Header Ads
Showing 54001 words to 57000 words out of 70788 words

Chapter 19 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt

Ads the beginning of article before Image

07 Jul 2024

756

Ads at the middle of Article

Ci.. Nayi tare da yin murmushi mai ciwo na goge hawayen dake bin idona. Ina ci gaba da kuka. Naci gaba da karatun takardar Inna.....


_Na farko:• a samun natsuwar aure shine hadafin yinsa. Bai taɓa yiwuwa aure ya kasance an ginashi kan wani hadafi sannan ya zamo ɗorarre. Wannan shi yasa Annabi {{ S A W }} bayan ya zayyano kaso na matan da ake aure. Ƙarshe yace "na hore ku da ma'abociyar addini. To haƙiƙa abun nufi anan shine ba wni hadafin da zai haifar maka da cikakkiyar kwanciyar hankalin aure sai hadafin tarayya domin Allah..._


_A cikin aure mai kawo natsuwa kenan. Haƙiƙa a yau munyi sake tare da watsi da haƙƙin junanmu ta yanda takei har wasu abubuwan ma an shafesu daga rayuwar auren sai wajen mutane jefi² mun barwa turawa wanda kuma mu addininmu ne ya koyar damu su. Ina horonki da ki zama mai biyayya , ki zama mai kunya da juyawa abin duniya baya. Kiyi kara ki zama mai haƙuri. Rayuwar gaba ɗayanta haƙuri ce , ki guji yaɗa sirrin mijinki wa kowa da koma waye. Kar kiyi abinda bakiyi shawara da mijinki ba , ki kiyaye fushin shi ki guji ɓata masa rai da gudun duk abinda baya so idan har bai tsaɓawa Allah ba. Haƙuri׳ ki zama mai haƙuri da biyayyar aure kinji uwar masu gida. ?_


_Ki kiyaye munanan kalamai. Karki kuskura ki jiyar da kunnuwan mijinki ɓatattar magana daga gareki. Magana mara daɗi ko muni kiyi ƙoƙarin kare kunnuwan mijinki dasu. Kar kiyi masa:• ƙarya. Ki kula dashi , ki zama mai tsafta , kar kici amanar shi , banda zargi ki guji abokai , karki raina masa iyaye. Ki kiyaye kuma kisan yadda zakiyu ma'amula da "yan uwansa._


_Kinga wa'anan abubuwan da zan lissafo su ? To ki kiyayesu domin sune ke taka rawa wurin rusa aure matsawar ba'a kiyayesu ba._


_Rashin ilimin zamantakewar aure , al'adu , rashin binken halin miji , rashin binciken halin mace , matsalar iyayen miji , rashin tsafta , matsalar dangin miji , rashin iya magana , rashin iya ciyarwa , rashin iya kwanciyar aure , rashin adalci , auren kisan wuta , cin amanar aure , ƙawaye , zafin kishi , sata , gulma , wayar miji {{ phone }} , rashin lafiyar miji wajen gamsar da iyali da itama rashin lafiyar macen wajen gamsar miji , sharrin boka. Ke kina tunanin ni bana sanki ? Taya ma zaki yadda ki fara wannan tunanin ? Tunda kike a duniya kin taɓa ganin uwar data haifa "yarta tace bata santa ne....? Ni ina so ne ki goge da rayuwa ke ɗaya , ki kuma iya haɗiyar baƙin ciki da magance damuwa dan ki zamar da kanki garkuwar rayuwarki. Domin idan yau ina nan gobe bana nan , yadda kike ke ɗayan nan babu abokin shawara ko na bar duniya barakiji wahalar rayuwa da kowa ba. Ina so ne kawai in auno iya girman soyayyarki a zuciyar mijinki. Na gani kuma ni nasan yana sanki dan nayi masa wani abu a abuja. Wallahi nayi tunanin yadda ake faɗar rashin mutunci zaizo ne kawai ya sakeki. Sai baiyi ba kuma nima baimin rashin kunya ko kallon banza ba kamar yadda nayi tunani... Wallahi inajin kunyarki ne , abun nan da nayi muku banyi da nufi ba , yayi ta damu nane banji daɗi ba , shi yasa na fara rubutun neman yafiya kafin mu haɗu dan mashala.Tou dake dashi duk ina san ganinku domin na nemi gafararku , sai kuma kema zamuyi zama na musamman...... sai mun haɗu kafin inyi tafiya_


_Fatima Salis Abbakar {{ Inna }}_


Wata irin ƙara nayi tare da cewa da yaushe ne zamu haɗu ? A ina me zaki ce man ne iye ? Cike da tashin hali ya kallo inda nake yace haba An mata wai meye kike haka ne ? Cikin muryar kuka na raunana murya tare da cewa ƙarshena yazo. Wannan kalma dana furta shine yasa Dikko kakkafawa , wani irin birkitaccen ihu na ƙarayi tare da matsawa inda yake , sautin ihun yasashi ɗaukewa gaba ɗayanshi. Da gudu na fita na gayyato Ashiru , cikin tashin hankali muka dawo tare dashi , shi ɗakin Dikko ya wuce sannan yazo ɗakina , haka yaita mishi shaƙe² harya dawo. Ɗan gajeren tsoki yayi tare da cewa insha Allahu saina mutu tunda dai baki bari in zauna lafiya. Fita Ashiru yayi ni kuma na matsa kusa dashi ina kuka , a gajiye ya jawoni jikinshi idonshi cike da hawaye yace wallahi bana san kina ihu , ki ƙyaleni in huta dan Allah. Kwanciya nayi a jikinshi nace na bari. Gefenshi ya nuna min in sauka daga jikinshi in kwanta , sauka nayi na kwanta ina kallonshi dakel ya lumshe idanuwanshi cikin yanayin jigatuwa kiyi bacci , rufe idanuwana nayi hannuna a saman gemunshi.


Bayan wani lokaci mai nisa ya sauke ajiyar zuciya tare da sauke hannun Sultana daga jikinshi. Wayoyinshi ya ɗauka ya fita a ɗakin. A gefen gado ya ajiye wayoyinshi bayan yaje ɗakinshi sannan ya wuce toilet kai tsaye. Wanka yayo ya fito ɗaure da rigar wanka yana tunane² , shi kaɗai yasan yadda yakejin rayuwarshi da kuma yadda yakeyinta a daddafe. Taƙaitaccen tsoki yayi tare da zuwa wurin wayoyinshi dan ganin mai kiranshi , Sharifa ce. Ɗauka yayi ba tare daya bari tayi magana ba yace yana zuwa....


Ajiye wayar yayi ya matsa wurin madubi. Kamar mace yaita ƙwasƙwarima , yana gamawa yabi kayan da zai saka ya bulbulesu da tulare shi zaije zance. Kallon kanshi yayi sosai a madubi shi kanshi yasan haɗaɗɗe ne shi ɗin. Murmushi yayi kaɗan tare da ɗan shafa gemunshi da bayan hannunshi na haggu sannan yayi kallonshi na gefen ido mai tabbatar da shi ɗin cikakken ɗan duniya ne.


Taf yauma Sharifa ɗif take ta ibi wuta sosai. Har bata iya tafiya sai layi takeyi , ga wasu irin kaya data saka kuma ko breziya bata da , kaf halittar surar ƙirjinta babu wanda baka gani kawai kamar buɗe yake. Full light yayi a dai² lokacin da yayi parking. Dogon kallo yayi mata daga cikin mota inda sukayi zasu haɗu dan yau ba g r a aka haɗe ba. Wasa yayi da fitilar mota ta nufoshi tana rangwaɗa , tana isowa ta wani kama murfin mota ta inda yake ta buɗe , rufe ta da faɗa yayi wai ita wata irin jaka ce ? Haka ta ratso duniya ta taho kowa yana kallonta ? Irin barinkinta zata yi mishi wai Dikko zata runguma , ƙara ƙufulewa yayi dan duk duniya ya tsani ana taɓashi , turata yayi baya da ƙafarshi cike da ɓacin rai yace Dikkon zaki kaiwa hannu eye ? Cikin hayaniya yace kai...... Lallai kin isa yayi maganar yana buɗo duk girman idanuwanshi. Ƙara nufoshi tayi da sauri ta ƙara ƙaddabeshi , ta ɗauka shiru zaiyi ya fara aiko numfashi kamar yadda Mai gilashi ta faɗa , sai taji karatu yasha ban². Da tsiya² ya fitar da ita jikinshi dakel. Kafin ya fito mota ta ƙara komawa ta cakumeshi , kai........... Da Allah ki daina riƙemin jiki , riƙo fuskarshi tayi tana matsar da nata kusa da nashi. Tureta ya ƙarayi da ƙarfi tayi baya. Da sauri yasa hannunshi aljihu ya ciro cingom kasancewar warin sigari da sauran wasu kayan mayen da yaji warinsu daga bakinta zuciyarshi ta tashi.


Tsalle tayi ta anshe cingom in tasa a bakinta wai yaci daga bakinta , kakarin amai Dikko ya farayi yana matsawa gefe tare da riƙe bakinshi. Caɓoshi tayi ta baya , aiko kamar jira yakeyi ya kakkaɓota ya fara kwallo da ita , saida ya bata kashin bala'e ya shige motarshi yai tafiyarshi ya barta kwance a hanya tana kuka.


Tsoki yayi tare da ɗaukar wayarshi dake wata ƙara zutt². Yusra ce , reject ya latsa yana gunguni. Cike da ɓacin rai ya koma gida duk saima yaci uwar matan nan dan ubansu , kawai ma dan ana magana dasu zasu ɗaukeshi wani daƙiƙi ? Bari har itama mai turo kanta tsirara zaici uwar ubanta ta sake zuba mishi banzayen hotunanta a waya saiya kasheta..... Ya faɗa yana kaiwa gado harbi da ƙafarshi. Dama su mata ma basu da wayau jira suke ayi musu magana su fara rainawa mutane wayau. Kamar shi ? Sai kace wani sa'ar wasansu ? Shi waccan jakar yarinyar ma zata wani daƙune ? Jinjina kanshi yayi da damuwa yace sai kace wani jaririn da yazo inda aka daɗe ana addu'ar samun shi , kai wallahi ya raina kanshi da har shi wata daƙiƙiya zata runguma. Tuno yadda Sharifa ta kasance a jikinshi da yadda harma ta samu damar tallabar mishi fuska , duk yana ina ? Aikin me yakeyi ina zamarshi ? Aiko wallahi da bai daketa ba har abadan duniya da baida kwanciyar hankali , tsoki yayi tare da cewa duk dai haka ta moremin wallahi...... Balgazar mace. Haka yaita masifa shi ɗaya a ɗaki dama tusa hali bare anci wake. Fushin mutum ɗaya ke sa idan yana fushi yake haɗawa kowa da kowa , wanda yasan anayi da wanda baiji bai gani ba , ai kuma kunsan laifin wani yake hucewa akan kowa. Yau duk wata macen dake cikin wayarshi Sharifa taja musu anyi blocking insu , anyi adding nasu zuwa blacklist. Wato shi harkarshi ba baƙin ciki bajin haushi sabgar Katsinawa.


Dikko shine ya shiga yai ruwa yai tsaki aka ɗaura auren Jiddah da Yazeed. Rabiya ta labarta mishi komai tsakaninta da Yazeed iyakar abinda ta gani , hankalin Dikko kuwa ya ɗagu domin shi yasan waye Yazeed. Sadaki da lefe har kayan ɗaki shine yayi dan Yazeed yace bashi da kuɗi , Jiddah ta faɗawa Dikko ita ta bada kuɗin aure. Shine Yazeed yace ɓarayi suka sace kuɗin. Andai ɗaura aure amarya ta tare a gidan angonta...... Ita kuma tana lissafin kwanakin fitowarta da ko nawa ga wata zata koma gidan Dikko.


Hafsa. Duk maganin da akayi ma Hafsa a asibiti hannu yaƙi ɗauka bare asa ran samun sauƙi har zuwa matakin warkewa. Bayan dogon bincike likita ya tabbatar Hafsa tana da ciwon shiga. Cire hannun shine maslaha inji malamin asibiti dan idan ba'a cire shi ba matsalar zatafi haka injisu. An cire mata hannu dai² gaɓa.


Amisty kuwa kafin ta gama warwarewa Momyn Hafsa tasa aka cafketa. Bayan tasha shegen duka aka tambayeta kuɗi tace babu , a yadda su "yan sanda suka fahimta Amisty tana da damuwa a ƙwaƙwalwarta. Haka suka gogawa Momy bayani dole tasa suka saketa dan Amisty ta samu ɗimuwar tunani. Amma duk wannan bai ishi Momy ishara ba saida ta siyar da gidan iyayenta da gidan Amisty na Qerau. Amisty dai ga hauka ga kuma yawon haya.... Bariki kuma ta kama gabanta , sheɗan ya fita a kanta ya sake sheƙa. Duniyar yanzu ba Amisty take buƙata ba zamanin wasu ne. Haka takeyin juyin ɗan mangwaro ita duniya dawowa take daga rakiyarka da zaran ta raka ka sai ta dawo ta sake raka wani halakakken wanda sheɗan yayi ma tusa a zuciya.


Halima dai ba kowa bace wannan amarya sai ƙanwar Hadiza. Wata garɗamemiyar budurwa ce takai shekaru 27. An tura anyi ciniki amma bata samu shigewa ba , anyi addu'a an bada sadakar ƙuli da alawa amma abu ya gagara dan haka ta shiga ta fita har gidan uwayen mijin Halima ta basu labari irin uƙubar da take ba ɗansu. Nan fa dangin miji suka fara cacai² , akai ta faɗo baƙin halinta , raina dangin miji uwar miji raina miji da baƙar rowarta. Itama dai Hadiza ta kawo nata sharrin ta raɓa da "yar ta² barikin dai ta samu aka siyi kanwarta. Shima Abdul haka aka ɗaurashi kunsan maza basa wuce tayin mace kamar almajiri ne da sauran abinci... Cikin ikon Allah yaga yarinya kuma tayi mishi. Gata "yar kyakkyawa kamar Rabi'atu Aminu Maman Dee. Mai kunya da laushin magana kamar Asmeenat Zeeyan. Mai kyawun kallo da iya murmushi kamar Aunty Musa Qerau. Ga iya wanka mai ɗaukar hankali kamar Hauwa Musa Qerau. Ta iya adon lalle mai burge kamar Zainab Abbakar Matawalle haka ta iya gyaran kai kamar Fati M Ga magana da salon ɗaukar hankali bakinta kamar Ruƙayya Sharif Maulaya hassan. Kai tafa haɗu haɗuwar haɗewa , idan zatayi kallo tanayinshi ne da salon bugun zuciya kamar Rabi Musa Qerau. Bari dai in daina zugata haka nan karta kamo Halimatu Musa {{ Uwa }} haɗuwa.


Abdul da yaga yarinya tayi mishi sosai dan haka suka antaya a duniyar munafukar soyayya. Ita kuma Hadiza kullum tana liƙe da gidan Halima tana ƙara kakkaɓowa "yar uwarta sirrin gida. Har daren ɗaurin aure duk suna tare da Halima sunajin hukuncin da zatayi wa amarya. Da taji saita dokawa "yar uwarta waya suyi shawara su san hanyar da zasu hudowa lamarin. Ina wanda ya raba faɗa bai kallo ba , sun haɗu sun haɗa ƙarfi da hikima duka ɗaya zasuyi su zare Halima a gidan miji idan tayi wasa saboda sunyi mata ƙofar raggo , ita bata sansu ba , su kuma suna tare da ita suna shirya mata gadar zare.


A kusa da gidan Halima Abdul ya kama haya ya ajiye amaryarshi Amina. Tunda bai shirya aure ba hawoshi yayi kai tsaye. Anan fa akayi uwar watsi , Halima ta fara bori da wallahi² data tabbatar amarya ƙanwar aminyartar ce. Nanfa fitina ya ɓalle suka kashe santa aikata ruwan bala'e babu ƙaƙƙautawa , Hadiza ta biya kuɗi ta ibo hayar "yan daba tace duk matar data sake cewa tuf ko ta leƙo daga gidanta idan dai ba Allah sa alkairi ta fito ba aradu su yagewa koma waye baki. Dan su sunaso suyi hidimar biki cikin natsuwa , a gefe kuma ga masu DJ sunata wulakanci da waƙoƙi na habaici umarni daga Hadiza , c b n gidan kuɗi. Can naga sabbin kuɗi suna wali bisa iska. Shagali wanda ko a bikin Halima basuyi irinshi ba. Hadiza kuwa a yanzu zasuci na ƙurya da bakin gado. Ballagazar mace ga ƙarsheki.


Tunda Mardiyya ta haura katangar maƙabarta ta ibi santa. Mota tahau ? Da ƙafa taje ? Oho , candai Yola ta yadda zango , hauka tuburan marar gane matsayin ido da ciki. A gidan mahaukata aka ajeta shine suka shiga neman "yan uwanta , bayan an samosu aka danƙata wa iyayenta , sai suyi ta magani har a dace , wa gari ya waya ? Ruwa ya ƙarewa ɗan kada bai gama wanka ba.


Amarya Jiddah kuwa an wani saki baki aci kazar amarci. Ai a ranar ango bai kwana gida ba. Tou dama me zai tsaya yi ne ? Abinda za'a tsaya danshi ayi murna da ɗoki ai ansanshi tun a gida. Saboda shi dama za'aci kazar tou yabi ya wuce , anyi karatu an tusa feji , allonta kawai take wankewa gwargwadon yadda ta biya karatun. Sati ɗaya da "yan kwanaki ta fara zance tafiya , Yazeedu yace ina ? Ai yadda baya tare da D ' K a yanzu gara ma yayi ƙoƙarin riƙe auren "yar uwarshi yasan ya mishi sauƙin gani. Haya² ta taso da rashin kunya ya nannagawa banza duka na fitar misali. Wannan shine horonta duk idan ta sake zance saki....


Duk wannan sa'a da Sharifa ta gwada na shawarar da mai gilashi ta bada taga ta faɗi ? Bata daddara ba. Dan haka ta faɗawa Mai gilashi Dikko ya rufeta a waya. Mai gilashi tace mafita na ƙarshe kizo makarantarmu ajinmu ɗaya da matarshi kashin bala'e zaki bata , daga nan idan kika daki matar zai nemeki danjin dalili , sai ki faɗamin ni kuma zan baki shawara na ƙarshe. Idan kika daketa zataje ta faɗawa mijinta , tana faɗa mishi shi kuma zai nemeki danjin ba'asi. Yana kiranki ke kuma ba ɗauka zakiyi ba sai ki kira ita Aunty Bilki ki farfaɗa mata maganar da zan faɗa miki idan kinyi dukan. Daga nan zatace kizo gidan gwamnati. Idan kikaje government house sai ki kira Dikko ki faɗa masa cewa kinga kiranshi bakya kusa ne sai yanzu. Zai ce me matata tayi miki kika daketa ne ? Sai kice ai ina nan gidanku ma. Fuuuu zai tako mota yazo , ai kinsan dai dama bawai wani can² yake santa ba suma nashi familyn basa santa. Ai nanfa za'a haɗu a bata rashin gaskiya duk idan kinyi dukan zan faɗa miki abinda zaki ce ya haɗaki da ita Sultanar.


Sharifa tace amma kina ganin wannan ba matsala ? Mai gilashi tace haba Sharifa idan da matsala harna faɗa miki kiyi ? Matsalata ai taki ce. Dole mu haɗu muyi maganin matsala kodan ci gabanmu. Sharifa tace idan aka faɗi fa ? Mai gilashi tace shikenan sai ki sake ƙawar shawara. Sharifa tace tou shikenan. Batayi tunanin matsalar da hakan zai haifar ba......


Hmmm su kuma zugar gidanmu duk abun nan wai sai yau suka zomin gaisuwa. Ƙwansu da ƙwarƙwata babba da yaro babu wanda aka rago har iyaye , jimillarsu dai su sattin da wani abu. Kacaniya kenan , gaskiya nayi farin cikin ganinsu sosai har farin ciki na yaƙi ɓoyuwa. Haka suka shigo wurjanjan kamar an ɓalle garken shanu. Kowa da irin siffarshi. Kai gaskiya Baba ɗan bala'e ne , wannan kwanyaman "ya "ya inama amfaninsu ba ɗaya na zaɓe. Haka suka shigo palo sukaita hayaniya , har bakajin maganar wani. Abinci nasa aka kawo musu. Ɗiff kowa ya ɗauke wuta suka fara caccaka.

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads