Showing 63001 words to 66000 words out of 204612 words
Chapter 22 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt
tunanin za'a yanke musu jin daɗin rayuwar ƴammatanci ko samartaka. Shiyyasa suke ganin masu aurar da yara 17years zuwa 20 tamkar ganganci sukai🤧).
*_______________________*
*_BINGO CITY_*
Kamar yanda aka nuna ɗaurin auren shugaban ƙasa Ramadhan live a gidajen tv haka aka nuna tahowar amarya da isowarta bingo ma. Inda duk da ɗunbin mutanen nan dake cike da Taura house da wanda sukayo ma amarya rakiya hakan bai hana Anne da ke fama da tsufanta ba fitowa tarbar amarya ita da su yafendo. Fulani na zaune tare da su suka fito amma batako motsa ba. Dan tona irin baƙin cikin da suke ciki game da auren nan ita da Asmah da gimbiya Su'adah ɓata lokacine. Abinda kawai suka sani shine sun tanadama Raudha bama-baman bala'in da sai ta gudu gidansu da ƙafafunta. Dan shi kansa Ramadhan ɗin jiya ya sha masifarsu saboda yace suyi haƙuri shi bazai iya bijirema Pa da Bappi akan maganar auren nan ba.
Aiko sukai masa ca gimbiya Su'adah harda kuka wai Anne ta asirce mata shi bayajin maganarta baijin ta mahaifiyarta da ƴan uwanta. Shi dai bai sake ce musu komai ba, da ga ƙarshe ma kiran wayarsa da akaine tai bailing sa ya samu ya gudu musu. Har zuwa yanzu kuma basu sake ganinsa ba, dan koda ya baro Hutawa kai tsaye wajen meeting ɗin da zasuyi da shugabannin jam'iyya na jihohi ya wuce.
Sosai ahalin Raudha sunji daɗin tarbar da akai musu. Tun daga kan shimfiɗar fuska har zuwa ta wajen zama da abinci dana sha koma Alhmdllhi. Mafi yawancinsu kuma ba ƙaramin rikicewa sukai da ƙaton mansion ɗin na Taura ba. Har takai wasunsu ma sun gagara bakin magana.
Babu wani event a yau, dan Bappi ba mai son yawan bidi'oi bane, shiyyasa da wahala kaga anyi taron biki a gidan ana wannan events ɗin na almubazaranci da dukiya, komai yana tafiyane gwargwado, sai abinda ya zama wajibi kamar abinci wannan kam har sai kaci nama ka gaji duk haɗamarka da zura...😜
WASHE GARI ma babu wanda yaga idon ango har kusan azhur, dan jiya bai dawo gidan ba sai kusan 3am. Hakan ya sakashi maƙalewa a part ɗinsa yaki fitowa. Ko sallar asuba a gida yayi saboda makara da yay. Masu kiɗan ƙwarya sunyi wasa daga safe zuwa azhar ɗin anan cikin gida. Abin kuma ya ƙayatar da mutane dan kowa yayi farin ciki. Inda amarya tasha ƙyau harta gaji. Dan nasiha da lallashin da Anne tai mata a daren jiya yasaka mata nutsuwa ta daure tabar kuka kasancewar a ɗakin Anne ta kwana tare da ita. Takoji daɗin kasancewa da tsohuwar, tare da ƙarajin ƙaunarta a zuciya da ɓargo.
Ansha ɗinkuna an kuma sha liƙi, abun mamaki harda gimbiya Su'adah da Adda Asmah a masu liƙi, dan Fulani ce ta basu shawarar suma suje suyi tunda su Hajiya Mufida sunyi. Karta yarda kishiyoyi su fita nuna iyayi ga auren ɗanta. Irin wannan sakacin tayi tun farko har Anne ta mallake mata shi a matsayinta na kaka.
Adda Asmah ta rungume Raudha da kanta ke a ƙasa bayan ta gama mata ruwan ƴan dubu-dubu. “Kinci nasarar shigowa cikin zuri'ar Taura ƴar *_KARUWAI_*”.
A bala'in firgice da rawar jiki Raudha taso janye jikinta. Sai dai Adda Asma ta sake matse a cikin nata jikin kasancewarta mace mai ƙiba. A kausashe ta cigaba da faɗin, “Sai dai hakan ba shike nuna Ni'imtacciyar inuwar da kike kwaɗayi keda Karuwan danginki bace kika shigo.....”
Ta saketa tana miƙewa tsaye da ƙyau, ƙasa Raudha tai da kanta jikinta na wani irin rawar tashin hankali. Adda Asmah ta saka hannunta dake cike da zabban gold da bangles ta ɗago haɓar Raudha. Idanunta ta tura cikin na Raudha da ƙarfin tsiya tana murmushi, wanda ya gansu daga nesa sai ya ɗauka wani maganar alkairi da yaba Raudha take. A kausashe da salon murmushin makircin tace, *_“BAƘAR INUWA_* ce da gwara ranar da kika baro da ita yarinya”.
Ta ƙare maganar da sakin fuskar Raudhan ta sake rungumeta sannan ta saketa. Ko tari gimbiya Su'adah batai ba. Sai dai fuskarta da ɗan murmushin ƙasaita. Kowa yasan halinta na girman kai shiyyasa babu wanda ya damu da yanayin nata, dan likin ma data fito taima amarya ya bama wasu mamaki. A haka dai taron ya tashi ƙwaƙwalwar Raudha a harmutse a kuma cushe. Dan tun kalaman Adda Asmah sai kawai ta koma ambaton sunayen ALLAH dan shine kawai zai iya zame mata mafita a zuciyarta yanzun.
Tana ɗakin Anne bayan ta idar da salla Fatisa da Fatima zaune kusa da ita suna magana take jiyo ƴar hayaniya ambaton sunan shugaban ƙasa dake amsa sunan mijinta a yanzun. Idanunta ta ɗan rumtse a hankali tana jan numfashinta zuwa tsakkiyar ƙirji. Buɗe ƙofar ɗakin na Anne da shigowar mayen ƙamshin turarensa cikin hancinta ya sata saurin buɗe ido. Ƙirjinta ya ɗan harba saboda haɗa ido da sukai, dan tuni su Fatisa sun miƙe daga kusa da ita suna gaishe shi. A taƙaice ya amsa musu yana janye idonsa akan wadda har yanzu bama gama tantance kamanin nata yay ba. Indama ace su Fatima kama suke da ita to da wahala ya iya ganeta a yanda ya shigo ya samesu.
Tuni Raudha ta janye idanunta tai ƙasa da kai, sai dai jin fitar su Fatisa a ɗakin yasa taji kamar ta miƙe ta zura da gudu ta bisu su fita tare.
“I..ina y..yini”.
Ta faɗa cikin rawar harshe da in'inar da batasan daga ina ta samota ba lokacin da take jin tamkar takunsa na kusantota, duk da kuwa akwai lallausan Turkey carpet da ƙamshin daya yake fitarwa ma na musamman ne tamkar ba ɗakin tsohuwa ba.
“Assalamu alaikum”.
Muryar Anne da buɗe ƙofar suka katse sauraren Raudha da ga jiran amsa gaisuwarta gareshi. A hankali ta saki numfashin data riƙe a tsakkiyar ƙirjinta tamkar mai jiran ace ar ta haɗiye abinta cikin ciki.
Shugaban ƙasa Ramadhan dake ƙoƙarin ƙarasawa saman ɗaya daga kujera biyun dake a bedroom ɗin na Anne ya kai zaune yana amsa mata sallamarta. Yayi matuƙar ƙyau cikin shadda ash color data wadatu da jiƙaƙen ɗinki da ƙyawun surar da ALLAH yay masa. Da gani basai an faɗaba maiƙonta kawai ya isa amsa ga mai hasashen kuɗinta.
“Wai sai yanzu ake ganinka a gidan nan Ramadhan?”.
Anne ta faɗa tana kaiwa zaune bakin gado gab da Raudha dake a ƙasan carpet. Dan ko Anne tace ta hau gadon bata iyawa saboda kunya.
Ɗan murmushin daya tsaya masa iya kumatu yayi yana duban tsadadden agogonsa _Breitling_ dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa Silver. “Anne barci ne naji zai halakani shiyyasa na kulle kaina kawai”. Ya faɗa cikin muryarsa mai faɗi da kauri. Sai dai a hankali yake maganar tamkar baya so.
“To ALLAH dai ya rabamu dayin ragon shugaban ƙasa anan, Aminatu sai kin dage da addu'a kam”.
Yanzun ma gajeren murmushi kawai yayi, sai dai ambaton sunan Raudha da tayi ya sakashi ɗan dubanta ya ɗauke ido. A ransa ko rayawa yake (a haka dai tamkar mutuniyar kirki, sanin gaskiyar al'amarinta sai ALLAH). Dan shi tozali kawai da yay da Mal. Dauda jiya ya sake gaskata maganar su Maa.
“Abinci fa?”.
Anne ta katse masa tunani. Agogon nasa ya sake kallo yana ɗan furzar da iska. “Idan da fura kawai a bani ya isa Anne”.
“Fura kam tayi kaɗan ga wanda baiko karya ba. Banajin ma kaci wani abu daren jiya”.
“To Anne ya zanyi”.
Ya faɗa a yanayin nuna rauni kamar na shagwaɓa. Kasa daurewa Raudha tayi sai da ta saci kallonsa. A ranta tana faɗin (humm). Oho baima san tanayi ba. Dan telephone dake kan table Anne tai amfani da ita wajen sakawa a kawo masa abinci. Babu jimawa kuwa ɗaya daga cikin amintacciyar ma'aikaciyar gidan ta kawo masu damammiyar fura datasha haɗi da gasashen naman rago mai romo, sai shawarma.
Babu ko jin nauyin Raudha dake zaune ya zare agogo ya gyara zama. Anne ta duba Raudha da keta wasa da zoben hanunta cikin kulawa. “Aminatu kema ai ba abincin kikaci ba, tashi kije kuci ko ƙyaji ƙarfi”.
Da sauri Raudha ta girgiza kanta. A ranta tana faɗin (tab ɗi ni zanci abinci da shi?) a fili kam sai tai saurin faɗin, “Anne na ƙoshi wlhy”.
Lallaɓata da lallashinta Anne ta shigayi amma ta dage ta ƙoshi, harda ƴar ƙwallarta da taso bama Anne dariya ma.
Duk da a kunnensa suke duk zantukan nasu ko nuna alamar yama san sunayi baiyi ba. Furarsa da nama yaketa ci a nutse hankali kwance. Hakan yasa Anne taɓe baki tana dubansa, cikin ɗan tsokana tace, “Da yake mai abincin ma marowacine Aminatu ai kinga yayi shiru dan kar aci”.
Yasan da shi take, dan haka ya ɗago idanu yakalli Annen. Cikin yamutsa fuska yace, “Kai Anne, kunzo kunce zakuci ne na hana?”.
“Ko bakace ba ai baka nuna alamar kana so aci ba”.
Murmushi kawai ya ɗanyi ya cigaba da cin abincinsa batare daya ƙara magana ba. Yan kammalawa kuma bai ƙara ko mintuna uku ba ya miƙe wai zaije su Ibrahim na jiransa a masaukinsu. Dan in baije yanzu ɗin ba da wahala ya sake samun dama. Bai kamata kuma ace sunzo dan shi ba amma yay musu wahalar gani duk da sun san yanzu da da akwai banbanci tunda shiɗin sunan shugaban ƙasa yake amsawa.
Addu'ar dawowa lafiya Anne tai masa, hakan yasa itama Raudha a hankali ta furta ALLAH ya tsare batare da tayi tunanin shi da Annen zasu jita ba. Sai dai kuma amsawar da Anne tai da “Amin ya rabbi Aminatu” ya sata fahimtar tajita. Shiko bata tunanin ya amsa harya fice abinsa.........✍
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥
_Mamuhgee_
Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261
__________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F
Guda biyu=400F
Uku=500F
Hudu=700F
Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please
*_Follow me_*
*_Share_*
*_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
*_Typing📲_*
*_Typing📲_*
*_Episode 25_*
..........*_8:15pm_*
Gagarumar dinner ɗin da su Alhaji yaro glass da Shugaban ƙasa mai sauka suka shiryama su Ramadhan ɗin ta fara gudana. Ƴaƴan manya ne da manyan ƙasar kansu kawai kake gani a wajen. Amarya da ango sunsha ƙyau har sun gaji. Dan zaman bayyana ƙawatuwar shigarsu da docration na wajen ma ɓata lokacine. Anci ansha daga kayan daɗi kamar babu gobe. Yayinda ango ya hana amarya tashi daga inda suke zaune ko sau ɗaya. Dan haka wanda sukai musu liƙi ma anan suka iskesu wajen zamansu sukayi. Cake ma nan aka kawo musu suka yanka a zaunen basu tashi ba. Humm sabon salo kenan wai rawa agaɓar gacci. Dan kuwa ƴan jarida da masu jiran ayi suce tuni sun sami abin faɗa.
Sai faman cece kuce suke na cewar wai mi Ramadhan ɗin ke ɓoyewane da ya hana a ga matar tasa yanda ya kamata. Dan kuwa duk da kwalliyar da taci yau fuskarta sanye take da facemask, kuma shine da kansa ya sanya mata sanda suke tahowa a mota. Ita kanta ta kasa fahimtar minene dalilinsa na son ɓoye mata fuska a duk sanda suka haɗu? Shin *_BABU SO! MIYA KAWO KISHI?!_* (Wannan littafi na nan tafe a gareku ba babu so miya kawo kishi? Insha ALLAH😉🤗😄). Bata da mai bata amsa dan haka ta haɗiye a ranta.
Ƙarfe sha biyu dai-dai aka tashi, bayan mawaƙa kala-kala sun baje basirarsu tunda daga kan na hausa har zuwa na turanci. Hakama masu wasan barkwanci. Kamar sanda suka taho yanzu ma sun koma gidane bisa tsaron na musamman daga jami'ai. Kamar kuma ko yaushe har suka iso ɗin ko kallo bai haɗasu ba ita da shi balle magana. Yay mata rakkiya har ɗakin Anne da basu riga sun iso ba su yay wucewarsa nasa part ɗin ya barta da sakin numfarfashin data tara a ƙirji. Duk da ko sau ɗaya bai wani taɓata ba, dan ko hannunta bai riƙeba a wajen dinner ɗin ƙamshin turarensu ya cakuɗe dana juna har baka iya banbance wanda take yi saboda ƙarfin nasa, ta kwanta lamo a gefen gadon Anne batare data iya cire ko zobe a yatsanta ba. Batasan mi zatai tunani ba a yanzu, girman mijin nata a mulki, ko auren nasu da baida alƙibilar kwatantawa?. Rabuwa da iyayenta ko shiga BAƘAR INUWAR da su suke hasashen Ni'imtacciyar inuwa ce a gareta?. Manufar su aunty Hannah a kan kashe su, ko tsananin ƙiyayya da ƙyamar da take hange a idon uwar mijinta da sai a yau wajen dinner tasan matsayinta na mahaifiya ga Ramadhan ɗin?. *_“Ya ALLAH kaji tausayina. Nayi tawassali da sunayenka ƙyawawa masu tsarki. Da kai na dogara dan bani da kowa sai kai ɗin tun farkon fari. ALLAH ka ƙyautata ni'imarka garemu a ƙarƙashin wannan BAƘAR INUWA da kowa kema kallon Ni'imtacciyar inuwa a garemu.”_*
Hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta zuwa kumatunta har saman facemask ɗin fuskarta da ta gagara cire koda shi ne. A wannan yanayin gidan ya fara ɗaukar hayaniyar mutane alamar an dawo dasu gida suma. Dole ta miƙe ta fara zare sarƙa da tarkacen jikinta gudun kar Anne ta zargi wani abu. Duk da kuwa a ranta yanzu hankalinta yafi karkata da kwanciya akan ta tunkari Anne da batun da taji a bakin su Aunty Hannah. Sai dai kuma bata son tozarta yayar mahaifiyar tata dan koba komai bata da kamarsu a duniya, tunda gashi har ana aibantata da halayensu da suka aikata tunkan haihuwarta.
★★★
WASHE GARI aka gudanar da rantauwa ga shugaban ƙasa da gwamnoni. Kum harda Raudha shugaban ƙasa Ramadhan yaje wajen. Sai dai tana cikin dogon farin hijjab da facemask yau ma. Abin ya sake burge jama'a musamman talakawa. Da kuwa idan akai dubi da yanda mafi yawan matan gwamnonin suka cakire cikin shiga ta rashin mutunci da kece raini a yau ɗin. Ga gwalagwalai dake ƙyalli da walwali a jikinsu tako ina. Hatta da Hajiya Fanta da aunty Hannah matan vice president shigar tasu ba'a magana. Sai dai a kallo guda zaka gane ran Hajiya Fanta a ɓace yake saboda kasancewar aunty Hannah a wajen bayan mijin nasu yace mata da ita kaɗai zaije banda Hannah. Dan tunda aka maida aurensa da aunty Hannah suke tafka rigima har yanzu kuma babu daɗi a tsakaninsu, tace sai ya saki aunty Hannah ɗin. Shiko ya tabbatar mata hakan bamai yuwuwa bane dan Hannah nada muhimmanci a tafiyarsa ta yanzun.
Ga ƴan siyasa kuwa sai suka fara takale-takale da zungure-zunguren batun saka facemask da amaryar ta shugaban ƙasa ke yawan yi, dan tunda ya far bayyanata wa duniya ranar zaɓe ba'a taɓa ganin real face nata ba sai da facemask. To yau ma al'amarin yaci uban na da, dan farin siririn gilashi da Raudha ta saka a idonta saboda kumburin da ya ɗanyi na kuka da rashin isashen barci ya ƙara mata wani ƙyau da burge mai kallo. Ga facemask da ya saka ba'a ganin ainahin face nata kuma. Sai haka ya zam ba'a ganin komai nata a waje sai tafukan hanunta kasancewar hijjab ɗin data saka mai hannu ne.
Uban gayyar shima fararen kayane a jikinsa na wani haɗaɗɗen boyal ɗinkin babbar riga. Ya kawo hularsa tangaran data fita a fice ya murza. Bayan kammala Rantsuwa suka wuce wajen bikin da aka shirya gudun mawa da ga Mai-martaba. Ƙarfe biyu aka tashi aka dawo da Raudha kawai gida, shugaban ƙasa Ramadhan kuwa gidan gwamnati aka tafi masa rakkiya. Bayan idar da sallar la'asar aka gabatar da walima da addu'oi daga manyan malamai har zuwa ƙarfe shida na yamma. Daga haka taro ya tashi