Showing 21001 words to 24000 words out of 70788 words
Chapter 8 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt
, kiyi tunani , ki tuna. Tuna׳... Ki tashi ƙura kuma kiyi ƙoƙori a yada dogon zango in jini...
Shiru nayi bayan na gama karatanta saƙon Mai gilashi , wato nine zata latsa ? Tou wai meye ma matsalar ta da Sharifa ? Bata zargin Dikko kamar ya kuma ? Shi Alhajin ina iyalin tashi take ne a wannan dogon daren ne ? Ita Sharifar kuma wai me yasa ne kowa yakejin tsoronta ? Nima lallai ina san sanin abinda kowa yake tsoron ma Dikko Sharifa , ina san gani kuma nima ina san sani. Ajiye wayar nayi tare da ɗaukar ɗamara kamar yadda Mai gilashi tace , cire hijabi na nayi na ƙara mammatsa turare naɗan kakkaɓe dai bayan na tabbatar nayi na nufi ɗakin Dikko.....
Da sallama na shiga , yana kwance a inda na barshi , amma yanzu ya juya baya yayi takurarriyar kwanciya mai nuni da gajiya. Itama sallamar a gajiye ya ansa ta. Saman hannun kujera na zauna tare da cewa sannu da zuwa. Ba tare da wani damuwa ko rashin jin daɗin da farko ban masa ba yace yawwa , shiru ya ziyarci palon har na tsawon mintuna 3. Nice na katse shirun da cewa ina Papi da Sharifa ? Shiru yayi baiyi magana ba , dakai nake. Juyo da kwanciyarshi yayi yana kallona amma baiyi magana ba , ɗan kauda kaina nayi gefe haka nan naji gabana yana faɗuwa. Ban sake magana ba na miƙe , riƙoni yayi tare da jawoni a hankali zuwa saman jikinshi yakai hannunshi yana shafo cikina.
Kwantar da kaina nayi haka ta tsaye ba ta gefen fuska ba ina kalloshi cikin damuwa. Murmushi yayi kaɗan ya tsareni da ido , gyara kwanciyar fuskar tawa nayi zuwa gefe fuskata na fara wasa da gemunshi. Zame hannuna yayi daga wurin , sake maidawa nayi ya sake zameshi duk munyi haka yakai sau biyar , zuciya nayi na tashi da niyar fita , karki fita zo kiji , shiru nayi fuuu na wuce , An mata dake nake fa kizo nace , haka nan naji zuciyata tanamin tuƙuiƙi. Da ɓacin rai naje ɗakina , ina zuwa toilet na wuce na wanke hannuna ina cewa kuma bazan sake taɓa gemunka ka ba har abadan duniya , dan kaga ina taɓawa shine zaka ciremin hannu tou bazan sake taɓa maka ba tunda baka so Dikko...
Cike da damuwa yabi bayan Sultana. Ita kuma a dai² lokacin data fito daga toilet. Rufe ɗakin yayi sannan ya matsa jikin bedsite ya ajiye tarkacen wayoyinshi bai mata magana ba ya wuce toilet shima. Gefen gado na zauna naci gaba da haɗe rai kamar an sace uwata , shima ranshi a haɗe ya fito kamar an kaiko mishi saƙon mutuwar uwa uba a lokaci ɗaya....
Bedsite in kusa dani ya zauna tare da bani umarnin ni in matso kusa dashi , ƙin matsawa nayi na ɗauki wayata ina latse². Ki matso nan nace kuma ki ajiye wannan wayar tun kafin raina ya ɓaci , basar dashi nayi naci gaba da latsan waya cikin taurin kai da ƙaddarawa ma bashi a wurin. Miƙewa yayi ya ɗauki wayoyinshi ya tunkari hanyar fita , me yaji me ya gani ? Oho ya dawo , saida ya zauna ya ajiye wayoyinshi ya ɗan riƙoni jikinshi da soyayya , hannuna ɗaya ya riƙe tare da ɗorawa a saman fuskarshi yana shafawa a hankali harya gangaro saman gemunshi yana shafawa kuma ya tsareni da ido da kallonshi mai burgewa yanayin wasa da iskar bakinshi cikin salo mai yanke damuwa.
A ɗan damuwance nace ai tunda baka so ina taɓa maka na daina , ina so yayi maganar yana rage girman idanuwanshi. Ai nayi fushi , na bari , ya faɗa yana min kallon rainin wayau. Ey dama dole zakace ka bari tunda ga Sultanar banza yanzu ne kasan amfani ta rashin kunya kawai. Da yanayin tsinkuwa ya kalleni yace wai me ke damun kanki ne ? Haba An mata ni banajin daɗin abinda kikemin haka ! Ey dama ai dole zakace bakajin daɗi tunda ka ɗaukeni Sultanar bayan fage.
Tou waye ta bayyanannen fage An mata ? Kasan inda ka barta , ya za'ayi in sani tou ? Jakar da ta rakaka tafiya , taje ta rakoka Katsina tunda baka san hanya ba , ni danma ka ɗaukeni bansan abinda nakeyi ba ai baka faɗamin zakayi tafiyar ba saidai na tashi na gani zaka tafi , ko inda zakaje baka faɗamin ba sai wasu "yan iska karuwan banza , kuma bana sanka dama jira nake ka dawo Allah bazan sake zama dakai ba na ƙarasa maganar ina fara kuka , cikin kuka naci gaba da cewa da wata "yar iskar karuwa mai turo maka hoton tsiranci tunda dai yanzu ka daina so na kawai ka sallameni nayi gaba abuna , dan dana fita daga nan wallahi wani babban Alhaji zai kwasheni ya tafi dani can ya gina min sabuwar rayuwa mai inganci. Wacce babu firgici ko tashin hankali a cikinta. Ni ɗawisuwa ce kuma ai kasan babu yadda za'ayi abar ɗawisu sake yana yawo. Martabashi ake , ɗawisu baka rayuwa gidan matsiyata sai gidan kuɗi. Idan ba gidan kuɗi ba sai gidan sarauta , da rubibi za'a kamani kuma duk sai masu kamanin sunsha wahala duk sai sun bugu da wahala sannan mai rabo zai sameni dakel , a dakel inma sai mai tsanantaccen rabo gidan kuɗi nawa ka leƙa amma babu ɗawisu ? Kuma kaji kunya an girma ba'a san an girma ba mai gemun yaudara. Taƙaitaccen murmushi yayi ba tare da yace wani abu ba ya tsare Sultana da ido.
Ci gaba nayi da feƙa rashin mutunci , Dikko ya tsareni da ido cike da mamaki shi al'ajabi ma ya hanashi yayi magana yadai bita da kallo , kuma gidanka banza kaje ka ajiye duk jakar macen da zaka ajiye ni bana zama da kishiya , ai da daka dawo sai kaje can inda kake zama sai 3 na dare ka dawo gidan , a gajiye ya jawoni jikinshi ya rufe idonuwanshi cikin ɓacin rai yace ƙaramar yarinya. Daga haka bai sake magana ba ya fitar dani daga jikinshi yanayin fushi. Nayi kwanciyata naci gaba da bacci....
Bayan Sultana tayi bacci Dikko ya tsareta ido yana sake² a zuciyarshi. A daren yau baiyi bacci ba , kuma ɓacin rai bai barshi yayi cht in dare ba , gyara mata kwanciya yayi tare da jan bargo dan lulluɓeta sai kuma ya tsaya yana kallon cikinta. Na tsawon wasu mintuna sannan ya tafi da bargon a hankali ya lulluɓeta cike da soyayyarta a zuciyarshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita bayan ya kashe hasken ɗakin.
Ya so a daren nan yaɗan rage nauhi amma An mata ta ɓata mishi , a gaban idonshi take cewa wani babban Alhaji zai kwasheta ! Ashe idan ya mutu An mata mantawa datayi dashi ? Bara tayi mishi addu'a ba ? Papi da wani babyn zata zubar dasu taje tayi sabgar gabanta ? Tunani barkatai a ranshi. Ya saƙa ya warware baisan iyaka ba , ƙaramar yarinya ta zauna tai ta faɗo mishi maganganu na yarinta , mtsww wannan damuwa tasa kafin safiya ta waye Dikko ya kwanta rashin lafiya..... Fatarshi ya wuce kawai kar yaga wannan baƙar ranar wallahi.....
Ni bansan Dikko bashi da lafiya ba , gari yana wayewa na shirya nai tafiyata makaranta banje ta ɗakinshi ba. Papi kuma yana can wurin Momy dan Nabeela ta dawo da suka fara zuwa tacan shine ya liƙe wurinta......
A makaranta. Yau ajin ba daɗi dan Mai gilashi bata zo ba , dana kirata na tambayeta abinda yasa bata zo ba , cemin tayi ina cht in da tace na turo mata ne ? Sai anjima zan turo miki , tou ya akayi kikaje makaranta bayan kuma ance D ' K baida lafiya ? Wata irin mummunar faɗuwar gaba naji , meya samu Dikko na tambayi kaina......? Meke damunshi har abun ya fita waje yabi duniya ni banda labari ? Tsinke kiran Mai gilashi nayi na fara kiran wayar Dikko , bai ɗauka ba , Ashiru na kira shima bai ɗauka ba , Umar na kira , tana shiga yana ɗauka , Umar kana ina ne ? Qerau , wai me yake faruwa a goruba ne ? Ba komai , kowa lafiyanshi qalau ? Lafiyan kowa qalau ya bani amsa... Kashe wayar nayi na sake kiran Mai gilashi. Tana shiga ta ɗauka , Mai gilashi waye yace miki Dikko bashi da lafiya ne...? Sharifa , ki duba a whatsapp na ajiye miki saƙo kiga cht inta da mijinki , gaskiya Sultana baki da wayo , duk kina ina wannan iskancin ke faruwa ne ? Waton shi mai wayau idan yayi magana sai ya goge maganarshi , na turo miki dai ki gani abinda na fahimta ni zanji da sauran aiki , saboda yaƙin yafi ƙarfinki nima nace na Dikko An mata , tana faɗin haka ta tsinke wayarta....
Haka nan naji gabana yana halbawa ɗil׳ sai tashin hankali da nakeji gaba ɗaya wani ruɗu yazo min na kasa zama. Wurin Farisa nabar jakata na nufi gida cikin tashin hankali , a ƙofar shiga palon ƙasa nayi parking kuma gidan yana nan cike da mutane maza da mata kamar yadda yake kasancewa a ko wane rana. Kowa yana hidimar gabanshi da gudu na shiga ciki kai tsaye ɗakin Dikko na wuce ko takalmi na ban cire ba danni bana shiga ɗakinshi da takalmi komai sabuwarsu dana shiga palo zan tuɓesu......
Zaune na sameshi gefen gado ya jingina bayanshi da kan gado ƙafafuwanshi miƙe ɗaya saman ɗaya ya rungume hannayenshi kanshi yana kallon ƙasa. A tsorace na isa wurin ina cewa Dikko me ya sameka ? Bai ɗago ba kuma baimin magana ba , kusa dashi na zauna na ɗago fuskarshi , kallona yayi. Kuka ? Na tambayeshi ? Gyara bakinshi yayi yana ci gaba da kallona , rumgemeshi nayi nima na fashe da kuka , cikin kuka nace me ya sameka kakeyin kuka ? Zuciyata , shine amsar daya bani , amma me yasa baka faɗamin baka da lafiya ? Na ƙarasa tambayar ina riƙe fuskarshi da duka hannayena biyu. Ba kinsan na kwana gidan ba ? Idan har ina da mutunci da daraja zaki tafi makaranta baki zo kika ce wannan banzan ka tashi lafiya ?
Kefa yarinya ce , ni kuma na tsufa inji ki fuskata ta fara squeezing. Kamar ƙaramin yaro yake cemin nima fa ɗan saurayi ne , duka²na a nawa nake hararata yayi cike da soyayya sannan yace , ni a haka nayi miki tsufa dai ko ? Idan dai ni tsoho ne kema tsohuwarce tunda daga ni harke kowa ɗanshi ɗaya da zaki wani kalli tsabar idona kicemin wani Alhaji zai kwasheki. An mata wannan mutunci ne ? Ke da , da ne lokacin ina Dikkona har kin isa ki faɗamin wannan iskanci ban kashe ki ba ? Kika mutu murus , babu wanda yaji ba kuma wanda yasan anyi saidai a nemeki a duniyar nan a rasaki. Ko yanzu ni ba iya dukanki ne banayi ba wallahi tausayinki nakeji saboda kina da ciki. Duk wannan iskarcin da kikeyi ba tsoro yasa na zuba miki ido ba , ko zan mutu idan bana tare dake ni banajin kaina ke nakeji. Duk a wahalce yake magana cikin shashsheka a sanyaye cikin laushin murya maisa natsuwa....
Ki kalleni tsaf daga samata har ƙasa na kinsan ni ba sakaran namiji bane ba , kuma kinma san na tsufar kikace kina so na ? Tou ni ba tsoho bane ba , duka² shekaruna nawa ma ? Tsoki yaja sosai , tare da nunani yana cewa a gabanki ma zan zauna ina kwancewa har nake da lokaci maida miki magana , tsohon ne yayi maganar yana min wasa da harshenshi cikin salo mai ɗaga hankali ya raka wasan da kallonshi maisa mutum yaji cikinshi na halbawa , a kasalace na matsa da fuskata kusa da nashi na ɗora bakina a bakinshi. Maida harshenshi yayi yana murmushin jin daɗi tare da lumshe idanuwanshi a hankali cike da shauƙi , yana nuna yanayin zaƙuwa kuma har yanzu idanuwanshi a rufe , baya nayo da fuskata ina kallon kyakkyawar fuskarshi , bai buɗe idonshi ba yana a rufe kenan yana jiran tsammani , jina shiru yasa ya laliboni tare da riƙo kaina da hannunshi jikinshi yana kyarma ya haɗe cikin soyayya , bayan wani lokaci ya cire "yar guntuwar hijabita ya kwantar dani gefenshi ya kwanto shima har yanzu idonshi a rufe cikin yanayin farin ciki. Battery low......
Mai gilashi kuwa saida ta gama tuɓe kaf sirrin Sharifa sannan take tambayarta shin ko Dikko yana da wani logo ne ? Sharifa tace bashi da. Shi miskili ne kuma yana da wahalar sabo baya maganar data wuce biyu , baya dariya kuma baya murmushi idan kuma surutunki yayi mishi yawa zai tsareki da ido ne. Kinga taya kuwa za'a iya gano logon shi ? Amma da me kike da ibar mishi fili ? { abinda takeyi tana ɗaukar hankalinshi kenan } Sharifa ta faɗa mata , Mai gilashi tace tou ko ya taɓa faɗa miki aibun matarshi ne ? Da dalilin yasa zai aureki ne ? Sharifa tace gaskiya a , a , yadai cemin shi yana san matarshi sosai kuma yana tausayinta bai haɗata da kowa ba kuma yarinya ce ni na girmeta. Duk kuma wanda ya taɓota tou ba itace ba shine aka taɓo. Idan An mata tayi kuka shine idan tayi farin ciki shine. Wanda yaso mata farin ciki shine yaso , kuma duk yadda yake san mutum idan ya aibata ko munana mata tabbas zaija layi tsakanin shi da koma waye , shine kaɗai ya isa ya ɓata mata kuma shine farin cikinta duk duniya bata san kowa ba saishi , haka bata gane kowa saishi. Shi kuma itace rayuwarshi , lumfashi , bugun zuciyarshi , itace komanshi dan haka in kiyaye. Kuma shi abinda yasa zai aureni shi bawai ra'ayin shi bace ni , ba irin tsarinshi bace ba. Umarnin Dad inshi ne , Mai gilashi tace tou me ya kawo akayi maganar ne ? Ko haka kawai ya faɗa ? Sharifa tace nice dai naɗanyi maganarta , duk dalilin maganar nan kuwa matar Babanshi ce tayi wani aiki akan shi bansan ko na miye ba shine tace idan naje wurinshi naɗan aibata ita matar tashi kome yace nazo na faɗa mata ta nan zasu gane idan nasara ta samu karɓuwa...... Bayan ta gama jin duk abinda take so taji. Ta turawa Sultana saƙo duk abinda takeyi ranar yau tayi ƙoƙari tazo gidanta , bayan ta ajiye mata adireshi gidan....
Hafsa da Amisty gurfane a gaban sabon malamin da ta samawa Hafsa kamar yadda ta faɗawa ita Hafsat in. Saida ya zana ƙasa ya goge , ya sake zanawa , ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama zane²n ƙasarshi sannan ya fara rattafo mata bayani kamar yana karantawa a rubuce. Ya kuma ɗora da cewa ta gode Allah da tazo wurinshi daga yau kuma damuwa ya ƙare. Aurenta da Dikko anyi an gama kuma a ƙarshen watan nan ne , yaci gaba da labarta mata rayuwarta ita kanta , Hafsa tayi na'am da wannan bayani sosai dan haka akayi ciniki bugun farko miliyan biyu ba tayi idan aka taya ko anyi aikin baya ci , za'a siya jajayen raƙuma da jajayen sanaye jajayen tumaki tattabaru jajaye da kaji suma ja kuma duk ko wane za'a siyo mata da mijinta guda biyu² , shanaye maza biyu mata biyu kenan huɗu² mace da namiji a cikin ko wace dabbar daya faɗo....
Zatayi magana Amisty ta rufe mata baki tana cewa malam yi haƙuri zamuyi magana , jibi idan Allah ya kaimu za'a kawo kuɗin , tana faɗin haka taja Hafsa suka tafi. Bayan sunje gida ne Hafsa take cewa ita ina zata wani samo 2million ne ? Tada ma sigari wuta Amisty tayi saida ta ibi hayaƙi tace riba zaki ci ne , duk gidan da kika ga anyi zazafen abinci tou karki bincika ma'ajiyar abinci dalilin haka da sanin gaskiyar sirrin yana wurin mutanen gidan. Ki zuba kuɗi gona yarinya ko kin samu albarkatun gona , wannan malami da kika gani malamin "yan siyasa ne shi yasa kikaji aikin nashi da kuɗi sosai , ga tsada fa amma akwai biyan buƙata , gwamna kanshi wurinshi yake zuwa shine ya ɗaurewa gwamna ƙugu ya koma mulki , ai ya miki sauƙi ma ne saboda ni. Ai da banje ba aikin nan kila sai ya kai miliyan huɗu , ba nace miki shine yayi ma Sultana aiki ba? Kinga tana can ta shige abunta. Hafsa tace miliyan biyu fa Kaka ? Amisty tace miliyan biyun , miliyan har kuɗi ce da zaki tsaya kina wani jinjinata ? Hafsa tace ai inda zan samosu shine damuwata....
Kashe sigari Amisty tayi sannan tace ke kuwa kike da miliyan biyu da wurin samunta. Idan baki dashi ai Babanki yana da. Kije kawai ki tattaro takaddar wani ƙaton gida ki siyar , idan aka ɗaura aure ƙarshen wata D ' K zai biya. Kinga basai mu siya ma Dady sabon gida ba a manyan anguwanni dake cikin garin nan ba ? Murmushi Amisty tayi tare da nuna Hafsa da ɗan yatsa manuni tana cewa anya ma mu D ' K zai barmu muje gidanshi......? Dariya Hafsa tayi cikin jin daɗi cewa sai kunje mana tunda yana aurena ai dole ma ne yaso duk abinda nake so. Amisty tace yawwa "yar gari yarinya ta gano hanya mai takaba ta buƙaci kwarto...