Showing 63001 words to 66000 words out of 70788 words
Chapter 22 - KWARATA RETURN BY JAMILA MUSA.txt
san Sharifa kika ga gaba ɗaya ya ɗauke wuta tabbas wata irin gagarumar jifa ce , sai kunyi da gaske kun ƙara miƙewa dan wannan tarayyar da babu "yan al'adu ai nasan da tafiyar bata yuwu ba. Tayi maganar dan bugun cikinsu. Ai nan uwar Sharifa ta saki baki taita hawa gefen layi , ina shi Malamin naku ne Mama ? Sharifa dake full charge tace yai tahiya tayi maganar cikin muryar mashaya tana layi. Cikin faɗa na duniyanci Mai gilashi tace gaskiya Mama kuma da laifinku. Laifin meye nawa ni a ciki ? Saboda Allah Mama kuɗan ƙiyasta dihun kai da wayayyar rayuwa , maza fa yanzu idonsu kallon rana yakeyi , akwai wanda baya san mace ? Taya Sharifa zata riƙa zuwa zance da hijabi dan Allah ? Su wa'annan "yan duniyar ai bakya nuna musu hijabi ba domin wayayyar rayuwa zaki fahimtar dasu kin iya , cake take dan haka maganarta bata fita.
Mai gilashi tace da Allah rufewa mutane baki muyi magana da magabata. Shiru Sharifa tayi Mai gilashi taci gaba da cewa Mama ni ina da Malami acan Zandar aiki yake kamar yankan wuƙa , saidai shi aikinshi sai an ɗebo fitina zama ɗaya yake buga aiki fitina ta koma tayi bacci. Malamin shine kika ga ya ɗauremin ƙugu nake baza hajar iskancina kasuwa². Kuɗin mota dana aiki duk ni zan bayar idan buƙata ya biya saiki bani abu na. Mamar Sharifa tace wane irin malami ne sai an jawo fitina yake aiki ? Izzar aiki ake gaya miki Mama , su bala'en suke kwantarwa dan dai kawai su nuna muku jajircewar su a wurin iya aiki , kuyi shawara sannan ku taro bala'e ni zan tsotse muku duk dafin masifar bala'en. Miƙewa tayi ta jawo Sharifa suka fito waje. Wuri suka samu dan ɗan keɓancewa gefe tace ke jaka bakuzo kun daki matar Dikko ba , sautin maganar kaɗai ke fita amma bakajin maganarta. Mai gilashi tace idan kunga dama kuzo ku daketan , tana faɗi haka tayi gaba abunta.
Shegu masu wayan tsiya , na gano kuma kuna haɗawa da ɗan tsibbunku , fashewa Mai gilashi tayi da kuka tana tafe a mota tana cewa Allah ya tsinemiki albarka Sharifa. Kin cuci rayuwata ƙarshe na ɓuge ga zaman b q , wai me nayi miki ? Laifin nena aikata haka da ciwo a rayuwarki ? Me na tsare miki a duniya ? Haɗu barimi rabuwa idan kowa ya tuba shine kika bini kika daƙilemin tafiyar sa'ar rayuwata. Na rantse da girman Allah yadda kika hanani kema sai kin jibge a gidan mai gadi ko ɗan share²n filawowi. Shima malamin naku zan ganoshi duk sai watse a sarari kuma idan na tashi uwar watsi zan muku yadda za'ayi rabuwa ko gaisuwa babu tsakaninku dashi. Wayarta ta ɗauka ta kira Sultana. Saida ta gama karatun da zatayi ta kashe wayarta tana cewa ki auri D ' K in zan gani , dani dake dashi da ita matar tashi an watsa kifi abinci a ruwa........
Misalin ƙarfe 10:19 na dare. Kai mai karatu ka tuno wacece ni tun farko dana fara baka labarin rayuwata. Na kira kaina da ma'abociya iya shafa turare tsantsar kyau da cikakken body. Da gudu turaren dake jikina ya fita daga jikina ya tafi......... Saida ya zagaye kaf ilahirin gidan sannan ya dawo mazauninshi. Ƙarar tafiyar takalmina da ƙaraurawar da jigidar keyi ya haɗu yake fitar da wani irin halakken sauti mai daskarar da zuciyar duk wanda yaji sautin. Na wanku daga jiki har kayan dana saka. Fili na iba na fara bada taku. Pa - Pi dake kwance yana kallona yace unguwa zakije....? Ƙaniyar anguwa. Dariya yayi tare da cewa kuma wayyayi baci cau ba. Kusa dashi na matsa nace niɗin ce banyi kyau ba ? Dariya yayi tare da rufe idanuwanshi yace waca nike wayyayi... Tsoki nayi cikin jin haushi na koma gefen gado na zauna. Buɗe idanuwanshi yayi tare da cewa baci zuwa ? Ka rufe min baki munafiki kuma bazan sake zuwa dakai ko ina zanje ba tunda kace banyi kyau. Ɓata fuska yayi ya fara kuka yace wayyayi waca ne. Cike da masifa nace ka rufemin baki kuma bana sanka. Shiru yayi ya tura ɗan yatsashi cikin hanci yana kallona. Ka daina kallona. Sauka yayi daga saman gado yana kuka , duk kiran da nake mishi tafiyarshi yayi yabar ɗakin.
Yaya wai Momy tace bata sona. Tsoki Dikko yayi yace ka wuce ka bani wuri. Gefen kujera ya raɓe yana kallonshi cikin kuka yace kaima baka can Pa - Pi cikin ɗaga murya yace fita ka bani wuri nace.... Fita yayi da gudu yana kuka kaima wayyayi na fata dakai , Daga ɗakin Dikko wurin Ashiru ya tafi kai ƙara...... Tashi nayi tsaye ina miƙewa naji jigidar nan tayi wata irin tsuwwa , cassssss....... Burgeni abin yayi na ƙara bada tako ina matsawa jikin madubi. Tana cossss casss. Dariya nayi na samu abin wasa kamar yaro sabon tafiya da takalmi mai tsuwwa.
A wannan yanayin Dikko ya sameni , shi kuma ya biyo Pa - Pi ya dakeshi daya ce wai ya ɓata dashi. Kamar wani gele ya kafeni da ido yana muzurai. Murmushi nayi danni ina cikin shauƙi ne , iska yaja ta baki sannan yace ina Pa - Pi....? Kaje can ka nemeshi mana. A fusace ya shigo ciki , gudun da nayi dan hawa saman gado yaba jidar nan damar yin ihu sosai , cacasss.. Cosss cisss² cuuu. Wahalallen dariya Dikko yayi dakel a gajiye yace menene ke ƙara......? Yayi maganar yana ƙoƙarin riƙo ƙafata. Da sauri na fizge nayi baya. Tsaya in gani mana. Yayi maganar yana fizgoni da ƙarfe. Da sauri ya hanakaɗe rigar jikina ya kunce zanin jikina. Na tsani jigida sai kin cireshi......... Wace karuwa ta baki ita.....? Ni zaki maida mahaukaci ki riƙa kaɗamin ƙaraurawa , da kokawa ya kamata yana ƙoƙarin tsinkawa. Karka tsinkamin abu , saina tsinka ni ɗan iska ne da zaki riƙa min alama iye ? Yayi maganar yana gauramin mari in sakar mishi hannunshi dana riƙe , cizon hannun nayi cike da ɓacin rai nace bazan saki ba , kai................ Ni kika cizarma hannu. Saina kashe ki.... , a tsorace nace shikenan tsaya baka so ko ? Ey bana so An mata. Shikenan bara in ciro maka , nayi maganar idona cike da hawaye. A tausaye ya kalleni ni kuma na cire jigidar na miƙa mishi. Taro hannunshi yayi dan ansa yana kallona..............
11/02/2020
*JAMILA MUSA...*
[2/14, 12:12] ~M K: ⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA RETURN...*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
Rubutawa...
*JAMILA MUSA...*
*SAI NA AURI D ' K*
🅿 ------ 11
Hararata yayi yana jinjina kanshi baraki bani ba. A shagwaɓe nace umm² ina maƙale kafaɗa daga kwance. Tou bani ya sake tambaya a karo na biyu da kwantacciyar murya. Kuka na farayi ina cewa nidai ka barmin kayata idan baka barmin ba aradu kashe kaina zanyi..... Hawowa yayi saman gadon a shagaɓe yace baki iyawa. A hankali na juya mishi baya ina shashshekar kukan ƙarya na rufe idanuwana tare da ɗora hannun damana a saman fuskata. Kusa dani ya kwanta ya fara ƙoƙarin cire hannuna daga saman fuskata.
Juyowa nayi da sauri na riƙeshi. Yiyh.... Yaja ajiyar zuciya da yanayin buƙatuwa tare da lumshe idanuwanshi da shauƙi. Wai me yasa ne.... ? Da yanayin matsuwa yace riƙe jigidarki mayi magana daga baya.
A makare na fito daga ɗakina da sauri. Yau na makara ko kalaci bazan tsaya yi ba. Ɗakinshi na wuce yana ta wani tattare²n wasu "yan guntattakin tarkacen dashi buƙatuwar shi ne , a ɗan zumuɗance nace muje na makara fa. Ba tare daya kalleni ba yayi ɗan gajeren tsoki wai ya manta bai faɗamin ba zaiyi tafiya. Cike ɓacin rai na matsa kusa dashi da hannuna na tambayeshi cewa ina kuma zakaje ne ? Nima ban sani ba saina fita , cika idona yayi da hawaye da siririyar murya nace haba Dikko bana baka haƙuri ba ? Shine kuma zaka tafi ka barni ? Riƙe kunnuwa na nayi a dai² lokacin hawayen idona suka samu damar gangarowa a saman kumatuna cewa dan Allah na bari na ƙarasa maganar ina riƙeshi. Tunda na baka haƙuri sai kayi haƙurin kuma ka bari idan na sake sai ka tafi haba Dikko........ Na ƙarasa maganar ina ɗagowa daga jiki nai mishi jigataccen kallo.
Kiyi haƙuri bazan wani daɗe ba. Ya faɗa yana taɓa hancinshi da ɗan yatsa manuni. Nima gaskiya idan ka tafi yau zanji kamar ince ban yafe maka ba , taƙaitaccen murmushi yayi tare da duƙawa yana gyara takalmin ƙafarshi. Ci gaba nayi da cewa tou kafa sani tafiya yau gaskiya shiga haƙƙina ne idan ka tafi ka barni zanji irin yanayin daka faɗamin jiya dan Allah , wallahi idan ka tafi gaskiya zan shiga tashin hankali. Da sauri ya ɗago kanshi ya kalleni da yanayin damuwa yace ke meye haka ? Ai gaskiya na faɗa idan ka tafi fa matsala za'a samu. Riƙeni yayi jikinshi ta baya da kwantacciyar murya yace wace irin matsala ƙaramar yarinya? Faɗamin inji mana yayi maganar yana wasa da gashin gemunshi a jikina. A kasalance nace kawai dai zanyi kewarka , mtsww yaja tsoki dan a yadda na fuskance shi ba haka yaso in faɗa mishi ba.
Rufe idanuwanshi yayi cewa taya ake kewar miji ? Faɗomin da me zaki ibe kewa yayin da kike tunowa idan muka kasance a inuwa ɗaya ? "Yar marainiyar dariya nayi cikin yanayin jin kunya nace Dikkkkoooo. Wata sheɗaniyar dariya yayi mara sauti mai ƙarewa da hmmm An mata kenan , yanzu dai idan na fahimceki kar inyi tafiya ? Ey wallahi kawai muyi zamanmi mu daina faɗa na ƙarasa ina juyowa na rumgumeshi. Me yasa baka san jigidar da aka bani ?
Takawa ya farayi ina kwance a jikinshi har zuwa bakin gado yake cewa. Mace ita gaba ɗayanta ƙyalƙyali ce , da hannunshi ya nuna yana ci gaba da cewa tangaram ne saboda su mata an haifesu ne domin kwalliya shi yasa ana haifarta ake mata huje dan ado. Baki ga komai na mace yasha ban²n dana namiji ba ? Maganarta tafiyarta kallonta sigarta da komai nata ya ban²ta. Tayi ado da kayan ado masu burgewa da ɗaukar hankali kamar zinari saboda yana gyara mata jini. Ko cikin duhu kikaji maganarta basai an faɗa ba kinsan ita mace ce , domin zakiji maganarta da sanyi² cikin natsuwa tako nagarta matsayi da kuma aji. Ha kuma maganar namiji yake. Kalli takalmin ƙafata kinga irin nawa da naki da ban²ci , naku masu ado ne na maza kuma ko oho. Ayi masu wani tsini² a saka musu duwatsu da maɗauri macen kenan shi yasa komai nata yake da burgewa. Ni ina san matana ta kasance mai ado da zobe , "yan hannu , ɗan kunne tsarkar wuya da ƙafa amma tsabar sharri yanzu ba damar mace ta saka tsarƙar ƙafa shike nan an kaita wani wurin daban dan rashin adalci. Hmm itama dai ado da ita wani ɓoyayyan sirri ne. Jigida duk tana cikin kayan ado na mata sirrinta daban ne amma matan bariki su suka sanshi shi yasa sukafi yin amfani da ita....
Mata 10 idan kika tarasu zaiyi wuya a cikinsu kaf ɗin su ki samu mace ɗaya data saka jigida a ƙugunta. Amma idan zaki tara karuwan da suka san kansu suka goge suka kuma daɗe tare da sanin sirrin bariki zaiyi wuya kika haɗa mace 10 ki samu mace biyun da ƙugunta bata ɗaura jigida ba....! Dalilin ɗaurata da sukeyi ni nasani amma bazan faɗa ba. Dalilinsu na sakawa da motsinta ai sunsan abinda take haifar da , kuma nima nasan dalilinsu. Nine dai ke baki isa ki ɗaurata ba tunda bana ra'ayi amma duk abubuwan da kikaji na faɗa a farko idan kika saka wannan ra'ayi na ne har tukuici ma saina bayar. Nidai dan Allah ka barmin abuna in saka , An mata na barki a saka lafiya amma da sharaɗi , tom , karki sakata ki fita , na yadda , duk kuma lokacin da kika buga ƙaraurawar tou fa lallai zanzo kuma kinsan ni bana zuwan banza. Wannan shine idan kin yadda ni da kaina ma zan ɗaura miki ita..... Na yadda , kin yadda ? Ey na yadda , banajin yi haƙuri babu wani wallahi² , jinjina kaina nayi tare da tabbatar mishi da ey na amince. Saukeni yayi daga jikinshi yace ina zuwa , inda ya ajiye jigidar yaje ya ɗauko da kanshi ya zagayamin ita so adadin ruɓin daya ruɓanyata a ƙuguna. Nima na shiga sahun mata masu ɗaura lambar ƙugu.
Yau banje makaranta ba haka kuma Dikko baiyi tafiya ba. Yadai shiga gari. Pa - Pi kuma yana wurin Momy dan tun jiya da yaje yakai ƙara wa Ashiru ? Ashirun cewa yayi suje yakai shi wurin Momy. Shine yakai shi kuma yace a faɗa mana dani da yaya ya fata damu , kuma duk bamuyi cau ba wayyayi. Itama Momyn goyuba bata hatu ba. Shima Yaya baiyi cau ba. Dokin ma shima baiyi cau ba. Itama motarshi bata da cau ta Dady tafi hatuwa. Kuma kada mu sake muma muzo musu gida.
Saida na gama hidimar gida kaf duk abinda zanyi nayi na ƙare sannan na ɗauki wanka na kulle wanka da wani irin kafirarren leshi mai sauƙin nauhi. Nasha ado da duwatsunan wuya kunne hannu da "yan yatsu. { bawai dutse ba no׳ cikin tsarabar da mai gida ne ya kawo na saka wani daga ciki dan burge shi a wannan sansanyar maren sakaliya. } na wani kawo ɗaurina dai² da zamani na kafe wankan dashi. Naɗan yayyafa ruwan turare bawai yadda kamshin zai zama mai cutarwa ba haka kuma bazai tashi zuciyar mai shaƙa ba. Cikin kujera na koma na soke da zama irin na matan masu kuɗi ina ta ƙasaita ni matar Dikko. Wayana dake gefe ta na ɗauka na kira Mai gilashi , cikin sakonnin da bata wuce 30 ba ta shiga , tana shiga ta ɗauka. Bayan gaisuwa nace mata maganar jigida wai meye sirrin ne ? Ke malama wannan jigida da kika ganshi yasha ban² da jigidar da zaki je kasuwa ki bada kuɗi ki siya kinji ? Wannan ɓoyayyar sirri ce kuma bawai na baki dan kije ki saka weldrop kiyi ajiyarta ba , ki ɗaurashi a ƙugunki hajiya kiyi tafiya da isarki.
Halbawarta ɗaya tsallen zuciyar duk namijin daya ji kukanta , adadin buguwar zuciyarshi adadin buƙatuwa , ke wannan jigidar bala'enta yasa sukayi mata suna da huce takaici. Baga namiji ba har kishiya saita shafa miki lafiya , idan uwar naci ce da rashin zuciya taita zama tana haɗiyar baƙin ciki , idan kuma tunburƙuƙu ce wato mai zuciya a maƙoshi filin gidan zata barmiki. {{ miye ribarki idan kin kora wata ? Idan ta tafi ma wata zata zo , itama idan kika sake korata wata rana a kawo wacce kema zatayi out dake.... }} Ma damar dai zaki motsa ? Idan har tayi kuka tou fa lallai ke kasuwa ya buɗe ba gareki ba garemu masuyi domin kasuwanci.
Hmmm amma ni kinaji da farko Dikko cewa yayi baya so fa , dariya tayi tare cewa ɗan duniya wai ko yace miki akan wani dalili ne ? A , a , kawai dai yace bana ɗaurawa danshi wai baya ra'ayin lambar ƙugu. Sake sheƙewa tayi da dariya tace kai kiyi haƙuri amma duniyanci mijinki ya shafe tudun da bakya tunani , yanzu ina jigidar ne ? Ce masa nayi dan Allah ya barmin ina so , shin ya baki ita ne ? Ya bani mana gashi a ƙuguna ɗaure. Taf lallai kam Sultana sannu da ƙoƙari. Yawwa na faɗa ba tare dana sake magana ba ita kuma taci gaba da cewa. Baice miki komai ba bayan haka ? Ni baicemin ba ? Karfa kiyi ƙarya ? Ai kinsan ni ƙarya ba ɗabi'a na ne ba. Ki ranste baice wani abu ba , Mai gilashi kinsan bana san ayi ta tsayuwa a magana ɗaya mu matsa gaba ko macimma matsaya. Gaskiya sirrin irin jigidar nan rufaffen sirri ne , buɗeshi da sanin matsayinshi sai tuɓaɓɓin mata. Mafiya yawan maza dubu a cikin ƙaso miliyan zaiyi wahala ki samu namiji dubu dake ra'ayinta , domin ɗaurata cikar duniyanci ne shi yasa mafi'akasari mu matan bariki ne mukafi amfani da ita. To ke me yasa baraki sakawa naki ba idan dai harshi mai ra'ayi ne domin gyara adonki da burgewa. Sarƙa "yan kunne zobe da ɗan hannu duk domin mata akayi su , shin "yan hannun basa ƙara ne ? Ke kanki da kika saka shin ya kikeji kanki dan Allah idan suka motsa ? Mata masu hikima sune suka san yadda abun yake badawa , amma iya ado dasu sai jajirtaccin mata masu duniya , ƙasaitacci bugun farko a filin sanin sirrin rayuwar zaman takewar aure.
Idan dai har ke mace kinsan damarki da haggu bazakiyi sake ko sakaci da ado ba. Kaso casa'in na mata , auna sauke min gashin kansu kiga yadda suffarsu zata zama ? Amfanin wanka da ma'anar yinshi ya tattara a wurin mu da mukeyin shi. Idan har mace ta sauke gashin kanta domin rashin buƙatuwarshi idan har ta haɗa da girarenta wane suna mu zamu kirata dashi ? Duk da dai cewa gaban rigarta ya turo. Zuwan farko ba'a kallon structure saidai a kalli yawan ado