Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 70788 words

Chapter 16 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt

Ads the beginning of article before Image

07 Jul 2024

749

Ads at the middle of Article

ni miye matsalar ne ? Kullum sai kin ɓatamin rai wai me nayi ne ? Haba An matana ya ƙarasa mganar yanamin kyakkyawan riƙo , cikin shashshekar kuka nace kaine , nine kuma ? Tou wai meye nayi da zafi haka ? Ka daina so na ai , haba Yarinya ke ko wani ne ya faɗa miki ai zaki ce a , a , duk duniyar nan wai waye yake dani idan bake ba ? Haba ƙaramar yarinya.... Duk kin burkeni na zama wani lusari sai anfani kike da soyayarki kina murzamin zuciya san ranki ya ƙarasa yana min kyakkyawan murmushi , shiru nayi ban mishi magana ba , kefa yarinya ce ? Kalli Dikko fa ? Akwai tazarar tsayi shekaru da kuma tunani , cikin dariya yace wallahi kin maidani kamar wani zararre ke ko tsoron Allah ma bakyaji ? Haba An mata , ɗagoni yayi daga jikinshi yace ai nasan ma kin yafemin ko ? Ey tou zo muje. Yana riƙe dani har toilet da kanshi ya wankemin fuska yana cewa dan Allah An mata ki daina ɓatamin rai gaskiya banajin daɗin abinda kikemin.


Wai ke baki san ba'a ɗagawa miji harshe ba ? Baki san idan mijin yanayin zuciya yadda ake saukeshi ba ? Ba'a hawo namiji yayin da yakejin tuƙuikin ɓacin rai , komai yana iya faru a dai² lokacin da yakeyin fushi , Juyowa nayi na riƙeshi ina ci gaba da kuka , a wahalce yayi gajeriyar dariya cewa ai nasan baki iya tafiya ki barni wasa kike , ƙaramar yarinya. Wai miye ke damun kanki ne ? Meye nake miki wanda baya miki daɗi....? Ni kifaɗamin , faɗamin matsalata dake sai nima in faɗa miki matsalolinki kowa ya daina ɓatawa kowa sai a daina faɗan tunda kin gaji. Kinga ko a rigima kin fahimci ni nafi sangarta bana gajiya haka zakiyi ta hawoni ina baki kashi kullum kina fama da jinyar fata , kuma kinsan banayi zuciya in zaneki kuma in maƙalƙaleki anjima inyi ta warwarewa ya riƙeni yana nuna yadda yakeyi idan yana kwance dani , dariya nayi ina kallonshi. Shima dariyar yayi tare da ɗagamin gira yace wallahi kuwa , tou ni ina ruwana ? Gani ga "yar yarinta ina fa morewa , niɗin mai sa'ar rayuwa ne , duk da dai kince wai niɗin tsoho ne , amma a haka dai ai ina bada wuta a tsakiyar filin wasa ko ? Ya ƙarasa maganar yana ɗan taɓe bakishi tare dayin wasa da girarshi.


Murmushi nayi ba magana amma har yanzu ina kwance a jikinshi , ɗan wayancewa yayi dai yaci gaba da yabona wanda nidai nasan a zuciyarshi ba haka bane ba , yana dai yabo na ne dan inyi farin ciki ya kuma sauke buƙatuwarshi yayi bacci da natsuwa. Koma dai bada gaske yakeyi ba ni naji daɗi , yana da kyau maza su riƙa farfaɗawa matayensu kalaman da zasuyi farin ciki su girmama musu kansu sai suji su suma ashe dai wasu manyan shegu ne , ta hakan ne zaka riƙa zaliƙo mata matsalolinta a hankali idan mai hikima ce saita riƙa gyarawa , irin dai kana yabonta kana cewa ai idan kikayi kaza kinga yadda kike bada haske ? Ko kike ruɗani ? Ko bana tare dake sai inyi ta tunaninki , kaza². Nan zaka ga ta warware tace you ai kaza da kaza ma da nakeyi kaza. Ni nayi farin ciki da yacemin duk nafi su Yusra kyau , gani "yar gayu kuma ni "yar yarinya su duk sun tsufa ma , ai haɗuwa ta ta wuce duk inda bana zato , shi a ganinshi ma yafi ko wane namiji sa'ar aure , bayan ni nasan Dikko ƙarya yakeyi , kuma wai da nace masa ba wani cewa yayi in kalli kaina a madubi fa , An mata kalli idanuwanki , ji lallausar bakinki ya nunamin saman lips ina , kalli nan ji can uwa uba kuma saikin dafe uztaz D ' K a gado. Kalamanki suna da daɗin sauraro bayan ni nasan duk lokacin da zai kwanta dani sai ankai ruwa rana , yanzu nan ya gama min faɗa ina ɗaga mishi murya , amma da yayi dai nayi farin ciki ,


Wai ni ina da kyakkyawar fata idan kuma nayi mata ado da lalle zan ƙara haɗuwa wai kuma lallen na hausa amma a zuba turare a cikin lalle dan ya kashe ƙaurin lallen , warware kaina yayi yana shafa gashin kaina wai na iya gyaran gashi ya mishi kyau a haka. Shiko banyi kitso ba yafi ibar mishi lissafi , haka na saki baki naita dariya kamar sakara ina cewa ai idanma nayi kitson warwarewa yakeyi , ey ai dama nima bansan kitso , saidai ina san wannan kitson kin tunashi ? Wani mai kyau ? Kai yayi miki kyau An mata , nifa nasan bana kitso harma gara kalaba , amma da nace masa ni banyi kitson nan ba , cewa yayi na manta yana ta nunamin yadda kitson yake. Yadda yake nunamin irinshi ni nasan ban taɓayin irinshi ba a tarihin rayuwata. Amma Dikko ya kafe kai wai nayi shi in tuno mana , saida na natsu sosai na gane irin kitson dake kan Yusra ne , dakel dai nayi yaƙe mai ciwo , shima zanen lallen a wurinta ya gani ai na gani itama lallen hausa ne akayi mata wani irin ado mai ɗaukar hankali.


Wato duk duniya ita mace baka da abinda takeso sama da a yaba mata , suma mazan haka suke , haka kuke mana "yan rainin hankali , kuma so kuke a yaba ku kan nan naku yana muku wani girma kunajin ku wasu manyan "yan duniya , kuna wani ciccika fuska ku masu gida ana zugaku kuna wani karkace baki kuna dariyar ƙasaita kan׳ dariyar cikin izza da nuna isa. Yana da kyau mazaje ku riƙa gyarawa matayenku da irin yajuju wama jujun da ku kuke gani a waje. Kuma a hikimance , ba zagi ba duka ba gori wance ta fiki ko wane matar shi kaza² a , a , ba haka akeyi ba a hankali zakayi mata dan kune kaɗai kuka san a inda kuke shiga kuna gano irin wannan duniyanci. Bawai nace kuɗin "yan duniya ne , ina nufin irin matan da kuke huɗɗoɗi dasu. Ba kuma ina nufin tasha ko sakarci ba , kamar a kasuwa ko a ofisoshinku da dai sauran wuraren da kuke mu'amula dasu , tunda suna ɗauko wanka da gayu kamar zasu tashi duniya dan haɗuwa , su barbaɗo muku turare a ciko ido da kwalli ana firfira muku idanuwa. Ku saki baki ba aji kuyita gaggaɓa dariya irin wacce ko matanku bakuyi ma irinta. Tou karta burgeka kuma karta ruɗa maka lissafi da tunani , ka riƙe karka bari tayi wasa da tunaninka nata ƙarya ne zahirin tana gida , idan tayi nata sai yafi baka sha'awa akan na sharar bakin titi , wai su kun gane matsalarsu.....? Matsallar auren su ba a gabansu yake ba. Haka zasu shaƙe miki wuyan miji suyi ta ranfa dashi , idan kuma ta gaji da cin aljihunshi taci shi har babunshi saita tura wata itama taci gaba da gayar miki miji babu tausayi , itama idan ta gaji tayi gwanjonshi shi kuma zuwa wannan lokacin ya zama ɗan gari. Ma'ana ya gane hanyar yadda take , kafin ki ankara an firgita miki miji , wata macen ma su biyu ne a wurin miji amma dai lusaranci da hauka yasa sunyi sake sun barwa karnukan bisa titi suna ta mishi haushi , baki jin haushin ta waje wai ta gidan itace ta tsone miki idon tsabar hassada , kullum kika tashi da ita a zuciyarki baki da buri da kwanciyar hankali yadda zakiyi waje da ita , tou idan ta tafi ance miki shikenan bazai sake aurar wata ba ? Ba matan gida ya kamata kuyi hassada dasu ba yaƙi zakuyi da matayen dake matse mazanku a waje , ku kuma maza gaskiya kuma kuji tsoron ku tausayawa matayenku , ku kyautata musu , kuyi musu magana da sanyi² ku lallaɓa su , ku tarairayesu , ku ririta su ku jawo su jikinku da farin ciki. Kuyi kwanciyar aure dasu cike da soyayya da kuma nuna musu finsu buƙaturwa hakan , ku gode musu ku yaba ƙoƙarinsu ku basu ƙwarin guiwa ku jinjina musu ko bakuji daɗi ba , a hikimance zaku riƙa nuna musu yadda abun yake har su ƙware su anshewa ɗan tama doki. Wasu matayen sunfi wasu mazan gogewa ta wannan harkar da kuma gogewar rayuwa ta zamantakewar rayuwarmu tayau da kullum. Wasu kuma mazan sunfi matan , idanuwansu a tsaye yake tsakiyar kai , tou koma dai waye tafi gogewa ta gogar da abokin rayuwarta sai kuyi rayuwarku gidan aurenku da natsuwa.


Kuma bawai ina nufin kuna biyewa matan waje ko ku fahimci magana ta da wani yanayi. Ku fahimce ni da kyakkyawar fahimta amma aradu ku ƙyale gaibu ku kama zahiri , idan kuma ka nuna mata taƙi gyarawa kayi mata...... Ba cewa nayi ka ƙaro aure ba , nufi na a ƙaro miki kayan ado a ci gaba da baki kula ana ta kwantanci nuniya da gyara har ki gane ki gyara , dan kunsan mu mata ba kishi mukeyi ba hassada muka iya. Sanin sirrin kishi zahiri babu munafurci da yadda akeyin shi kanshi kishin aradu yana nan wurin maza. To kuyi kishi yayin da akafi matayenku ku tsaya tsaye da gaskiyarku kuyi gyara.


Tou lallai fa idan taƙi gyarawa ka lallaɓa kayi mata ƙarin...... Haske , dan inda kuke shiga mu bama shiga wurin , irin matayen da kuke gani mu bama ganinsu , kuke ganinsu kune kuma kuka san inda kuke ganosu har sukeyin abinda kuke ganin mu bamayi muku irinshi , wata matar daga gidan aurenta maƙotanta sai familynka da nata ahalin su kaɗai ta shiga kuma ta sani , sai abokan arziƙi , kuma kila su basu da wayayyun idanuwa bare ta waye da wayewarsu. Sanin da daka santa dashi tun tana budurwa kafin kuyi aure shine dai har yanzu babu wani ci gaba , wata macen kuma da wayewar ido take zuwa gidan auren amma sai ta zama wata aljihun gefen riga ta daƙiƙance ta zama wata sai addu'a kawai. Tou kai da kake shiga kana fita kana zuwa inda ita bata zuwa kuna ganosu suna labbatarku da irin abubuwan da suke jan hankaliku ka sanar da ita mana , ka koyar da ita , idan ka faɗa mata raguwa kayi ne ? Kaɗan faɗaɗa mata kwalwarta ka buɗar mata da idonta dai² irin yadda ka gano suka ɗauki hankalinka. Ka wadata matarka da sutura dai² ƙarfinka ka wadata ta da kayan ƙamshi mayuka masu kyau hoda sabulun wanka ka ciyar da ita karka riƙa maƙalewa wurin mai indomie ko mai tsire da wasu lafiyayen kaji kabar matarka taita kokowa da tuwo , wallahi kuji tsoron Allah kuci irin abinda kuke ba iyalinku irin abun nan da kukeyi kuci daɗi ku barsu da marmarin irin abinda ku ya gundireku dan nacin cinsa da kukeyi wallahi zalinci ne. Cuta ce , ku kuma matan kuma muji tsoron Allah masu siyar da shinkafar miji kuna zubin adashe Allah yana kallonku tom.....


Idan an gyara miki kema ki riƙa gyarawa mana , kar yace kije kiyi kisto two step , ki karkace baki ah ni wallahi bana san wannan kitson kaza² , to wane iri kike so ? "Yar rainin hankali. Ke harma sai ya faɗa miki kiyi irin style kaza ? Ashe ma baki san abinda kike ba. Idan akwai abinda yafi two step kiyi mishi mana , ke meye naki a ciki ? Ba shine yake so ba ? Tou ayi mishi mana a zauna lafiya ? Ko yace miki wallahi kaza na gani ya burgeni , kiyi irinshi , ke uwar tsiwa maimakon kice tou sai kice ah sai kaje can idon daya gano a wurinsu kaje kayi ta gani. Ƙalu balenki da bawa namiji wannan ansar idan ya fara gani tou fa lallai ƙaryaki ya ƙare , kenan kinma yadda yaje ya gano na wajen ko ? Shin wai mema kika tsaya yi har namiji yafi ki hikimar rayuwa ? Ke bakya kishin kanki ne eye ? Haba Hajiyata da Allah karki bani kunya mana. Ko ke baki so tou kiyi mishi idan dai shi zaiyi farin ciki mana , sai sunje sun kallo na wajen a ɗauke miki hankalin miji ayi yamma dashi a barki da ciwon tunani , idan shima ɗan rainin hankali ne kuna gari ɗaya fa da kinyi waya zaice yana abuja ko kaduna ina nan airport zan hau jirgi in tafi lagos , ke ya maida jirgin tana can ta ɗaukeshi an barki gadin gida , kar kuma mijinki yayi tafiya ki tuno cewa kila yana miki ƙarya ne baije ko ina ba , kulli inki ahir inji tsofi , ƙalubalen ki da zargi. Damuwa ta dameki daga nan sai neman shawarar abokai , idan kinyi sa'a da ƙawar kirki ta baki shawara ta gari , idan baki dace ba ta haska ki da malam tsibbu suma daga nan kasuwa ta buɗe , idan kuma kika hau layin maijin taushinki tasa ki , ki kakkaɓo auren , dama tana can tana ta yawon zawarci ita ɗaya ta rasa ƙawar cin titi tou ta samu abokiyar yawo , idan kuma ta ƙwarewa cin amana ta auren miji a barki da wallahi² , ke baki gane illar abun sai kin shiga makarantar , baza ki fahimci wuyar karatun ba sai an shiga second semester ku kula dai......


Gadai Dikko yana faɗawa Sultana , wanda ita a ranta tasan ba haka bane ba. Amma taji daɗin yadda ya yabeta tare da nuna mata tasha gaban mata da yawa. Tou kai idan ka tashi faɗar naka kalaman ka faɗa mata su da gaskiya cikin soyayya. Ku daina haɗe fuskoki wa matayenku haka babu kyau , wani namijin idan kika ganshi a majalisa yafi kowa harshe dariyarshi tafi ta kowa , duk mai tallar da tazo sai yajata da surutu , sai matarka zaka rainawa wayau idan ka tashi shigowa gida ka haɗe fuska kayi ta wani gadarar banza wai kar ta raina ? You bayan ka manta kun haɗu a tsakiyar filin wasa ? Allah wani namiji idan ya shigo gidanshi kamar "yan fashi sunyo samamen dare. Ba "ya "ya ba iyayen suma kansu gabansu harbawa yake kamar an ɗorawa mutum wuƙa a maƙoshi.....


Cike da soyayya mukayi wanka muka baro toilet in cike da tsantsar muradin san kasancewa da junanmu. Kuma har muka fito bai daina zugani ba sai dariya nakeyi ina watse baki kamar lefen wacce babu uwarta a gidan babanta , ina ta sakin layi , zuwa wannan lokaci gaba ɗaya na manta da wasu banzayen hotunan da na gani a wayarshi na fuskanci rayuwa mai daɗi da gusar da damuwa a wurinshi........


Bayan kwana huɗu.


Ni na rasa inda mai gilashi ta sake a cikin jahar katsina , na nemeta na rasa inda take , kuma har gidanta naje bata nan kuma Dikko da kanshi ya kaini. Wayarta ma a kashe. Daga gidanta gidan Inna mukaje kamar dai kullum yauma haka taita habaice² tana zagin Dikko wai bazai zauna mata a kujera ba , ƙiri² Inna ta koma wata zararra , shiko murmushi yayi kaɗan ya samu wuri a saman kafet ya zauna , nima kusa dashi na zauna. Haka taita zaliƙe²n da ita kanta bata san dalilin yinshi ba , taita zaginshi tana aibatashi saida ta gama kaf tace idan yaji fushi ya sakar mata "ya , shafa kanshi yayi ƙasa² yace ban gaji ba ya faɗa yana suɓaro baki a sakace , saida ta gama dashi ta juyo kaina tace kema ɗayar mara zuciyar kaza² nima taci gaba da sheƙeni har ta gaji tayi shiru , saida ta sauka ta gama da kanta ta rufe bakinta mukayi mata godiya mai gida Dikko ya sauke mata manya kuɗi muka wuce gidansu.


Ajiyeni yayi ya tafi huɗɗoɗin shi , Momy kuwa sai ɗan zungurar min ciki takeyi tanasan ta gano wani abu ne daga gareni akan Sharifa. Shiru nayi nidai idan ta matsa min da tambaya saidai ince mata Momy ban sani ba wallahi , wai har yanzu munayin faɗa da Dikko ? Tambaya ɗaya takemin ni kuma ansa biyu nake bata , ah umm. Gajiya dai tayi ta ƙyaleni , har ɗaya saura na dare bai dawo ba saidai ya turo Ashiru ya maidani gida , wato yau ya samu hanyar tafiya wurin "yan iskan matanshi ko ? Ita kuma Momy harma ta yadda da ƙaryar da yayi mata wai ya fita da Dady. Dan da Ashiru yazo tafiya dani sai ta kirashi wai shi yazo da kanshi ya tafi dani mana , shine yace mata yana tare da Babanshi kenan dan karta dameshi. Tun a mota nake kiranshi , shine ya turamin da saƙo wai yana meeting , danma ya ɗaukeni kidahuma. Ci gaba nayi da kiranshi ƙarshe kashe wayarshi yayi. Ashiru ka kaini wurin Dikko , lafiya ? Ya tambayeni ? Lafiya qalau shine yace ka kaini. Mai gidan ranki ya daɗe ? Tou meye a wurin da bazanje ba ? Ai banma san inda yaje ba , daga haka bai sake magana ba , nice naci gaba da cewa amma ai a wannan motar yake a ina ka samoshi ka ɗauko motar ne ? Shiru yayi ya ƙyaleni , fita nayi daga motar ba tare dana sake cewa komai ba na nufi ciki , Papi yana kwance a palon ƙasa yana bacci saman kujera. Ɗaukarshi nayi ina taɓashi ya buɗe idonshi yana shashshekar kuka , ɓata fuska yayi a hankali ya rufe idonshi yana cewa Yaya.... Kila ya dakeshi ne. Me yayi maka ? Saida ya sake sauke

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads