Showing 69001 words to 70788 words out of 70788 words
Chapter 24 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt
gilashi. Ƙarshe Mai gilashi cewa tayi Malam yace da zaiyi mata aiki amma daya buga ƙasa ya gano ta taɓacin amanar wata aminiyarta , wani attajiri ɗan siyasa yazo auren ita aminiyar ke kika rufe ciki wai haka yace , shine nace shin ko kin gane ko wace ce ? Iyakar tunanin Sharifa ta kasa hasasowa. Mai gilashi tace tou daƙiƙiya wannan ba ko bace nice..... Kuma nice nan na shirya komai ta yadda kika gani na rusa miki wannan auren jaka , tunin duniya nake ƙufule dake yadda kika hanani ci ga kaiwa ga nasara tunda naji kince SAI KIN AURI D ' K nace ma zuciyata idan dai ta bari kika aureshi saina rabata rayuwa da gangar jikina. Nice nan na ɗauki nauhin komai na shirya na kuma gabatar , idan kika sake kirana zan saki sauran hotunan wa duniya naki kamar yadda kema kika ɗauki hotuna na da nake a gurɓataccen yanayi kika samu nasara wurin ganin kin hana auren. Kin hana nawa kema na hana naki 1/1 sai kuma kin sake , idan kuma kika sake kirana saina shafe farin ciki daga rayuwar ahalinki tana faɗin haka ta ajiye waya.
Shi kuma a ranar har dare yana gidansu yana yayyafa ruwan rashin mutunci , waishi ko shi baya dukan An mata tunda ta samu ciki. Shine aka samu wata tsagera taje tayo gayyar ƙatti ? Waishi maza zasu dakar mishi mata ? Da ciki aka dakar mishi mata ? Har dare yana can yana abu ɗaya , Momy tace a fitar dashi ta daina ganinshi , wannan riƙo da akayi mishi da zumar lallashi shikenan ya birke ya fara sai kashe , waye yace wai a riƙe shi ne ? Yace baya so ana taɓashi kaza². Shikenan fa ya mimmiƙe ko za'a tashi duniya saiya ramawa An mata dukan nan bazai yadda ba , wai ko an faɗa musu jakace matarshi ? Sai ayi mishi abu dan cuta idan kuma yayi magana sai ace bashi da haƙuri , tou saiya rama kuma bamma gajiya duk wanda yayi mata sai yayi mishi ko waye kuma ko wacece............. Daga nan ya ɗauke.
Dady kuma tara su Ashiru yayi yace gaba ɗayansu sun cuceshi sun kuma munafurceshi. Me yayi musu sukayi mishi haka ? Bayan su sukace mishi Babanshi ya warke ya haƙura ya daina neman magani , me yasa² ? Me yasa sukayi mishi haka ne ? Wannan ce soyayyar da suke bugun ƙirji cewa suna iya bawa Babanshi fansan rayukansu ? Karo na farko daya ga cin amana zahiri. Ba kuma zai sake yadda da kowa ba. Haƙuri Ashiru ya bashi sannan ya buɗe mishi gaskiyar lamarin yadda yake cewa.
Rashin lafiyar da Mai gidansu yayi bayan ya samu sauƙi. Sun faɗa mishi abinda Mustapha yace , amma sai kuma wata matsala dashi dai Mustaphan yace. Wai asirin da mutum yaci a abinci da wanda mace tayi "yan maƙale² dashi a jiki ta kwanta dana miji wannan asirin wahalar fita gareshi wallahi. Cikin magungunan dashi Al ' Ameen ya bawa Sadiya da sunan taimako yace wannan na kayan mata ne , shine taje tayi amfani dashi kuma shi Al ' Ameen ya bawa Mai gida magani a london , sanin manufarshi da aikin maganin bamu sani ba kuma shima Mai gida bai sani ba , wannan dalilin ne yasa yace yaso ya haɗu da Al ' Ameen akwai tambayoyin da zaiyi mishi. Gadai asiri an fitar na fili amma na jiki bai daina tasiri ba , ganin bai warke ba yasa yace kawai bara ya haƙura da Hajiya yaci gaba da sabgoginshi dan yasan bazata yadda ta sake zama dashi ba , a ranar daya bar gidan gwamnati ya koma gidanshi lalurar ta tasoshi a gaba , daga nan ne ya tafi jinya bayan ya dawo ya ƙarƙare aurenshi da Hajiya Jiddah yace itama Hajiya Sultana zai jira yaji me gidansu zasu ce. Shidai Allah ya sani shima yasan tunda yake a duniya rayuwarshi bata taɓa san wata mace ba wallahi sai a kanta.
Akanta ya san soyayya kuma akanta ya farayi ma shaƙuwa kuka , itace macen farko daya sa hannu ya daka a duniya wacce bata gidansu ba , kuma itace mutum ta farko data ɗaga hannu ta mareshi , yace shi a gidansu wallahi baisan wani abu da ake kira duka ba , tayama za'ayi tunanin dukanshi bayan kowa sanshi yake amma zuwanta rayuwarshi yasa ya anshi hukunci mari daga iyaye , itace macen da ta ɗaukeshi kamar wani sa'arta kuma bata iya zuciya dashi. Shine yace a yadda suka rabu yasan har abadan duniya ta gama dashi ashe ba haka ba. Yayi alƙawari har abadan duniya ya gama aure zai jira daga gidansu ita Sultana ayi magana kawai zai haƙura da ita , yasan babu uwar da zata haƙura tabar "yarta ta zauna da shi da kuma lalurashi. Yayi kuka shi da kanshi yaji tausayin kanshi.
Kamar ya haƙura amma ya kasa. Duk abinda yakeyi zaiyi zuru yana tunani , idan zaici ko zaisha zaiyi murmushi yace ko a wane hali kike ? Ya shiga ɗimuwar rayuwa da zaucewa ganin zai ida warwarewa yasa yasha ta dubu ya tafi gidansu bayan ya fara tura Abbakar. Bayan ya dawo da itane yake faɗa mata ya warke dan abinda yasa ya ɓoye mata kila idan tasan har yanzu yana da damuwa bara ta zauna dashi ba.
Sa hannun masu sa hannu a ciki Ashiru ya faɗawa Dady , Bilki yasa aka kira mishi tana zuwa ta fara zazzaga rashin mutunci. Wai ita zai tirke ? Tou tayi taje tayi yayi maganinta , ta fara azaƙaƙura rashin mutunci nan fa gida ya ruɗe aka fara tone²n asiri , Dady yace Bilki sai ta bar mishi gida , "ya "yanta suka fara kuka Dady zai tona musu asiri. Ita kuma cewa takeyi su daina kuka ya saketa, saboda mahaukacin ɗanshi zai tara yaran Dikko a gabansu yaci mutuncinta ? Har nawa ma Dikkon yake ? Wato shi tunda baya nan bara yayi a gaban yaran Dikkon idan shi Dikko ya dawo daga duniyar ɗimuwar rayuwa su bashi labari yaji daɗi.
Har tsakar dare ana abu guda Momy ita kuma tana cewa sai an warkar mata da ɗa wallahi. Kuma shi Dady karma ya kuskura ya saki Bilki dan wallahi bata riƙe mashi "ya "yanshi , Dady yace ko bata riƙesu shi ya isa ya kula da rayuwar yaranshi. Har Dikko ya dawo ba'a gama faɗa ba , shine ya bawa Dady haƙuri akan kar yayi saki wa Aunty Bilki , Dady yace tou kinji haƙuri yake bani akan ki duk ke kinyi masa abu na rashin kyautawa. Cewa tayi wallahi idan dai akan Dikko zaiyi haƙuri ya zauna da ita wallahi ta haramta zaman aurenta dashi , nan suka sake buɗe sabuwar rigima Dady yace saboda Babanshi yayi haƙuri rigima dai da tashin hankali har aka rabu , ita bata zama albarkacin Dikko saboda bata ƙaunarshi kuma sai ta kashe Dikko ta ɗauki alƙawari a gaban Dady , dariya Dikko yayi cewa inma ki kasheni ko ki fasa lumfashi yana wurin Allah sai lokacin daya so zai tsinkeshi. Shawara ɗaya zan baki kidai bi sannu domin ni ko hassada mutum ya cikamin saiya lalace......
Jiddah ta ladaftu domin Yazeed ya zabga mata bulalar saki mai ɗan bara'un zafi. Tayi iya ƙoƙarinta a koma G R A da ita amma ina ? Nima na rama maganar data faɗa a lokacin aurena nace nima G R A nawa ne ni ɗaya daga ni sai yarana. Umar Faruk {{ Pa - Pi }} Aliyu {{ Khalifa }} DIKKO {{ Junior }} Maryam {{ Ummie }} sai ayarin gidanmu da kuma wanda naso nima nace mata Dikko nawa ne ni ɗaya. Bata ga Sharifa ba da tace SAI TA AURI D ' K yadda ta ƙare ? Taje tayi haƙuri tayi maleji da Yazeedu. Dole ta lallaɓa ta koma gidanta kuma ya rage iskancin hanaci masa abincin gida saidai shine yake auna musu kamar "yan boarding.
Mai gilashi ta rabu da tsohon mijinta tana Abuja tana aure sa'ar rayuwa dabance , wato duk iya iskancin mutum idan Allah yaso mishi jin daɗi saiya shiryar dashi.
Halimatu dai ƙanwar Hadiza bata samu kwanciyar hankali ba saida tayi waje road da ita ga miji ya samu ƙarin matsayi a wurin aiki. Ta dafe kan mijinta ram an shiga lugudan wuta.....
Amisty Mardiya Hafsa Aunty Suwaiba kowa tana can tana ansar wuta dai² da irin rayuwar data aikata a zamanin ƙuruciyarta , duk wadda bata mori rayuwar ƙuruciyarta da kyakkyawar ɗabi'a ba ƙarshen faɗan tayi makauniyar ƙarshe.
Sharifa dai har yanzu ba'a samu anyi aure ba. Ita dai Mai gilashi ta haye ta ibi filin abuja suna can sunacin duniyarsu. Tacemin kila dai tana da rabon a nunota a talabijin tunda ta auri ɗan siyasa nikam nace mata kila dai aljannun shiga talabijin gareta.
Jamila Musa gareki jinin katsinawa.
Tam Alhamdulillahi Hajiya Maryam ko nace Hajiya Sultana. Duk dai baki faɗa mana shin Mai gidanki ya warware ko har yanzu yana ta faɗar saina kashe ki........ *Sultana:•* Murmushi ni harma kin bani dariya , gaskiyar lamari Mai gida Dikko dadai sauƙi ba kamar cancan baya ba , dan mafi akasari saina ɓata mishi yake wannan ihu kuma ai kinsan yanzu ba'ayi. Gulmar Dady kukeyi ko ? Inji Pa - Pi tou bari in kirawo shi , ɗage kanshi yayi tare da cewa Ya.......................Ya........
Abun arziƙi ai yayi bari kiranshi kar yazo ya karkashemu muma a bar mutanen Qerau da jimami.......
Alhamdulillah
Masu biye da labarin kwarata anan ne ubangiji ya bani ikon dakatawa. A madadin duk wani bakatsine ko ina yake a faɗin duniyar nan muke ma duk wani daya karanta littafin kwarata fatan alkari domin nuna muku halakci da kara irin namu na katsinawan Dikko. Kai har wanda bai karanta ba kyakkyawar fata da dubun gaisuwa ta musamman data fito daga yankin jihar katsina,
Jinjina da gaisuwa gareku Kanawan dabo tunbin giwa , saƙon gaisuwa da jinjina a gareku mai kyau albarkacin Umar Sanyi.
Alhamdulillah.
🔚
Rubutawa.
*JAMILA MUSA QERAU....*
14/02/2020
Na barku lafiya. Cike da kewarku , sai Allah mai kowa mai komai ya sake haɗamu idan muna da rayuwa a cikin labarin *ƁOYAYYAR SOYAYYA...*
*JAMILA MUSA ce...*