dan tana son tasan mike faruwa kafin a zauna zaman meeting duk da tasan har dasu Adda Asmah ɗin za'ayi. Lokacin da motar su gimbiya Su'adah ke shiga layin su Adda Asmah a lokacine driver daya ɗakko fulani zai kai Taura House shi kuma ke fita. Dan Addah Asmah tace fulanin tayi gaba suma zasu ƙaraso ita da mijinta da Aynah da kuma mijin Ayana ɗin da suke so ya saketa take a yau.
Saboda yanayin hayaniyar mutane yasa Safina bata tsaya da motar ko'ina ba sai ƙofar falon baya data san su Adda Asmah nada ita. Dan kafin tai aure idan tana son haɗuwa da Faisal mijinta tasha satar fita ta wajen taje ta dawo wani bai sani ba. Ta wajen babu kowa, sai daga ɗan bayansu ta backyard suke jiyo ƙananun hayaniyar masu wanke-wanke. Ginbiya Su'adah takai hannu zata buɗe ƙofar wani furici mai kama da saukar aradu yay azamar taka mata birki, tai kuma saurin damƙe hanun Safina dake shirin yin magana tana girgiza mata kai....
Su gimbiya Su'adah sun iso gidanne a dai-dai lokacin da Adda Asmah da Aynah ke tare a wannan falo, waya Adda Asmah keyi da bokanta akan abinda zasuyi idan anje wajen taro. Shine furucin ƙarshe data maimaita kamar yanda bokan ya faɗa ya shiga kunnen gimbiya Su'adah. Kasancewar sun gama wayar Adda Asmah ta ajiye a sanyaye tana duban Aynah data kafa mata ido.
“Mom wai yanaga jikinki kamar yayi sanyi?”.
“Tabbas dole jikina yay sanyi Aina'u. Sai dai zan iya aikata komai saboda ke. Kamar yanda malam yace na kirashi kafin muwuce wajen taron shine na kirashi, dan wannan dalilinne ma yasa nace Ammy (fulani) tai gaba zamu biyota. Yanzu har ita ta bar sanin sirrinmu tunda bazatace batason Su'adah kamar yanda take sona ba.....”
“Hakane Mom, amma nidai sanar dani mike faruwa kawai?”.
“Daɗina dake wutar ciki. Abinda kikaga ya girgizani da maganar malam ya tabbatarmin bincikensa na jiya ya nuna masa zasuyi taurin kai akan yarda da buƙatar mu, amma idan muka jajirce za'a iya samun nasa ƙila. Sai dai Ramadhan ɗin shine babbar matsala yanzu, saboda akwai yarinyar dake tsaye a kansa game da addu'a hatta azkar baya wasa yanzu safe da yamma, yace inhar tana tare da shi mawuyacine duk wani aiki namu yanzu yay tasiri a kansa dan tanada jajircewa. Hasashena ya bani tabbas shegiyar yarinyarnan ce ƴar karuwai. Maganarsa ta ƙarshe data firgitani itace zaɓin daya bamu akan Ramadhan ɗin, kodai akawar da shi kowa ya rasa shi da yarinyar, kokuma mu haƙur......”
“Ina bazai yuwuba Mom, wlhy bazan iya haƙura da Ramadhan ba. Idan nai haka ko to tabbaci ban cika mace ba. Har yaushe zuciyarki ta fara tausayine Mom?.”
“Nima ba tausayi nake jiba Aynah, domin zan iya komai a kanki, ciki kuwa harda kauda duk wanda ya tare min gaba. Tunda muka taso a gidanmu kowa yafi son Su'adah duk da kasantuwarta yarinya mai girman kai da ɗaukar kowa ba komai ba. Ba ƙyau tafini ba, amma ko kaya mukasa kafin a yabamin an yaba nata saboda ta iya tsara ado. Kullum a makaranta takan ɗauki maki na jarabawa fiye da nawa. A gida mahaifinmu yafi sonta fiye da kowane ɗa, dan hatta da shawararsa mai muhimmanci yakanyi da Su'adah baiyi da su Ammy ba. Mu duka ƴaƴan sarki ne amma ita kaɗai ake kira da gimbiya duk da nice babba. A koda yaushe wannan abu nacimun rai, taya zan fita komai amma yazam kullum itace da nasara sama da tawa? Hatta a shekarufa na fita. Abinda ya ƙara baƙanta raina da rayuwa lokacin da muke UK a school, tunda na fara ganin Basheer Hameed Taura na kamu da sonsa. Amma abin mamaki saina tsincesa tare da ƴar uwata Su'adah har sun fara soyayya ni ina nan ina ƙulla yanda zan tunkaresa da tawa soyayyar. Na shiga tashin hankali mara misali Aynah, har takai naji bazan iya jurewaba na tunkaresa da batun. Hummm karkiga irin korar kare da Basheer yamin tare da dogon gargaɗi, tun daga nan karatuna ya shiga hanyar taɓarɓarewa har muka dawo gida babu komai a result ɗina. Itako ta dawo da sakamako mai ƙyau cike da nasarori. Muna dawowa babu ɓata lokaci aka fara shirin aurar damu, ita aka aura mata wanda take so ni aka auramin mahaifinki batare da ina sonsa ba, dan iyayenmu ne suka ƙulla hakan. Watan Su'adah goma cif a Taura House ta haife ɗanta namiji santalele. Niko a lokacin ko ɓatan wata. Naji zafin hakan matuƙa amma naita ƙoƙarin dannewa. Bayan shekara biyu da yayensa ta sake Mardiyya, har lokacin ni babu labari. Nadai taƙaice miki sai a harhuwar Lubnah muka haihu tare, lokacin tanada yara har uku kenan niko 1 kuma mace ke. Na ƙara na biyu ma mace. Wannan ya ƙaramin tsanarta dan koba komai ta ɗarani da namiji kuma ƴaƴanta sunfi nawa. Daɗin daɗawa ɗanta shine ɗa tilo namiji agaba ɗaya Taura family. Nasha auna cutar da Ramadhan amma bai yuwuba saboda kakankinsa kullum nane suke da shi kamar sun san burina. Iyayi nayi Su'adah ta amshi Ramadhan a hanunsu amma sun hanata. Dan haka nasa akai aiki akansa aka tura masa wasu hatsabiban ajanu dakan maidashi tamkar wani mahaukaci. Sai dai mahaukacin ma naso ya koma baki ɗaya hakan bai kasance ba. Tun lokacin aurensa na farko naso ki auresa amma ya nuna baya ra'ayi, dan a yanzu babban burina shine ki auri Ramadhan ki ƙwato mana duk wani abinda Su'adah kejin tanada shi a hannu daya fini, amma kuma sai komai ya lalace bayan mun ɗakko hanyar nasara......”
“To amma Mom duk da waɗan nan abubuwan shine kike tunanin bazamuyi abinda malam yace ba. Ramadhan nada taurin kai, na tabbatar da wahala ya yarda da aurena, sai dai in uwarsa ce tace zata tsine masa. Idan ma tace hakan shi wannan jakin da aka auramin zai sakeni ne ta cikin sauƙi.....”
“Inko har duk abinda kika lissafo haka al'amarin zai zama to tabbas dolene Ramadhan ya mutu. Dan kawar da shine kawai zai sakama zuciyata salama akan Su'adah. Tunda bazamu samesaba to kowa ya rasa shikenan ƙurun-ƙus!!....…”
Wani irin banko ƙofar da akai ne ya dakatar da Aynah data fara dariya, atake sukai diri-diri, gimbiya Su'adah da kanta ke wani irin juyawa tanajin hajijiya ta shiga nuna adda Asmah da hannu sai dai abinda take son faɗa ya gagara fita. Safina datai wani tsalle ta shaƙo wuyan Adda Asmah ta buga da bango, hakanne yasa itama Ayna yin kukan kura a kanta ta shaƙeta. Ƴan biki ne suka fara shigowa a guje saboda ihun da Addah Asmah ta buga na azaba, har goshinta ya fashe jini na zuba......
*_TAURA HOUSE_*
Kowa ya hallara su kaɗai ake jira, mai-martaba da ransa ya gama ɓaci yana ƙoƙarin cewa a kirasu sai ga kiran daddyn Aynah ya shigo masa. Cikin tashin hankali ya shiga ambaton kalmar innalillahi.... Har ƙarshe, kafin ya ajiye wayar ya sanarma ƴan falon da duk hankalinsu ke kansa iya abinda Daddyn Aynah ya sanar masa. Zaram Ramadhan ya miƙe amma sai Bappi ya dakatar da shi.
“Ina zaka kuma?”.
“Bappi can gidan mana, kanajifa faɗa mizai haɗa Maah da Mom faɗa a duniyar nan?”.
“Koma miye ai zamu sani yanzu, ko kana mantawa da matsayinka a yanzune wai. Koma ka zauna Basheer yaje ya taho da su”.
Babu yanda ya iya ya koma ya zauna kamar zaiyi kuka. Zuciyarsa sai kaikawo take da tunanin mike faruwa? Miya faruwa? Mi akayi?. Hakama sauran kowa tunaninsa kenan sai dai babu mai bada gamsashiyyar amsa akai zaman jiran isowarsu.
★Kusan awa guda suna zaman jira dan sai da Pa yay jan ido suka yadda suka taho dalilin ita gimbiya Su'adah na tsoron nata mijin, itako Adda Asmah ta raina nata. Wujiga-wijiga suka shigo musamman gimbiya Su'adah da sai da Safina ta bata taimakon gaggawa acan amma da yanzu labarin ba wannan ake ba kuma. Kowa hankalinsa ya tashi da yanayin nasu, musamman ma Ramadhan da cikin rawar jiki yaje ya taya Safina riƙo Maah dake tafiya kamar zata zube ƙasa sai hakki take sama-sama. Shidai Bappi uffan baiceba, binsu kawai yake da kallo hakama mai-martaba. Pa kuwa yanayinsa na nuna ko'a jikinsa dan dama irin wannan ranar yake addu'ar tazo duk da bai san mike faruwa ba shima har