Header Ads
Showing 84001 words to 87000 words out of 204612 words

Chapter 29 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

3098

Ads at the middle of Article

kakkauran numfashi.
“Garin yaya haka ta faru? Dama tanada Asthma?”.
Maimakon Ramadhan ɗin ya bama Anne datai tambayar amsa sai Bilkisu ce ta ɓige da bada amsar. “Wlhy Anne Accident ɗin ya faru a sashen Maa ne. Saboda wani turaren wuta da suka saka. Yanayinsa zaisa dole mai Asthma ya samu attack gaskiya.”
Babu wanda ya sake cewa komai, sai sannu da suka shiga jerama Raudha ɗin. Shiru babu wanda ya biyo bayansu daga sashen gimbiya Su'adah har kusan mintuna arba'in. Hakan ya bama su Anne mamaki, sai dai basuyi magana ba. Pa da yasan ƙiyayyar da matar tasa kema surukar tasu ransane ya ɓaci. sai dai komai baiceba. Ganin Raudha ta dawo normal harta tashi zaune sai ya sake miƙewa ya nufi sashen mahaifiyar tasa somin gaisheta.
Yanayin sallama a falon sukai shiru daga taruwar zaman zagin Raudha da sukai, Lubnah na sake tabbatar musu mayyace ai. Tunda gashi ansa tsakin kuka a wuta ta kasa zama. Basma ce kawai babu dan tana ɗaki tamayi barci batasan bidirin da akeyi ba.
Komai baice musu ba, duk da baiji akanmi suke ƙus-ƙus ɗin ba ya wuce bedroom ɗin mahaifiyar tasu. Itama acan tararwa yay tana waya da Adda Asmah tana sanar mata sun tabbatar Raudha mayyace yau. Sallamar tasa baisa ta dakata da wayarta ba sai da ta kammala. Sama-sama ta amsa masa gaisuwarsa kafin ta rufesa da masifa, tare da jadada masa su Lubnah zasu dawo zama tare da su domin su saka mata ido akan Raudha karta lashe mata shi dan yau ta sake tabbatar da Raudha ɗin mayya ce. Tunda gashi nan ta saka tsakin kuka a wuta Raudha ta kasa zama a sashenta. Komai baice da itaba har tayi ta gama. Ya bata haƙuri sannan yay mata sallama ya fito.


Koda ya dawo sashen su Anne bai zauna ba yace Raudha ta tashi su wuce. Sabuwar gasassun kajin da Anne tasa aka gasa aka kawo musu tare da fura da farfesun naman kai da shugaban ƙasa Ramadhan yace a saka masa a cooler zaije da shi.
Har bakin mota Bilkisu da Anne sukai mata rakiya, itako tanata musu godiya. Shiru motar babu wanda yake ko ƙwaƙwaran motsi har sukai ƴar tafiya. Shugaban ƙasa Ramadhan dake lafe jikin kujera idanunsa a lumshe yace, “Dakata anan”.
Gangarawa drivern yay gefen titi kaɗan, yayinda Raudha ta ɗan dubesa a sace dan catake barcima yakeyi. “Malama bada kuɗin nawa kilishin”.
Sam Raudha batai tunanin da ita yake ba, amma sai ta ɗan juyo ta dubesa. Dai-dai ya buɗe nasa idanun shima da ɗan karkato kansa gefenta suka haɗa ido.
“Kina zaton zaki sayama kowa ne ni na haƙura”.
Ƙasa tai da kanta mamakinsa na neman hakalata. sai kuma tai saurin cewa, “To ai ban fito da kuɗi ba ALLAH”.
Kamar bazai tanka ba, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ya kwantar yana lumshe ido kamar yanda yake da. “Ba damuwa zan ara miki, idan munje kiban abina”.
Yanzun ma dai sai da ta sake kallonsa saboda al'ajab. Bata ida narkewa da al'amrin nasa ba sai da taga ya miƙama driver atm ɗinsa batare da ya buɗe idon nasa ba.
“Na nawa zaki siyamin?”.
(Ya ALLAHU, mutumin nan so yake ya kasheni). Raudha ta faɗa a cikin zuciya. Kafin a fili cikin fisgar numfashi tace na “10k”.
Yasan driver yaji kuɗin, dan haka ya faɗa masa pin ɗin atm ɗin har yanzu yana a yanda yake. Shiru motar ta sake ɗauka Raudha nata juya al'amarin a ranta har driver ya dawo da kilishin.


Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gidan, kamar yanda suka fita ta barauniyar hanya tanan suka dawo. Raudha ce ta amshi ledar kilishin, shi kuma ya ɗauki saƙon Anne, duk da driver yaso dauka amma ya hanashi. Suma securitys ɗin sun gwada amsa ya hana nan ma. Suna shigowa ya miƙa mata hannu alamar ta bashi. Babu musu ta miƙa masa. Ya ajiye mata na Annen. Ciki-ciki yace, “Raba ki ɗau naki, ki kuma kawomin kuɗina”.
“Na bar maka”.
Ta faɗa kanta a ƙasa ganin zai wuce riƙe da kilishin da aka sakata saya dole.
“Oh nice”.
Ya faɗa a daƙile yana dawowa baya ya ɗauka kulolin biyu. Sai da yaje gab da corridor ɗin ɗakinsa ya sake faɗin, “Wannan ƙyautar bashike nufin zan yafe kuɗi na ba fa”.
Karon farko da lamrin nasa ya sakata sakin murmushi, ta ɗan girgiza kai tana nufar nata hanyar ɗakin itama. Tana shiga batai ƙasa a gwiwa ba ta ɗakko sauran kuɗin da suka rage mata. 10k ta irga ta fito. Karo na farko a zamanta gidan ta nufi corridor ɗin da bedrooms nasa suke. Rasa gane wanda yake a ciki tayi, taita canki canka. Daga ƙarshe dai ta yanke shawarar yin knocking ɗin na ƙarshen. Tayi knocking kusan sau uku babu alamar akwai mutum, har zata juya na kusa da shi sai kuma aka buɗe ƙofar.
Saurin yin ƙasa tai da kanta gabanta na faɗuwa ganin da gashi sai guntun towel. Jikinta naɗan karkarwa da tsuma ta miƙa masa kuɗin. Komai baice mata ba ya amshe abinsa ya maida ƙofar ya rufe. Da sassarfa tabaro corridor ɗin zuwa nata bedroom ɗin, tana shigowa ta zube a gado dan jitake kamar numfashinta na sizing..........✍



*_Ku garzaya AREWABOOKS ta link ɗin dake sama farkon page, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*






*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*




*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_


*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_


*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_


*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_


*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_






Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k




*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_09032345899_*




*KATIN MTN*👇👇


09166221261
__________________


*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*






Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F




*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼


+227 95 16 61 77






*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*


_____________________




*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*




Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.




*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3




Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*




*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*


+234 903 177 4742




_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*














*_BAƘAR INUWA👉🏻AREWABOOKS👇🏻_*




https://arewabooks.com/chapter?id=62ac32dac3c5aa93405acd94








*_Episode 31_*




..........*_WASHE GARI_* koda Raudha ta farka a barcin safe data koma ta samu Ramadhan ya wuce. Cikin mamaki takebin kulolin jiya da Anne ta zubo musu nama a ciki da kallo. Ta miƙe da ƙyar tana cire hijjabin sallarta dan akan sallaya barcin ya kwasheta tana azkar. Kulolin ta nufa. Ya cinye farfesun naman kan tas sai ƙasusuwa. Kazar kuma kusan ɗaya da kwata. Sosai mamakin hakan ya rufe Raudha, shiko wane irin kuren nama ne haka? Sai kace ya haɗa iri da mayu (😱😝 Raudha ta rama bani ba). Ta ɗan girgiza kanta zuciyarta na raya mata da alama dai ba shikaɗai bane akwai aljanun cin nama tare da shi. Da wannan tunanin ta nufi toilet. Wanka tayo da brush, bayan ta fito ta kimtsa jikinta da ɗakin. Itama kular sauran naman ta ɗauka da nufin ci duk da yayi sanyi kaɗan sai taci karo da takarda guntuwa da ATM card. Ɗauka tai ta ƙarasa kan sofa sannan ta buɗe takardan. Pin ɗin atm ɗinne a farko. Sai gajeren rubutu da bai wuce words goma sha biyu ba. *_(Anne zata aiko da sabuwar mai aiki, tare da masu zuwa miki yawo)_*. Shike nan abinda ke jiki, sai wani ɗan zane kamar emoji data gagara gane ma'anarsa.
Saƙon ta dinga maimaitawa a zuciyarta, haka kawai take jinsa da girma. Tasan dai Anne bazata kawo wadda zata cuta mata ba, sai waɗanda zasu zo mata yawon ne take ɗar-ɗar, dan inhar yaran gidan ne akwai matsala kenan.


Duk yanda taso samun nutsuwa ta gagareta, dan hankalinta bai tashi ƙololuwa ba sai dai baƙin nata suka iso har su biyar. Aina'u, Lubnah, Basma, Bilkisu, Muneera. Ta gane Lubnah ta kuma gane Aina'u. hakama Basma da Bilkisu da sukazo cike da murna suka rungumeta.. Su Aina kam suna mata wani kallone kamar trash. Dan Lubnah harda faɗin, “Kurwarmu dai ɗacine da ita, kar aga mun dawo kusa ai tunanin nama yazo. Wlhy mutum yace zaici ya taɓoma kansa mutuwa ne kawai”.
“Tuna mata dai”. Cewar Muneera.
Komai Raudha batace musu ba. Sai gaishesu da tayi. Duk da basu amsa mata ba sai ta danne. Falon tsakkiya ta nufa inda tacema mama tambaya a gyara musu ɗakunan ciki. Mama Tambaya tai ɗan jimm kafin tace, “Amma ranki ya daɗe kodai ɗakunan falon farko zaifi, dan falon tsakkiya dana karshe da upstairs ke ce kawai keda hurumin yin huɗɗa da shi. Sai ko idan kunso kai baƙi masu muhimmanci ”.
Murmushi Raudha tayi, “Mama waɗan nan ma ai sunada muhimmanci, dukansu ƙannen mai gidan ne”. Daga haka ta juya ta koma ciki.
Sai dai kuma mi, koda aka gyara ɗakunan tsakkiyar sai su Lubnah sukace bazasu zauna anan ba sama suke so. Kobi takan Raudha da roƙon da Basma da bily ke musu basuyi ba suka nufi saman. Corridor ɗin ɗakinta suka nufa, duk bedrooms ɗin sai da suka buɗesu kowa ya zaɓi ɗai-ɗai. Da Aina ma na Raudha ɗin tace tana so, sai da Lubnah ta jata gefe ta raɗa mata wani abu a kunne sannan ta canja dana kusa da ita. Dama 4bedrooms ne, dan haka su uku kowa ta ɗauka guda.
Mama Tambaya zatai magana Raudha ta hanata, dole tai shiru. Koda Basma ta kira gimbiya Su'adah ta sanar mata sai ta hau banka mata zagi akan ina ruwanta, tunda can ɗin sukeso basai a barsu ba, daga ƙarshe taja mata gargaɗinta bayan ita takira wani ta sanar masa sai taci ubanta. Kuka sosai Raudha ta shiga ɗaki tayi, sai dai a gabansu bata yarda murmushi ya bar fuskarta ba.
Abinci da kansu suka bama kuku umarnin abinda za'a dafama kowannensu, Raudha dai batai ko tari ba, hasalima tunda ta shige bata fitoba sai da Mama Ladi ta iso. itace Anne ta aiko ta zauna da ita. Tayi hakane kuma domin ta dinga koyama Raudha abubuwa masu muhimmanci dan ta kula ba komai Raudha ta iyaba kasancewar mu ƴaƴan talakawa munada ƙarancin wayewar wasu abubuwan irin na masu hannu da shuni. A wahalar rayuwa da ilimin zaman cikinta kuwa duk da Raudha nada ƙarancin shekaru tanada wayo saboda irin rayuwar data tashi a ciki.
Mama Ladi mace ce wayayya dan tayi iliminta na addini dana zamani gwargwadon iko. Ƙaddarar rayuwa da jarabawar iska yasa bata zaman aure. Tayi aure yafi sau uku mazan na rasuwa. Wannan yasa ake gudunta a garin Taura. Harta kai ko gittawa tai ta waje sai a dinga gudu. Abin ya isheta ta tattara kayanta zata gudu a garin tsautsayi yasa Alhaji Basheer Taura (Pa) ya bugeta da mota lokacin yazo Taura ɗin. Taji ciwo sosai, dan haka ya kaita asibiti, bayan tayi jiyya ta warke sarai yaji matsalarta. Daga nan ya kaita family house ɗinsu na Taura ta zama shugabar ma'aikatan gidan tana kula da komai da kowa. Amanarta da iya mu'amula yasa suke ƙyautata mata sosai. Wanda ma bai sani ba yakan ɗauka ƴar uwarsuce a yanzun.
Maimakon sashen ma'aikatan gidan a falon farko Raudha tasa aka bata ɗaki. Hakan yasa su Lubnah basu san da zuwan mama Ladi gidan ba. Duk da ba wani damuwa sukai da ita ko a Taura ɗin ba. Hasalima yanda suke ƙyarar masu aiki da hantararsu haka sukema mama ladi itama


★Ranar da su Basma sukazo government house gimbiya Su'adah ta nufi masarautasu dake a jihar Bina. A can ta samu Adda Asmah na jiranta, dan dama haɗuwar tasu akan Raudha ce dai da suke kira karamar alhaki ta kuma zame musu damuwar zukata. Bayan sun samu shiga sashen mai-martaba suka gaisheshi sai suka ɗan shiga sashen tsohuwar kakarsu dake fama da jiyya kusan shekara bakwai kenan. Sun duba jikinta itama kafin su koma sashen fulani. Dan a tsarinsu sauran matan sarki basu ishesu kallo ba balle gaisuwa. Shiyyasa sam babu haɗin kai tsakanin yaran gidan tunda suna kallon su gimbiya Su'adah dake amsa sunan manya basu mutunta iyayensu da jansu a jiki balle su ƙanana.
A babban falon kusa da fadar fulani suka yada zango, bayan sunci sun sha gimbiya Su'adah ta labarta musu yanda sukai da Raudha akan turaren tsakin kuka.
Adda Asmah taja tsaki cikin ƙyaɓe fusaka da takaici take faɗin, “Kuji makirar yarinya, to ai tasha a no-no ke kuwa ai dole. Jinin karuwar gogaggun duniya ai dole tayi makirci irin haka wai Asthma ta tashi..”
“Humm ki bari kawai Adda. Babban abinda ya ban takaici da ƙonan zuciya yakema bisa kan sake ƙonamin har yanzu wai ko kunyar idona Ramadhan bai gani ba ya ɗauka yarinyarnan cikin rawar jiki ya fita da ita saboda shi fitsararrene...”
“Karkiga laifinsa Su'adah. Ke kina ganin zasu barsa hakane babu wani ƙulli? Kinsan kuwa wacece hajiyar birni? Gogaggar karuwa uwar karuwan manyan ƙasar nan. Yo uwar karuwan manyan ƙasa mana, tunda kuwa ƴaƴanta harda uwar yarinyar sune hajarta a wajen manyan ƙasar. Dan an tabbatarmin harda aurensu bin maza sukeyi”.
“Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Wlhy Adda sake firgitani kikeyi”. Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin nuna razana da tashin hankali.
Kafin Adda Asmah ta sake cewa wani abu Fulani dake waya tun dazun ta ajiye wayar tana maida hankalinta garesu. “Ita hajiyar birnin har wacece ita, har mi akai akayita. Ai wlhy lokacin da kuka kawomin labarin tushen yarinyar ma sam ban kawo Hajiya Ɗahare bace hajiyar birnin, da ko aurenki zai mutu Su'adah bazan yarda da wannan kwamcalar haɗin ba. Dan nasan baku manta wata shegiyar karuwa da mukaita kicimillin raba mai-martaba da ita ba shekara ashirin da ɗaya kenan”.
Cikin zaro idanu waje su duka har haɗa baki suke wajen faɗin, “Ammy wai kina nufin matsiyaciyarnan data like masa a loss lokacin ana shirye-shiryen basa mulki”.
“Ƙwarai kuwa ita fa, to itace hajiyar birni kakar wannan shegiyar yarinyar da aka mannama Ramadhan.”
Sosai tashin hankali ya bayyana a garesu, dan su ɗin shaidane akan wahalar da iyayensu mata musamman mahifiyarsu taci a wancan lokacin. Ko randa kakansu ya rasu mutane nata raɗeraɗin da karuwa mahifinsu yazo da ga loss. Sakamakon acan yake aiki. Ba kowa bane kuma face hajiyar birni. Bayan an bashi sarauta ma tasha kawo masa ziyara a ɓoye kamar yanda sukeji, harma ya furta cewar zai aureta shaƙiƙan dattijan masarauta sukai masa kacaca, aka kuma saka masa ido matuƙa har sai da aka rabashi da ita.
(Kowa yasan mahaifinsu mai-martaba na yanzu mutum ne da dama bayajin magana tun ƙuruciya, dan ita kanta fulani dake wannan babbotan adai rufe rufau, akwai babban akasin daya faru tsakaninta da mai-martaba ɗin tun tana ss2 secondary, bayyanar abin kunyar daya ƙunsa mata yasa iyayenta saurin zubar da shi aka rurrufe akai musu aure ya wuce da ita ƙasar waje sukaci gaba da karatu a can. Dan dama shi acan ɗin yake, wani zuwa hutu da yay ya ganta daga haka yayta jan ra'ayinta da soyayya har ya ƙunsa mata ciki. Gashi kuma ƴar uwarsa ce, dan kuwa ɗiyace ga ƙanwar mai martaba mahaifinsa kenan, kuma ƴar waziri ta wancan lokacin. Amma sai gashi yau duk sun manta da waɗan nan ta murje ido tana faɗin munin wani harda nuna ƙyamarsa.
Wannan tunani na Fulani akan hajiyar birni kakar Raudha ya sake tada hankalin su gimbiya Su'adah. Duk da dai ita Addah Asmah tanayin komai ne dan ƴarta Aina, gefe kuma ga tsananin hassadar ƴar uwarta da take fama da ita shekaru aru-aru na finta da mijin nunawa sa'a. Dan kuwa Taura family sunfi family ɗin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads