Showing 27001 words to 30000 words out of 65672 words
Chapter 10 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt
tunda shiya jawa kansa
dukda abinda yayi b laefi bane amma yasan a wajenta shi me laefi ne
" Dan haka kasan yanda xakayi d wannan maganar Dan kuwa wlh souban k dauko abinda ze iya fin qarfinka ni kuma baxan jure b "
Maganar Maman ta daawo dashi daga tunanin daya tafi
Tana gama fadin hakan ta wuce ta barshi nan xaune xuciyarsa fall cike d tunani kala_kala .
******Yau kam a gajiye ta daawo gida Dan sun sha lectures tun safe se yamma
Tana shiga parlourn ta tatadda mamama kadae a ck tana jona turaren wuta
Ta qarasa tana xubewa kan kujera a lokaci guda tana kae hannunta kunnenta kamar xata cire hearing aid din
Tasowar mamama y sanyata fasawa
Mamama ta qarasa ta zauna kan kujerar
Kamar jira take se kuwa ta dora kanta kan cinyar mamaman kamar xatyi kuka tace
" Mamama vana jin dadi bansan meke damuna b ni komae ma ciwo yake min "
" Subhanallahi Allah y sawwaqe amma may be gajiya ce kwae kije kiyi wanka seki huta " ta fada tana shafa sumar kanta d mayafin y xame
Kamar an xabure ta kuma seta miqe tana kallan mamama
" Mamama wae ina baby yaje ?
D mamaki mamana take kallanta
Kaddae silar wannan abu y janyo ta6ar6arewar alaqar dake tsakaninsu
" Be fada mk b ?
" Ehh " ta fada tana turo baki
Dogon numfashi mamama taja tana saqawa a ranta Cewar dole ne tayiwa tufkar hanci tun kapin avin yazo yafi qarfinta ...
Cyprus..
Washe gari d safe Arman y daawo gidan
Be taradda ita a parlourn b hakan yayi masa dadi dan haka kwae y wuce bedroom din d yake a matsayin nasa
Sedae ko minti 10 beyi d shiga b Catherine ta turo qofar
Dauke kae yayi yana qarasa rufe akwatinsa d alama ma bata dade d tashi daga bacci b dan sanye take d rigar bacci iya gwuiwa me santsi fuskarta babu walwala tace
" K kyauta kenan ?
Kallanta yayi yana sake dauke kae kamin yace
" Sorry !!
" Is ohk ! But pls yau dae k kwana a gida uhmm ?
" Ohk " kwae y furta dan so yake ta fita y sake ficewa daga gidan .
Yau dinma dae haka y silale y bar mata gidan
Washe gari kuwa daya dawo d safe ta tubure cewar duk inda zashi qafarsa qafarta hadda kukanta tace ko y dinga kwana a gidan ko kuma duk inda y saka qafarsa ta saka tata
" Shi kam yau yaaga masifa a rayuwarsa ( ๐๐ฑ ) ! Ba don er Stephen bace da babu abinda xe hanashi yi mata rashin mutunci
Y yazo gari dan yayi jinyar xuciyarsa ita kuma tana so ta dagula masa lissafi amma dukda haka y kamata y taka mata burki dan haka yce
" Look ! In kina so na xauna a gidan nan sekin dena shige min haka din nan
Ki chanja shigarki sannan ki dena shigo min daki kae tsaye ke kima dena shigowa gaba 1 koma mene we should meet a parlour base kin shigo b
xaki iya ko in tafi ?
Kallansa take sosae abubuwan sun mata tsauri amma xata jure couz since first sight ta rufta qaunarsa ( wato tunda sukayi 4 eyes ๐น )
Dan haka tace
" I will try my best " But about shigowa dakinnan
Will u pls just leave me in dinga shigowa plsss..?
" Nop " y fada kansa tsay ye kuma a taqaece
Turo baki tayi sannan ta juya ta fice
Shi kuma y sauke ajiyar xuciya yana Neman gefen gado y xauna xuciyarsa a cunkushe yana fatan abubuwa d dama su gushe masa .
***
A hankali take ta kowa xuwa farfajiyar gidan sanye cikin doguwar rigar atampha d hijab jalbab hannunta dauke d wayarta
" Sanah ! Sanah !!
Ta jiyo muryar yah imam
Seda ta tsaya kapin tayi relaxing snn t juya fuskarta dauke d murmushin yaqe d ake kira yafi kuka ciwo
Y qaraso shima fuskarta sa dauke d murmushi yce
" Ina xakije ne ?
" Gidan baba xanje ne wajen amrah " ta fada b tare d ta kalleshi b
Yce
" ohh toh ki gaeda umman "
" Xataji in sha Allah "
tana qoqarin juyawa yce
"Ammm sanah naaji kuma abinda y faru In Sha Allah na dauki dangana Allah y bawa souban ikon riqeki d amana
ynx kam ki manta na ta6a furta miki Kalmar so ki koma gani na a matsayin yayanki kamar da "
Murmushi tayi tana jin dadin maganar yah imam din sedae can qasan xuciyarta tausayinsa ne fall ciki
Kana ita kadae tasan me take ji kapin sukayi sallama ta wuce part dinsu amrahn.
Bata baro part din nasu b se maghrib dan ma taji kunnanta yana mata radadi kamar yanda ya saba yi mata a kwanakin nan.
Tana shiga dakin ta zame hijab din dake jikinta gami d cizge hearing aid din tana cixon la66anta na qasa .
Sam bata lura d mamama dake xaune b seda tayi magana
" Sanah lpia dae ? Xo nan "
Seta dago d sauri tana kallan mamama kapin cikin sassarfa ta qarasa wajen mamaman ta xauna gefenta
" Meya sameki ne sanah ? Mamama ta fada tana janye hannun sanah din daga kan kunnenta
Abin ba qaramin tsoro ya bata b ganin yanda kunnen yayi jajir sosae
" Subhanallahi sanah meya sami kunnanki ? Dama yana miki ciwo ne amma baki fada min b ?
" Ehh mamama y dade yana min ciwo ban fadamk b saboda bana so hankalinki y tashi ko ke ko daddy "
" Yah salaam ! Mamama ta fada tana Dora hannunta kan goshi
" Banda yarinta irin taki sanah meye amfanin 6oye rashin lpia dan kar hankali y tashi ae 6oyewar shine yafi cutuwa ynx kalli yanda kunnanki pah yayi ? Bana son irin haka kinji koh karki qara uhmm ?
Gyada kae tayi tana kallan mamaman.
A ranar seda sukaje asibitin daddy likitan dke on duty y dubata sannan y bata magunguna aka mata wankin kunne sannan suka dawo gida.
Mamama ce ta faara shiga gidan ita kuma kasancewar tare sukaje d afrah ya sanya seda suka fara sallama sannan ta nupi part dinsu .
Dae dae qofar shiga sukayi kaci6us d Khalid
Take qirjinta y tsananta bugu amma seta basar kwae ta faara neman hanya ta wuce
sedae y babbake hanyar yana mata wannan shu'umin kallan nasa
" Beb naga kin qara kyau ? Y fada yana shafa gefen fuskarsa
Ko kallansa batayi b amma beyi haquri b y cigaba d fadin
" Ina fatan ynx kin chanja ra'ayinki akae na Ynx ma naxo ne dama inji amsata ko kin chanja inxo a daura mana aure !
Jajayen idanunta ta watsa masa shi kuma se cewa yayi
" Wow beb irin wannan kallo haka ae seki sani in susuce "
shigowar motar Abba farfajiyar gidan ne ya sanya shi matsa mata hanya yana fadin
" Se mun hade beb "
D sauri ta shige part dinnasu xuciyarta kamar xata faso qirjinta ta fito
dan sam harga Allah ta manta d wani Khalid a rayuwarta musamman ynx d ba a gidan yke b sedae jifa jifa yke xuwa.
Sam bata manta da maganar daya fada mata b na cewa duk ranar data auri wanin d bashi b toh ta fara irga kwanakin takabarta !
Ta riga da tayi amanna wani be isa y kawo qarshen numfashin wani dan Adam b sedae idan shekarun d aka dibar masa sun cika
ballantana wani banxa Khalid shi b komae bane saboda haka komae yana a wajen Allah.
****************Duk wadanda ke cikin parlourn sun amince d abinda daddy y fada akan fitar d sanah qasar waje d xa'ayi akan matsalar kunnanta dan gudun matsala
" Sedae wani hanxari b gudu b ! Baffa y fada yana gyara xama
Daddy , Abba , Baba , dukka suka bashi hankalin su kapin shi kuma y dora d fadin
" Naaji duk abinda kuka fada kuma hakan shine mafita dama amma pah Sanah ba xata bar qasar nan b seda igiyar aurenta akanta !!!!
Seda wajen y dauki shiru kowa yana naxarin maganar kapin Abba yce
" Gskiane baffa wannan shawara ce me kyau
toh amma aekin d akeso a gabatar dashi nan d two to three weeks yaushe har xaa bari sae an daura aure sannan xaaje ?
Murmushi kyakykyawan bafillacen yayi kana yce
" A yanxu in akae niyya xa'a iya daura aurennan
sedae gaggawa dama ance aekin shedan ne
toh abinda y kamata shine ynx haka xa'a saka bikin ne nan d 3weeks in Allah y kaemu se a daura auren sannan ranar d aka daura ranar xasu wuce xuwa Los Angeles din "
Gaba daya sukayi amanna d wannan magana ta baffa .
A take a lokacin daddy y kira yayan mahaefin sanah wato alhaji Ahmad y Sanar dashi abinda suka yanke inda y nuna musu babu komae amma se a satin bikin xasu shigo kano.
Manyan gidan ne kwae suka san d xancen amma duk yaran basu sani b .
Gadan gadan aka fara shirye shirye duk da dae abin yaxo a qurace ba wani abu xa'ayi b daurin aure ne kwae xa'ae .
Ko kayan daki ba'a siya b tunda ynxn bama a fara ginin filin souban din b sedae daga bayan biki .
Amma lefe kam har an fara hadawa hakan ne ma ya saka aka fadawa souban maganar auren nasa next two weeks ....
Farin ciki jin dadi walwala baxe musaltu b
yanayin daya tsinci kansa a ciki alqalamina be isa ya bayyana muku b........
In Sha Allah ynx kam kullum xaku na samun posting Sedae idan wani uzrinne y riqeni tunda kunsan ance dan Adam ba'a rabashi d uxuuri
Qaunarku ga littafin nan tana d yawa haka qaunarku gareni tana d yawa ๐ซ๐ฅบ
Heart u owl ๐ฅบ๐ป
Naaji dadin addu'o'inku gareni Allah y bar xumunci ๐ป
Munyi graduation lpia se patan Allah yasa muga result me kyau ๐๐
Mhiz Innocent ce.........โ๏ธ
*โกโA ZURI'AR ARABโกโ* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent ๐ป
Page 24__25
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES ๐๐ Mhiz Innocent luv u owl ๐๐ป
( Baby WhatsApp group link ) ๐๐
https://chat.whatsapp.com/F2PiRdNnrwMKT4mHlIIisl
_Cyprus_
........... Yana zaune a dakin nasa wayarsa ce a hannunsa yana dannawa can kuma se ya tsaya kamar me nazarin wani abu
Zuciyarsa zafi take sosai amma dukda haka ya kaasa mantawa da ita ya kaasa goge ta a rayuwarsa ! Toh ta Yaya ma hakan ze kasance ? Shine yake qoqarin gano hanyar
Dai_dai lokacin wayarsa tayi qara
Ko kallan inda take beyi ba ballantana me kiran ya saka ran ze daga
Kiran na katsewa wani ya sake shigowa
Tsaki yaja yana maida hankalinsa kan wayar don ganin wanda ya masa kira har 2 duk da be daga kiran farko ba
" Bro " ya bayyana kan screen din
Wani tsakin ya sake ja yana danna accept ya kaara wayar a kunnensa ba tare da yace komai ba
Can 6angaren souban yace
" Wai ina ka shiga ne ina ta kiranka baka daga ba ?
" Am on d network " ya fada a taqaice
Girgiza kai souban yayi daama yasan da wuya ya bashi amsar tambayar daya masa dan haka yace
" Hey doctor we missed u a lot yaushe zaka daawo ?
" Soon " ya sake fada cike da qosawa
Numfashi souban ya ajje kamin yace
" Uhmm always da an tambayeka tun kafin ka taafi se kace soon , Any way dai nasan zaka daawk aurena koh ?
Dafe kansa yayi ji yake kamar ya yanke kiran amma se beyi hakan ba but y gaji da wannan maganganun na souban Dan kuwa suna qara masa wani miki ne a cikin zuciyarsa
" Kasan fah saura 2weeks "
Kalaman souban suka daawo dashi daga tunanin daya tafi
" What ? Be san sanda ya furta hakan ba
Souban yace
" Bikin mana an daawo dashi kusa couz ciwon kunnen sanah ne ya tashi , so ana daura aure zamu wuce los Angeles , wait ! Wai kana nufin baka sani b ?
" Is..oh...k " da qyar ya iya tattara wadannan kalmomin ya fada a lokaci guda yana katse kiran
Ruwan dake kan side drawer ya dauka ya zuqe shi dukka be rage ko kadan ba
Zuciyarsa na wani irin suya
Me yake faruwa ne ? Yanzu qiyayyar da en gidan nan suke masa har takai haka ? Wato saboda a nuna masa kowa farin ciki yake da abin shine harda rage lokacin da aka saka a saka irin wannan gajeran lokacin ?
Yazo Cyprus dan ya manta da ita amma hakan yaqi yiwuwa , shi kam ya zeyi ? Zuciyarsa zafi take masa tamkar zata 6allo qirjinsa saboda radadi
Knocking din qofar aka farayi beko kalli qofar ba
Ita kuma jin shiru kuma bata ji motsin ruwa ba alamar baya toilet ya sanyata tura qofar dakin , akayi sa'a kuwa a bude take ta tura ta shige
Can ta hangoshi gefen gado kansa a qasa kamar me tunani
Qarasawa tayi kusa dashi kaana takai hannunta kafadarsa ta dafa tana fadin
" Lurv ! What happened ?
Cikin fushin da bata a6a gani a tare dashi ba ya ture hannunta ya dago kansa ya watsa mata jajayen idanunsa da suka rine saboda fushi sannan ya nuna ta da yatsa yana magana cikin daga murya
" Don't dare repeat dis nonsense again , Is not I will definitely deal with u , get out of my room " y fada yana nuna mata hanya
Idanunta da suka ciko da qwalla takai hannunta kai sannan ta durqushe a wajen tana sakin kuka
Se a lokacin ya gaane yadda ya huce haushinsa a kanta Dan haka waje y samu ya zauna yana dafe kansa
Seda yayi cooling kansa down sannan yace
" Sorry Catherine sorry buh pls ki fita a dakin nan "
Seda tayi kukan ta qoshi sannan ta tashi ta fita dukda dama ita ba haushinsa taji ba tsawar daya mata ne bata saba jin irinta ba .
Ze iya kasancewa mafita 1 ce gareshi itace ya bawa Catherine dama ta shiga rayuwarsa ko kadan ne koda wani abun ze sauya koda kuwa bame awa bane
Ya gaane tana mugun sonsa ta yadda bata qaunar ta ganshi a damuwa
Zeyi qoqarin cire wani kason daga damuwarsa shida kansa In Sha Allah.
**** Tun daga ranar seya kasance arman da Catherine suna fita haka lunch ko dinner kodai something lyk dat
Dama abinda take buqata kenan aikuwa ta dinga bayyana masa irin qaunar da take masa
Taaso ya batta ta dinga masa wasu abubuwan haka na soyayya lyk hug kiss and so_on , but ya nuna mata in ta cigaba da Neman wadannan gaba 1 damar daya bata ze maida ita couz he is not dah stupid yasan muhimmancin addininsa
Hakanne yasa ta barshi , damar fita dashi ma kawai daya bata ta gode masa
A hankali taaja ra'ayinsa akan hakan .
*****Tana zaune akan gadon nata tana karanta suratul isra'i a hankali cikin zazzaqar muryarta
Seda takai qarshe sannan ta ajjiye tayi addu'a tana janyo wayarta da tayi ringing tun dazu
Kafin takai ga duba missed call din wani kiran ya sake shigowa
" Sanam " tayi murmushi tana sauke ajiyar zuciya kamin ta kara wayar a kunnenta
Seda suka shafe wajen 20mins sannan sukayi sallama ta ajje wayar tana jingina kanta da pillow
haka kawai bata san dalili ba kwana biyun nan se tayi ta tsintar kanta da bugun zuciya
" Hasbunallahu wa ni'imal wakeel " ta fada tana dafe saitin xuciyarta
Dai_dai lokacin mamama ta shigo dakin tana fadin
" Sanah har yanzu karatun ne baki gama ba kizo ki daura dinner , daddynku ya kusa dawowa " ta qarasa fada tana Neman waje gefen gadon ta zauna tana karantar yanayin sanah
" Zo nan ! Mamama ta fada in a lower voice
Qarasowa tayi ta dora kanta kan kafadar mamaman
" Meya faru ? Ko ciwon ne ?
Kamar jira take kuwa se kuka hadda sheshsheqa
Hankalin mamama in yayi dubu ya tashi tace
" Subhanallahi sanah meya faru ne ?
Seda tayi me isarta sannan tace
" Uhmm mamama tsoro nakeji
Haka kurum nake jin fargaba mamama bansan dalili ba "
" Ya isa haka sanah , yi shiru kowacce mace haka takeji idan lokacin aurenta ya gabato , ki kwantar da hankalin ki dena saka damuwa a ranki , babu abinda ze faaru In Sha Allah kinji koh ?
Daga kanta tayi alamar " Ehh "
Mamama ta cigaba dayi mata nasiha me ratsa jiki .
Cigaba da shirye shiryen biki shine ya biyo baya a cikin familyn na Arab .
6angaren ango souban yanzu haka ya shiga busy ne sakamakon hada lefe d yakeyi d sauran shirye shirye dae d aka san ango yana yi .
A gefe guda kuma mamama ta kae dinkin hadaddun kayan d daddy ya siyo musu dukkansu daya wansu wanda sanah din zata saka da ita kanta mamaman harma da amrah da afrah dukka mamaman ya bawa yayinda ya kaiwa aunty ma nata kayan.
A cikin satin sega en maiduguri mata qannen mahaifin sanah sunxo su 2 da wata mata .
Ba qaramin farinciki mamama tayi ba nan ta fara ina taka saka ina taka aje dasu
A parlour suka zube ana gaggaisawa kapin aka fara gabatar musu d kayan ciye ciye da motsa baki
Suna nan zaune sanah ta shigo gidan d sallama a gajiye dan ba qaramin gajiya tayi b dan yau sun Dade a school gashi kuma daga yau universities xasu shiga strike
Qarasawa cikin parlourn tayi ta gaida baqin da fara'a dan tasan su amma fa a matsayin en uwan mamama ne
Mamama tace
" Sanah en uwana ne daga maiduguri
ga aunty umma wannan kuma aunty ilham "
Murmushi tayi se taji duk gajiyar da take ji ta tafi a hankali ta qarasa gabansu
Aunty umma tace
" amarya sanah daga makaranta kike ne ?
" Ehh aunty "
Aunty ilham ce ta kar6a da cewa
" Toh maza kije kiyi wanka kiyi sallah se kizo yanzu za'a fara gyaran "
Duk da bata fahimci abinda take nupi b amma dai ta amsa da
" toh " tana miqewa ta shige dakin.
Seda tayi wankan tayi sallah sannan ta fito parlourn lokacin duk basa nan se mamama kawai dake xaune kan dinning
ta qarasa itama dinning din tana jan kujera fuskarta dauke d murmushi ta zauna
Itama mamaman mayar mata tayi da murmushin tana fadin
" Y kunnan ?
" Da sauqi mamama ya dena zafi ma yanzu fah "
" Toh masha Allah maza kici abinci aunty umma na jiranki a common room "
Bata san me aunty umman zata mata b amma bata tambayi mamaman b kawai