Header Ads
Showing 6001 words to 9000 words out of 204612 words

Chapter 3 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt

Ads the beginning of article before Image

26 Jun 2024

3053

Ads at the middle of Article

akan kuskurensu shanyewa akeyi ayi haƙuri. Saɓawa ALLAH ne kawai ba'a yarda kamusu biyayya akansa ba wannan haramunne.
Raudha taji wannan nasiha hartazo ta bama iyayenta haƙuri. Daga lokacin kuma ta dinga taka tsantsan da harshenta a kansu da fushinta. Idan ma taga abu zai basu saɓani ta gwammace ta amshi laifin ita koda zasu mata hukunci ne. Idan batasan tushen rikicin nasu ba kuma zatabi duk hanyar data dace ta sasantasu cikin hikima. Sai dai kuma kuka ya zame mata tamkar abokin rayuwa, dan sam bata ƙaunar halin mahaifan nata guda biyu ko kaɗan.
A yanzu haka Raudha da sauran ƴan uwanta na sauran ƴaƴan ɗakunan biyu sa'anninta suna akan zana jarabawar gama secondary school ne. A ƙalla shekarunsu Fatisa goma sha takwas, Raudha kuwa sha bakwai ita da Iklima da Binta. Kasancewar babu wani batun Noziri a karatun nasu yasa suka kammala da ƙarancin shekaru, musamman ma ita dasu Binta duk sun girme mata.
Halin talauci da fataran da suke ciki ga shegen son kuɗi na Asabe ya saka ƴaƴanta su Fatisa fara kaucewa hanya wajen biyema samari. Duk da kuɗin da yaran ke shigowa dasu na ban mamaki da kayan kwalliya basu sana'ar ko asi bai taɓa saka Asabe nuna damuwa ba balle tuhumarsu. Sai dai ma ta baje suci su sha mai daɗi tana kiransu masu farin jini. Tabbas *ZINA* tamkar sharri take, dan ƴar aikece komin daren daɗewa saita dawo cikin zuri'arka. Hakanne ya faru akan su Fatisa dama wasu a ƴaƴan mal ɗan azumi na sauran ɗakunan, dan kuwa cikin ƙanƙanin lokaci rayuwarsu ta ɗakko hanyar lalacewa Dauda naji na gani babu halin magana, duk da abun na ƙona masa rai da soya zuciyarsa. Dan ko yayi magana Asabe ta taresa da masifar cewar yanama ƴaƴanta sheri saboda shima aikinsane zina. Maƙiya masu baƙin ciki da hassada wa farin jinin ƴaƴanta na ɓoyewa bayan ƙofa suna musu dariya. Sai dai abinda Asabe bata sani ba na ƴaƴan ɗakintane ya fito, amma itama Larai nada Kangararru irin su Fatisa har su uku. Wani lokacin duk da gogewar ɗan-azumi a bariki, Asabe ta fisa bala'i, shiyyasa idan taja yaja sai ya sakar mata dan zuwa yanzu girma yaɗan fara kamashi, ga ciwo dake cinsa a tsaye na hawan jini wanda ko ba'a faɗaba asabe ce silarsa, gefe ɗaya taba ta gama cinye masa naman jiki sai ƙashi da jijiya da fata.
Halayyar su Fatisa na matuƙar ƙona ran Raudha, sai dai babu yanda zatayi dan ko tayi nasihar basaji. Ita kanta samarin na yawan kawoma rayuwarta hari, musamman daya kasance ta fisu ƙyau nesa ba kusa ba. Hankalinta yakan tashi matuƙa, shiyyasa akoda yaushe cikin suturta jikinta take da kayan mutunci harma da niƙab wani lokacin. Takan yawaita neman tsarin ALLAH daga ƙaddarar zina a gareta.
Rashin samo kuɗi da batayi yasa Asabe tsangwamarta a ɗakin fiye da kowa. Dan hatta Yasmin ta fita daraja duk da kuwa Asaben tafi son Raudha fiye da kowa acikin ƴaƴan nata. Sai dai lallaɓa da lallashin da take mata akan ta dinga kula samarin sai tafi su Fatisa samo kuɗi, amma Raudhan na bijirewa yasa ta ɗauka karan tsana ta ɗaura mata ita da su Fatiman. Kullum cikin caccakarta suke da magana mara daɗi. Da yake miskilace kuma bauɗaɗɗiya ko kulasu batayi ma balle ta nuna ta damu, fatanta kawai tai aurenta tana gama secondary school da ya-sayyadinta Abubakar da kowa yasan suna soyayya zuwa yanzun.

A ɓangaren sayyadi Abubakar shima babban burinsa mallakar Raudha matsayin mata. Dan haka suna fara exam ya sanarma iyayensa akai kuɗi. Sunyi farin ciki da farko dan basusan ƴar waye ba a Hutawa. Dan haka suka tambayesa acewar mahaifinsa sai sun fara bincike tukunna. Abubakar ya shiga fargaba, amma sanin Raudha yarinyar ƙwaraice mai kamun kai, kuma da ita zai zauna yasashi jin ƙwarin gwiwa.
Bayan kwana biyu mahaifinsa ya kirasa shida ƙanensa sukai masa wankin babban bargo, tare da gargaɗinsa ya fita sabgar Raudha bata fito cikin gidan arziƙi da mutunci ba, su bazasu haɗa zuri'a da ɗan-azumi ba. Idan ma ƙyawun yarinyar ke ɗiɓarsa yaje akwai ƙyawawa da suka fita ya nemo. Idan kuma ya sake koda yima Raudha magana ne ALLAH ya isa basu yafe ba. Itama sunje har gida sun gargaɗi ubanta akan ta fita hanyarsa. Daga karshe suka hanashi cigaba da koyarwa a islamiyyar su Raudha ɗin baki ɗaya. Sukama maida rayuwarsa can cikin birinin Ɗillo wajen wani ƙanin baban nasa dake can da iyalansa.
Wannan shine sanadin raba Raudha da Sayyadi Abubakar. Tayi kuka kamar yanda shima yayi nasa. Kusan dukansu sai da suka kwanta a asibiti dan ba karamar shakuwace a tsakaninsu ba. Halin data shiga yasa ɗan-azumi da Asabe zuwa har gida sukaima iyayen sayyadi Abubakar tas. Wannan ya ƙara harzukasu suka kara jin tsanar tushen Raudha da ƙyamar haɗa zuri'a da su.
Sosai wannan lalacewar aure taima Larai daɗi, dan kuwa tana ɗaya daga mutanen da suka sake lalata zancen auren, mahaifin Sayyadi Abubakar nada ɗan hali, shiyyasa tun yana zuwa wajen Raudha takeji baƙin ciki da hassadar hakan. Sai dai tabi duk wata hanyar rabasu hakan bai samu ba, sai gashi cikin sauƙi komai ya lalace. Da wannan damar tai amfani wajen zuwa har gida ta sakema Asabe da ɗan-azumi batanci fiye da wanda iyayen Sayyadi Abubakar suka jiyo ga wasu mutanen. Sai ka rantse ɗan-azumin ba mijinta bane.
Raudha ta ɗanɗana azabar rashin Ya sayyadi Abubakar har batasan mi take rubutawa a jarabawa ba har suka kammala. Bayan kammalawar tasu ta sake dawowa gida zaman sabuwar jiyya, a dalilin hakan ciwon Asthma ɗinta da bai cika karfi ba ya sake ƙarfi har takai yana yawaita tashi yanzu. Gefe kuma ga azababben ciwon mara idan zatai period har suma take wani lokacin. Dama dalilin ciwon marar natane sayyadi Abubakar ya yanke shawarar data kammala secondary school suyi aure kawai, sai ta cigaba da karatunta a gidansa. Sanda suna tare saboda tsabar kiyaye yanayin nata da wata ya kama zai kawo mata magunguna da allura ta ajiye, da abin ya fara mata za'a nemo wani yaron makwafcinsu dake da kyamis yay mata allurar. Ta hakane take samun sassauci sai abun yazo da sauƙi..


_Wannan kenan😚👌🏼._


*_Mun dawo labari_*🏃


Kiran sallar isha'i ne ya sata miƙewa da ga kwanciyar kukan da tayi, ta fito daga ɗakin baki ɗaya batare data ko kalli inda su Fatisa ke zaune suna hira da shewa ba su da Mommynsu. Sai ma Yasmin ce data miƙe zumbur tana ƙwala mata kira da faɗin, “Aunty R zanje”. Dan tasan massallaci zataje sallar asham. Bata tanka mata ba, dan ƴan miskilancin na kusa ne, sai dai ta mata alamar tai alwala. Itama kuma ta ɗauka buta ta ƙarasa inda sukeyin duk wani hidimarsu na harkar ruwa a gidan tai alwalar sannan suka fice..........✍




*_Humm Sayyadu Abubakar Abubakar ya tafi, wa kuma zaizo? Ta ina zaizo? Yaushe zaizo AMINATU Raudha?. Dukkan amsarku na cikin BAƘAR INUWA ne, dan bazan gaji da faɗaba ba'a fara komaiba har yanzun masu karatu. Kar dai ku bari a baku labari😉⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️._*






*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*




*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥
_Safiyya Huguma_


*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥
_Billyn Abdul_


*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅
_Hafsat Rano_


*1*~ *_MASARAUTA_*💪
_Miss Xoxo_


*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥
_Mamuhgee_






Guda 1👉300
Guda 2👉400
Guda 3👉500
Guda 4👉700
Guda 5👉1k




*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*


Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank


Number shaidar biya👇🏼


*_09032345899_*




*KATIN MTN*👇👇


09166221261




*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*


_____________________




*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*


https://arewabooks.com/book?id=628103f05798291d0ecedd09




_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_




*YADDA AKE BUDE ACCOUNT A AREWABOOKS*


Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form din kamar haka: -


*Enter your name:* (Cikakken sunanki)


*Enter your mail:* (Email ɗinki)


*Enter an username* (Sunanki)


*Enter your password:* ( misali 12341234)


*Confirm password:* (misali 12341234)


Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.


*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.


*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.




*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*


https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3




Masu iPhone


Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com


*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*




*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*


+234 903 177 4742




_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*










*_Typing📲_*










*_🌳BAƘAR INUWA....!!🌳_*
_{Gara rana dake}_








*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*




________________
*_Episode 4_*




..........Ruwa kawai tasha tunda aka kai azimin na yau na kusan ashirin da ɗaya, sai dai hakan baisa ta damu ba, duk da yunwa dake cin hanjinta dan koda asuba ma batai sahur ɗin kirki ba kasancewar tuwo sukai na sahur, itako a rayuwarta sam bata shiri da tuwo musamman miyan kuɓewa ɗanye. Sau da yawama idan taci gudawa yake sakata shi da shinkafa. Kai duk ma wani abu irinsu basu ciga damun Raudha ba. Tafi so da buƙatar abinci mai ruwa-ruwa irinsu fura, kunu, koko da sauransu. Suna fita Yasmin ta fiddo goran ruwa madaidaiciya dake ɗauke da kunu ta miƙama Raudha. “Aunty R gashi kisha”.
Cak Raudha ta dakata daga tafiyar da takeyi ta dubi Yasmin ɗin, ganin abu a leda yasata daka mata tsawa dan sam bata fatan abinda zai lalata rayuwar Yasmin ɗin itama. Cikin ruɗewa Yasmin ta fara rantsuwa. “Aunty R wlhy bani akayi, baba ce ta bani (Baba Nafi) sanda naje mata aika gidan kawu Rabi'u (Ƙanin Baba Nafi) na amso mata kunun batare da Mommy ta sani ba. Niko kinga banyi azumi ba shiyyasa na ɓoye miki shi dan karsu aunty Fatisa su gani su shanye ko Mommy”.
Ajiyar zuciya Raudha ta sauke da kamo yarinyar ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu. “I'm so sorry my little girl, bana son ki fara koyon hali irin nasu Aunty Fatisa ne shiyyasa. Dan ALLAH ki kiyaye karki bari wani ya yaudareki da abinda bamu da shi ya lalatamin rayuwarki kinji”.
“Inaha ALLAH Aunty R bazan yarda ba ai”.
Yasmin ta faɗa duk da ba komai take fahimta ba da ga gargaɗin ƴar uwar tata kai tsaye, saboda ƙarancin shekarunta. Dan Raudha ta bata kusan shekara shida a duniya, bayan haihuwarta Asabe ta jima kafin ta samu ciki, harma ta ɗauka haihuwar ta kare sai kuma ga cikin Yasmin ɗin..
Kama hanunta tai suka ƙarasa massallacin batare data amshi kunun ba, can gefe ta samu ta saka musu abin salla inda bazasu takura ba, dan sam bata ƙaunar zafi ita, sanyi ma idan yay yawa yana taɓa rayuwarta.


An gabatar da sallar isha'i da asham, bayan addu'oi da malam yayi tamkar yanda ya saba kowa yay ƙoƙarin kama gabansa. Raudha bata tashi ba, sai roban kunun da Yasmin ta ajiye a gabansu ta ɗauka ta buɗe murfin, duk da ya huce haka tasha kusan rabi ta miƙama Yasmin dake gyangyaɗin barci sauran dan tasha itama. Amma sai Yasmin ɗin tace mata ta ƙoshi. Sanin kunu bai damu Yasmin ɗin ba sosai yasa Raudha ƙarasa shanyewa sannan suka miƙe.
Sai da ta gama tattare musu kayansu sannan ta duƙa Yasmin tahau bayanta danta lura barci takeji. Yarinyar ta saki sassanyar ajiyar zuciya tamkar yanda Raudhan tayi itama. Koda suka iso gidan a tsakar gida suka iske kusan kowa a ƙofar ɗakinsa. Yaran nata hayaniyar surutu iyayen kowa na sabgar gabansa. Sannu kawai tai musu bayan sallama ta shige ta kai Yasmin ɗin ɗakin barcinsu da gaba ɗaya ƴammatan gidan kan kwana musamman idan ranar Babansu a ɗakin mamanka yake. Idan ɗakin wata yake daban zaka iya kwana a ɗakin mamanka ɗin. Fitowa tai tai ɗan uzirorinta batare data tankama kowa ba ta sake shigewa tai kwanciyarta dan su Fatisa a ƙofar gida ta barsu suna hira.


*_WASHE GARI_* Raudha ta tashi da ciwon mara mai tsanani tamkar yanda takeyi duk wata. dama tun kusan jiya takejin alamarsa kaɗan-kaɗan, batai wani yunƙuri ba dan maganin da take sha ya ƙare. dama Ya-sayyadi ne ke saya mata shi kasancewar yasan lalurar tata. Idan har zatai period sai kowa ya sani. ba ƙaramar azaba take sha ba na ciwon mara dana ƙafa. Daga ƙarshe taita kwara amai. Idan ka ganta a irin wannan halin ma saika ɗauka yaron ciki ne da ita. Dan a farkon fara hakan tana jss1 secondary kowa a gidansu dama makaranta sun ɗauka ciki ne da ita, duk da lokacin batafi sa'ar Yasmin ƴar shekara goma sha ɗaya ba. Sai da aka dubata likita yace period zata fara sannan hankalin malaman ya kwanta har sukazo da ita gida akaima iyayenta bayani.
Duk murƙususun azabar da takeyi a ɗakin babu wanda ya sani, dan gidan shiru alamar yaran duk sun fice sabgogin gabansu, manyan kuma kowa barcinsa yakeyi. Sosai take cin azaba, dan tun tana kuka ma har kukan ya gagara, tsanani yay tsanani har takai Raudha da suma.


Kamar yanda ya saba shigowa gidan fagan-fagan babu ko sallama yauma haka ya shigo, dan tun fitarsa sallar asuba bai sake shigowa ba yana rumfar ƴan gulma kamar yanda ake kiran majalisarsu. Jin gidan shiru ya sashi fara ƙwala kiran Raudha, dan a rin wannan lokacin ita kaɗai zaka iya samu a gidan tana bautar gyarawa, data gama take wucewarta wajen tafsir sai sha biyu ta dawo.
Shiru babu wanda ya amsa masa, yabi gidan da kallo a harzuƙe, ko'ina kaca-kaca da kwanika da tulin tsummokaran kayansu kusufi-kusufi. Tsaki yaja yana nufar ƙofar ɗakin Asabe. “Asabe! Asabe!!” ya shiga ƙwala mata kira, dan har yanzu haushinta na jiya bai bar ransaba, musamman daya kasance yanzun nan jabiru mai shago ya sake masa maganar kuɗinsa, shine ma dalilin shigowa gidan da yay.
Cikin barci Asabe taji muryarsa bisa kai, ta miƙe a zabure tana yaye labulen daya saya falon nata matsakaici, komai babu a cikinsa sai ledar ƙasa dan duk ta siyar sun cinye kuɗin a ciki ita da ƴaƴan.
“Wai wane kalar jidaline kuma haka da wannan farar safiyar? bazaka barni nai barcin dana gagarayi ba da asubahi!”.
Tsaki yaja yana turo kai cikin falon, yaci tuntuɓe da ƙafar Fatisa dake barci a gefenta itama, da sauri Asabe ta tarosa. “Gashi nan wajen gargajigarka ta masifa zakaima kanka lahani a banza, wai nikam mike faruwa ne?”.
Numfashi yaja da ƙarfi, batare daya amsa mata ba ya kai zaune a tsakar falon yana godema ALLAH a zuciyarsa da bai faɗi ba. “Asabe ina Raudha!?”.
“Raudha kuma? Wani laifin ta ƙara maka ne?”.
Kansa ya jinjina mata cikin tausasa murya tamkar bashine ya shigo da bala'i ba yace, “Laifi kam tana da shi a gareni kema kin sani, to amma abinda ya fara kaɗoni gida yasani yafe mata zan ma biya jafarun kuɗinsa insha ALLAH. Ina Alhaji Maude Dallatu uban gidan falalu mai shagon kayan ƙwalam ɗin can na bakin titi?”.
“Eh na gane!”.
Asabe ta faɗa da sauri cikin ƙaguwar son jin inda zancen ya nufa. Fahimtar hakan ce ta sakashi cigaba da faɗin, “Wai shine fa ya aiko Falalu ɗin akan ya sameni ya faɗamin zaizo akan Raudha wajena.....”
“Ni bangane ina zancenka ya dosa ba wlhy ɗan-azumi, fito fili ka faɗamin kasan bana son wani kwana-kwana.”
Baki ya washe sosai cikin raɗa yace, “Inagafa cazai na bashi aurenta, idan ko haka ta kasance Asabe ai mun haye wlhy. Shiyyasa a koda yaushe bana gajiya da alfahari da ƴaƴanki ƙyawawa”.
Itama tuni fara'a ta baibaye fuskarta, nan fa suka shiga ƙus-ƙus akan batun wai kada magauta su jiyosu. Tun ma kan suji ta bakin Alhajin harsun gama yanke hukuncin tsaida ranar biki. Bisaga wannan shawara da suka tsaida cike da zumuɗi Asabe ta miƙe kiran Raudha.
Da sauri Larai dake laɓe tanajin komai ta afka ɗakinta har tana neman faɗuwa. Asabe kuwa da bata lura da itaba ta nufi ɗakin su Raudha.
Kururuwar ihun Asabe ne ya saka kowa fitowa a gidan har masu barci da Larai daketa faman kai kawo a ɗakinta ranta a dugunzume da zancen da taji.
Suna ƙoƙarin jin dalilin ihun nata suka hango Raudha a sanƙame tana girgizawa. A tsorace duk suka afka ɗakin, Baba Nafi tai dabarar ɗakko ruwa ta shafama Raudha ɗin. Sai gashi ta kawo wani nannauyan numfashi. Sai kuma ta ƙudundune jikinta tana ƙanƙame Asabe da sakin wani kuka maiban tausayi dako sautinsa baya fita saboda azabar da taci.
“Mommy zan mutu”.
Kawai take iya furtawa da ƙyar tana sake ƙanƙame Asabe da itama tarasa ina zata saka kanta taji sanyi, dan sun fahimci ciwonta na marane ya motsa. Fatisa ce ta bada shawaran a kaita asibiti ko za'a iske Doctor Rufa'i abokin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads