Header Ads
Showing 108001 words to 111000 words out of 204612 words

Chapter 37 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

3082

Ads at the middle of Article

ta zaro hotunan cikin envelope ɗin tana dubawa. Ƴammata ne cikin shigar uniform na aiki, wasu kuma suit na mata. Dukansu bazasufi shekaru ashirin da biyar zuwa da bakwai talatin ba. Sai da ta duba duk hotunan guda biyar sannan ta zaɓa na mutum biyu dake sanye da baby hijjab alamar musulmai ne, maybe ma yarenta ne duka.
Kamar mai jin tsoron maganar yanzun ma tace, “Waɗan nan sunyi”.
Kai kawai Ramadhan ya jinjina mata batare da ya ɗago ba. Dan rabin hankalinsa na ga abinda yake dubawa a file ɗin hanunsa. Kusan mintuna uku sannan ya ɗan duba cos da alamar ɓacin rai a fuskarsa... “Jafar! Abinda ke rubuce anan kuwa gaskiya ne? Ko idona ne?”.
“Tabbas gaskiya ne ranka ya daɗe. Dan duka mutane goma sha ukun nan daka gani akwai kwangilolin ayyuka a kansu, wasun su sun fara basu ƙarasa ba, wasuma ko niyyar farawar basuyi ba. Kuma munada tabbacin kuɗaɗen aikin sun fita a bitalmani harda saka hanun shugaban ƙasa mai sauka. Waɗan nan sune evidences na fitar kuɗaɗen duka”.
Yay maganar da miƙa masa wani file ɗin. Sosai Raudha ta ɗago tana kallonsu yanzun kam, dan zancen nasu haka kawai ya ɗauka hankalinta. Ta ɗan kafama Ramadhan daya dafe kansa bayan duba takardun idanunta.
“Cos!!”.
Ya faɗa a kausashe.
“Yes your excellency!”.
“Ina buƙatar a tura ma dukansu takardar gayyata, ku zauna da su kai da minister Abubakar Gandu Ku tattauna dasu domin bibiyar gaskiyar lamarin. Bayan kun tabbatar da gaskiyarsu ku basu kwanaki biyu kacal su dawo da kuɗaɗen kafin mu miƙa sunansu ga hukuma”.
“Okay sir!”.
Ɗan murmushi Raudha ta saki daya ƙawata fuskarta, cike da ƙarfin halin danne ciwon marar dake tsinkulinta, sai hakan yay dai-dai da ɗagowar Ramadhan suka haɗa idanu. Harara ya sakar mata yana sake tsuke fuska. Sai kawai murmushin ya sake suɓuce mata batare data shirya hakan ba. Idanu ya ɗan ƙanƙance ɓacin ransa na sake bayyana a fuskarsa, tai saurin girgiza masa kanta da kama kunuwanta dake cikin hijjab alamar “Am sorry”.
Baya ya ɗanyi da jikinsa yana lumshe idanu da furzar da huci. Hakan da yay ya saka Raudha cikin dauriya tace, “Ranka ya daɗe idan babu damuwa nace wani abu dan ALLAH?”.
Babu shiri ya buɗe idanunsa dan baiyi zaton jin hakan daga gareta ba. Ta marairaice fuska kamar zata fasa kuka. “Dan ALLAH abokina”
Tai maganar cike da marairaicewa. Sai yanayin yay kama da wadda shaƙuwa ke tsakaninsu sosai take masa shagwaɓa. Harga ALLAH sai da zuciyar Ramadhan ta motsa. Domin shima dai mutum ne tamkar kowa, sannan zuciya gare a ƙirji ba kuma dutse bane....
Kafin ya gama dawowa hayyacinsa ta ce, “Ranka ya daɗe maimakon a damu da zancen su dawo da kuɗin kuma su sake faɗawa hanun ɓata gari kafin su koma a bital mali, mizai hana a zaman da zakuyi dasu, mizai hana ku tilastasu ƙarasa aikin da suka fara, waɗanda basu faraba su fara kawai. Idan da buƙatar ƙarin wani abu da zai inganta aikin fiye da farko ko zai kammalashi sai ku daɗa musu. Koba komai hakan zai sa talakawa su tabbatar aiki kukazo yi da gaske......”
Yanda ya kafeta da idanu ya sata haɗiyar yawu da ƙyar. Cikin ɗan shakku da ganin zaƙewarta ya sata faɗin, “Ban faɗi haka dan ganin gazawar maganarku ba. Sai dan kawai a nawa hasashen shari'a da su tamkar zaman ɓata wani yanki na lokutankune masu muhimmanci ga alƙawran da akaima talakawa. Dan fallasasu zai ɗauke hankulanku ne kacokan ya maida can, aikin da kukai burin yi lokacinsa yayta tafiya. Bai kuma zama lallai su da suka basu kwangilar ba su yarda su tozarta kai tsaye tunda maybe akwai ƴan uwansu ko abokansu a ciki da makamantan hakan. Ƙila kuma dalilin hakan da zaku musu su shiryu su koma mutanen kirki wajen gyara halayyarsu har na ƙasa dasu masu tasowa suyi koyi idan kun ɗorasu akan irin wannnan matsayin. Idan na shiga hurmin daba nawa ba a gafarceni ranka ya daɗe”.
“Raf! Raf! Raf!”. Cos ya fara sakin tafi bakinsa a washe da murmushi.
“Oh my god uwa garemu. Ranki ya daɗe wannan shawara ce mai daraja data warware kowanne irin tarnaƙi cikin sauƙi ai. ALLAH ya kara girma da nisan kwana masu albarka.”
A ɗarare Raudha tai murmushin yaƙe. Dan bata da tabbacin mai gayya mai aikin shi ya amshi zancen kamar yanda taga cos ya nuna jin daɗinsa kai tsaye ba.
Cos da ya sha jinin jikinsa ga yanayin shugaban ƙasar shima yay saurin dakatawa yana faɗin, “Ranka ya daɗe m....”
Hannu shugaban ƙasa Ramadhan ya ɗaga masa yana buɗe idanunsa da furzar da iska mai nauyi...........✍



*_Humm su Ustazah kai ya fara buɗewa fa, an fara samun kan😹😹😜🚶🏻_*





*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*






*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*




*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_


*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_


*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_


*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_


*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_






Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k




*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_09032345899_*




*KATIN MTN*👇👇


09166221261
__________________


*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*






Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F




*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼


+227 95 16 61 77






*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*


_____________________




*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*




Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.




*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3




Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*




*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*


+234 903 177 4742




_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*














*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*


https://arewabooks.com/chapter?id=62b6073efa0b02c20d2ac11e






*_Episode 37_*




..........“Vary interesting”. ya faɗa a hankali, batare da ya basu damar maganaba ya cigaba da faɗin, “Inaga zamubi exactly idea ɗin nata, sai ka shirya muku zama a tura musu invitation ok”.
“Yes ranka ya daɗe. ALLAH ya ƙara lafiya da shekaru masu albarka.”
Raudha ce kawai ta amsa da amin tana sauke ajiyar zuciya kusan sau uku a jere. Harga ALLAH tayi matuƙar yin ƙarfin hali ne kawai wajen faɗa. Ba komai ya sata kawo hakan ba sai tunawa da su tsohon shugaban ƙasa. Dan tabbas zasu iya bin kowacce hanya domin ganin anƙi hukunta su waɗan nan ƴan kwangilar, sannan yanda suke ɗane da shi a tarko fara fiddo manufarsa kai tsaye ga duniya cutarwa ce garesa. Dan ta tabbatar bazasu ƙyalesa ba yay aikin shekara biyun da suka ƙudiri aniyar bashi damar yi ɗin. (Duk da tasan su basu isa hana zartar da ƙaddarar da babu wani hannu daya ƙirƙiri rubutata a doron duniya).....
Hotunan dake saman cinyarta da ya ɗauka ya sata dawowa a hayyacinta. Bayan ya duba waɗanda ta zaɓa batare da yace mata komai ba ya mikama cos.
“Okay sir an gama insha ALLAH. Za'a kaima Chairman ɗin zuwa safiya zasu fara aikinsu.”.
Kai kawai shugaban ƙasa ya jinjina masa tare da tura masa sausan files ɗin dake ajiye saman centre table ɗin. “Babu yuwuwar zan duba waɗan nan ɗin a yanzun. Inaga ma ƙarasa a office idan ALLAH ya kaimu, idan na fito ina buƙar fara ganawa da vice president”.
“Okay ranka ya daɗe, ALLAH ya huta gajiya ya ƙara lafiya. A huta lafiya ranki ya daɗe”.
Cos ya faɗa cikin rissinar da kai alamar respect sannan ya mike da takardun daya tattare ɗin ya tura a bag ɗin da ya shigo da su. Raudha na ganin ya fice itama ta yunƙura da nufin miƙewa dan mararta ta takura mata dauriyarta neman fara ƙarewa takeyi. Jitai an cafko mata hannu.
Da ƙarfi ta rumtse idanu dan harga ALLAH wannan sabon salon nashi na harmutsata. Abune da shi kaɗai ya fara mata su a rayuwa....
“Nace na gama da ke ne?”.
A hankali ta girgiza kanta tana faɗin, “Kayi haƙuri” ta koma ta zauna tana ƙoƙarin cire yatsun hanunta a nashi. Gaba ɗaya yanda yake murzasu ɗin harmutsa mata jinin jiki yake yi. Sakinta yay shima, ya koma jikin kujerar ya lafe yana ɗan furzar da iskar bakinsa. Sai dai yanda maƙogwaronsa ke kai kawo zai baka tabbacin magana yake da zuciyarsa. Dan harda ɗan matse idanu yayi lokacin da yake tura lip nashi a baki yana ɗan ciza. Sai kuma ya buɗe idanun a kanta da alamun kore tu anin dake bijiro masa ya ɗan tsuke fuska

Takardun da ke gefensa ya ɗauka ya miƙa mata, “Komai ya kammala akan school naki. Akwai sabon driver da zai dinga kaiki yana maido ki.”
Hannu biyu tasa ta amsa tanajin kamar ta tashi taita tsallen daɗi. Amma sai ta daure ta shiga masa godiya da addu'a cikin dauriyar danne ciwon da ke taso mata.
Gyaran murya ya ɗanyi cikin kausasa harshe ya cigaba da faɗin, “Barinki kije makaranta bashike nufin zaki iya duk abinda ranki ya so ba. Ki kama kanki dan a yanzu kinada banbanci da baya. Akwai aure a kanki banason shigar banza. Sannan ki sani ke matar shugaban ƙasa ce, komai naki a yanzu abin tallatawa ne ga mutane koda bai kai ya kawo ba. Ya rage naki ki riƙe wannan darajan ko kiyi sakaci da shi komai zai iya faruwa. A waɗan nan takardun akwai na bank a ciki, ki cika komai kiyi musu singing za'a maidasu can. Karatu nada muhimmanci a gareki matuƙa a wannan gaɓar, saboda ƙarancin shekarunki da matsayin da kike kai a yanzu, ya rage naki ki maida hankali kiyi abinda ya kaiki kokiyi wasa da damarki.”
Ganin yanda yake magana serious ya sata sake nutsuwa itama. “Insha ALLAH zaka sameni mai kiyayewa. Bazan gaji da maka godiya ba da fatan alkairi a rayuwarka. ALLAH ya baka ikon sauke nauyin al'umma ka gamawa lafiya cikin farin ciki tamkar yanda aka zaɓeka cikin farin ciki. ALLAH ya saka maka da alkairi kai da zuri'arka baki ɗaya”.
“Amin, thanks”.
Ya faɗa yana miƙa mata leda mai tambarin apple ƴar madaidaiciya. Sai kuma ya marairaice fuska cike da salon tsokana ya fara faɗin,
“A duk lokacin da zaki fita a gidan nan ina son na dinga sani Ustazah. Dan bana bukatar matata na rayuwa tamkar akuyar sake da ko'ina zata iya jefa ƙafa a lokacin da take so. Kinada damar canja driver ko securitys ɗin da za'a kawo miki idan halayensu basu miki ba. Karkiyi tunanin yin amfani da matsayin da ALLAH ya bamu wajen taka wani, idan haka ta kasance hukunci zai iya bi ta kanki kamar kowa. Idan kinada buƙatar wani abu zaki iya faɗa”.
Murmushi mai faɗi Raudha ta saki har haƙwaranta na bayyana a waje. Ramadhan dake kallonta yay azamar lumshe idanunsa da jan numfashi a fisge. Raudha da batasan murmushi nata ya zama wani abu daban ba ta ɗago idanunta taɗan kallesa tana jera masa addu'ar fatan alkairi a rayuwa.
Kansa kawai ya jinjina mata batare da ya buɗe idanun ba. Wani irin murɗa mata maranta yayi, tai saurin kife kanta a hanun kujerar jikinta na rawa. Sunan ALLAH take ambata a zuciyarta da damƙe hanun kukerar da iyakar ƙarfinta.
Shurun da Ramadhan yaji ne ya sashi buɗe ido da nufin sallamarta dan yana son zuwa shima ya hutama ransa. A gajiye yake matuƙa sakamakon motsa jiki da yayi yau sosai da yammar nan. Dan ya fita a keke, sai dai securitys na biye da shi a mashina da mota ɗaya badan yaso haka ba.
“Zanje ciki, kije abinki kema”.
Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa. Sai dai ganin taƙi ta ko motsa ya sashi sake dubanta dai-dai yana tsayawa kan ƙafafunsa. “What happend?”.
Ya faɗa yanabin hanunta data matse hanun kujera da kallo, ga kuma kamar jikinta ma na rawa. Duk yanda taso ɗagowa ta amsa masa kasawa tai, sai ma ƙoƙarin zamowa da take akan kukerar alamar abin ya fara tsauri. Shi tsoro ma abin yaso ɗan bashi, amma sai yay dauriyar matsowa ya tareta ganin zata kai ƙasa. Birkitota yay a jikin nasa, amma sai yaci karo da uban zufan data haɗa cikin ƙanƙanin lokaci. Ta ƙanƙamesa da iya ƙarfinta cikin azaba.....
“Ya ALLAH. K! What's wrong with you?”.
Ina batama san yanai ba, dan hankalinta ya fara nisa da duniyarta. Ganin yanda ta matse cikinta da hannu guda ya sashi kai hannu wajen ta saman hijjab ɗin. Sai kuma ya furzar da iskar bakinsa yana miƙewa ɗauke da ita gaba ɗaya. Dan ya fahimci yana buƙatar zuwa ɗaki da ita ya bincika da ƙyau.


Hawowarsa cikin falon yayi dai-dai da fitowar su Aynah da ga ɗakinsu zasuje ƙasa cin abinci. Turus sukai cikin al'ajab. Sai dai tun kallo guda da sukai musu kowanne yay ƙasa da kai dan sun san halinsa. Shiko baima ko kalli inda suke ba ya nufi bedroom ɗinsa ɗauke da Raudha da zuwa yanzu ma numfashinta ya fara nisa da ƙirjinta.
“What!”.
Munirah ta faɗa lokacin da ya ɓacema ganinsu.
“What! Ko what sisto. Amma dai wannan tsinanniyar yarinya anyi makira dai. Ɗauka fa? Lallai an gama shanye kurwar Yah Ramadhan a wajen nan”.
Cikin takaici Lubnah ta juya bedroom ɗin nasu batare data tanka musu ba tana ƙoƙarin kiran Gimbiya Su'adah.


A can ɗakin Ramadhan kam lokacin da yake shinfiɗe Raudha a gado sai ya fahimci ma ta suma ai. Mamaki abun ya bashi tamkar almara ko wani shirin film. Suma fa. Duk da abun ya bashi tsoro sai baiyi wani irin nuna rikicewa da ruɗani a zahiri ba dan mutum ne shi da bai iya gaggawa ba akan komai. A nutse ya zare mata dogon hijjab ɗin jikinta. Sai ga kayan barcinta wando iya gwiwa da mitsilar rigar best sun bayyana. Ruwan dake ajiye a side drawer nashi ya ɗauka ya shafa mata a fuska. Na farko ko motsi batai ba, sai da ya zuba mata da yawa ta kawo nannauyan numfashi. Sai kuma ta fashe da sabon kuka tana kiran sunan ALLAH da kira Mummy.
Hanunsa ya ɗan kai a goshi ya murza hanunsa ɗaya riƙe da ƙugunsa yana kallonta, sai kuma ya kai zaune kafarsa ɗaya a ƙasa ya tanƙwashe ɗayar a saman gadon ya ɗan tallafo fuskarta.
“Please relax mike damunki ne Ameenatu?”.
Duk da ta jisa bata iya bashi amsa ba, saima damƙo hanunsa da ke ƙoƙarin riƙo nata tayi cikin rashin fahimtar manta dawa take tare ta ɗora saman mararta tana jan wahalallen numfashi.
Duk da akan rigane sai da tsigar jikinsa ta tashi. Ya ɗan lumshe idanu sa sakamakon jin wani irin ɗumi da marar ta ɗauka. “Oh my GOD ”. Ya ambata akan laɓɓansa. Da ƙyar ya samu ta barshi ya janye hanunsa a wajen, ɗaya a cikin wayoyinsa ya ɗauka ya fara neman layin Anne. Dan shi dai baisan wata doctor mace ba bayan kanwarsa Safina da zai nema tazo ta dubata a yanzun. Bugu ɗaya kuwa Anne ta ɗauka saboda wayar na hanunta ne tana duba abu.
“Kai lafiya kira a daren nan Ramadhan?”.
Hannu ya kai saman goshinsa ya murza da tura lip ɗinsa a baki ya ɗan ciza kafin cikin damuwa yace, “Anne akwai damuwa ne. Bata da lafiya ko zamu samu doctor ne?.”
“Ya ALLAHU, waye baida lafiya? Aminatu?”.
Yanda tai tambayar ta kuma bama kanta amsa ya sashi sakin ɗan murmushi duk da damuwar da fuskarsa ta nuna.....

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads