Showing 90001 words to 93000 words out of 204612 words
Chapter 31 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt
yake saka ƙafarsa ɗaya waje. A mamakinsa sai yaga kanta duƙufe akan Al-qur'anin duk da kafin ya waugo ɗin yana jin idanuntane a kansa. Lip ɗinsa na ƙasa ya kamo da haƙori ya tura cikin baki tare da cijeshi da ƙarfi, kafin ya galla mata hararan ‘Wannan abar ko’ ya fice yana ƙwafa.
Tanajin ya rufe ƙofar itama ta sake ɗaggowa ta dallama ƙofar harara da murguɗa bakinta. Kafin ta rufe Al-qur'anin ta cire hijjab ta haye gadonta bayan ta kashe filar ɗakin gaba ɗaya tabar lamp na gefe side drawer ɗaya kawai. Dan kayan da yaci abincin ma batabi takansu ba tunda tasan bata da ƙarfin kaisu kitchen.
★★
Tun da ga wannan ranar Raudha bata sake sakashi a idonta ba, sai dai ta gansa a television, kai ko ƙannensa dake a gidan bata tunanin yama san da zamansu. Oho ita ina ruwanta, a ganinta wannan matsalarsa ce shi da su.
Kamar ko yaushe tana yawanyin baƙi, dan yau data kasance alhamis ma ta samu baƙuncin wasu matan gwamnoni guda huɗu. Dukansu manyan mata ne da zasu iya haihuwarta koma yin jika da ita, amma yanda suke mata kalamai cikin girmamawa da kwantar dakai batasan ta dinga tsinewa da tsige mulki da siyasa a zuciyarta bama. Yo banda mulkin babu ta yanda waɗan nan natan zasu iya ko kallonta. ƴar aikisun ma sun fita shekaru, ilimi, wayewar rayuwa, da ma ta siyasar. Amma dan abun kunya sunzo gabanta suna damunta da wani your excellency da ranki ya daɗe. Taja tsaki a ranta tana ƙarajin takaici da bama inuwar muliki suna BAƘAR INUWA.
A ɓangaren shugaban ƙasa kuwa ya sake komawa matuƙar busy. Dan abubuwane birjik saman kansa musamman na talakawansa da suka zuba ido da kunen sauraren farajin naɗe-naɗen muƙamai, tunda sunsan wannan hanyarce kawai shimfiɗar fara musu aiki. Anan kuma cikin gida gasu tsohun shugaba ƙasa sun tasashi gaba akan tursasashi amincewa buƙatunsu kamar yanda god father's nasu ke control nasu suma a bayan fage. Sai dai taurin kai da tsaurin ido na Ramadhan ya sashi jajircewa akan maganarsa ta farko na yarda da sharaɗin 50-50 amma ragamar zaɓin speaker na hannunsa. Sukuma sanin tasirin speaker ɗin a garesu yasa sukace sam bazata saɓuba. Ga list ɗin shugaban ƙasa na cabinet ɗin da suka kasance zaɓinsa duk yarane matasa da basu wuce talatin da biyar, arba'in zuwa ƙasa ba. Ma'ana duk sa'aninsa ne. Waɗan da zasu ɗara shekrunsa ƙalilanne.
Tabbas jayayyar ta fara gundurar manyan jam'iyyar, domin kuwa ta wani fanin a tsorace suke da dagiyarsa. Ba komai ya jawo hakan ba sai zuwansa ƙasar Nigeria. Dan bayan zaman tattaunawa da sauran shugabannin Africa da sukai a Nigeriar shugaban ƙasar Nigeria yayi zaman na musamman kuma na sirri da shugaban ƙasa Ramadhan ɗin. Kuma har zuwa yanzu babu wani bayani daya fita akan tattaunawar tasu ta ko wanne fannin na ƙasashen biyu.
Daga can bayan fage kuma god father's nasu na cigaba da shirye-shiryen tsara ta yanda za'a halaka dattijon arziki alhaji Hameed Taura da suke kallon shike bada gudunmawar kafiyar Ramadhan kai tsaye.
To bayan dai an turza an kuma turzo dole su Alhaji Usama suka amince suka sakarma Ramadhan tashi jayayyar badan yafi ƙarfinsu ba, sai dan akwai wata a ƙasa. Bayyi wani farin ciki ba, dan yasan a yin hakan da sukai kwai manufa mai ƙarfi. A cikin kwanki uku kacal da amincewar tasu akai zaɓen fidda gwani a majalissa. Dan sai da sune za'a gabatar da jerin subayen cabinet na shugaban ƙasa dama duk wasu muƙamai daya shirya tsaf.
Duk da akwai ɓoyayyen zaɓi hakan bai hana bama ƴan majalissa damar yin zaɓen fidda gwani ba akan speaker ɗin ba, daga ƙarshe dai dole aka nuna zaɓin bayan fage badan hakan shine fatan wasu ƴan ƙasarba da ma wasu a cikin ƴan majalissar, musamman da ya kasance babu wanda yasan da ainahin speaker ɗin sai da akaga sunayensu. Dan haka zaɓin ya bama kowa matuƙar mamaki da sanya mafi yawan al'ummar ƙasar NAYA farin ciki da sake ganin kimarsa. Musamman matasa da aka ɗakko matasa ƴan uwansu da ko'a wajen zaɓe ma ba'ai tunanin zasu kai labari ba amma aka aza a kujerun guda biyu da bayan kujerar shugaban ƙasa sai su a faɗa ajin ƙasar, dan kuwa duk matasane suma masu ƙwazo da aka zaɓesu da yaƙini tun daga jihohinsu. A ɓangaren manyan kuma da shugabannin jam'iyya hakan yayi matuƙar ƙona ransu da sakejin tsanar Ramadhan. Taya zai ɗakko yara ƙanana ya ɗora kan shugabancin manya, bayan ga wanda ma suka haifi ubanninsu a wajen ba'a su ba. Wannan zaɓin speakers yasa a ranar sau kusan uku jam'iyyar da shugaban ƙasa ya fito suna zaman meeting wanda ko guda a ciki ba'a gayyaci wani na jikin shugaban ƙasar ba kuma.
Raudha kanta da basanin minene siyasa ko mulki tai ba zaɓin ya mata ɗari bisa ɗari. Ta kuma sakasu a cikin addu'ointa sosai akan ALLAH ya cigaba da tallafa musu wajen ɗaura mutanen kirki bisa muƙaman da dole sai dasu ne mulkinsa zai tafi cikin nasara da sauke hakki.
Bayan fidda speakers shugaban ƙasa ya cigaba da wasu naɗe-naɗe da suka shafi office nashi da suka sake bada mamaki, masu bashi shawara akan fanoni da dama na mulkinsa da sauransu akwai manyan dattijai da akasan su akasan jajircewarsu wajen faɗar gaskiya da yin gaskiya akan ayyukansu da ma tsaurinsu. A zaɓin nasa ya kasance akwai matasa masu jini a jika irinsa ya muƙar sake ɗaukar hankalin talakawan ƙasa a kansa, har yanda wasu ke nuna masa ƙauna ma sai ya baka tsoro. Yayinda dattijan ƙasar NAYA musamman waɗanda suka ƙwallafa rai a mulkin suka fara shaƙa daga takun na shugaban ƙasa, dan suna masa wani kallone kamar na TAKUN SAƘAr nuna kishin matasan ƙasar da mayar musu murtanin sun babake komai a baya suma. Hakan yasa ba ƴan jam'iyyarsa kawai ba, har wasu ƴan jam'iyyun da sarakunan gargajiya suna zaman yin meeting da tattauna take-taken Ramadhan ɗin.
Sarai yana jin wasu abubuwan dake faruwa, amm sai yay biris kamar kunnensa a toshe yake, idanunsa kuma a makance. Yay matuƙar maida hankali wajen tsara yanda yake buƙata a tantance masa cabinet nashi da taimakon mayan mutanen dake zagaye da shi na kirki duk da akwai masu fuska biyu kuma a cikinsu dai suma harma a matasan, kafin su amshi muƙaman da ake burin bama kowannensu..
_________★_________
A daren yau manyan dattijan nan, da al'amuransu ke keɓantattu ga al'ummar ƙasa sukai zaman tattaunawa na musamman a tsakaninsu, dan gane da ganin bayan Alhaji Hameed Taura, da zukatansu ke raya musu komai shugaban ƙasa Ramadhan yanayine bisa umarninsa. Wato a zahiri dai Ramadhan shine shugaban ƙasar NAYA, amma a baɗini Alhaji Hameed Taura shike mulki. kamar dai yanda suke ga sauran shuwagabanin baya, wanda shima Ramadhan ɗin haka suka tsara a kansa. Sai dai tun kan aje ko'ina ga komai na shirin sukurkurce musu.
A cikin tattaunawar tasu ne. Oga kwata-kwata ke ambaton “A wannan gaɓar ya kamata matar shugaban ƙasa ta nema office nata”.
Cikin mamaki sauran duk suka dubesa, dan sam basu fahimci muhimmancin yin hakan ba a garesu. Ɗan murmushi ya saki tare da ɗaukar kofin abinda ke gabansa ya zuƙa ya ajiye. Cikin ɗacin rai yace, “Na fahimci a yanzu da kujerar first lady kawai zamu iya fara yaƙar wannan yaron tunkan al'amarin nasa ya ƙara nisan kiwon da bola sai ta fimu daraja”.
“Amma ranka ya daɗe, ko ka manta first lady sweet seventeen ce. Sannan girman ƙawai, iyakar karatunta o level ne. Babu abinda ta taɓa sani a siyasa balle sha'anin mulki, rayuwarma yaushe ta gama fahimtarta?”.
“Duk wannan raunin nata ne ya sani tunanin a bata office”.
Shiru sukai suna sake ninƙaya a nazari, dan har yanzu basuga wani alfanun hakan ba a garesu sam sai tsagwaron kwamacala da shirmen da ƙasar tasu ke tunkara. To amma sun san halin oga da shegen zakule-zakule. Sai dai duk sanda ya zaƙulo abu zaka samu mai muhimmanci ne a garesu daga baya....
★★★
A lokacin da suke can suna tattauna yanda first lady Raudha Dauda Hutawa data koma *_Raudha Ramadhan Taura_* zata mallaki Office, anan Taura House Ramadhan dake ganawar sirri da kakansa ke zaune a keɓantaccen falon baƙi na Alhaji Hameed ɗin suna tattauna muhimman batutuwa. A cikin tattaunawar tasu ne kuma Alhaji Hameed Taura yay ma Ramadhan batun saka Raudha a makaranta ta cigaba da karatu, dan hakan nada matuƙar muhimmanci a mulkinsa da ita kanta.
Ramadhan dake kai yankan kilishi bakinsa yay wani ɗan guntun murmushi da baida maraba da takaici, kafin cikin tausasa harshe ya ce, “Bappi wannan shi naso nuna maka akan auren nan. Taya za'ai shugaban ƙasa da mata mai matakin o lavel a ilimi, sannan ƴar shekara sha takwas tayi yarinta da yawa?”.
“Wannan duk ba damuwa bane Ramadhan, sai ma kafi jin daɗin control nata yanda kakeso, zakace nina faɗa maka nan gaba idan idanunta suka buɗe akan abinda kake ganin kai bazata iya ba”.
“To amma Bappi ni a wannan gaɓar ma banga amfanin yin karatun nata ba, dan nidai yanzu bazan bari ta ƙetare ƙasar NAYA ƙaro ilimi ba, sannan bani da sha'awar iyalina shiga harkar siyasar nan”.
“Sosai tunaninka ya sani farin ciki, sai dai kuma baida nasaba da daƙile mata zancen cigaba da neman iliminta. Ba lallai saitaje ƙetaren
NAYA ba. A cikin ƙasar nan dama ya kama tayi, kai kanka hakan kimace a gareka, da ƙara bama talakawa hope game da mulkinka. Zata iya shiga duk jami'ar da takeso a ƙasar nan, kokuma tayi online school na ƙasashen ketaren inma suke take so, amma zamanta babu karatu bazai yuwuba. Koda bazata shiga siyasa ba akwai abubuwa da yawa da suke bukatarta a mulkin koda kai da ita baƙwa buƙatar ta kasance a cikinsu”.
Ɗan jimm Ramadhan yayi, sai kuma yaɗan ɗage kafaɗa da cigaba da cin kilishinsa. “ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi”. Kawai ya faɗa ya tsuke bakinsa. Shima Bappi komai bai sake cewa akan hakan ba. Bayan murmushi da yay ma sai ya ɗakko masa wani zancen daya shafesu kuma..........✍
*_Typing📲_*
*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*
https://arewabooks.com/chapter?id=62b0ba6cf0deac225fe20185
*_Episode 33_*
..........Yau ta kasance asabar, Ramadhan na gida bai fita ko'ina ba, dan yana buƙatar hutu saboda doctor ɗinsa ya tabbatar masa sugar nashi yayi low, sannan jininsa ya haura sama alamar hayaniya ta fara masa yawa. Shawarar doctor yabi, dan ayanzu yana matukar buƙatar ganin ingancin lafiyarsa fiye da baya, kodan ya samu damar sauke hakkin mutane a kansa. Barcin safe yayi sosai har takai su Raudha basuyi tunanin yana a gidan ba.
Kusan sha biyun rana su Lubnah na baje a bedroom na sama, wanda a tsari shugaban ƙasa da iyalansa ne kawai keda hurumin zaman cikinsu. Zaune suke a baje kowa na sabgar gabansa, ga kayan ciye-ciye da suka saka kuku ya shirya musu, wasuko anyi order nasune a wajaje daban-daban. Su duka ukun babu mai shigar mutunci, daga mai bomshot da best sai mai 3quarter singlet.
A can falon ƙasa, wanda shine na uku a jerin faluka uku da kai tsaye zai kawowa sashen iyalan shugaban kasa Raudha da Basma da Bilkisu ne zaune. Bilkisu na daga gefe tana aikin nata na karatu da bincike-bincike, Basma da Raudha na kallo a lap-top ɗin Basma ɗin cike da shauƙin film ɗin. Sai mama ladi da ke gefensu tana saƙar hannu, wadda alama ya nuna kayan sanyi ne na yara. Sai dai rabin hankalinta nakan television da ake nuna maimaicin labaran daren jiya.
Sanye cikin ƙananun kaya nashan iska ya fito, baƙin trouser dogo mai layin fari guda biyu a gefe da gefe, sai baƙar t-shirt. Kayan sun masa matuƙar kyau kasancewar sa mai hasken fata, sai dai fuskar sam babu ɗigon fara'a alamar barcin da yay bai gama sakinsa ba, duk da dai dama bawai ya cika yin fara'ar bane sai ga wanda ya gadama.
Tsaf falon yake a tsaftace, ga wani ƙamshi na musaman na tashi mai saka nutsuwa da kwanciyar hankali. Da ga can gefe cike tebirin dining yake da kayan breakfast kamar yanda kuku bai gajiya da shiryawa a kullum, duk da bai taɓa ganin alamar wanda akeyi da shi yaci ba sai matar gidan kawai.
Duk da yunwar dake cin cikinsa, maimakon ya nufi dining ɗin kai tsaye sai ya samu ɗaya da ga cikin kujerun falon ya zauna. Yana ƙoƙarin kunna television su Lubnah suka fito daga corridor ɗin bedrooms na Raudha suna kwasar dariya.
Turus sukayi a tsaye suna duban wanda basuyi tunanin gani ba zaune hakimce a falon. Yayin da Ramadhan yay tsam shima domin shigar muryoyin dariyar ƙanen nasa cikin kunnensa da shi sam baima san da zamansu a gidan ba ko yace ya manta da batun zuwansu.. Duk da kuwa Maa ta jima da sanar masa zasu dawo nan da zama kafin ta dawo. Amma jin Bappi da Anne babu wanda ya masa maganar ya sashi ɗaukar mahaifiyar tasa ta janye batun duk da a yanzu haka tana ƙasar England ita da Pa.
A hankali ya ɗago idanunsa ya zuba musu, tare da watsa musu wani irin gigitaccen kallo daya gama kiɗima su gaba ɗaya har fitsari na neman kufcema wasun su, dan a rayuwarsa yayi matuƙar tsanar shigar banza. Shi ko akan iyalinsa ne bai cika son ganin matarsa da ƙananun kaya ba anyhow.
Sanin dokarsa ya saka Lubnah da Muneera kwasa a guje suka koma hanyar da suka fito, yayinda Aina ta daburce matuƙa, dan tun randa ya kamata a U.S tana aikata abinda bai dace ba suke wasan ɓuya, ta kuma haramtawa kanta zama duk inda zasu haɗun tunda ya dawo NAYA. Ko maganar haɗata aure da ake da shi, tana matuƙar buƙatar hakan, dan tana mutuwar son Ramadhan tunba yanzu ba, sai dai tana fargaba da sanin mawuyacin haline ya amince da aurenta, shiyyasa tafi yarda da zuga mahaifiyarta (Adda Asmah) akan tarwatsa auren Ramadhan ɗin kawai.
Tun kafin abinda ta hango a cikin idanunsa ya fita a fatar bakinsa ya sake gigitata ta kai durƙushe ƙasa, sai kawai ta tafi da rarrafe dan batasan taya zata miƙe ma tayi gudun ba tsabar rikicewa..
Wani irin numfashi Ramadhan yaja na tsananin ɓacin rai, lip nashi ya tura cikin baki ya cija da ƙarfi, yayinda zuciyarsa ke ambaton sunayen ALLAH domin son yin controling fushinsa. Tsahon mintuna biyu ya buɗe idanunsa, tare da miƙa hannu ya ɗauka telephone ɗin dake bisa copy table na kusa da shi. Sai kuma yay shiru da tunanin wayar ina zai kira?.
Telephone ɗin ɗakin Raudha ya kira. Sai dai harta katse ba'a ɗauka ba. Siririn tsaki yaja, tare da maida akalar kiran zuwa ta falon ƙasa, dan iya nan yasan zata iya zama inhar bata bedroom da nan falon upstairs
Da sauri Mama Ladi data ɗaga kira ta mikoma Raudha da suka maida dukan hankalinsu a kallo ita da Basma kan wayar. Ta ɗago da sauri tana duban mama ladi dake miko mata kan wayar, suma su Bilkisu ita suke kallo. “Ranki ya daɗe inaga daga sama ne kiran nan dan ba'ai magana ba”.
Komai Raudha batace ba ta kai wayar kunnenta da tunanin kosu Lubnah ne.
“Ameenatu! Ki sameni yanzun nan”.
Duk da ba kowa ke kiranta da wannan sunan ba hakan bai hana gabanta faɗuwa ba tai saurin duban Upstairs ɗin a ɗan firgice. Jin ƙarar ajiye wayar da yay ya saka Raudha mikewa har tana cin tuntuɓe da ƙafar Basma ALLAH dai ya hanata kifawa Bilkisu ta tareta.
“Yi a hankali aunty Raudha karki ji ciwo”.
Kai kawai ta iya jinjinama Bilkisun tai ƙoƙarin fara haura steps ɗin da ɗan gudu-gudu, duk da hakan bai hana bayyana nutsuwarta a tafiya ba, wadda ta zame mata halitta tun bayan da sayyadi Abubakar ya saita mata rayuwa.
Ramadhan dake zaton ganin bullowarta dama daga downstairs ɗin ya shiga watsa mata kallon da tunkan ta karaso hanjin cikinta suka fara barin jikin sauran kayan ciki suna kaɗawa. Tana masa kallon mutum mai ƙarancin kirki amma kallon da yake jifanta da shi a yau yayi tsanani da yawa, gashi batasan akan mi yake yi ɗinba kuma. Dan koda wasa bata taɓa kawoma ranta tunanin zaman su Lubnah a saman zai iya fusatashi ba tunda taga dai ƴan uwansa ne ai.
Bilkisu ta ture books ɗin gabanta ta miƙe da sauri tana gyara gyalen jallabiyar jikinta. Dan bata raba ɗayan biyu su Aina'u ne. Upstairs ɗin ta fara haurawa da sauri-sauri itama. Dan haka Basma ta