Showing 48001 words to 51000 words out of 65672 words
Chapter 17 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt
tumbin giwa cikin matuqar kewar garin .
*****Tun kafin driver ya gama parking ta 6alle murfin motar ta fice
Ya bita da kallo yana kada kae hadi da murmushi, se kace ba ita ce yanzu ta gama cika tana batsewa ba .
A parlourn ta taradda mamama zaune kan kujera tana kallan ARTV
Da gudu ta qarasa ta fada jikin mamaman tana sakin kuka
" Subhanallahi sanah ! Lafiya kuwa ? Meya sakaki kuka ? Mamama ta fada tana dago sanah daga jikinta
Dae_dae lokacin daya shigo dakin yayi dae_dae da sanda mamama ta qara maemaeta mata tambayar
" Meya sakaki kuka ?
Dan kuwa mamama tasan wannan kukan na sanah ba kewa bace kadae akwae wani abin dae a qasa, Dan kuwa da kukan kewa ne tasan yadda sanah din ke yinshi cike da shagwa6a
Tsayawa yayi be qarasa shigowa ba ya tsaya kamar an kafeshi, yana kallan fuskar sanah din yana jiran yaji amsar da zata bawa mamaman.............
Mhiz Innocent ce...........✍️
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent 😻
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
Page 38
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻
( Baby WhatsApp group link ) 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e
..........Cikin sheshsheqar kukan tace
" Nayi kewarki ne mamama !
Se yaji wani sanyi ya ratsa kafatanin jikinsa, se a lokacin ya samu damar qarasa shigewa cikin parlourn da sallama
Mamama ta kallesho tana amsa sallamar tasa cike da kewarsu su duka
Ya qarasa ya durqusa yana gaeda ta
Mamama ta amsa tana tambayarsa kwana 2n
Yayinda sanah har yanzun tana jikin mamaman
Ya kalleta ta gefen idanu a zuciyarsa yana fadin
" Se son jiki kamar mage "
Mamama ta maeda dubanta wajen Sanah sannan ta dubi Arman tace
" Meya faru ne Arman ? Meyasa sanah ke kuka haka ?
Wani yaqe yayi kafin ya sosa kansa yana fadin
" Uhmm ! Mamama ae kinfi kowa sanin halin diyarki, bata ganki ba ? Ae shiyasa ta fara shagwa6ar ta ta " ya qarasa fada yana satar kallanta
Sekwa ta watsa masa idanunta tana murguda baki gami da kautar da kanta gefe
Besan sanda ya saki wani murmushi ba
Mamama ta ta6a kunnen sanah tana fadin lokaci 1
" Ya aekin kunnen ? Babu wata Matsaala dae koh ?
" Ehh mamama na warke " inji sanah
" Toh Allah y qara mana lafiya ! barkanku da dawowa ! Ku tashi kuje cikin gida ku gaeda jama'ar gidan , Sa6ani ma kukayi da souban dan kuwa jiya ya tafi Cyprus bayan jinyar satittika da yasha fama da ita "
Sanah ta miqe daga kwancen da take dan kuwa ita tama manta da wani souban a rayuwarta, tun abinda yayi mata ta shafe babinsa daga rayuwarta, ta shige daki
Arman yace
" Subhanallahi Allah y sawwaqe, Meya sameshi ?
Mamama tace
" wlh ciwo yayi sosae....Nan mamama ta fada masa abinda ya faru har souban ya fasa auren sanah, ta qare masa da rashin lafiyar da yayi bayan sanin tayi aure harya kasa jurewa seda yabar qasar tukunna danya samu kadaeci bayan binceken da har yanzu ake akan gano mutanen da suka dauke shi din "
" Toh pah " arman ya furta yana jijjiga kae sannan ya dora da
" Allah y tsare gaba ya tona asirinsu "
" Ameen " mamama ta fada
Yayinda arman ya fada duniyar tunani
" Lallae wannan abu abin mamaki ne ! Gashi a dalilin sace souban din da akayi shiya samu farin cikin zuciyarsa , abinda ya fitar da rae akae kenan ,Allah ne ya taemakeshi da tuni yanzu sanah matar waninsa ce ? Lallae ya godewa Allah dan kuwa Allah na sonsa.
Ranar gidan farin ciki kamar gidan biki, kowa farin ciki yake da dawowar tasu, Haka kowannensu yaje ya gaeda mutan gidan gaba dayansu .
Anan ne suke samun labarin bikin Afrah da Yah Imam Wanda saura sati 1 ayishi, sunyi mamaki qwarae ta yadda babu wanda ya fada musu, bayan suna waya da junansu amma a cikin en 3n nata babu wadda ta fada mata.
........A parlour ta samu umma tana jona turaren wuta ta qarasa ta gaeshe ta sannan tace
" Umma amrah fah ?
Umma na murmushi tace
" Tana ciki, karatu take"
Ta qarasa dakin amrahn ta sameta tana karatun kamar yanda umman ta fada
Amrah ta ajjiye littafin tana kallan sanah
" ahh amaryar yah arman barka da zuwa, wallahi nayi missing naki sosae "
Wani irin haushi taji ya kamata ta yadda seda ta gallawa amrahn harara sannan ta fara qoqarin tashi ta fice
" Ahhh sorry mana babyn baby is dis ohk ? amrah ta fada tana dariya
Dawowa tayi ta zauna tana fadin
" Ke dallah ba'a abin arziqi dake sekin 6atawa mu2m rae "
Kallan sanah kawae amrah take tana mamakin ta, ita da take son arman din amma bata samu ba, ita gashi ta samu a 6agas shine zata dinga wulaqanci tana wani shan qamshi ?any way dae itama yanzun ta daawo daga rakiyar sa dan ba cikakken mutunci ya cika ba yanzun se ya dizga ka ( 😱😂 babyn guda )
Kauda tunanin tayi gefe lokacin da sanah tace
" Zuwa nayi inyi muku rashin mutunci, wae saura sati 1 bikin afrah shine ko labari babu ? Da bamu dawo ba da shikenan seda muji ance anyi bikin ?
Amrah tayi dariya
" pls maeda wuqar mrs Arman, wlh mamama ce tace kar a fada muku saboda tasan halinki cewa zakiyi sekin taho ko baki warke ba, shiyasa ma ban fada miki ba "
Turo baki sanah tayi tace
" Uhmm mamama , nifa Allah tun ranar da akayi min aekin na warke.
......Mamama ta shiga dakin nata wanda sanah ke ciki
Ta qarasa ta zauna
Ganinta yasa sanah din miqewa zaune daga kwanciyar da take
Mamama ta kalleta sosae, ta gane har yanzu akwae sauran rina a kaba, dan haka dole tayi wani abun
" Sanah ki tashi ki shirya dare nayi, nasan yanzu zezo Ku tafi "
Turo baki sanah tayi tace
" Ni dae mamama bazan bishi ba fah "
" Meyasa ? Wani abun ne ya faru ?
" Ni ba komae " ta sake fada still tana turo baki
Mamama tace
" Zo nan ! Zoki fadamin kinji ?
Seta qarasa cinyar mamaman ta dora kanta sannan tace
" Mamama wata ce fa yake so acan qasar "
Wani qayataccen murmushi mamama ta saki seda tadau sakanni sannan tace
" Ahhh ehh gskia wannan hujja ce kam, yi kwanciyarki zamu hadu da ja'irin " Mamama ta fada tana qudurcewa yadda zata gyara diyarta ta kafin ta koma gidanta
Aekam ta sake bararrajewa akan gadon, tana sane taqi shiga dakinta saboda ma karya ganta.
**Wajen qarfe 9:30pm ya shigo parlourn
Mamama ce kadae a zaune a parlourn ya qarasa ya zauna
Da mamaki mamama ta kalleshi tace
" Har yanzu baka tafi ba ?
Sosa kae yayi kafin yace
" A'ah mamama daga can nake, zuwa nayi mu tafi "
Murmushi mamama tayi tana girgiza kae kafin tace tana kallansa yana sinne kae wae shi a lallae dole kunya yakeji
" Toh ae zefi kyau ka tashi ka tafi, dan kuwa ma bacci take "
Dan shiru yayi kafin ya miqe yana fadin
" Bari naje na tashe ta !
" Iyeeeee ! Mamama ta fada tana riqe ha6a
" Toh kaje yau ka raba dare kana waya da budurwartaka, yau kam babu me takura maka "
Seya koma ya zauna
" Ae shikam shikenan ya shiga uku tunda har zancen nan yaje wajen mamama seta wajigashi yasan kafin zata bashi matarshi " ( Ahh su mata manya 😹 )
" Wlh mamama ba abinda take nufi bane, duk bata fahimci.....
" Allah ya tashemu lafiya " mamama ta katseshi da fadin hakan
Be qara cewa komae ba ya miqe a sukwane yana fadin
" Seda safe "
" Mu kwan lafiya " inji mamama
Seda ya fita sannan ta bishi da kallo tana murmushi .
Kwanakin da suka biyo baya sune na gyaran jiki da aka farawa sanah, wanda aka hadata da amarya afrah ake musu tare, kafin kace meye wannan, tuni sanah ta fito tayi dass da ita ta qara haske fatarta har wani qyalli takeyi, gashi tayi wani acan acan da ita kamar wadda aka sanya a inji .
Ana saura kwana 1 daurin aure me lalle tazo tayi musu me shegen kyau, amarya da muqarrabanta sun fito Cass dasu .
Ranar daurin aure da daddare za'ayi dinner, wadda daga nan za'a wuce kae amarya,
Dan haka qarfe 5 na ranar daurin auren masu Kwalliya suka fara aekinsu
Suna dakin da akewa amarya Kwalliya su 3n
Amrah akewa kwalliya dan se an gama mata za'a yiwa amarya
Ana gama mata kuwa aka yiwa amarya afrah ta fito a amaryar sak kuwa tayi matuqar kyau
Wayarta dake ajje tayi ringing
Amrah dake kusa da wayar tace
" Kae yah imam !
Afrah ta galla mata harara tana fadin
" Dillah can ni bani inji muryar mijina "
Sanah dase a lokacin da kalleta tace
" Ahh lallae afrah ! Ni wlh bansan sanda kika lalace haka ba "
Dae_dae lokacin data daga wayar ta amsawa sanah da
" Ranar da aka daura min aure mana "
" Lallae madam aure " sanah da amrah suka hada baki wajen fadin hakan.
Ita dae sanah tace ba zatae Kwalliya ba zataje a yadda take
Seda qyar ta yadda ayi mata light makeup bayan su afrahn sun saka baki, sannan suka fita daga dakin dan zasu fara yin gaba ne kafin sanah din
Kwalliya er kadan ta mata mara hayaniya
Sanda akazo saka Jan baki win sakuwa yayi saboda taushin bakin, haka me kwalliyar ta haqura ta saka mata lipgloss kawae
Se ta fito kamar wata er tsana, tayi kyau sosae abinta, sukayi sallama da me kwalliyar sannan itama ta fito daga dakin dan tafiya wajen dinner
Dae_dae lokacin da take qoqarin wuce motar taji an janyeta ciki
Cikin matuqar razana ta bude baki zatayi qara
Se taji tattausan hannunsa wanda ya wadatu da qamshin turarensa dako a mafarki taji shi zata gane wanene
" Shhhhh !!! Ni ne ! Ya fada cikin wani irin salo kuma a hankali cikin kunnenta
Seta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta fara kiciniyar qwacewa daga jikinsa
Shi kuwa ya sake riqeta yana shaqar qamshin dake tashi daga jikinta me matuqar sanyi
Tayi masa masifar kyau, ga fatarta data sake wani laushi kamar ta jariri
A hankali yace
" Ina kike shirin zuwa a haka ?
Ta turo baki tana kauda kanta gefe tace
" Dinner mana "
" Ohh dama haka ake ? Mata ta tafi unguwa ba tare da mijinta ya Sani ba ? Ya fada yana dage mata girarsa 1
Se ta sake tura bakin kamar yarinya er goye
Bakin yabi da kallo yana nazartarsa kamar wani maye
A very cute lips, dan qarami dashi gashi daga gani zeyi taushi and se wani sheqi yake
" Ae ka sani "
Yaji ta fada, Se yaji kamar ana fuzgarsa ne ya sake maeda dubansa kan dan qaramin bakin nata
Babu zato babu tsammani kawae ta tsinci bakinsa akan nata,
Cikin firgici gigicewa da tsoro gaba daya ga6o6in jikinta suka fara rawa, tayi azamar qoqarin tureshi amma ina Arman fa yayi nisa..............
Mhiz Innocent ce.............✍️
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent 😻
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
Page 39_40
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻
( Baby WhatsApp group link ) 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e
............Bata haqura ba dae ta cigaba da tureshi din, sedae kamar ma besan tana yi ba
Seda ya gaji dan kansa sannan ya saketa yana shafa kwantacciyar sumar kansa fuskarsa dauke da wani qayataccen murmushi
Aekuwa kamar jira take seta saki kuka kamar wadda aka duka, ta fara yinsa hadda sheshsheqa
Da sauri ya riqo hannayenta yana fadin
" Am sorry, ki dena kukan kinji ?
Kamar bada ita yake ba dan kuwa cigaba tayi da kukanta tanayi tana qarawa
Wani iri yakeji a zuciyarsa wannan kukan da takeyi, hakan yasa a hankali ya janyota ya rungume yana sake lallashinta
Qoqarin tureshi take amma dukda haka bata dena kukan ba
Seda tayi me isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya akae_akae still dae be saketa ba
Se can kuma cikin shaqaqqiyar murya tace
" Ni ka sakeni zan tafi "
" Ina ? Ya fada kamar besan Inda zataje ba
Shiru tayi kafin taga dae shirun ba abinda ze mata yasa tace
" Dinner mn "
Seya kwantar da murya yace
" Yanzu kina nufin a haka zaki tafi dinner ? Kinci wannan kwalliyar ga jikinki ko ina tashin qamshi yake ? Fisabilillahi kinmun adalci kenan idan kika fita ? Ko wani qato ya kallemin ke ?
Seta juyar da kanta gefe ba tare da tace komae ba,shi kuma ya cigaba da fadin
" Toh kafin ma ayi haka, bari kiga ni in gyara zamana inyi ta kallanki ya fiye miki fitar da zakiyi "
Seta juyo ta kalleshi idanunta sunyi rau_rau alamar koda yaushe zata iya yin kuka
Be gama kallannata ba kuwa ta fara aekin nata na kuka
Ya yamutsa sumar kansa yana sauke ajiyar zuciya sannan cikin taushashshiyar murya yace
" Baby meyasa kike so ki dinga wahalar dani haka ? Meyasa ba zaki tausayamin ba ? Wannan wahalar da kike bani ta isa haka, tun ina daurewa har na kaasa daurewa yanzun, plsss ki tausayawa zuciyatah mana "
A hankali ta fara rage sautin kukan nata se taji tana buqatar sauraron abinda zece mata din
Ya cigaba da fadin cikin wani salo wanda bata Zata babyn nata bane
" Baby I luv u I luv u and I will always do "
Shirun dae tayi har yanzu kanta na qasa
Haka suka cigaba da zama cikin motar yana kallanta kamar wata T.V, ita kuma idan ta tuna yadda ya hanata zuwa bikin nan da nan se qwalla ta taru a idanunta .
...Wajen qarfe 12pm yana kwance akan tanqameman gadon nasu, tun dazu yake kwance amma ya kaasa baccin,baccin yaqi daukarsa se juyi yake daga wannan kusurwar se waccan kusurwar
Tashi yayi ya zauna akan gadon ya kunna light din dakin yana dafe kansa, sannan ya dauki gorar ruwan sanyin dake ajje akan side drawer yasha yana ajiyeta
Dole ne ma yasan abinda zeyi zuwa gobe, dole ya dauko matarsa yabar kwana haka nan kamar wani tuzuru,da wannan shawarar ya sake kashe light din ya kwanta amma fah bacci babu bayaninsa .
............Washe_gari qarfe 8 na safe a gidan na Arab tayi masa
Seda yakae motarsa bakin qofar part dinsu sannan ya ajjeta ya fito
Yana fitowa wayarsa nayin qara, kamar baze duba ba kuma seya tsaya ya dakkota daga aljihunsa, Daddy ne
Hakan yasa ya daga cikin girmamawa yana karawa a kunnensa bakinsa dauke da sallama
Daddy ya amsa cike da kulawa yana dorawa da fadin
" Arman ! Ina son ganinka yau idan baka da uzuri "
Cikin tunanin abinda yasa daddyn keson ganinsa yace
" Tohm daddy, yanzu ma na shigo gidan bari na qaraso "
Da " Ohk " daddy ya amsa yana katse wayar
Shi kuma ya chanja akalar tafiyar tasa zuwa 6angaren baffah da yasan indae ana biki acan duk mazan gidan suke zama
Da sallama ya shiga parlourn baffahn
Daddy ne kawae a cikin dakin yana kallan tashar France 24
Ya amsa masa sallamar yana daukar remote ya saka t.vn a mute
Arman ta qarasa ya zauna a qasan carpet yana fadin
" Barka da safiya daddy "
" Barka dae Arman, ya aeki ?
" Alhamdulillah mun godewa Allah daddy "
" Toh madallah " daddy ya fada kafin yayi shiru sannan can kuma ya dora da fadin
" Arman ! Wato Dr Stephen yazo min da wata magana akan kaeda diyarsa cewar kuna soyayya kuma yana nema mata aurenka, ya abin yake ?
Cikin sakanni fuskarsa ta koma a dinke tsaff kamar hadari haka zalika fushin kan fuskarsa be hana bayyanuwa a cikin muryarsa ba
" Daddy ! Ya fada a kaurare sannan ya dora da fadin
" Ni ba sonta nake ba daddy, tace tana sona, ni kuma saboda alaqar dake tsakaninka da Dr Stephen ya saka bance bana sonta ba, amma daddy na nuna mata duk wasu alamomi da zasu saka ta gane bana sonta amma ta kaasa fahimta, but daddy bazan ta6a iya aurenta ba "
Shiru daddy yayi yana nazarin maganar arman din
" Qwarae arman yayi dae_dae daya kare wannan alaqar dake tsakanimsa da Dr Stephen amma shima besan yadda za'ae su hada zuri'a da kafira ba, but In Sha Allah Allah ze kawo musu mafita "
" Kayi qoqari Arman, ka tashi kaje Allah ze kawo mafita In Sha Allah "
A hankali ya sauke ajiyar zuciya danso yake kafin yabar wajen nan 6acin ransa ya ragu, ya tashi yana fadin
" Allah ya yadda daddy, nagode "
" Amm baka ji ba " daddy ya fada
Seya koma ya zauna
Daddy yace
" Zaka shiga hospital ne yau ?
Seya sosa kansa yace a hankali
" A'ah daddy gskia babu tsarin haka yau a wajena "
" Ohk toh pls taemaka ka shiga hospital din ka duba idan akwae wata matsalar seka gyara, in kuma babu shikenan kawae "
Da " Toh " ya amsa yana miqewa ya fice ya dauki motarsa ya wuce asibitin.
Shida ya shiga tun 9 saura bashi ya sami kansa ba se dab da magrib sannan yaje yayi sallah kae tsaye ya sake wucewa gidan nasu.
.......A hankali yake takawa part din mamaman bayan ya sake ajjye motarsa a bakin wofar part din yana addu'a a bakinsa ya qarasa shiga ciki
Babu kowa a cikin parlourn, seya fara wuwwulaga idanunsa koze hango 1 daga cikinsu
Dae_dae lokacin da take qoqarin sakkowa daga stairs sanye cikin doguwar riga me taushi da hula wadda ta zameta rabin sumar kanta ta bayyana, seya sami kansa da qare mata kallo tun daga qafarta har zuwa kanta, ya wani lumshe ido yana budewa still akanta
Dae_dae lokacin ta dago kanta sanda take dabb da qarasa sakkowa inda qwayar idanunsa suka shige cikin na juna
A hankali ta qarasa sakkowa shi kuma ya gyara tsaewarsa yana kallanta
" Ina mamama ?
" Yanzu ta shiga part dinsu amrah " ta fada tana kauda kanta danta gujewa wannan mayataccen kallan da yake mata
Wani qayataccen murmushin gefen baki ya saki sannan yace
" Ohk toh jeki dakko hijab dinki ki wuce mu tafi "
Dakatawa tayi daga niyyar tafiya da tayi ta tsaya tana kallansa
Ya dage mata girarsa yace
" Yeah ! Tunda sunqi bani matata in sunga na daukeki ae dole su shafawa kansu salama koh ?
Seta juya ba tare da tace komae ba ta fara qoqarin komawa saman
Cikin azama ya bita yana shan gabanta yace
" Allah kuwa kikace zaki min taurin kae zan tsaya ne in daukeki " ya fada yana fara tattare hannun rigarsa
Seta zaro ido ganin da gaske yake ta fara qoqarin bin gefensa ta wuce
Gaba dayanta