Showing 30001 words to 33000 words out of 70788 words
Chapter 11 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt
dasu ta ɗauko har 3 ta ajiye ƙasa sannan ta maida sauran ta mayar da kayan yadda suke , ta rufe weldrop in ta fice yana nan kwance kamar asarar safe yana bacci....
Itama a wurin Sultana haka ta kasance , tana kwance gefen mijinta kamar asarar itama shi kuma yana cht. Murmushi yayi kaɗan tare da juyawa ya ɗauko bluetooth wurin dawowa ne ya bugeta , da sauri ya ajiye wayarshi yana rirrigata irin yadda akeyi ma yaro idan ya farka , riƙeshi tayi taci gaba da bacci , ajiyar zuciya ya sauke. Cikin jin daɗi ya lumshe idanuwanshi a gajiye yana numfashi kaɗan. Saida ya tabbatar ta koma bacci ya cireta daga jikinshi ya gyara mata kwanciya ya lulluɓeta , a hankali ya sauka daga saman gadon ya ɗauki wayarshi ya koma palo..... { kunga bai iya gani ba , amma yau da gobe tasa zaije ya kalla , tou a hankali suke raka mana mazaje suna dawowa , idan abun ya ɗaure haka tun tana mishi tayin kanta yana a , a , a hankali zata labbaceshi ta nuna mishi ai ba wani abu bane ba. Da kaɗan take ɗorawa idan kuma tafiya tayi nisa haka zata rufta miki miji , daga nan sai ta Allah , karuwa ba.... }}
Kashe fitila yayi bayan ya shiga palo , ƙasa ya kwanta saman kafet ya sargafa bluetooth a kunnenshi sannan ya buɗe cht in da Yusra ta turo mishi. Hotunan ya fara kallo da yanayin mayata , bayan ya gani ya kunno voice note ya saurara a kasallance ya furta mata yana ci gaba da kallon hoton Yusra , a voice note kuwa lallausar magana ce da manyan kalaman irin na "yan tasha wanda yaji sunyi mishi dai² da sauron kunnuwanshi , daya kai ƙarshe sai ya sake kunnuwo , taɓe bakinshi yayi tare da fara kallon video , da sauri ya rufe idanuwanshi yana murmushi , amma yanajin maganar da takeyi lokacin tana video , buɗe idonshi yayi ya sake kallo yana murmushi , bayan wani lokaci ya sake rufewa yana dariya..... Gyara kwanciyarshi yayi yana miƙa alamun saƙo ya fara shiga jikinshi. Dariya ya sakeyi mara sauti sannan yagoge ya kifa kanshi saman pilown da yake kwance yanajin wani baƙon yanayi yana shigarshi. Bayan wani lokaci ya ɗago yaci gaba da dubawa bai bawa Yusra amsa ba , ya duba saƙon Sharifa itama baice mata umm² ba ya wuce wurin na Jiddah , kallon hotonta yayi data turo tayi kyau sosai wai ga Jiddah tana godiya Yaya , itama bai bata amsa ba , ya duba saƙon da wata number ke turo mishi hotuna , gani yayi ya wuce yana duba na abokanshi , zuciyarshi kuwa sai san ƙara jin labarin Yusra takeyi , komawa yayi ya gogeshi da hotunan yasan idan An mata ta gani kuka zatayi.... Ɗayar wayarshi ya ɗauka ya fara kallon hotunan da yayi mata ɗazu , da wanda itace tayi musu tare , bayan ya gama gani yace An matan Dikko......
Yauma shirye na fito cikin kayan makaranta amma Dikko ya rufe ido wai babu inda zanje , ai da kwata² na daina zuwa makaratar. Dan naga ya dawo daga tafiya yana huta gaji shine zance makaranta , kuka na farayi tunda yanzu na lura kukan shine ƙarfina a wurinshi , shikenan muje in kaiki ya faɗa yana cewa jirani ,
_kiyi ƙoƙari ki riƙeshi gida na kwana3 karki barshi ya fito...._ maganar Mai gilashi ta dawomin da turomin a saƙo jiya , binshi nayi ciki ina ƙara yawan kukana nidai bazanje dakai ba , idan dai ba tare dani ba saidai ki fasa zuwa , zama nayi gefen gado nace tou naji na fasa ina cire takalmina. Kallona yayi cikin ɓacin rai yace wato ni ban isa in jera dake mu fita tare ba ko ? Ko kuma karki tafi dani ace kinzo da tsoho ? Tou sai kinje makarantar wallahi , kuma nine da kaina zan kai daga yau ma idan ina nan nine zan riƙa kaiki ko ina tunda na lura so kike ki ɗaukeni wani bansan abinda nake ba , nine ma tsohon ? Yayi maganar yana shafa gefenmu , to idan dai dan wannan na zama tsoho yau saina kwasheshi , da sauri nayi wurin nace yi haƙuri dan Allah , rufe idanuwanshi yayi da yanayin haukarshi yace ke........ Saina cireshi duka wai shekarata nawa ne ? Ke baki da lissafi ne ? Ko dan kinji ina ce miki yarinya ne ? Tou nima bara in dawo yaron tunda kin rainani dani dake duk mu haɗu muyi yarintar , ya ƙarasa maganar yana nufa hanyar toilet , da gudu nasha gabanshi cikin kuka na haɗa hannayena ina cewa na roƙeka da girman Allah kar kayi min haka , daka min tsawa yayi tare da cewa matsa ki bani wuri ya janyeni ya shiga toilet in , binshi nayi ina ƙara yawan kukana dan Allah Dikko kar kayi , so kake idan na fita naga masu gemu in riƙa kallonsu ? Nayi maganar cikin sanyi , tou me yasa kikemin abinda bana so ne ? Bazan ƙara ba , nunani yayi da ɗan yatsa yana cewa daga yau ko me kikayimin zan cireshi kuma banajin yi haƙuri , goge hawaye na nayi tare da jinjina kai nace na yadda , maimatawa yayi a karo na biyu cewa ko me kikayimin. Zan , ya nuna da hannunshi yana fitar da sauti mai kamar fito , kenan zai cireshi. Nace na yadda , tou wuce muje yayi maganar yana murmushi , fitowa mukayi saida ya tsaya gaban madubi ya sake gyarashi kalar fizgar hankali sannan yace muje yayi gaba.....
Binshi nayi ina sauke ajiyar zuciya. Gaskiya yana da kyau maza ku san abinda yake ɗaukar hankalin matayenku daga gareku , kuma ku ɗan riƙa cancaɗewa kuna yin kalar burgewa a gaban matayenku , ita fa mace abu kaɗan ke ɗaukar mata hankali , idan dai bakayi ma matar ka gayu ba tou gaskiya baka haɗu ba , wallahi wasu mazan ko ɗaki ɗaya baka iya haɗawa dasu , ba wanka bare kuma kasa ran samun ƙamshi a jikinsu , yadda yaje kasuwa ya dawo haka zai dawo ba wanka ba wanke baki duk ƙurar kasuwa ta gama barbaɗeka , ita kuma matarka tasha wanka taɗauki fili da gayu kamar zataje gasar wanka , ta haɗu tana ta zuba ƙamshi kamar matar sarki sai kace a haka zaka zo ka wani rungumeta , tsakanin ka da Allah kayi mata adalci kenan ? Gaskiya duk mu haɗu mu gyara gaba ɗaya sai a zauna lafiya. Idan kuwa ba haka ba ta sauke ka daga saman gadonta har sai ka koyo wanka wanke baki da kuma shafa turare.... {{ ba cewa nayi ki saukeshi ƙasa ba , ah kidai ɗan gyara mishi dan kema zakiji daɗin tafiyar idan da ƙamshi , ai kindai gane ba , kinsan wasa bai tafiya idan ba abokin wasa haka kuma baya daɗi idan babu abun wasar , kenan wancan hikimar da nake magana tafi daɗi idan da gyaran fili }} haba kuma kuyi koyi da Dikko mana. Ku zama "yan gayen mazaje shalelen matayenku.
Da sauri Ashiru ya fito yana cewa Mai gida bari in kaita , bai mishi magana ba ya wuce wurin mota ina bin bayanshi , da kanshi ya buɗemin na shiga ya rufe , wurinsu Ashiru ya koma suna gaisawa , duk banajin me suke cewa bayan ya gama ya dawo yana ɓata rai , juyar da kaina nayi nima ina fushi har muka fita daga gidan.....
Har mukaje makaranta baimin magana ba , nima banyi mishi ba. Tuƙinshi ya jawo hankalin mutanen dake kusa dan baya tuƙi da natsuwa kwata² , fita. Yace bayan yayi parking , matsawa nayi na shafa fuskarshi nace amana nayi maganar idona cike da hawaye , naji jeki , saida na sumbaci gemunshi sannan nace ina sanka na faɗa ina kallon idonshi , murmushi jin daɗi yayi yace Allah yasa da gaske kike , da gaske nake Dikko , riƙeni yayi tare da cewa zanzo in ɗaukeki idan kun tashi , kuma ki daina ɓatamin rai An mata kinga banajin daɗin abinda kikemin , wallahi maganar da kikamin shekaran jiya bakiji yadda naji ba har yanzu zuciyata ciwo takemin , ki daina haka babu kyau , to , ngode ya faɗa yana ɗan gyarawa. Nima godiya nayi mishi tare da fita , addu'ar Allah ya tsare yaimin nima nayi masa Allah ya tsare hanya , saida ya tafi na wuce......
A aji kuwa Mai gilashi ta tambayeni yadda aka ƙare jiya , kai tsaye nace mata janshi nayi mukayi faɗa duk dai abinda ya faru na faɗa mata. Cewa nayi kuyi faɗa ? Ta tambayeni ? Waike baki iya irin ɗan karuwancin nan ba ? Waye yace miki da faɗa ake hukunta namiji ne ? Ai namiji bakiyi mishi hauka , da sannu kike latsashi , kuma da kinja kika ga yaja sakar mishi ki kuma bishi da swry My President. Shiru nayi bayan wani lokaci nace nima yadda kika ganki a da haka nake , wani abokin Babana ne yayi min asiri naɗan firgice bayan kuma an samu nasara lalatawa na zama sai a hankali , tunda kinga abinda nakeyi dama bani ce nakeyi da kaina ba , tsoki Mai gilashi tayi. A hankali ta ɗan fara labarta min halin Sharifa tare da cewa kuma idan ta faɗamin na daina zuciya ina aikawa Dikko da saƙon zagi , in kwantar da hankali in bata haɗin kai yauma inyi ƙoƙarin riƙe Dikko karya fita domin tana shirya ma Sharifa gadar zare ne , so take ta rifto cikin rami ita kuma sai ta bita da ƙasa ta rufe , tana min maganar taga wani malami ya wuce , miƙewa tayi tare da cewa bari inje wurin wancan mai zanzaron inji me yasa zai ɗauro mana ƙugu yana tayar mana da hankali , tana faɗin haka ta fice daga ajin.
Har aka tashi makaranta Mai gilashi bata dawo ba , Dikko ne yazo ya tafi dani gida , ina ta tunanin yadda zanyi in hanashi fita a daren yau , dan nayi imani yadda ya samu sauƙin nan tou fa lallai babu abinda zai hanashi fita.........
*JAMILA MUSA....* ce.
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*
*SAI NA AURI D ' K*
🅿 ------ 6
Gareku 👇🏻
UMMIEE ZARIA
UMMU FATIMA
&
ZAINAB MUSTAPHA MUSA { Mmn Sadig }
Wata irin zufa ce ta ratato ma Dady. Da sauri ya cire hular saman kanshi ya fara firfita da ita , itama wayar tashi ya sauke daga saman kunnenshi. Miƙewa tsaye yayi bayan ya ajiye wayar da hular a saman tebirin gabanshi ya cire babbar rigarshi ya ajiye cikin tashin hankali , kamar wani zararre ya dafa tebirin yana furzar da hayaƙin ɓacin rai , ganin banza bata kai zomo kasuwa yasa ya ɗauki makullin mota da waya ya fita.... Da irin tuƙin Mai gida Dikko ya fita kuma dashi ne yaje har gidanshi......
Ba kowa gidan. Dan haka kai tsaye ɗakinshi ya wuce. Inda yake ajiye takaddar ko wane ƙaddara nashi ya nufi wurin ya fara ɓaro kaya harya sauko da kaf kayan ya ɗauko fiyel in. Salati ya farayi jikinshi yana kyarma , a hankali yake ɗagawa yana salati harya gama dubawa amma babu takaddun gidajen da akace masa anga Hafsa tana takai dillah² , da gaske kenan ? Wata irin luƙeƙiyar ashariya ya atura yana fizge² ya ɗauki wayarshi.....
Matarshi ya fara kira , amma harya ƙari kiranta ya gama bata ɗauka ba dan bata da lokacinshi. Hafsa ya fara kira itama tanaji tana kallo ta watsar da kiran nashi wanda Amisty ce ta hanata ɗaukar kiran , fita yayi da sauri yabar sauran takardun watse a tsakar ɗaki , har ya fita me ya tuno ? Oho ya dawo ya tattara su ya ƙanƙame a jikinshi kana kuka kamar gawar jaririn mahaukaciya......
Hello......... Ta faɗa cikin irin yanayin da mata keyi idan zasuci banzar samari. Tsoki Yazeed yayi cikin gunguni yace ummm , Ya Yazeed ya naji sai wani riƙe fili kakeyi ko baccin rana kakeyi ne ? Ummm ya faɗa da yanayin rashin san yayi wayar , kuɗi fa sunzo ta faɗa cikin farin ciki da zaƙuwa , yaji daɗi sosai amma bai nuna ba , yace wasu kuɗi kuma ? Yayi maganar yana ɗan sakin muryarshi kaɗan. Cikin warwarewar lissafi tace Yaya D' K ya turomin da 10miliyan na biko , da sauri Yazeed ya miƙe tsaye yace kina ina ne yanzu ? Ina inda ka sameni jiya , yanzu D ' K yana sanki kenan ko ? Ummm itama ta bashi amsa cikin yanayin jin daɗi da kuma kunya haka kaɗan , ba damuwa gani nan zuwa muyi magana , sai......ka.....zo muah. Ta bashi kiss tare da tsinke kiran.
Yazeed yace wawiya wane ɗan tashar bokan ne yace miki D ' K yana bikonki ne ? Halan yayi haka ne dan ya ruftaki , tunani yayi sosai bayan wani lokaci yace kai ai ba haka yake fitar da zakka ba , jakunnan banzaye kuso Yazeed ko ba kuɗi yarinya ta hau network mai service , ai dake da Sharifa da ma duk wata ƙazarma mace na rantse da girman Allah baku gabanshi , da dai yana ɗan biya allon mata { danbe } da sai ince zai wanke ku ne yayi gaba abunshi. Bara dai in tafi da wuri kafin wani malamin tsubbun ya rigani ƙwacesu.
Da wata irin rashin lafiya mijin Halima ya tashi yau , ko idonshi baya iya ɗagawa , yayi amai tun cikin dare baisan iyaka ba , yayi na safe yayi na rana har a marecen nan sai yunƙuri yakeyi , waƙƙƙ , yaci uwashi yaci ubanshi har yai laushi. Duk ƙawayen matarshi zagaye dashi sai jera mishi sannu sukeyi kamar sakin kurwar mayu. Halimatu kuma na gefe tana ta duba sabbin kayan matar da ƙawarta ta aiko mata dasu tana karantawa da kuma irin matsayinsu da wutar da suke bayarwa idan an shiga tsakiyar filin wasan danbe. Saidai ayi murmushi idan aka karanto "yan bala'e , ita a gefe ƙawaye a gaban gado.....
Da gudu na fito daga toilet jin wayata na ƙara , nayi tunanin kila ma ko Mai gilashi ce ? Dikko na gani tsaye gaban wayar zai ya ɗauka , aikinshi kenan idan yana nan aka kirani , An mata waye ya kiraki ? An mata me akace ? Kawo in gani ? Shi gani yakeyi ta waya ake zuge mishi ni. Da Allah nace ka daina taɓamin waya , kai ake nema ko ni ne wai eye ? Haƙuri ya bani tare da miƙomin yana cewa na ɗauka fa Mama ce ta kira. Idan Innar ce kai take kira ne ? Nifa gaskiya bana san abinda kakemin ko kai zuwa nakeyi ina tsareka idan kanayin cht da karuwowinka ne ? Sa ido kamar maƙocin mai kura. Ansar wayar nayi daga hannunshi , baƙuwar number ne kuma kiran ma ya tsinke. Kayan dana cire na ɗauka na wuce ɗakina ba tare dana gama wankan ba , ina zuwa na rufe ƙofa na zubar da kayan ƙasa na wuce toilet.
Gefen gado Dikko ya zauna cikin ɓacin rai.... Yana ƙoƙarin riƙe ɓacin rai amma An mata bata gani dai ko ? Tou wallahi idan dai ta kuskura ya riƙeta na lahira sai yafita jin daɗin , wai karuwowinshi ? Jinjina kai yayi cikin tsananin ɓacin rai a hankali ya furta saina kashe ki.... Ya faɗa yana riƙe wuyanshi... Rufe idanuwanshi yayi yana hasko lokacin data fito da gudu daga toilet , banda ma hauka da yarinta ji yadda ta wani fito da gudu ? Da taje ta faɗi ta kashe mishi babynshi , taci albarkacin ko ma waye kwance a cikin cikinta , amma akwai ranar ƙin dillanci , wato ranar da wandon mai gari ya ɓace.......
Tunda na shiga wanka kiran yake ta sake shigowa har na gama wanka ba'a daina kira ba , ni nayi tunanin Mai gilashi ce dan haka na ɗauka , suna na *SHARIFA...* , wai Allahna na rantse da girman Allah na kaɗu gabana ya yanke ya faɗi kawai dai naji tsoro , dakel nace to ya akayi ne ? Kiranki nayi in faɗa miki nice wacce Dikko yake so. Kuma ni kaɗai yake ma soyayyar da bata da farko ballantana ƙarshe , ya gina min soyayya mai girma tsakanin saman sararin filin zuciyarshi zuwa tawa. Ni kuma na gina mishi tawa soyayyar bulo da bulo tsauni da tsauni tafiya da tafiya kalma da kalma tsakanin dare da rana na gina a cikin zuciyarshi..... Nice yake ma soyayyar da bayayi miki irinta , iska ce ni idan na kaɗo saina ɓaro da "ya "yan kanya daga jikin uwarsu iska ta tana ƙarfi. Ki tsaya ki gani haka zan kakkaɓeki tsaf inyi waje dake.......
Murmushi nayi mai sauti tare da cewa aikin banza an tura agwagwa ruwa. Duk lokacin da kikabi kika gina ko ya gina wannan ba matsala ta bace ba. Nidai abinda na sani na kuma fahimta ke daƙiƙiya Dikko ya ɗaukeki , idan kuma kina ganin shi zai aureki tou