Showing 36001 words to 39000 words out of 70788 words
Chapter 13 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt
da taga hotonshi ta matsa sai ta ganshi da idonta , matashi ne kyakkyawan yaro amma kai da ka kalli Dikko kasan baida mutunci ko kaɗan ɗan iska ne bugu ɗaya , kuma wasu irin firgitaccin idanuwa gareshi tsaitsaye na rashin kunya , ita a yadda ta auna shekarunshi zasu fara daga 35 har zuwa 38 ita dai a yadda ta ajiyeshi fa , dan yana da suffa mai ɓoye shekaru yana da cikar zati da ƙwarjini saidai daga ganinshi kasan sangartacce ne , yana da tsayi dai² kyau , yana da murzajjen jiki na zubin jaruman maza ba ƙaton jiki ba dan baida ƙiba kuma ba siriri bane ba yana dai da jiki mai kyau sai hutu ya zauna. Gaskiya Dikko yayi mata kyau , kuma kyakkyawar fatarshi ta dace da gemun daya ajiye mata , zuwa ɗaya idan kayi mishi dogon kallo yana da ɗabi'un mutanen kirki amma gogaggen ɗan iska ne kuma bashi da kunya yadda ta fahimce shi , tou taso ace gidan ya ƙone taga yadda zaizo yayi ranfar da akace yanayi wallahi yau taso aci ƙaniyar Dady a murje bakin tambayar kuɗin gidaje har sai Kaka ta dawo suma ta basu kasafinsu.... Itama dai Dikko ya burgeta gaskiya addu'arta ɗaya Allah yasa da rabon Hafsa a cikinshi.
Misalin ƙarfe 11 da wasu "yan mintuna na dare na ɗaure Dikko dake kwance yana bacci saman gado da igiya. Buɗe idonshi yayi ya kalleni cikin ɓacin rai , cike da rashin kunya na murguɗa baki tare da zazzaro ido nace yau na ɗaure ƙafar yawo wallahi , sai naga ta inda zaka bi ka fita , da chat in dare da fita yau gaba ɗaya An mata ta hana nayi maganar ina watsa hannunawa alamar babu , fiffizgewa ya farayi yana cewa idan na kwance sai na zaneki An mata , zama nayi gefen gado tare da faɗa cikin rainin wayau cewa ai bama zaka iya kwuncewa ba , taimako ɗaya zanyi maka. Bara in kunna maka kwallo ka kalla , nayi maganar ina ɗauka rimot kusa dashi na kunna tv. Tsoki yayi a gajiye ya koma ya kwantar da kanshi yana bina da kallon takaici....
Ka daina kallona ka kalli talabijin na nuna mishi tv , ajiyar zuciya ya sauke tare rufe idanuwanshi. Tashi nayi daga inda nake zaune na koma cikin kujera na zauna inacin gurguruna { pop corn } ina cin abuna ina kallon kwallo , buɗe idonshi yayi ya kalli Sultana sannan yace An mata kizo ki kunce ni kafin raina ya ɓaci , naji shi sarai amma sai na ƙure volume ina cewa ka rufe min baki bana san surutu ina kallon kwallo ka kalla nace , nayi maganar ina watsa gurguru baki. Ke......... Zoki kunce ni nace , cikin faɗa nace anƙi a kuncen kan kuma ka rufemin baki bana san surutu idan ina kallon nace maka , An mata......... Ban barshi yayi magana ba na zaro ido tare da haɗa masa da shittttt 🤫 nayi masa ina ɗora ɗan yatsa na a saman baki.
Kallona ya ƙarayi. Bayan wani lokaci yayi ɗan taƙaitaccen murmushi kaɗan ya kauda idonshi gefe yana nazari..........
*JAMILA MUSA...*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*
*SAI NA AURI D ' K*
🅿 ------ 7
Ƙasa² nake magana ina cin gurguru cewa. Ƙaryar rashin kunya. Ai sai an bar zomo yake zama guza. Kowa ai ɗan iskan kanshi ne , ni har an nunamin hanyar hukunci , a dai² lokacin daya sake kalloni da dogon kallo , murmushi nayi kaɗan tare da ibar gurgurun kamar zan bashi bayan kuma muna da tazara. Ya² ne ? Zakaci ? Na faɗa ina murmushin nasara. Girgizamin kai yayi alamar a , a , ya bani amsa. Ban sake magana ba na ci a bakina ina cewa saina..... Na nuna da hannun hagguta yankawa alamar zan yanka mishi wuya kenan. Idan bai daina kallona ba kalli can nace ma na ƙara nuna mishi tv...
Gyara bakinshi yayi ya kalli talabijin. Ni kuma naci gaba da cewa wato da ka kwanta kayi bacci , misalin 12 saura ka tashi. Daga saman gado zaka wuce bayi ka watsa ruwa , zaka fito ɗaure da rigar wanka. Kana fitowa sai ka tsaya jikin madubi , zaka goge jiki da towel , da hannuwa na na nuna yadda ake shafa mai ina shafawa a fuskata , daga fuska naci gaba da nuna duk inda ake shafa mai a jiki. Bayan ka gama saika fara goge fuska , ummm na nuna yadda yake sharce gemu da kuma yadda yake shafa turare dariya nayi sosai tare da komawa da baya na kwanta cikin kujera , bayan ka saka kaya sai ka wani fece abunka. Cikin dariya naci gaba da cewa tou yau Jarumarka ta ɗaure kafafuwan yawo , no cin cingom & no cht na nuna yadda yake riƙe waya da wayata , da hannun dama na sake nuna babu. Ina cewa kaji....??? Na riƙe kunne na dan ya tabbatar min yaji.
Baiyi magana ba kuma bai kalleni ba yaci gaba da kallon tv kamar yadda na sashi. Banda tuƙuƙi babu abinda zuciyarshi ke mishi , yana ta ƙoƙarin riƙewa da kuma dannewa ya gagara , cikin wata irin murya yace ke kunceni nace miki. Ya faɗa yana rufe idanuwanshi. Da hannu na nuna karka dameni da baki kuma nace ka fita idona in ba haka ba mizanete kana daga kwancen nan. Kai............. Nine zaki dakar ? Tou saina kunce kuma saina kashe ki , da sauri na tashi ganin yana fiffizgewa da ƙarfi , saina kashe ki........ Da gudu na fita a bakin ƙofar fita daga ɗakinshi na zame , shi kuma ihunshi ya ƙara yawa , ninen ma zaki daka ? Yau idan basai na ma kasheki ba tabbas saina kashe kaina...... Da sauri na tashi nayi ɗakina ina kuka ashe har yanzu Dikko bai warke ba. Rufe ƙofa nayi har nayi fitsari saboda tsoro. Har yanzu ina jiyo ihunshi yana faɗin saina kashe ki...........² ƙyarma jikina ya farayi kodai in fita in gudu ? Nine zaki daka ma.......... ? To zo ki dakenin , kai.............. Saina kashe ki............. Kowa da kowa ma saina kashe shi....... Ah² ba lafiya ? Na faɗa ina ƙara fashewa da kuka. Babu wani ruwana da ciki har babyn shima sai na kashe shi................. Kai......... Wai nine ma mace zata zane , a sauƙaƙar murya yace aiko dana zama lusarin namiji. Daga haka ya ɗauke. Tunda ai kunga yana kwance ne , dan dama idan ciwon ya taso mishi kwantar dashi ƙasa akeyi , idan dai aka kaishi ƙasa anci galabarshi. Sai a bashi magani dan idan ya tashi dawowa ya dawo da tunani.
A firgice na juya inda na yada wayata tana ƙara , ummm na faɗa tare da goge zufar dake bin fuskata. Rairafawa nayi inda take na ɗauka , Ashiru ne yake kirani , ɗauka nayi cikin kuka nace Dikko ne baida lafiya , ke kina ina ne ? Na kulle a ɗakina. Waye ya ɗaureshi ne ? Cikin kuka nace ai kaine ka siyo igiyar , Ashiru yace ba wanda ya siyo igiyar ba wanda ya ɗaure shi nake magana , nice na ɗaureshi , meya haɗaku ? Shiru nayi banda abin cewa , Ashiru yace kizo ɗakinshi. Cikin kuka nace ni gaskiya bazan zo ba , ranki ya daɗe kizo mu duk muna ɗakin , tou na faɗa tare da ajiye waya. Toilet na shiga na wanke jikina sannan na fito na gyara inda na ɓata da fitsari , kaya na canza bayan na gama na kira Ashiru yana nan ? Ya tabbatar min suna nan , hijabina na saka na buɗe ɗaki na nufi ɗakin Dikko.
Gaba ɗaya su Ashiru suna wurin , Dikko yana kwance a ƙasa ya dafe kanshi da hannun damarshi cikin yanayin jigata , ya fiffizge igiyar , wurin saukowa daga saman gadon ƙafarshi ta riƙe shi yasa ya faɗi kenan ? Kallona Ashiru yayi cikin ɓacin rai yace amma me kika faɗamin maganar siyo miki igiya ? Shiru nayi ina ta karkasa ido kamar an kama ɓarawon "ya "ya ina kallon Dikko sai kuma in kalli Ashiru. Gaskiya baki kyautawa abinda kikeyi. Mai gida dai kike ma haka ? Ya faɗa yana jinjina kanshi , kausasa murya yayi da fushin zuciya yace tabbas ke yarinya ce. Amma komin yarintarki ya kamata ki riƙayin abu da lissafi , tunani da kuma hasko abinda kaje ya dawo. Wannan ɗin dai da kika raina shine bangon rayuwarki idan har kika ɓata mishi ko wulaƙantashi kanki , idan kuma ya mutu tabbas ke zaki shiga3nki. Shawara da neman mafita ya rage naki. Ya ƙarasa maganar yana gyara mishi kwanciyarshi.
Durƙusawa yayi gaban Dikko yana kuka kamar ranshi zai fita , bayan wani lokaci yayi magana cikin hayaniya cewa ke bake kaɗai ba. Bango ne kuma jegone ga duk wani da kika ganshi yana tsaye a wurin nan yayi maganar yana nunasu hada kanshi , ƙasa² yayi da murya cewa duk yawancinmu nan da kika ganmu kusan mu goma sha wani abu rabin mu duk mu marayu ne , rabi daga cikinmu duk basu da uwa uba ko ahali , haka akaje aka kwaso mu aka kawo mu domin kula dashi , an ɗaukomu ne kamar karnukan shi muyi haushi yayin da wani yake tunkaroshi , babu wanda yasan darajarmu ko tausayin mu rayuwar da zamu shiga. Mu rayu ko mu mutu ba damuwar su bane ba shiɗin dai ake so mu ba rayuwarshi kariya , muyi haushi wan² yayin da wani yake zuwa dan taɓashi , mu kula dashi bayan ƙarshen wata biyu abamu naira dubu hamsin.
Cikin ɗaga murya yace amma shi bai mai damu karnuka ba........... Shine ya jawo mu jikinshi ya ɗauke mu kamar "yan uwanshi , ya soke wata banzar dubu hamsin da Mai gidansu yake bamu {{ wato Dady }} bayan ya nuna mana kowa yaje yayi rayuwarshi , haka mukai ta kuka ya rufa mana asiri ya barmu mu zauna dashi koda an daina biyanmu albashin zamu zauna dashi saboda dubu hamsin ɗin dashi bai ɗauketa kuɗi ba , ganin yadda muka shiga tashin hankali yasa shi da kanshi yace zai riƙa biyanmu , shin kinsan farashin da yake biyan ko wane ɗaya a cikinmu ? Me mukeyi masa ne ? Bamayi masa wanka bama dafa mishi abinci bama masa wanki bama shara komai bamuyi mishi , zaiyi fita goma bai fita damu ba. Muci musha kowa dake wurin nan mazaunin shi yana a cikin gidan da yake rayuwa. Duk inda yake muna da gidanmu muma a can ƙarshen gida , palo bedroom toilet yadda yake da A C a ɗakinshi muma namu dashi. Yaga munyi kuka shi yasa yake san ya rayu damu domin muma muyi farin ciki kamar shi. Masu kuɗi nawa sukeyin haka ? Wanda sun ɗauki duk wani ɗan aikinsu kamar wani jakinsu. Shi yasa suka kira talaka da suna bawa.......... Cikin kuka yace wai talaka shine bawa , wai bawa ? Kuma alere dangin jaki wai ya mutu gobe a sake sabo. Tou shi bai banbanta ba saboda soyayya , abincin da mukeci shi kanshi abun duba ne , idan ciwo ya kama ɗayanmu shine magani kuma ba'a cikin wanda zai bamu ba , albashin kowa a cikinmu da yake biyanmu idan kikaji sai kanki ya kwance , kafin albashi kuma ya bamu׳ , ya ƙara mana² , kullum cikin bamu yake , da marainiyar murya yace wai dandai muyi farin ciki , shi bai ɗauki duniyar a bakin komai ba dan ba itace gabanshi ba , tsaye yake ba dare ba rana , ya hana idonshi bacci zuciyarshi da kwalwarshi sunƙi samun natsuwa , bawai dan ya rasa yake nema ba. Ba kuma dan zai rasa yake tarawa ba , akwai su... Kullum zuwa suke da yawa..... An tarasu tun ba'asan amfanin kuɗi ba , tashi yayi ya ganshi cikin arziƙi tunda ya buɗe idonshi duniya kuɗi ya fara gani ba labarinsu yaji ba. Tunda Mai gidanmu ya girma suma kuɗin san ganinshi sukeyi , da kansu suke zuwa domin suma kansu sun san shine zai yaɗasu domin suje inda ba'a da labarinsu. Yana nema ne domin al 'umma kuma nemanshi yanayin shi ne domin ya gina rayuwar duk wanda yake da rabo a ciki. Akan Mai gida gaba ɗayanmu zamu iya sadaukar da rayuwarmu dan nema masa farin ciki. Ya ƙarasa maganar yana dukan ƙirjinshi bisa gaskiyar shi. Mu bazamu yadda ba , haka kuma bazamu lamunta ba , idan ke baki san darajarshi ba mu mun sani , idan bashi da amfani a wurinki mu yana dashi a wurinmu , idan kin gaji mu bamu gaji ba. Ya ƙarasa maganar suna maida Dikko saman gado. Duk ma wani mai cewa Mai gidanmu bashida mutunci ko ɗan duniya ne ko ya raina mutane koma dai miye mu yana da kyakkyawan hali a wurinmu. Mune muka sanshi muka zauna dashi muka kuma san ɗabi'unshi dan haka mune zamu faɗi ko waye shi...... Yayi maganar yana kaima bango naushi da hannunshi. {{ yadda yayi maganar hasashe na ya bani da Inna yake... }}
Duƙawa yayi tare da dafa gefen allon gaban Dikko yana ci gaba da cewa. Me kike so ? Idan soyayyar ce an baki , kuɗi ne damuwarki ? Suma an baki. Sultana me kike nema ne wai .....? Ko har yanzu kuɗirin fansa bai goge ba ? Rungume Dikko yayi ya ƙara yawan kukanshi yana cewa bawan Allah da wannan dalilin ya ƙwammaci ƙare rayuwarshi ba aure. Yana sanki amma yarinta da rashin tunani ya hana ki fahimta. Iya ruwa iya fidda kai......... Ko wae'...iya allonshi ya wanke. Gaki ga Mai gida tunani da samun mafita yana wurinki , dabara da sanin sirrin rami ya rage ga mai shiga rijiya. Daga haka bai sake magana ba ya riƙe hannun Dikko cikin soyayya yana mishi kallo mai nuni da tausayi , janshi aka suka bar ɗakin Ashiru yana ci gaba da kuka.
Kamar wata jaka haka nabi bayansu da kallo har suka gama fita daga cikin ɗakin. Goge hawayen daya taru a fuskata nayi. Na maida kallona inda Dikko yake kwance yana bacci. Tou ya haka ? Meya faru Dikko ya sake warwarewa ? Ko wayau yayi min daya bani labari cewa ya warke ? Ko yayi tunanin ni bazan iya ci gaba da zama dashi ba idan bai warke ba ? Labarin daya bani G R A a ɗakinshi ya tunomin da yacemin.....
_Naso naga Al ' Ameen dan naso zanyi magana dashi amma hakan bai yuwu ba. Shi Mustaphan yayi ma Ashiru jagoranci zuwa inda suka binne tsafe²nsu , komai Ashiru yayi saida suka gama komai lunfashi na ya dawo , tunda nake ban taɓajin irin wannan tashin hankali ba wai an shanyemin numfashi kiji wani masifa ? Hmmm Yazeed kuwa Ashiru yaci ubanshi kuma shine ya maido Abbakar company duk bansan anyi ba._
Dogon nazari nayi , na hasko duk maganganunshi na baya. Tabbas a maganar Dikko akwai lauje cikin naɗi. Wato ni zaima ƙarya ? Dani da ku masu karatu idan baku manta ba , ni yacemin wai yaje yayi jinya har na tsawon shekarun da nayi ina zaune a gidan Inna , ku kuma tuno. Tou ya akayi ya saki Jiddah bayan shi baisan inda kanshi yake ba tun daga ranar da ni nabar gidanshi naje gidan Inna ? Ya akayi takebinshi har Abuja ? Me yasa yayi min ƙarya cewa dawowarshi kenan yazo ya tafi dani a ranar daya aiko Abbakar ya kawomin waya ? Bayan tafiyar Abbakar kuma Ummar yazo da Umar ya tafi kuma shi Dikkon yazo da kanshi ! To me gaskiya ? Ni miye matsayi na a wurin shi ? Meya ɗaukeni ne ? Me yake nufi dani ? Tabbas duk yadda akayi maganar Inna itace gaskiya Dikko baya so na......... Mai gemun yaudara na faɗa cikin hayaniya ina cewa yau saina bar maka gidanka kaje ka samu daƙiƙiyar da zata zauna dakai , ka raina mutane ni nafi ƙarfin kai ka rainani...... Wai ni zaka faɗawa ka ɗaure kanka da wayar wuta ni zaka ba labarin "yan sfires {{ Express }}....? Fuuuu na fice daga ɗakin na koma ɗakina. Wayata kawai na ɗauka da makullin mota na fice.....
Da gudu na fito waje ina kuka har wurin mota ta , ina shiga mota Ashiru ya iso wurin yace ina zakije ne ? Cikin ɓacin rai na nunashi da makulli cewa zanje gidan Babana. Ai kasan nima Babana da Mamana suka haifeni ko ? Yadda iyayen Dikko sukeji dashi kuma suke ƙaunarshi nima Babana haka yake so na , yadda yakeji shima ɗa ne a gidansu nima ɗiyace na nuna kaina , yadda aka haifeshi nima haifata akayi ba ta sama na faɗo ba , har yanzu hannu na yana kan ƙirjina ina nuna kaina. Goge hawaye nayi da hannun haggu na ina ci gaba da cewa duka׳ kullum Dikko saiya dakeni doke²n shine soyayyar da kake iƙirarin yana nunamin wacce har kake min gori akan ta ? An baki soyayya da kuɗi. Cikin marainiyar murya nace shin baka tambayeni me nake nema ba ? Saki nake buƙata daga wurin Mai gidanku. Bana san ɗaya ko biyu a rubutoshi duka a aiko dashi a gidanmu na ƙarasa maganar ina karta makullin motar