Showing 135001 words to 138000 words out of 204612 words
Chapter 46 - BAKAR INUWA Original Book Complete Document by Billy Abdul .txt
“Anne sanyi nakeji ki ƙara min bargo, Anne kaina ciwo kamar zai fashe, wayyo Anne kaina jikina zafi Anne ko'ina ciwo”.
Dariya, tausayi, tsoro, mamaki, duk suka dira a zuciyar Raudha lokaci guda. Gata matse a jikinsa tamkar zai ɓalla mata ƙasusuwa ga zafin jikinsa na matuƙar ratsa nata jikin. Sosai ƙirjinta ke bada sautin fatt! Fat!! Da ƙarfi, da ace lafiya yake babu abinda zai hanashi da kiranta matsoraciya. Cikin rawar murya tace, “To ka bari na tashi na baka magani gashi magrib ma tayi”.
Jin muryarta saɓanin ta Anne da yake tsammanin ji ya ɗan buɗe ido, ba ganin fuskarta yake ba dan ya rufe musu har kai a bargon, “Kinada tausayi kuwa?”. Ya faɗa yana sake ƙanƙameta har saida tai ƴar ƙara saboda ƙirjinta. gaba ɗaya a birkice yake, “I'm sorry”. Ya sake faɗa a hankali cikin kunenta yana sassauta mata riƙon, sai kuma ya sake faɗin, “Kiyi shiru bana son magana kaina na ciwo”.
To yau dai Raudha taga takanta. Ɗan ƙwalisar nan Ramadhan mai shegen ɗaukar kan nanne haka. Shugaban ƙasar NAYA jinin Taura da ko kallon arziƙi sai ya gadamar wanda zai yimawa. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai jinƙai. Maiyin yanda yaso, ga wanda yaso. Cikin ƙanƙanin lokaci in yaso kamaka da ƙanƙanin abu sai ya firgitaka ka mance kai waye? Miye matsayinka?. Taja numfashi a hankali da shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na REED. Zuwa yanzu ta nutsu a jikin nasa badan taso ba, babu abinda ke ratsata sai zafin jikinsa da sautin bugun zuciyarsa. Sai saukar numfashinsa a wahale. Magana yake a hankali bisa laɓɓa da bataji, sai dai tanajin alamar motsin bakinsa. Ta fahimci sambatune na ciwo kawai ke ɗawainiya da shi. Kusan mintuna talatin suka samu a haka, ganin lokacin salla na sake shigewa ta fara magana a hankali cike da lallashi.
“Lokacin salla nata sake nisa, ga abincin na kawo maka kuma da magani kayi haƙuri na tashi na baka kar mu makara salla”.
Sarai ya jita, dan idonsa biyu. Sai dai bai nuna alamar yajin ba har bayan shuɗewar wasu mintuna.
Da ƙyar Raudha ta samu ya rabu da ita ta tashi, toilet ta shiga tana sauke tagwayen ajiyar zuciya da taɓa jikinda da yay zafi kamar itama ta kamu da zazzaɓin. Ruwan ɗumi ta daidaitamsa domin yin alwala. Tayo tata sannan ta fito. Har yanzu yana cikin bargon ƙudundune. Cikin lallashi tace, “Ya Ramadhan ka daure kayi sallan sai kaci abincin da magani”. Kamar bazai motsa ba sai kuma taga ya miƙo mata hanunsa da ga cikin bargon, duk da kunya dake ɗawainiya da ita hakan bai hanata kamawa ba danta fahimci abinda yake buƙat kenan ta taimaka masa ya tashi. Da taimakon nata kuwa ya tashi, ganin kamar yana tangaɗi sai taƙi sakinsa sukaje ƙofar toilet, sai da taga ya shiga sannan ta sauke numfashi. Kasancewar akwai hijjab jikinta tasa abin salla tayi anan, tana raka'ar ƙarshe ya fito da alama ba alwalan kawai ya tsaya ba yayi wani uzirin nasa daban. A ɗayan abin sallar data saka masa ya tada sallar shima yana faman riƙe kai, kafin ya idan da sallar aka shiga kiran isha'i, hakan yasa Raudha komawa ta zauna domin gabatarwa.
Su dukansu sai da sukai salla har isha'i sannan ta haɗa masa abinci. abin mamaki yau yanka uku Ramadhan yaci na nama, sai romon farfesun kawai ya cigaba da sha. Raudha dake gulmarsa a zuciya ta shiga jinjina kai tana mamakin eh lallai magana ta girma kure na gudun nama yau. To ashe akwai ciwon da zai iya hana Ramadhan cin nama a duniyar nan?. Batace komai ba ganin ya ɗan sha ruwan kunun ya kuma sha romon nama. First aid box data gani a ɗakin ta ɗakko ta duba, cikin sa'a ta samu maganin mura data san yanada inganci tunda tasha amfani da shi itama. Da ƙyar ta samu yasha maganin yana yamutse fuska har yaso bata dariya, ta dai daure ta gimtse.
Koda ya koma saman gado da nufin kwanciya a ɗofane taɗan zauna. gadon da nufin gyara masa bargo kawai sai jitai ya ɗaura kansa a cinyarta, tare da riƙo hanunta yay filo da shi a kuncisa. Idanu Raudha ta ƙwalalo sai kuma ta ƙwaɓe fuska. Oho basai tanayi ba dan harya fara lumshe idanu, dole ta hakura da ƙudirin idan yayi barci ta zame jikinta ta gudu...........✍
End of book
Leave a comment
Post
Comments
104835043420935222197
Fist to read😍
8 hours ago
Contact Us
Arewa Books Publishers
WhatsApp: 09031774742
Email: arewabookspublishers@gmail.com
Navigation
Home
About
FAQ's
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram
Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
Chapter 46
46
............Tun Raudha na irga sakanni harta koma mintuna, kamar wasa suka cinye rabin awa. Data yunƙura zata tashi Ramadhan zai sake ƙanƙame mata hannu, ga kansa bisa cinyarta. Fahimtar kamar barcin nasa baiyi nauyi ba yasata haƙuri ta sake bashi lokaci harda jingina da fuskar gadon, cikin rashin sa'a itama barci yay a won gaba da ita a wajen mai nauyi dan a gajiye take yau ga rashin barcin jiya cike da idonta dama.
A hankali ya fara buɗe idanunsa da sukai masa nauyi irin na mai farkawa a barci da rashin jin daɗin jiki. Alhmdllhi zazzaɓin ya jima da sauka. Hakama ciwon kan kaɗan-kaɗan yake jinsa shima yanada alaƙa da maganin murar da bai gama sakinsa ba dan barcine taf a idanunsa. Sabo da tashi sallar asuba akan lokacinta ya sashi farkawa. Hanunta da ke riƙe a nasa fuskarsa a kai ya ɗan tsurama ido, tun yana kallonsa dishi-dishi cikin ɗan hasken lamp har idonsa ya dai-daita. Zuciyarsa ce ta ɗan motsa na alamar mamaki, yay saurin ɗaga kai ya dubi sama. Itace kuwan da gaske, kuma akan cinyarta kansa yake. Ta ɗan zama kaɗan ta kwanta saɓanin da da take zaune. Sai dai a kallo ɗaya ya fahimci kwanciyar batai mata daɗi dan a matuƙar takure take a wajen.
Idanunsa ya dafe tare da cije haƙoransa ya tura yatsun hanunsa cikin sumar kansa. ‘Ya ALLAH’ ya faɗa a hankali cike da jin haushin kansa. Dan ya gama fahimtar lallai anyi abun kunya a daren jiya. Inhar irin sambatun daya san yanama Anne idan yana zazzaɓi yay mata itama to shikan dai yagama ganin takansa, raini kuma tsakaninsa da yarinyarnan ya samu gurbin zama. ‘Ni Ramadhan miya shiga kaina ne wai?’.
Ya sake faɗa a fili lokacin da yake tashi zaune hanunsa dafe yaɗan karkata yana kallonta. Duk da takaicin kansa da yake ji hakan bai hanashin jin tausayinta ba. Shi kansa ya sani idan shine bazai iya juriyar kwanciya haka ba dan kawai wani yaji daɗi shi. Jin za'a tada salla ya sashi miƙewa ya sakko a gadon da ƙyar, sai da Raudha ta tabbatar ya shiga bayin sannan ta buɗe ido a hankali. Tun motsawarsa itama ta farka, ta ɗaga hanunta da yay matuƙar tsami da ƙyar taɗan yarfar, wani irin azaba ya ratsata. Saurin riƙewa tai da ɗayan tana cije baki. Da ƙyar ta iya tashi dan kafaɗarta zuwa wuya suma duk a riken suke.
Cikin dauriya ta fita a ɗakin zuwa nata dan shima taji motsin ruwa alamar wanka yake. Itama da gasa jikinta ta fara, duk da ba saki hanun da wuyan sukai ba haka ta daure bayan idar da salla ta nufi kitchen. Tunda ta fito ma'aikatan gidan daketa fitowa domin tsaftace sashen ke zubewa suna gaisheta. Babu sa'anta a cikinsu, ta tabbatar kuma ko'a ilimi sun fita, dan haka take matuƙar jin nauyin wannan girmamawa da suke mata. Sai dai tana dauriyar dannewa da amsa musu a dake dan wani girman idan ALLAH ya baka dole kai haƙuri ka riƙe.
A kicin ɗin ma duk zubewa su kuku sukai suna gaisheta, sukam har sun tsaftace ko'ina sunama ƙoƙarin fara ɗora abinci ne. Tambayar mi zasu dafa tayi, suka sanar mata. Babu abinda ya kwanta mata da yanayin mara lafiya, dan haka tace suyi iya wanda za'aci kawai. Ita kuma ta fara ƙoƙarin haɗama Ramadhan da taimakon Agnes da ita kaɗaice kuku mace a cikinsu. Haka kawai nutsuwar Agnes ɗin ke burgeta. Gata dai ba muslma ba amma bata da rawan kai, kuma bazaka taɓa ganinta da shigar banza ba. Haka farce da ƙarin gashi duk bata sakawa.
Komai suke Agnes a girmame take tayata duk da ta girmeta sosai, amma tsabar girmamawa Mommy take kiran Raudha. Tsaf suka kammala komai, Raudha zata ɗauka basket ɗin Agnes ɗin tai saurin ɗauka cike da girmamawa. “No Mummy zan ɗauka”.
Cikin ɗan Murmushi Raudha tai gaba dan bata son gwasale Agnes ɗin. A tare suka haura saman, Agnes zata nufi dining Raudha ta dakatar da ita ta amsa da mata sannu. Kai tsaye ɗakin Ramadhan ta nufa, haka kawai murmushi ya suɓuce mata tunawa da abinda ya faru jiya dama abinda taji yana faɗa ɗazun, ta gama fahimtar baya ƙaunar raini sam. A zuciyarta take faɗin (karka damu, indai Aminatu ce har abada babu raini tsakaninmu).
A fili kam sai tai knocking ƙofar kaɗan dayin sallama. Bataji an amsaba sai kawai ta tura ƙofar tana ƙarayi. Duk abinda take yana kwance yana jinta, sai dai yay luf fuska a tamke dan kawai yasan tunda har jiya yay abun kunya ta gama samun hanyar rainasa. Raudha har zuciya bata kawo lanbo yay mata ba. Ta ajiye basket ɗin ta fita.
Da kallo ya bita harta fice.
★★Sai da ta kammala shirinta na fita tsaf cikin kayan mutunci sannan ta fito tare da kulle ɗakinta dan tasan a koda yaushe su Lubnah zasu iya dawowa gidan. Koda ta koma ɗakinsa ta iskesa still kwance sai jikinta yay sanyi, duk zumuɗinta na son tafiya makarantar kuma sai ya fita mata a kai. Ajiye bag ɗinta da hijjab tai ta nufi toilet, tsaftacesa tai ta fito ɗakin shima ta gyara iya inda bazata takura masa ba. Daga haka ta ɗauka bag ɗinta ta koma ɗakinta dan ta haƙura da makarantar kawai tunda shima bazai fita ba.
Acan waje tuni securitys ɗinta da jiya ta gudumawa suna falon ƙasa suna jiran fitowarta. Hakama driver ya shirya tun da wuri dan gani suke jiya sakacinsu ne ya sata fita a gidan badasu ba. Basma ta kira ta sanarwa yau bazata shigo school ba. Daga baya sa nuna mata abinda aka kawai. Bata bama Basma damar yin ƙorafi ba ta kashe wayar gaba ɗaya itama ta kwanta, dama barcine taf a idonta ga ciwon da jikinta ke mata akan kwanciyar jiya.
Tunda cos ya ga takwas ta wuce shugaban ƙasa bai fitoba yasan murar jiya ta kwantar da shi kenan. Saƙo ya tura masa kawai ya cigaba da abinda ya dace dan Alhmdllhi ma yau abubuwan da Ramadhan ɗin zaiyi duk ba masu tsawwalawa bane. Zaman meeting ne sau kusan huɗu duka kuma an riga an tsara wanda zasuyi zaman. Abinda yake tilas saka hannu ne akan wasu takardu.
_______________________________
Tunda su Basma ke bada labarin Raudha ta fara karatu a school ɗinsu zuciyarta ke a ƙuntace. Lallai ta sake tabbatarwa ɗanta baya tare da ita. Komai daya shafesa sai dai taji a shanun ƴan talla. Tana cikin wannan yanayi Mardiyya tazo gidan, ɗiyarta ta biyu dake bin Ramadhan. Daga office take taga ya dace ta biyo ta gaishesu dan rabonta da gidan tun bikin Ramadhan ɗin. Haka take ita bata da kwaramniya, ga haƙuri. Lokuta da dama mutanen gidan kan ɗauketa wadda bata ɗaukar abu serious, sai dai kuma ba haka bane. Ita irin mutanen nan ne da babu ruwansu da shiga sabgar daba tasu ba, muguwar ƴar I don't care ce ta bugawa a jarida. Halayyarta ya saka bata wani shiri na'azo a gani da Gimbiya Su'adah. Yaranta huɗu, tare da mijinta suke aiki a companyn su na kansu da sukai haɗin gwiwar ginawa ita da shi. Ba ƙaramin bala'i a lokacin taci ga Gimbiya Su'adah ba. Amma tai fumfurus ta shareta. Da farko robobi companyn ke fitarwa, a hankali abubuwa suka kara bunƙasa takai har designes na wasu abubuwan daya shafi kayan kitchen suna sarrafawa. Kamar wasa sai gasu sun bunƙasa suma ana kwatantasu a jerin manyan kamfanoni dake sarrafa abubuwa masu muhimmanci a ƙasar.
“Maah! Lafiya kuwa naga kamar ranki a ɓace?”.
Duk da tasan halin ɗiyar tata na rashin ɗaukar abu da muhimmanci hakan bai hanata fara zayyane mata cikinta ba rai ɓace.
“Miyema bai faruba Mardiyya. Yanzu a duniyar nan babu abinda ke cimun rai da ƙonan zuciya sama da auren ɗan uwanku. Na tsani yarinyarnan da duk wani mai alaƙa da ita a duniya. Ji nake zan iya kasheta da hannnuna wlhy.....”
“Wa'iyazubillah Maah miya kawo wannan maganar haka?”. Mardiyya tai saurin katseta.
“Humm Mardiyya kenan, yanzu ke tunda kike a duniya kin taɓa jin matar shugaban ƙasa mai shekara sha takwas? Jahila da ko karatun sakandire banajin ta kammala? Daɗin daɗawa ƴar karuwai marasa tarbiyya da kowa yasan aikinsu a bayyane yake.” hawaye suka silalo mata, ta kai hannu ta share da cigaba da faɗin, “Mardiyya na tabbatar a ƙuntace Ramadhan yake, biyayyar da yakema kakanninku ce kawai ta sakashi haƙura ya amshi raunanniyar yarinyar nan, wai dan takaici sai yanzu take shiga jami'a. Matar shugaban ƙasa fa daya kamata ta zama vary educational, wayayya ta nunawa a duniya, wadda duk inda tasa ƙafa zata fiddashi a kunya muma ta fiddamu. ALLAH dai ya tsinema wannan aure na Ramadhan albar.......”
“Haba dan girman ALLAH Maah wane irin furicine haka babu daɗin ji. Idan kin tsinema auren Brother tamkar shi kika tsinemawa dan zata iya yuwuwa yanzu haka an samu rabo tsakaninsu. Maah ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, ni wlhy banga wani aibu ga yarinyarnan ba. Inma iyayenta sunada wancan halin ai ba itace kedashi ba. ALLAH kuma yana fidda rayayye a cikin matacce, ya fidda matacce a cikin rayayye. Karatu ko karancin shekarunta normal ne ni a wajena. Miye amfanin ya auri wayayyar mai ilimin tazo ta zame masa damuwa shi da mulkin nasa damu kammu. Yanzu ko shi zai bama matarsa tarbiyyar data dace akan tsarin mulkinsa ta tashi akai kuma yay alfahari anan gaba Maah. Dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan ki musu addu'a sai kiga wataran komai ya zama yanda kike so. Kwana nawane zata kammala karatun ma, ina amfanin ya auri sa'arsa tazo ta rigashi tsufa........”
Hannu Gimbiya Su'adah ta ɗaga mata a fusace. Cikin zafin rai ta nuna mata ƙofar fita. “Tashi ki fitarmin kafin na saɓa miki Mardiyya. Nama manta tare nake da mara kishin kanta balle waninta. Shasha kawai da batasan abinda ke mata ciwo ba”.
Miƙewa Mardiyya tai ta ɗauka bag dinta da faɗin, “ALLAH ya huci zuciyarki Maah, amma nidai gaskiya na gaya miki, ita rayuwa bata da tabbas. Banga kuma aibun yarinyarnan ba, hasalima yanda take da ƙarancin shekaru idan kika jata a jiki zakisha mamakin ribar da zaki samu akan shi kansa Ramadhan ɗin da kike ganin kamar an nisantaki da shi. Ni na wuce dama zuwa nai na dubaku tunda ban samu shigowa gidan ba koda babbar salla”.
Ko kallonta Gimbiya Su'adah bata sakeyi ba. Itama saita fice a ranta tana nemawa mahaifiyar tasu shiriyar ALLAH da fatan ganewa. Dan tuni ta fahimci Adda Asmah na ɗaya daga cikin masu rikita lissafinta akoda yaushe. Su kansu wani lokacin haɗata ake dasu taita zuba musu tujara kamar ba ita ta haifesu ba.
Waɗan nan maganganu na Mardiyya sun sake harzuƙa gimbiya su'adah. Rai ɓace ta shirya bayan sallar zuhur ta nufi sashen Anne. Abinda takan haɗa kwanaki huɗu batai ba. Dan gaida surukai kullum baya cikin tsarinta duk da gida ɗaya suke rayuwa. Anne tayi mamakin zuwan nata amma sai ta danne ta tarbeta kamar yanda suka saba. Babu wani ɓoye-ɓoye gimbiya Su'adah ta sanarma Anne abinda ke a ranta.
Murmushi kawai Anne keyi jin bayanin surukar tata. Ita bazata hanata zartar da hukuncin aurawa Ramadhan wata matarba, sai dai bazata amince a cutar mata da jika ba dan ita kanta ta jima da fahimtar wacece Adda Asmah.
“Shike nan kije zan samu Dattijo da batun, zai kuma nema Ramadhan ɗin yaji tabakinsa. Idan ya amince da auren mu masu murna da farin cikine akan hakan. Fatanmu ALLAH ya basu zaman lafiya kawai.”
Duk da ranta ya ƙara ɓaci sai ta amsa da amin. Ta fice zuciyarta na ayyana mata maganin Ramadhan da zatayi. Dan bazata taɓa yarda ya nunama kakaninsa baya son auren ba. Tasan yana bijirewa shikenan bazasu bata goyon baya ba.
*__,,,,___________,,,,__*
Barci ya sake sha sosai har wajen sha ɗaya. Ring ɗin wayarsace ma ta tilasta masa buɗe idanu da ƙyar. Ido a rufe ya kai hannu a side drawer da nufin kashe wayar sautin ring ɗin ya hanashi hakan dan yasan Maah ce. Komai bai kawo ransa ba sai tunanin taji baida lafiya maybe. Ya buɗe ido da ƙyar yay picking yana kaiwa kunnensa.
“Barka da asiba Maah!”.
Gaban Gimbiya Su'adah ne ya faɗi, tai saurin cire wayar a kunenta tana kallo.....
“Maahhh!”.
Daya sake faɗa cike da kasala da barci ya sakata gaskata zarginta. Da sauri ta latse wayar ta kasheta gaba ɗaya kanta na juya mata. (Har ita Ramadhan zai amsawa waya yana tare da mace. Innalillahi..... Shikenan yaronta ya gama watsewa hanun jikar karuwai).....
A ɓangaren Ramadhan kuwa tunanin network ne ya sashi sake dialing number ɗin tata da ƙyar yana kaiwa kunne da lumshe idanu. Sai dai switch up ma ake sanar masa. Yanayin rashin ƙarfin jikin har yanzu ya sashi ajiye wayar kawai da tunanin zuwa anjima zai nemeta. Sai dai ya sake jan ƴan mintunan a kwance kafin ya tashi zuwa bayi, sosai yunwa yakeji na ci masa hanji, badan haka ba