Header Ads
Showing 87001 words to 90000 words out of 204612 words

Chapter 30 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

3082

Ads at the middle of Article

da take aure komai, shiyyasa take son ƴarta ta shiga gidan kodan su mallaki abinda ƴar uwar tata ke taƙama da shi, musamman daya kasance Ramadhan shine jika ɗaya namiji tilo a zuri'ar Alhaji Hameed Taura. Wanda ko a yanzu ALLAH kaɗai yasan iya abinda yake mallakinsa kodan kasancewarsa ɗan gaban goshin kakanin nasa. A gefe kuma shima ba azaune yake ba yana kan neman na kansa ne. Adda Asmah tasha saka gimbiya Su'adah a hanyar banza, sai dai ALLAH ya timaketa tana saurin gyara kuskurenta saboda samun tsayayyen miji irin Pa da tuni ya gama gano wacece yayar matar tasa. Sai dai bai taɓa gaya mataba gudun shiga tsakanin ƴan uwan juna.
A take anan Adda Asmah ta gama tsara musu dolene wannan al'amari a haɗa da malamai gaskiya, Fulani ta amince, Gimbiya Su'adah dai tana ɗan janjeni, dan kuwa ita dai barta da ƙasaita da isa harma da rashin mutunci, amma bata yarda dabin malami ba. Shiyyasa anan ɓangaren kam basa shan inuwa ɗaƴa da adda Asmah ɗin..
“Su'adah kinyin shiru! Ko baki amince ba ne?. Idan baki aminceba bawaifa dole bane, sai dai fa ki tabbatar Ramadhan ya sake miki nisa na har abada. Dan a baya gwara tunda a gida ɗaya kuke kina ganinsa yana ganinki, sai dai kawai an rabaki da shi bai miki kallon uwarsa sai kakanni ya ɗauka iyayensa. A yanzu ko ku dukane zaku rasa harsu karuwar su ɗauka. Dan kuwa dai sune masu amfana tunda ƴarsu yake aure.....”
Wani dogon numfashi da ya katse Addah Asmah a magana Gimbiya Su'adah taja da ƙarfi, tuni idanunta sun kaɗa sunyi jazur saboda damuwa da ɓacin rai. Ji take tankar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan baƙin ciki. “Adda dan ALLAH kibar wannan mugun fatan, dan wlhy inhar ina raye har gaban abada babu su babu wannan nasarar akansa. Ni kin sanni kawai dai bana son harka da maƙaryatannan, dan bokaye da malmn tsubbun nan mafi yawanci lokaci abinda suke faɗa ƙaryace kawai, sai dai aci maka kuɗi a barka sakarai”.
“Bazan musa miki akwai irinsu ba, amma kema kinsan namu ba irin waɗan nan bane. Kuma ni da Ammay dai bazamu cutar da ke ba balle Ramadhan. Mu dama hausarmu anan muje musa a masa roƙon ALLAH ya karesa daga sharrinsu. sannan muɗau mataki kar yarinyarnan ta samu ciki, mu kuma dawo da hankalinsa kan Aina'u dan ɗanmu ya dawo hanunumu baki ɗaya”.
Numfashi gimbiya Su'adah ta kuma ja a hankaki, kafin tace, “To shikenan na amince aje ɗin, amma gaskiya sai dai a samu wani amintacce yaje ni dai bazanje ba dan Abbansu ba yarda zai ba”.
Fulani dake matuƙar jin takaicin ƴar tata Su'adah ta balla mata harara. “Tunda ke ɗin shashasha ce sanar masa zakiyi zakije wani waje. Wai nikam Su'adah yaushe zaki san ciwon kanki? Anya kuwa Basheer haka ya barki kuwa? A haka dai duk wanda ya ganki sai ya ɗauka wata jarumar gaske ce, sai dai basu san ƙatotuwar shashasha bace ba”.
Ƙin cewa komai gimbiya Su'adah tayi, sai dai ta sake ɓata fuska alamr maganar mahaifiyar tasu bai mata daɗi ba. Haka suka sake ƙulla abubuwa daban-daban harda maƙudan kuɗaɗen da za'a kaima malaman wanda kaso biyu bisa uku Adda Asmah duk cutarsu tayi kawai.




*_BINGO. GOVERNMENT HOUSE_*


Gaba ɗaya zaman gidan ya sakema Raudha tsanani tun zuwan su Lubnah, ga damuwar zancen aunty Hannah da kuku da taji shima ya kasa barin ranta. A wajen su Bilkisu kawai take samun sauki. Su kuma suna fita school tunda safe sai yamma suke dawowa. Duk da suma dai su Lubnah ɗin na fita aiki, Aina'u ce kawai bata aikin uwar komai sai kallon series kullum a lap-top. Sai ko gantalinta da samari dan a yanzu haka duk hanyar da zatabi ta sani na zuwa club da dare. Shiyyasa bata sakewa. gidan su Ramadhan idan tazo, saboda su dokane da 6 na yamma tayi aka kwaso yaran gidan daga islamiyya babu mai sake fita sai safiyar gobe. Kuma duk inda zaka sai dai driver ya kaika ya dawo da kai.

Kwanan Ramadhan biyu ya dawo NAYA daga taron da suka gudanar a ƙasar Nigeria. Duk da dawowar rana yayi bai shigo gida ba, kai tsaye office ya wuce su Raudha ɗin ma a labarai sukaga dawowar tashi. Har kuma suka kwanta barci bai shigoba alamar wani abun ya tsayar da shi wanda bazai wuce zaman meeting ba.
Ilai kuwa hasashen haka yake, dan kuwa dai zaman meeting ɗin sukai da su forma president anan cikin gidan akan son sasantawa game da batun cabinet daya sharɗanta yarda da 50-50 akan zaɓin shugabannin majalissa. Sai dai kuma a yau ɗin ma babu nasarar, dan kuwa dai Ramadhan yana akan bakansa. Da ga ƙarshe rai ɓace aka watse babu abinda aka cimmawa. Shima kansa rai ɓacen ya dawo gidan, dan haka baibi takan kowa ba yay shigewarsa ɗakinsa.
Sai dai kuma kamar koyaushe dawowar tasa ta wanzu ne a kunnen Raudha dake zaune tana karatun Al-qur'ani bayan ta idar da salla. Agogo ta kalla, ƙarfe biyu saura. Taja numfashi zuciyarta na mamakin yanda al'amrin ke tafiya. Dama haka mulkin yake mutum ko lokacin kansa baida shi?. zata iya rantsewa tunda suka tare a gidan nan sau uku kacal taga ya dawo gida kafin takwas na dare. Sai ko randa suka fita ɗin nan daya shigo kusan biyar na yamma. Bakinta ta ɗan taɓe ta cigaba da karatunta zuciyarta na raya mata *_BAƘAR INUWA_* kennan. Gara rana da ke. Dan zama a ƙaton gida da cin mai daɗi da sunanka babba a ƙasa ne kawai jin daɗin. Talakan dake cikin waccan ranar yama fi mai mulkin jin daɗin duniyar. Tunda koba komai shi zai shigo ya huta a gidansa kan lokaci. Yaci yasha hankali kwance tare da iyalansa. Amma gasu anan kullum cikin haɗa tuggun yanda za'a halaka rayuwarsu akeyi. Bashi dake mulkin ba ba ita ƴar karoro ba dake amsa sunan matarsa.


Koda ya kimtsa jikinsa duk yanda yaso kwanciya kasawa yay, dan yunwa yakeji sosai. Rabonsa da abinci tun breakfast na bankwana da sukayi a Nigeria shi da sauran shugabanin ƙasashe da suka halarci taro. Ga kansa na ciwo ga ɓacin ran da aka ƙara masa yanzun. Siririn tsaki yaja yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa, kafin ya tura lip ɗin nasa cikin baki ya fara tauna a hankali har sannan idonsa na a lumshe. Dan kwance yake a saman katafaren gadonsa da yaji lafiyayyun shimfiɗu na alfarma. Ƙafafunsa a ƙasa suke yana rigingine, sai filo da yay da hannayensa. A hankali ya buɗe idanunsa dake cike da gajiya da barci. ganin agogon na ƙara gudu ya sashi miƙewa ya fice a ɗakin, dan yafi buƙatar abinci mai nauyine baya son shan kowanne juice ko milk.
Yasan bai dace yace zaije kitchen nema abinci ba, dan haka ya nufi ɗakin Raudha kai tsaye duk da zuciyarsa batason aikata hakan kuma.........✍




*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*






*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*




*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_


*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_


*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_


*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_


*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_






Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k




*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_09032345899_*




*KATIN MTN*👇👇


09166221261
__________________


*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*






Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F




*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼


+227 95 16 61 77






*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*


_____________________




*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*




Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.




*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3




Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*




*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*


+234 903 177 4742




_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*














*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*




https://arewabooks.com/chapter?id=62b0ba6cf0deac225fe20185


_________________




KWANGILA COLLECTION 🌺🌺


Assalamualaikum tallah maganin watarana komi ake buqata da akeso asiya ku kira lambarnan kaway inshallah zakusamu,07046881166


Shin kinshafa Mai kinyi duhu har kinajin kunyar duban kanki a madubi? Kokuma sokike kiyi haske kiyita walwali kowa yadinga santinki?ga hadin set dinmu me bala'in kyau inkikayi amfanidashi kinrabuda kowani irin matsala ta fata insha Allah chat 07046881166.


Matsalarki t zamantakewar aurene kinkasa gamsar d miji? Infection ne matsalarki ko budewar gaba kokuma,bushewa,kimin mgana yar uwa,07046881166.


Uwargidaye d amare kinaso duk Wanda yazo dakinki yatafi yana zancenshi da fadin allahunma arzuqni? Munayin frames tsala tsala n daki da madubai donsawa a falo bbu ruwanki d (nunamin daki inga fuskata) kede kira wannan number 07046881166


Munada kayan Yara masu kyau masu inganci duk kushewarki d Kaya namu bazaki iya tafiya kivarsuba,kisawa yaro/yarinya sufito kmar dangin ashwariyya nemeni t wannan number 07046881166


Sekuma duk abinda kikeso d bamu lissafaba zaki iya turomana mu Nemo maki mesauqi dakuma qarko,


Duka kayanmu suna zuwane a farashi sari kayanmu nada arha matuqa kizo ki kwashi garavasa,mesiyan daya daya ko sari duk muna marhabun daku, 07046881166 nagode senajiku🥰


_______________________
*_Episode 32_*






..........Buɗe ƙofar ya saka Raudha saurin juyowa dan batai tunanin ganin wani ba a wannan lokacin. Su Bilkisu ne dama dai ke shigo mata a kwana biyun nan, tasan kuma yanzu sunyi barci. A bazata ta ɗan waro idanu waje, domin ganin abinda batai zato ko tsammani ba. Tunda bai taɓa mata hakan ba...
Ɗauke kanta tai da ga garesa da sauri, ganin ya cigaba da takowa cikin ɗakin kuma idonsa a kanta ko ƙyaftawa bayayi. Kayan barci ne jikinsa farare tas, wandon har ƙasa, hakama rigar mai dogon hannu ce. Ko ba'a faɗaba kallo da ga nesa zaisa ka fahimci zasuyi taushi kayan. Duk da kasancewarsa farin mutum kuma badan kwalliya ba sai da suka masa ƙyau. Sai da ya ƙaraso gaban gadonta ya dauke idanunsa a kanta ya koma bin ɗakin da kallo kamar yau ya fara shigowa ciki, hannayensa dake zube cikin aljihun wandon pyjamas ɗin nasa ya zare sannan yakai zaune a bakin gadon.
Mamakine ya sake turnike Raudha, sai dai babu damar yin magana ko neman dalili. Sosai fuskarsa ke a cinkushe babu ɗigon fara'a, wanda yay masa ma farin sani yana ganinsa zai gane ransa a ɓace yake.
“Sannu da zuwa”.
Raudha ta faɗa a hankali kamar mai raɗa. Sai dai hakan bai hanashi jinta ba. Amma maimakon ya amsa mata sai jeho mata furucin data kasa jurewa sai da ta ɗago ta dube...
“Bani abinci”.
Shine abinda ya fito a bakinsa batare da ya damu da girman mamaki da maganar zata zo wa Raudhan ba. Bawai dan bai isaba, sai dan ba haka ya saba ba. Batama tunanin ya taɓa cin abinci a gidan kamar yanda kuku ya faɗa.
“Kallona zaki tsaya ko abincin zaki bani?”.
Tsam ta miƙe har tana bige ƙafa da gado. Ta matse ido raɗaɗin na ratsata ta fice zuciyarta na gudu-gudu fiye da takun kafafunta. Ita yanzu ina zata nemo abinci 1 harya gota? Tasan dai kuku yayi barci. Ƙwalla suka cika mata idanu, amma sai ta haɗiyesu tana ƙoƙarin sauka downstairs.
Turus ta ɗanyi ganin Bilkisu zaune a falon duk da dai babu haske mai yawa, iyakar lamp ne na gefen kujera kawai. Amma hakan bai hanata ganinta ba. Ta baje books da takardu saman centre table da taja gaban kujerar da take zaune. Itama Bilkisun a ɗan firgice ta ɗago, sai kuma taja ajiyar zuciya da ɗan shafa ƙirjinta. Da'alama da farko tsoro taji, farin glass ɗin idonta ta zare tana faɗin, “Aunty lafiya bakiyi barci ba?”.
Raudha ta ƙarasa takawa inda take, “Ke ya kamata na tambaya aunty Bilkisu, ko tsoro bakiji ke ɗaya anan?”.
“Karatu nakeyi aunty, cikin ɗaki Basma ta hanani yi a nutse da gurnanin barcinta. Shiyyasa na dawo falon. Kuma banji tsoro dan securitys ma ai gasu nan sunata kai kawo a compound”.
Kai kawai Raudha ta gyaɗa mata, dan tasan gsky aunty bilyn ta faɗa. Haka securitys ɗin gidan ke kwana tsaye kamar zasu iya tare mala'ikam mutuwa ɗaukar ran wani a gidan.....
“Aunty ko baki da lafiya ne?”.
Bily ta katse tunaninta.
“A'a lafiyata ƙalau. Abinci yace zaici shine zan duba. kitchen”.
Ɗan jimm Bilkisu tayi dan da farko bata gane wa Raudha ke nufi ba, sai kuma ta ce, “Oh ko Yaya ya dawo ne?”.
Kai Raudha ta jinjina mata cikin ɗanjin nauyi, dan Bilkisu ta girmi su Fatisa ma ba itaba. Bilkisu tai ƴar dariya. “Oh yanzu a daren nan kuma?. Amma bana tsammanin abinci a gidan nan. Ya kamata kema dakin ajiye masa tunda kinsan komi dare zai shigo”.
To kawai Raudha tace. Dan bayan hakan bata da abin faɗa. Taya zata zauna fadama Bilkisun ɗan uwansu bai taɓa cin abinci a gidanba. Ita huɗɗa makamanciyar wannan ma bata taɓa haɗasu ba.


Kitchen ɗin ta nufa, ganin hakan yasa Bilkisun bin bayanta. Komai sun buɗe babu wani abincin arziki da zasu bashi ya ci, dan haka Bilkisu ta bata shawarar su dafa masa wani abu kawai mai ɗan sauƙi. Ba musu Raudha ta amince, abinka da na'urorin dake sauƙaƙa aiki, cikin abinda bai ƙulla awa guda ba suka haɗa masa abinci mai sauƙi da Bilkisu tasan bazaiyi ƙorafi ba. Raudha ta haɗa komai a wani ɗan basket mai ƙyau ta ɗauka suka fito. Sama ta nufa, Bilkisu ma sai ta hau tattare komatsanta domin komawa ciki ta kwanta haka nan...


Saɓanin yanda ta barsa zaune yanzu a kwance ta samesa saman gadon, sai dai ƙafafunsa duka biyu na a ƙasa cikin tttausan slippers ɗinsa bakaƙe da suka sake haska ƙafar tasa. Yaja karamin filo ya saka kansa, amma duk da haka sai da ya tallafe kan da hanun haggunsa. Na damar kuma nakan cikinsa riƙe da hisinil Muslim ɗinta daya kifa saman cikin. Kamar yanda Raudha ta zarga barci ne ya fara figarsa, sai dai tana buɗe ƙofar ya farka dan dama bai nisa ba. Amma sai bai motsa ba harta ƙaraso gabansa taja table dake can gaban sofa ta ɗora basket, duk da bata da tabbacin anan ɗin zaiyi zaman ci.
Sai da ta kai durƙushe sannan tace, “Ga abincin”.
Shiru kamar bai jita ba, harta fara tunanin ko barcin nasa yayi nauyine. Tana shawarar yanda zata tadashi sai taga ya motsa hanunsa, littafin ya ajiye gefensa kafin ya tashi zaune da kyau. Fuskar ta ƙara tsukewa fiye da farko alamar dai yunwa nacin bawan ALLAH da ba wasa (😹🤭😝lol).
“A zuba?”.
Ta tambaya cike da taraddadi. Mai makon ya amsa mata sai ya zuba mata hararar da ta sakata fara buɗe bowl ɗin da suka zubo abincin babu shiri. Ya ɗauke kansa kamar bai lura da yanda hanunta ke ɗan rawa ba. Ji yake ma kamar ya mangareta, ga takaicin kansa ya ishesa. Dan sai yanzu yake ganin kamar ya zubar da ajinsa ne. (Malam shugaba da baka san da ajin ba sai da kaga girki a gabanka🙄😝😂?).
Yana ganin tanata zubawa bai tsaidata ba, sai dai ta zuba mai isarta da take zaton zai cinye sannan ta mike zuwa karamin fridge dake a ɗakin nata ta ɗakko bottle water ta buɗe ta tsiyaya a karamin glass cup data haɗo da shi ta ajiye masa ta miƙe. Shi dai tuni ya fara cin abincinsa ma.
Har ya kammala cin abincin natsuwa na saukar masa bai sakejin motson Raudha mai ƙarfi ba. Shi yama zata kwanciya tayi, sai da ya ɗan waiga ya ganta a inda ya shigo ya same tana cigaba da karatun Al-qur'aninta. Sai dai kuma harga ALLAH barci takeji, amma batasan taya zata kwanta yana a ɗakin ba.
Koda yaji uwar hanjinsa ta ɗauka baiyi yunƙurin barin ɗakin ba, sai da ya sake share kusan mintuna ashirin a zaune yana cigaba da karanta hisunil Muslim ɗinta da ya sake ɗauka. Hammar da yaga ta jera kusan sau uku a jere ya sashi mikewa riƙe da littafin. Ta bishi da kallo dan ko inda take bai kalla ba har yaje ƙofa. sai da ya kama handle ɗin zai murɗa ya furta kalmar “Thanks ”. Tamkar mai ciwon baki.
Ƙincewa komai tai itama, dan Raudha badai zuciya ba. Hakan ya sashi waigota lokacin da

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads