Header Ads
Showing 168001 words to 171000 words out of 204612 words

Chapter 57 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

3102

Ads at the middle of Article

ko gaisuwar da Bilkisu ke masa bai amsa ba. Ƙofar ya maida ya rufe tare da jingina a jikinta lokcin da ya iso bedroom ɗin nasa. Ya ja ajiyar zuciya da sauke nanauyan numfashi idanunsa har sun kaɗa sunyi jajur. Ya jima a wajen tsaye kafin yaja kafafunsa da ƙyar zuwa toilet, agogon kawai ya cire ya sakarma kansa shower. Sai da yay sharkaf daga shi har kayan dake jikinsa sannan ya ragesu yay wanka....


Raudha da dama a cikin yanayi. dauriya take zaune a wajen ta miƙe da gudu tabar wajen hanunta toshe da bakinta. Da sauri Bilkisu ta bita har cikin toilet data shiga. Amai ta shiga kwarawa tamkar zata amayar da hanjin cikinta. Hankalin Bilkisu ya sake ɗagawa matuƙa ta riƙe Raudha. Sai da komai data ɗanci ya fita tas sannan aka samu lafiya. Bilkisu ta tamaka mata ta gyara jikinta da wajen suka fito tana jera mata sannu.
Cikin sauke numfashi a wahale tana kaiwa kwance ta ce, “Kai aunty B ƙamshin turare nan na Yaya babu daɗi”.
Sosai Bilkisu ta zaro idanu waje, sai kuma tace, “Kutt Aunty Raudha ƙamshin _Boucheron_ ɗinne baida daɗi? Anya kuwa kin shaka dai-dai?”.
“Ni wlhy lafiya lau na shaƙa, kuma dai tun yashe muke zaune a falon na ƙamshin komai bai dameni ba sai daya shigo ne ƙamshin turaren nan mai kama da ka.....”
Da sauri Bilkisu ta ruƙe mata hannu tana dariya, “Uhmm to lallai Taura grandchild bai zo da wasa ba.”
Sam Raudha ba wani fahimtarta tai ba. Bakuma tabuƙaci ba'asin mganar ba tama lumshe ido dan barci ke ɗan figarta ga kanta daya fara ciwo.


*_TAURA HOUSE_*


Cikin matuƙar bayyanar tashin hankali Ramadhan ya ɗago yana duban Bappi da ya gama masa jawabi. A take idonsa ya rufe yama manta da wanda yake tare.
“Gaskiya bazai yuwuba Bappi, duk ma wada yake tunanin sharɗanta hakan ya janye dan ba yarda zanyi ba. Tayama kamar ni za'ace a ɗaura aurena a sirri sai kace wani funafunci? Na muku biyayya na amince da zabinku kukai yanda kuke so nima dole a barni nai yanda nake so akan nawa zaɓin. Sannan maganar events banajin akwai ɗaya da za'a janye a ciki, ba sai kun dinga nuna hassadarku da adawa aka dangin mahaifiyata zan san kun isa da ni b.....”
Ji kake “tauuuu!!” Wani bazafaren mari ya sauka a saman kuncin Ramadhan har sai da ya kifa kamar zai faɗi. Pa da yake a fusace zai ƙara masa Bappi ya dakatar da shi. “No Basheer barsa barsa. Kai Ramadhan mu kake faɗama muna adawa da hassada da dangin uwarka!!”.
Har yanzu hanunsa a saman kuncinsa dan da gaske marin yay matuƙar ratashi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake birkicewa gaba ɗaya, idanunsa suka rufe ruf. “Idan ba hassada ba a gayamin mi kuke musu? Kun rabani da su komai sai ku, tun ina 2years a rabani da uwata tayi kawaici ta bar muku amma hakan baisa kunga haƙurinta da kawaicinta ba. To wlhy daga yau ku sani ta ƙare, idan kuma kunce a'a to muzuba mu gani!!”.
Ya ƙare maganar cikin ƙaraji da nufar hanyar fita.
Da sauri Pa ya miƙe cikin wani irin fushi yay kansa shima. Sai da Bappi yay azamar riƙo hanunsa yana girgiza masa kai. Duk yanda Pa yaso yin magana Bappi ya hana shi, ganin yanda jikinsama ke rawa sai kawai ya rungumesa yana shafa bayansa murmushi na subuce masa na tsantsar zafin da yakeji a ransa. Da wahala kaga fushin Bappi. Mutum ne mai yawan fara'a da dattako, akoda yaushe fuskarsa ɗauke take da murmushi. Duk abinda kaga faɗansa akai an ƙuresane.


*_GOVERNMENT HOUSE_*


Baƙaramin faɗuwa gaban Raudha dake zaune a gado tana karatu yayi ba. Babu haske mai yawa a ɗakin. ta zabi tai zaman karatu ne kafin lokacin da zata tashi ganawa da UBANGIJI ne. Ta zaro manyan idanunta akan Ramadhan daya shigo a tsananin fusace. “Innalillahi.....” har ƙarshe take ambata a jajjere harya iso inda take, wata irin muguwar damƙa yayma gashinta dake daure a tsakkiyar kai da hanunsa....
“K!! Har kin isa saboda aurenki a hanani yin yanda nakeso akan auren wadda zanyi? Wacece ke? Mikika taka?!.. Wato kinje kin kai munafunci garesu dansu hanani, to ai in gaya miki babu ubanda ya isa. Yau zan tabbatar miki ke ɗin ƙaramar mara kunyace kuwa wlhy...”
Kuka sosai Raudha keji jikinta na tsananin rawa. Ta shiga yarfa hannayenta duka biyu kuka mai ƙarfi na ƙwace mata ganin yana kunce belt ɗin wandon jeans ɗin jikinsa. Abu biyu ta kawo a ranta. Duka ko abinda yay mata ranar, dan haka tai yun ƙurin ceto rayuwarta sai dai hakan ya gagara. Dan tuni ya damƙota ya jefa saman gadon har sai da bayanta ya amsa dan azaba.......


★★★


Ihun Raudha ya matukar tada hankalin Bilkisu da ke ɗaki har barci ya fara daukarta. Ta fito a waje zuwa ɗakin sai dai ta samesa a kulle. Bugawa ta shigayi tana kiran sunan Raudha. Sai dai wata shegiyan ashariya da batasan Yayan nasu ya iyaba sai yau ya mulmulo mata daga ciki. Ai babu shiri tabar wajen a guje. Sai dai koda ta koma ɗaki wayar Anne ta kira. Tana dagawa ta fashe mata da kuka da fara zayyana mata abinda ta sani.


Sosai hankalin Anne da Bappi ya tashi, dan sun san ba kamar yanda Bilkisun ke tunanin Ramadhan dukan Raudha yake ba. Su sun san illolin daya dingama Amnah idan irin wannan ɓacin ran mai tsanani ya riskesa. sai dai suna ƙoƙarin rufe hakan ga kanensa idan ka cire Mardiyya da Safina dakan san wasu a wani lokutan.
Hankali a tashe tsoffi nan suka baro gida a daren nan tare da Dr Hauwa da suka taso itama ta waya suka nufo government house. Dan Dr Hauwa ce ma da kanta taja motar.


Lokacin da suka iso Ramadhan ya riga ya gama illata Raudha har jini ya ɓalle mata. Tunda ya fito a hargitse Bilkisu na son shiga tanajin tsoro. A durkushe suka sameta bakin ƙofar tana kuka. Tana ganinsu ta faɗa jikin Anne ta rungumeta.
“Anne ya kasheta, wlhy ya kasheta Anne!!”.
A tsawace Bappi yace, “Yana ina!?”.
Cikin kuka Bilkisu ta sanar masa ya koma dakinsa. Hakan ya bama Anne da Dr Hauwa damar shiga. Bappi kuma ya tisa keyar Bilkisu ta nuna masa bedroom ɗin Ramadhan.


Hankalin Dr Hauwa da Anne ya tashi a yanayin da suka sami Raudha, dan haka babu wani kace nace Dr Hauwa ta fara ƙoƙarin ganin ta tsaida jinin. Tsahon lokaci ta ɗauka da taimakon Anne dake fama da tsufanta suka samu nasarar hakan.
“Anne bazai yuwu mu barta anan ba. Inaga muje da ita can wajenki dan tana buƙatar kulawa mai tsanani yarinyar nan a wannan gaɓar tunda Alhmdllhi cikin dake jikin nata mun samu ya tsaya. Da dai anyi dilay kam da labarin da ake ba wannan bane”.
Wasu hawayene masu sanyi suka sakko akan fuskar Anne. Farin ciki da cikin Raudha, da damuwar halin da jikanta yake sakamakon son zuciyar mahaifiyarsa.


A can kuwa ɗakin Ramadhan shigar Bappi tayi dai-dai da fitowarsa wanka, ya sauke towel ɗin da yake goge fusakarsa zuwa suma kawai yaji saukar mari haggu da dama. Gaba ɗaya wutar kansa ta ɗauke ganin wanda ya maresan. Bappi, abinda bai taɓa faruwa ba ko a tarihin ƙuruciya. Dan ko laifi yayi yana yaro sai dai Anne ko Pa su dakesa amma ba Bappi ba. A karshe ma Bappin ke komawa lallashinsa da masa nasiha. Amma sai gashi yau da girmansa. Shekara dai-ɗai har 36 a duniya kakan nasa ya rufe ido ya yarfata masa maruka har biyu bayan wanda Pa ya masa ɗazun....
“Ramadhan ka kiyayi haduwata da kai wlhy!!”. Bappi ya faɗa cikin gargaɗi da ke nuna tabbatarwa. Kafin yay wani yunkuri kuma ya juya yay ficewarsa.........✍




*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*






*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*




*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_


*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_


*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_


*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_


*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_






Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k




*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_09032345899_*




*KATIN MTN*👇👇


09166221261
__________________


*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*






Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F




*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼


+227 95 16 61 77






*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*


_____________________




*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*




Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻


Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.


_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_




*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.




*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3




Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*




*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*


+234 903 177 4742




_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*






*_Typing📲_*














*_Episode. 60_*




.........*_TAURA HOUSE_*


Tunda suka baro government house a sirrance da Raudha kai tsaye Taura house suka nufo. sai dai anan ɗin ma dai babu wanda yasan da dawowar tasu kamar yanda kowa bai san da fitarsu ba. Sake dukufa Dr Hauwa tai akan Raudha har sai da ta tabbatar komai ya daidaita. Abin tausayi har ɗinki akai mata saboda bidirin da Ramadhan yay a jikinta. Hakan ya sake kona zuciyar Bappi da Anne sai dai babu wanda ya iya cewa komai har Dr Hauwa ta kammala aikinta ta wuce.
Barci Raudha take saboda allurar barcin da Dr Hauwa tai mata. Dan haka Bilkisu ta zauna ta zayyanema Anne komai data sani har wanda Raudha ma bata san ta sani ɗin ba. Anne harda hawaye tausayin Raudha mai tsanani na cin zuciyarta. Koba komai sune suka jefata a wannan masifar. Maybe dasun barta ta aura dai-dai da ita da duk hakan bai faruba. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Sannan kuma babu mai sawa ko hanawa daga abinda yazo a littafin ƙaddarar wani bawa koda yana kalon kansa matsayin SILA.


*_WASHE GARI_*

Raudha ta jima bata farka ba har kusan tara, koda ta farka ɗin kuma Anne fidda kunya tai ta taimaka mata sosai kodan ɗinkin da akai mata. Ga Dr Hauwa ta tabbatar musu kar ai wasa da wani motsin Raudha mai karfi saboda cikinta a ɗofane yake. Hasalima bed rest shi tafi bukata fiye da komai a yanzun.
Tabbas abu biyu da Raudha tayi ya matukar birge Anne da Bappi. Na farko tambayar duniya sun mata akan abinda ke tsakaninta da Ramadhan ta keƙashe ƙasa ta dage akan babu komai. Tushen abinda ya faru tsakaninta da shi a jiya harya doke ta (dan duka suka danganta abun saboda alkunya da kawaici irin nasu) amma sai Raudha tace wai faɗuwa tai a toilet. Batasan su da idonsu sukaje sukaga halin da take a ciki ba. (Saboda sun ɓoye mata cewar Bilkisu ce ta kaita asibiti suma acan suka amso ta). Na uku tunda ta tashi babu wanda yaga ko ɗigon hawayenta alamar ta dake, wannan ya sakama Anne ƙwarin gwiwar cewar lokaci yayi da zatai training ɗin Raudha a bigiren da sai Gimbiya Su'adah da shaiɗanunta sunyi dana sani. Ramadhan kuwa zai matuƙar gane kuskurensa, ba ita zata hukuntashi ba Raudha ce da kanta zata hukunta shi.


Hhhhh ashe akwai sabon show😋😉🤣.


*____★____★_____★_____★_____*


Tsahon kwanaki uku Raudha na a Taura house babu wanda ya sani sai Bilkisu da Pa da su Anne. Koda Gimbiya Su'adah taga Bilkisu bataji komai ba tunda tasan dama tana shirin dawowa gida ai. Zuwa yau baƙi sun fara isowa daga masarautar su gimbiya Su'adah. Hakama a bangaren sauran matan gidan tunda kowa zai aurar da ɗa. Daga Taura ma dai wasu sun iso sai dai maza ne.
Babu wanda ya sake jin labarin Ramadhan babu kuma wanda ya bibiyesa, a kwanaki ukun nan ma ko a labarai sai dai kaji ance Shugaban kasa Ramadhan ya kaddamar da kaza da yawun wane. Amma shi ko sau ɗaya ba'a nunasa ba sai a yau da kowa yasan za'a tafi hutu na ƙarshen shekara da Christmas. Kuma kakakin shugaban ƙasa ya sanar a Taura house shugaban ƙasa zaiyi hutun nasa baki daya.
Hankalin Adda Asmah ya tashi matuka, musamman data kira bokanta yace sam karta yarda. Ita da suka gama cin burin kai Aynah government house kai tsaya ya Ramadhan ɗin zai musu haka, ya tabbatar mata ajiye Aynah a Taura house bazai taɓa haifar musu ɗa mai ido ba. Garama tayi duk yanda za'ai ta gyara barnar. Zuwa dare kuma tazo tare da Aynah zai mata wankan magani na ƙarshe da shine sirrin mallakar Ramadhan da duk ma wanda zai raɓesa, zai koma baijin magana ko umarnin kowa sai nata ita kaɗai Aina'u.
A rikice tai kiran Number Gimbuya Su'adah. Ita kanta gimbiya Su'adah ranta ya baci dan yau bata maida hankali akan television ba balle tasan da labarin. Tana can suna tafka rigima da Pa akan kofa dinner sai sunyi har guda uku idan ance sauran an hanasu. Shi kuma yace isar da bataiba kenan.
Ramadhan ta shiga nema, dan rabonta da shi yau kwana uku kenan tun randa ta kunna zuciyarsa akan kiran daya sanar mata su Bappi sun masa. Maimakon hankalinta ya tashi matsayinta na uwa ta nemesa sai ta share da cewar yana lafiya shiyyasa ko kuma aikin office ne ya rikesa.
A lokacin kwance yake yana barci, dan tunda aka baro Raudha daga gidan ya tsinta kansa a wani irin yanayi mai matukar wahalar fassara a garesa. Ya rasa mike masa daɗi mi kuma zai kama. Ransane a ɓace? Ko damuwa da halin daya jefa ƴar mutane? Kokuwa halin da ke shirin riskarsa na auren wadda shi kansa har yanzu baisan dalilin da yasa yake mata wannan mahaikacin son ba. Bisa lallabawar cos yake fita office. Sai dai baya wani jimawa yake dawowa gida. Kuma kullum ya shigo sai yaje ɗakin Raudha da mama ladi bata gajiya da gyarawa. Hatta jinin da Raudha ta zubar a wancan ranar idan bama faɗa maka akaiba bazaka sani ba. Yakanje ya kwanta a saman gadonta. Sai dai baya haɗa mintuna biyu kansa zai shiga sarawa da karfi har sai ya fito ya koma nasa.
Kunnawar da Ginbiya Su'adah tai masa yau ma ya sakashi tashi cike da fusata. Yay azamar dafe kansa dake juya masa da karfi. Sai kuma ya mike yana kallon agogo. Ƙarfe kusan sha ɗaya na dare. Amma tsabar yanda yake jin zuciyarsa tuni ya fice cikin ɓadda kama dan bazai iya jira sai gobe da zai huce Taura house ɗin ba ma, yanda yake komai saika ɗauka ana controling nashi da remote ne, dukya birkice, baya gane komai sai abinda su gimbiya Su'adah sukace yayi. Maimakon ma ko a motane yay fitar sirrin kamar yanda yakeyi, sai kawai ya fice da ƙafa ta karamin gate da taimakon odilan ɗinsa da baida ikon hanashi yin hakan saboda akwana biyun nan sam baya gane kan shugaban ƙasa, baya son yace wani abu kuma ga wani game da hakan saboda gargaɗi da Ramadhan yaja masa mai ƙarfi akan yanda yake fitar sirri inhar ya bari wani ya sani bayan shi duk hukuncin daya zartar a kansa yay kuka da kansa kawai. Cab ya tare sai taura house.

A dai-dai lokacin da Ramadhan ke nufar Taura house Adda Asmah ce da Aynah sun dawo daga gidan bokanta anyo mata wankan maganin mallaka. Sam batai tunanin haɗuwa da Ramadhan ba, shiyyasa ta yanke shawarar biyawa ta Taura House takai maganin da bokan ya bata akan gimbiya Su'ada tai turare da shi matsayin na rufa idon su Bappi akan events ɗin da suke sonyi. Sai dai a zahirin gaskiya ba hakan bane. Na rabata da Ramadhan ne baki ɗaya yanda zai koma karƙashin ikon ita Addah Asmah ɗin.
Kusan a tare Ramadhan da su Addah Asmah suka iso Taura house. Sai dai shi ya rigasu shigowa saboda an tsaya buɗe musu

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads