Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 70788 words

Chapter 10 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt

Ads the beginning of article before Image

07 Jul 2024

743

Ads at the middle of Article

shi ba ma'abocin fitar rana ba ne. Ganin na kasa tashi ne yasa aka kawo mishi abinci daga gidansu , na nashin dandai ina da cikin amman da ko ba abinda zanyi mishi saiya tasheni dan dai ya ɓatamin rai. Ba abinda naci tun kalacin safe sai bayan sallah isha'e na jiƙa garin rogo { garin kwaki } kuma Dikkon nasa da kanshi a siyomin , dan bana ra'ayin abincin da aka kawo. Shine yasa aka kawo buhu ɗaya. Bayan yayi faɗa wai salan inje inba babynshi wahala zanci wani gari bana daijin magana , nace baby ne zaici garin ai bani ba , wai babu wani ya faɗa yana hararata nace da gaske shine yasa aka kawo.


Bedroom na sameshi zaune saman gado da irin zaman ɗazu yana kallon ƙwallo. Kusa dashi na zauna , ina zama ya gyara min zamana tare da matsowa ya kwanta ya ɗora kanshi a jikina ya riƙe ƙuguna da duka hannayenshi yana kallona , nima kallonshi nayi tare da cewa tashi muci , ɗauke idonshi yayi daga kallona yana kallon tv yace me ye ? Gari , murmushi yayi me sauti yana cewa Allah ya sawaƙe , garin ne Allah ya sawaƙe ? Ah ni bana iya cin garin gaskiya sai kace inyamuri....? Aini inyamurar ce shi yasa zanci , shiru yayi bai sake magana ba , ya ɗauki wayarshi yana duba dokuna.... Shikenan tunda bara kaci ba bari in tafi nayi maganar ina ƙoƙarin tashi , riƙeni yayi sosai yaci gaba da abinda yakeyi a waya....


Ni tafiya zanyi , ba tare daya kalleni ba yace kinyi fushi ? Ey , tou ina ci kawo min cokali , ai bada cokali akeci ba , da me akeci ne ? Da hannu , tou bani ya ƙarasa maganar yana buɗe bakinshi ba tare daya kalleni ba... Ai haka kayimin haggunce , ya zanyi ? Ka tashi.... Tashi yayi zaune amma har yanzu hankalinshi yana kan wayarshi saidai bakinshi a buɗe yake , bashi nayi , riƙeshi yayi a bakinshi tare da ɓata fuska ya taɓe baki yana juyashi , ƙara ibowa nayi. Da garin a bakinshi yayi magana cewa dan Allah An mata ki kyaleni kinga banda lafiya..... Dan Allah kaci , kallona yayi a sakace yace baya tafiya , jeka dashi kawai ka kora da ruwa..... Idan banci ba zakiyi kuka ? Dariya nayi dan yadda yayi maganar kamar ƙaramin yaro wallahi. Shagwaɓa tana mishi bala'en kyau kuma yana burgewa idan yayi , hada hawaye. Na faɗa ina kallonshi da irin kallon da yakemin. Ɗan kauda kanshi yayi gefe tare da shafa kanshi yaci dakel , yace ngode. Hahahaha bawan Allah , yau da Jiddah tana nan da nace mata Dikkon ma da kowa da kowa yake taƙa dashi ni nasa ma yaci garin kwaki dan ubanta....


Aimu dama mun saba , kuma ni ban manta ba har yanzu nasan martabar gari , duk irin matsayin da nake a yanzu baisa na manta da rayuwar baya ba. Ai gari yayi mana kuma mu bama wulaƙanta shi duk matsayin da mukaje muna tare da gari gaskiya , kuma ina ƙara godiya da Allah yasa nake a wannan matsayin , haka nan naji ina sha'awar garin. Na ɗan haɗo rayuwar baya da yanzu ! Nayi tunanin nima bazan iya ci ba , ashe dai zan iya ? Allah ya ƙara yalwata arziƙin Dikko amin.... Da gefen ido yake kallona har na gama ci. Saida na gama ya kalleni ta gaba yace sannu , yawwa na faɗa tare da tashi dan fitar da filet in , idan kin jiye kizo , ni bazan dawo ba , ki dawo nace miki , ban sake magana ba na nayi gaba , tana fita ya tashi dakel yaje ya ɗauki cingom yabi bayanta.....


Ɗakina na sameshi kwance yana waya , ɓata rai nayi tare da samun can gefe na zauna na ɗauki wayata , text in Mai gilashi ne kaɗai , ban zo ba , me yasa ? Idan naga D ' K baya nan in kirata dan Allah , yau D ' K bai fito ba lafiya ? Ko har yanzu baida lafiya ne ? Inyi ƙoƙari in riƙeshi gida na kwana 3 kar in barshi ya fito in rufa mata asiri don girman Allah za tayi wani aiki , kuma inzo makaranta duk yadda za'ayi idan Allah ya kaimu inzo makaranta dan Allah.....


Taya zan riƙe Dikko a gida in hanashi fita ? Abinda ma baya yuwuwa ne gaskiya. Wane aiki ne zatayi ? Koma dai miye Dikko bai zama , yanzu ma jira yake dare yayi ya lallaɓa ya fece abunshi , zuciyata kuwa cewa tayi ai saidai ki jashi kuyi faɗa kawai tunda dai yace bazai dakeki ba tunda kina da ciki. Ci gaba nayi da cika fuska ina ɓata rai , bayan ya gama waya yace An matana miye ? Dikko wai mema yasa kaje kayi ma karuwa liƙi ? Da yanayin rashin jin daɗi yace ba karuwa bace ba , Mamanta fa ƙanwar Dady ne. Ni bana san sanin wani dangantaka ko alaƙa , amma me yasa baya bakimin magana ba sai yanzu ? A lokacin abun bai shafeni kamar yanzu ba , yanzu kinajin fitina kenan ko ? Ey fitinar nakeji , tou ai ba ƙyaleki zanyi ba , zaneki zanyi. Fashewa nayi da kuka sai abun yaci gaba da zungurar min zuciya kamar yanzu ne akeyin abun wani irin azababen kishi yaci gaba da ƙwal²rmin zuciya. Da videon da Yusra ta turo mishi gaba ɗaya na ƙwace na fara ɗuɗɗurma ma Sharifa da Yusra zagi , da sauri ya taso yazo kusa dani yace haba An mata meye haka ? Cikin kuka nace dama ai dole zakace zaka dakeni tunda na taɓo karuwowin ka , kiyi a hankali kinsan bamu kaɗai ba a gida , so kike ace kin rainani ne An mata ? Ace na rainanka kaima ai raini yasa kaje kayi mata liƙin a gabana , da Jiddah ce ka isa ? Saini duk wani shararka da komai akan An mata. Saina faɗar da ƙarfin dandai kar asirinka ya tonu asan kana da karuwowi , salati Dikko yayi tare da cewa idan dai kika kasheni hankalinki ya kwanta... Nine ma nake da karuwowin ko ? Ni An mata ? Ya ƙarasa maganar yana riƙoni jikinshi , fizgewa nayi na miƙe naci gaba da kuka ina zagin su Sharifa.


Riƙeni yayi da ƙarfi. Ya rumgumeni jikinshi , bayan wani lokaci ya sassauta riƙon zuwa riƙo da tako mai kyau ya fara maida lumfashi da salon da yasan zaisa na ɗauke wuta da wuri , ƙasa² na farayi da murya cikin shashshekar kuka ina cewa amma ai kasan baka kyauta ba , yi haƙuri yarinya na yake faɗa yana ƙara sautin. Kasala ta fara zuwa. Dakel na sake furta kuma na ɓata dakai , ai bamu ɓatawa An mata yayi maganar yana fara kukan kissarshi , wani ɗan iskan kuka yakeyi cikin kurman sauti maisai jiki ya mutu da sauri , sai ya riƙayin wani jaririyar ƙara "yar ƙararrama yana numfashi , shidai yasan yadda yake abunshi amma dole dai idan kikaji sautin sai tsikar jikinki ya tashi , kasala da san kasancewa dashi ya tattaru ya lulluɓeki a lokaci guda dan da shagawaɓe yake fitar da sautin sai kuma ya ƙadaddabe ki da raunanannen riƙo , hmmm Dikko ? Bayajin magana kona misali. Saida ya gama sinsineni ya fara lasar bakina , muƙus nayi shiru , a gajiye yaja ni ya ɗora saman tsakiyar gado dakel. Yana maida numfashin wahala da yanayin rashin lafiya cewa bakijin magana kuma tunda kika ɓatamin rai naushin mai ƙarfi zanyi , riƙeshi nayi ina kuka , kallona yayi a shagwaɓe yace me ye kuma ? Yayi tambayar yana ɗaure fuska , na bari , a , a ya faɗa badai bakijin magana ba ? Yi haƙuri. A wahalce ya gyara kwanciyarshi yana cewa tou zoki bani haƙuri ya ƙarasa maganar yana min dogon kallo ranshi a haɗe........ Matsawa nayi kusa dashi nace yi haƙuri , kallona yakeyi har yanzu , bayan kamar mintuna biyu yayi murmushi tare da ɗan tattauna cingom da salon jan rai sannan ya huroshi irin abun nan kwai ya kuma riƙe kwan. Da kanshi ya nunamin in sauka muje , sauka nayi. Shima ya sauka ya biyo bayana har ɗakinshi , inda aka ajiye kayan da ya dawo dasu daga tafiya yace in buɗe inyi ta sakawa yana gani. Ya ƙarasa maganar yana kwanciya saman gado,


Wasu irin riguna ne masu kyau da tsada , bawai baƙaƙe bane ba dukansu kaloli ne masu kyau launin "yan gayu , takalma masu kyau haɗaɗi suma , sai sarƙa da "yan kunne "yan hannu da zobe kala biyar kuma duk na zinari ne masu masifar tsada. Manya² bawai "yan kucilaye ba kamar na wasan yara. Jakunkuna turaruka masu ƙamshin gaske da dai duk abinda yasan zai haɗani ya siyo , haka naita gwadawa ina saka takalmi ina bada step yana daga kwance yana kallona , idan bai burgeshi ba sai ya gyaramin , idan na burge shi da yawa yana daga inda yake zaice inzo , idan naje saiya sumbace ni yace An mata mai kyau. Ko kuma yace bara in miki hoto Yarinya....


Mai gilashi yau ta kasa fita zuwa wurin Alhaji. Sai zagaye takeyi tsakanin ɗakinta da ɗan madaidaicin tsakar filin BQ insu , meke faruwa ne ? Sultana ba reply kuma ba fita ba kira ? Kardai zuwa tayi taje ta nunawa Dikko cht in ? Kila ana can ma ana faɗa , ta shiga 3nta , ɗaki ta koma ta ɗauki wayarta ta fara kiran Sharifa.....


Babu wani daɗewa ta ɗauka , ko gaisuwa babu Mai gilashi tace alherin Allah dai ya kaimu wannan rana amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida , ni Mai gilashi ? Oh , naga Nana Ade a gidan amarya , ashe ina da rabon ganin wannan rana..........? Hmmmm , ׳ Sharifa tayi dariya cike da izza ita amaryar Dikko , Mai gilashi taci gaba da cewa ni ina nan na duƙa addu'a Allah dai yasa karya haɗaki da matarshi. A yatsine Sharifa tace ni wannan ai ban ɗauketa a mace ba. Kinsan da haɗemu zaiyi sai nayi wani nazari nace masa bana so kowa ya raba mata gidan ta , yanzu ke ina ne zai ajiyeki ? Cike da kwarin guiwa tace G R A , wannan gidan duk ke ɗaya Sharifa ? Cass ni ɗaya abuna daga ni sai bataliyata ga kuma Dikko nawa abuna , kai zanfa zuba tasha danni wannan banzar matar tashi banajinta wallahi. Dan bata da ban²nci ita da kashin da nayi a toilet ruwa kawai zan sheƙa tabi 5v abunta.... A hankali dai Mai gilashi taci gaba da zungurar mata ciki , daga ƙarshe tace ko tayi magana da Dikko ne ? Tace ai zasu haɗu 1:00am a G R A , Mai gilashi tace idan sauran kishiyoyin naki sun bar miki shi ya samu zuwa wurinki ko ? Sharifa tace waye su ? Bana ce komai ba , amma ni na faɗa miki yau gobe da kuma jibi Dikko ba naki bane ba , na waye......? Murmushi Mai gilashi tayi tare da cewa na wata gogaggar ce , tana can ta ɗaukeshi sai sun dawo.......... Tana faɗin haka ta tsinke kiran tare da kashe wayar gaba ɗaya....


Ya Yazeed ni wallahi na kasa gane wannan farashi da kake magana. Jiddah da Yazeed zaune a mota kuma a gidan Rabiya ake zancen , dan jiya da Dikko ya dawo daga tafiya da Papi ya maƙale yace shi zai zauna wurin Nabeela sai Momy tace ita Jiddah ta tafi can gidan Rabiya ta zauna , kora ce da hali akayi mata amma ta kasa ganewa jakar. Shiru Yazeed yayi yana kallon sitiyari , Jiddah tace Ya Yazeed kayi shiru baka ce komai ba.....!!!


Cike dajin haushi yace tunda bakya ganewa a daina maganar ko dole sai anyi auren ne wai...? Haƙuri ta bashi tare da cewa bara in kira Nabeela. Tayi maganar tana danna wayarta dan neman lambar Nabeela , anshe wayar Yazeed yayi daga hannunta yana cewa kema kanki zawara baki fahimta ba taya ita Nabeela zata sani ? Shiru tayi tana saurarenshi , Yazeed yace waye zai saci kayan wani tou inba ɓarawo ba ? Jiddah tace gaskiya , shi kuma yaci gaba da cewa ni sakarai sai in biya sadaki lefe wurin zama abincin da zakici har na tsawon sati biyu da kuɗin hidima sai su tashi a banza bayan kwana biyu in sakoki alhalin ban gama gurje kuɗin ba....? Tou ya akeyin abun ne ? Yadda akeyin abun tsarin da komai kawai ki bada miliyan 5 zanji da komai , Ya Yazeed yanzu banda kuɗi duka² fa a account ina baifi miliyan ɗaya ba ,


Kallon rainin wayau yayi mata yana cewa karki ɗauki Yazeed sakarai mana ? Wallahi kuwa Yaya ta faɗa kamar zatayi kuka , kina nufin duk zaman da kikayi da D ' K haka nan kika fito fayau ba wasu manyan kuɗi a account ? Yaranshi ma sunyi kuɗi bare kuma ke matarshi ? D ' K da macen zai bari kiyi talauci ? Nafa san D ' K fiye da yadda ke kika sanshi. Halinshi da komai na rayuwarshi ni ina iya rubuta littafi Jiddah , ai bana tunanin nan da shekaru biyar miliyan biyar za tayi miki wahala wurin bayar da ita a matsayin kyauta. Bare kuma wannan ba kyauta zaki bayar ba kece za'ayi ma hidimar dasu , ina gwala²i ? Ina kuɗi Jiddah......? Wallahi duk na siyar na ba malamai , sakaran kallo yayi mata , taci gaba da farfaɗo mishi irin manyan malaman data bi amma har yanzu shiru kuma kullum idan ma Ya D ' K ya ganta kamar zaici ƙaniyarta ne. Yazeed yace tunda kinbi malamai ba'a dace ba ki zubo hannun jari a asusun banki na , zaki sha mamaki , Yaya banda kuɗi wallahi , Yazeed yace idan ba kuɗi ba aure karta sake kiranshi idan bata samu ba , daga haka fira ya tsaya. Yazeed ya tafi ita kuma ta koma ciki da tashin hankali , ita dake so suyi aure ya sakota ta koma gidan Dikko ? Ya kuma Yazeed zai rusa mata bajet haka ? Dole ma a samu kuɗin a daren nan...


Tunda ta shiga take tunanin inda zata samu kuɗi. Ta juya ta zaga ta rasa yadda zatayi , tayi waya wa ƙawayenta ko zata samu duk kowa yace babu , Ashiru ta kira yace shi baima san yadda miliyan take ba bare kuma miliyan 5 , tambayarshi tayi idan ta tambayi Dikko zai bata ne ? Ashiru yace tou shidai bai sani ba amma ta jaraba kila ta dace tunda su ɗin "yan uwane. Bayan Ashiru ya gama waya da Jiddah ya kira Dikko yake faɗa mishi. Tun kafin Jiddah ta kira Dikko ya tura mata miliyan goma , shi a ganinshi idan ta nema bata samu ba zataje tayi iskanci ne , shi kuma dudduniya abinda ya tsana yaga mace tana barbaɗewa..... Shi kuma Ashiru wallahi da yasan Dikko zai bata kuɗin da bazai faɗa mishi ba , dan koshi yana iya bata kuɗin amma haushinta yakeji kamar ya babbakata da wuta tunda taba Papi fiyaya². Dan yasan bata iya tunkararshi da zancen ya bata wani abu saboda abinda tayi ma ɗanshi. Shi kuma Dikko ba haka yake ba , idan dai ta haɗoku zaiyi hayaniyar shi yayi bobbotanshi tare da rufe idanuwanshi ya zazzaga ma mutum rashin mutunci dai² iyawarshi , kuma wani dalilinshi bazai hana shi ya kyautata maka ba , haka ta faru dashi da Yazeed ai. Lokacin da yake tarayya da Sultana akace ya korashi daga company yace su ƙyaleshi , yanzun ma bashi ne ya koreshi ba. Ashiru ne kuma ya kawo Abbakar ya ɗora , da Dikkon yayi magana yace Mai gida haka za'ayi , kuma shikena ya wuce wurin......


Wani irin ihun farin ciki Jiddah ta kwarara , lokacin da taga kuɗin da ya shigo account inta kuma daga Dikko ne , tayi murna sosai ta fara kiran wayarshi , a kashe yake , ita kuma a tunaninta na neman biko ne , dan haka ta zauna ta tsara yaudararrin kalamai ta aika dasu ta whatsapp tasan komai dare zai hau kuma zai gani , kila yana jin kishi ne Yazeed zai aureta shi yasa ya fara neman shiri , ita kuma batayi tunanin Ashiru ya faɗa mishi ba a ganinta kai tsaye ya bata dan kyautatawa , ai tasan wannan sharar fage ne idan manyan suka taho account inta baya ɗauka. Kai Yaya D ' K mahaukaci ne , aiko bayan kwana biyu zatace ya bata 20 tasan zai bada 40 ne kaɗan ne daka aikinshi , kai ai dole ma ta koma a ci duniyar nan da ita , tayi murna har ta rasa irin wacce zatayi , gaskiya Dikko baisan darajar kuɗi ba haka nan yake nemansu mutane na cinyewa , a nata tunanin kenan...........


Bakajin komai sai ƙarar ragonshi dake fita { munshari kenan } kwar , kwar , kir² kwar² , da sanɗo ta shiga ɗakin bayan ta tabbatar da babu mai ganinta har jikin wadrof, a hankali ta buɗe wadrof ƙiyyyy , ƙarar buɗewa , a ɗan tsorace ta cije haƙoranta tare da yaƙewa cikin yanayin tsorata ta kallo inda Dady yake kwance yana jan rago. Maida hankalinta tayi wurin neman takaddun gidajenshi , saida ta sabko kayan tass sannan ta taka tayi sama bayan wani lokaci ta sauko da wani fayil , a ƙasa ta ajiye ta dudduba tsadajjin gidaje da Dady yake taƙama dasu a cikin anguwannin "yan gayu da akeji

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads