Showing 12001 words to 15000 words out of 65672 words
Chapter 5 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt
yah imam xaune yana sipping juice
Har tana shirin juyawa taga ya dago ya kalleta
seta baasar ta faasa komawa ta qarasa taja kujera ta xauna
Y kalleta fuskarsa d murmushi yce
" malama sanah hala dae wani abun kike nema ko buqata "
Murmushi tayi kapin ta gaesheshi snn ta dora d fadin
" ehh yah souban nake nema "
Seda yaji wani duuumm amma seya waske yace
" souban km ? Me xe miki ?
Tace
" laptop dinsa xan kar6a "
Seda y saki wata ajjiyar xuciya kapin yace
" Ohh..ohk amma shine ni baki tambayeni b ko dole seta souban din ?
D sauri ta girgixa kae alamun " a'ah "
Yce ohk toh inna baki tawa banyi shishshigi b ?
" Kae yah imam shishshigi kuma ? Ta fada tana kallansa
" Ehh mana "y fada cikin maraeraecewa
Dariya ya bata dan haka ta dara tana fadin
"A'ah nikam kwae k dakkomin "
Da " toh " y amsa mata yana miqewa yce
" ohk pls wait 4 me .
Ita kuma ta cigaba d xama ta fada duniyar tunani kala kala
Ba taji tahowarsa b se inuwar mutum kwae d taji a kanta
Cikin sauri ta miqe tana ja d baya
" Wae Khalid meye haka ne ?
Dariya ta bashi yce
" Haba beb karki nuna min cewa ke ba er hannu bace mana ! kina xatan ban ganki lokacin d kuke dawowa daga club cikin dare b ranar ?
Cikin rashin fahimta take kallansa ta kaasa gane inda xancen nasa y dosa kwata kwata
Kapin ta bashi amsa imam y taho
Ganinsa y sanyashi tafiya yana kashe mata idanu da yiwa iska kiss
" xamu hadu ne beb "
" Waye wannan ne sanah ? Imam y tambaya
" Dan gidan aunty ne pah " ta bashi amsar b tare dt kalleshi b
" Ohhh y fada yana miqamata laptop din "
Ta kar6a tana godia ta juya xata tafi yce
" Amm baki ji b "
Juyowa tayi b tare d tace komae b
Yce
" akwae wata muhimmiyar magana d nakeso muyi dke in babu damuwa "
Haka nan kwae taji qirjinta na bugawa tce
" tohm Allah y kaemu gobe "
Ameen y fada fuskarsa na yalwatuwa d fara'a..........
Mhiz Innocent ce.............✍️
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent 😻
Page 10__11
~08105359153~
Number dina d take always welcoming naka a DM 😍 but pls message me amfani couz number nan an tanade ta ne especially sbd ku 🌚😻
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 😍
Kamar yadda ta tsammata kua washe gari kalmomin so sune suka fito daga bakin yah imam
ta rasa yanda xatayi masa dan ita kam Ynx xuciyarta tayi nisa akan son yah souban .
Haka dae suka rabu b tare da ta bashi qwaqwqwarar amsa b .
Tana komawa daki kiran yah souban na shigowa wayarta
Seda ta nemi waje ta xauna kapin ta daga wayar
Daga 1 6angaren yace
" dear wae me yake hadaku d imam ne ?
Dariya y bata dan haka tace
" Soyayya mana "
A xabure y miqe sedae y gaxa furta komae
Dariyar tayi sosae dan jin yaqi cewa komae
" Kaaga yah souban k kwantar d hankalinka wlh b abinda ke tsakani na dashi se en uwantaka na yaya d qanwarsa "
Wata doguwar ajiyar xuciya yaja kapin a hankali taji yana furta
" alhmdlh alhmdlh "
Kiran mamama ne y shigo wayar ta ta dan haka tayi taking excuse ta daga kiran
Miqewa tayi ta fita dan mamaman kiranta take
yana xaune a parlour kan dinning d alama wani abun yke jira
Bata kulashi b tayi wucewarta
Binta yayi d kallo yana mamakin wae yau baby ce ta ganshi amma ta nuna kamar bata sanshi ba
Kae tsaye ta shige dakin mamaman ta tadda ta tana ninke kaya
Tashi tae tana shirin kar6a
Mamama t katseta ta hangar fadin
" kinga yayanki na parlourn qasa jeki hada masa fruit salad "
Kamar xatayi kuka tace " toh "
Ta sakko qasan kae tsaye kitchen din ta wuce tana turo baki
Tunda take bata ta6a jin haushin aekin d baby y sakata b se yau
indae xata masa abu a cikin farin ciki take yinsa sa6anin yau komae take yi da sauri take tana bubbuga kayan d qarfi
Seda ta gama yanka duk wani fruit ta juyesu cikin bowl kapin t saka qanqara a ciki ta dauki madara d sugar ta wuce dining din
Yana nan dae yadda ta bashshi shi be tashi b shi be chanja gurin xama b
ajjiyewa kwae tayi
Har xata tafi ta jiyo muryarsa a qasan maqoshi kamar baya son maganar
" Spoon "
Ji tayi kamar ta nuna bata ji b tae wucewarta
se kuma taga rashin dacewar hakan dan haka ta koma kitchen din ta daawo ta ajjiye ta koma dakinta tana harare harare d murguda baki ( nikam nace a banxa wae harara a duhu 😂 )
****Ranta a mugun 6ace tace
" kinga afrah babu wata magana d xaki fadamin na yadda
yah na shigo na tarar d amrah na kuka kuma n tambayi dalili kuce min b komae ?
Ohhhh ohkkk na fahimci wanne irin zama muke daku insha Allah ba wadda xan sake tambaya " ta fada tana juyawa xata fice
D sauri amrah tasha gabanta
" sorry pls sis ki daawo ki xauna xan miki bayani "
Seda taja lokaci kapin ta daawo ta xauna din
Afrah tace
" sister Wlh amrah ce ta fada soyayya "
Fuska ta hade
" kamar yaya ta fada soyayya ? toh dan tana soyayya kuma kwae seta fara kuka "
" A'ah pls qasa louder mana kar umma taji !
Wanda ta fada qaunartasa ae baya sonta koma ince miki be masan tanayi b
koda yake just take it as yasan tanayi din but be ta6a nuna y sani din b "
" Wae waye ne ? inji sanah
Ta6e baki afrah tayi
" waye kuwa in b yah arman b !!!
" Baby ?
" Ahh akwae wani yah arman dinne bayan shi ?
" Noh b haka nake nupi b abinne y dauremin kae
yanxu shi baby meye aebun amrah hadda ta xubda ajinta ta fada masa tana sonsa amma be kar6a b ?
Afrah tace
" ae kwantar d hankalin ki ni Wlh cewa nake ma ta haqura tunda dae bata ta6a fada masa ido d ido b
ae kinga ko abun be tabbata b b xata dinga jin kunyarsa b kamar yadda xataji inda ta fada masa "
" Haka ne ! inji sanah
amma gabadaya hankalin ta y karkata kan baby
wato danshi bashi d ra'ayin soyayya se yake ganin kowa ma baxeyi b ? Yanxu kuma gashi yazo yana wahalar d xuciyar er uwatta
" gskia baby baka kyauta b " ta fada a fili
Afrah tace
" amma sanah me xe hana ke ki masa magana d kanki nasan wlh xe saurareki "
Ta6e baki tayi tace
" ke yanxu pah baama magana dashi "
Cikin rashin fahimta afrah tace
" ke kamar yaya ban fahimce ki b ?
Sanah ta Dage kafada
" yanda dae kunnuwanki sukaji haka dinne "
Duk d haka bata yadda b tana dariyar raenin hankali tace
" ke kinga bari na miki gwari gwari baby pah nake nupi "
" Ehh shi din dae " sanah ta fada tana maeda dubanta kan amrah
Ita dae amrah batace musu komae b kwae sauraronsu take yi .
**********Fitowarsu kenan daga b.u.k sun gama registration
sedae a wannan karan course dinsu y bambamta kowacce d wanda xata yi.
Yah imam ne y kawo su abin mamaki har ynxn yana nan be tafi b
ita mamaki ma yake bata duk aekin daya ke dashi seyae ta jiransu
Ba 6ata lokaci suka shige motar kamar ko d yaushe itace a gaban motar yaja motar suka fara tafiya.
Tafiyar kurame suka so su fara kapin y faara jansu d hira
Jefi jefi Sanah kan sako baki idan xancen y shafe ta
Harga Allah kunyarsa take ji d wanne ido xata kalleshi bayan tarin hallaccinsa a gareta tace akwae wanda take so ?
Sam bata san yanda xatayi b.
Daedae sanda suka shiga gidan motar souban itama ta shigo gidan
Suna fitowa shima y fito hannunsa riqe d suit sannan ga alamar gajiya a tattare dashi
Seda suka gaesa d imam duk suka wuce part dinsu kapin y qara so gun sanah
" Kyakykyawa tah wae me yake hadaku ne d imam ?
Dagowa tae ta kalleshi
" kae yah souban school pah kwae y kaemu mukayi registration "
" Ohhh har naji xuciya ta tana farr fari " y fada yana dariya
Itama dariyar tayi kapin tace
" Yah souban ynx pah duk ka gaji don Allah kaje k huta mayi waya anjima "
Da toh y amsa mata yana dorawa d fadin
" Nipah na gaji d cemin yah souban dinnan d kike
ke kice min souban su amrah sucemin souban su daddy ma suce min souban su....
Be qarasa b ta katseshi tana dariya
" kae yah souban wannan lissafi haka "
" Ehh toh ae dole nidae don Allah a samu a chanja min wannan sunan " y fada yana tsareta d ido
Jinjina kae kwae tayi tana fadin " ohk bye "
Binta yae d kallo har ta shige part dinsu shi km y juya xuwa part din mazan gidan.
A parlour y taddashi xaune yana karatun qur'an cikin Suratu Yusuf amma qarshe
be dade d shiga b y idar d karatun
Zubewa souban yyi kan kujera yana fadin
" man soyayya akwae dadi ! Ina fada maka especially in ka samu me sanka abin ba'a magana "
Bece masa komae b y tashi y barshi a wajen dan b shakka inya cigaba d xama komae xe iya faruwa.
Binsa souban yyi d kallo yana ta6e baki
" a haka xaka qare cikin takaeci indae b xaka cire wannan girman kan ka faara soyayya b "
Satikan d suka biyo baya suka qarasa abubuwan d xasuyi a makaranta har suka faara xuwa cikin ikon Allah d yaddarsa.
Kowacce ta faara shiga class dinta har sun kusa cinye wata 1.
*****Shigar ta ajin kenan ta xauna tana kallan wadda suke yawan xama a kusa " fateema bashir "
tana fata iri iri na katta ji jiya anyi attendance dan bata shigo school din b
Seda suka gaesa kapin tace
" fateema don Allah jiya anyi attendance ?
" Eyyah ehh wlh wani sabon malami ne y faara shigowa pah ze riqewa doctor Khalil kinsan yayi tafiya " inji fateeman
" Yah salaam ! Ta fada tana dafe kanta
Fateema tace
" kuma wlh jiyan naso yi miki amma babu dama sbd malamin akwae tsare gida "
" Eyyah b komae fateema nagode sosae .
" Arab ! Arab !! Taji fateeman na fada bayan ta fada dogon tunani
ta dago tana kallanta
Fateeeman tace
" kinga malamin d nake fada mk gashi nan shine xe shigo ynx "
Kallan inda take nuna mata tayi amma bata hango shi b hakanne ysnya ta fadin
" bari in y shigo sena je na same shi ko xe gyaramin in yaji banda lpia "
" Toh Allah yasa " inji fateema
" Amma pah guy din y hadu wlh ni sena ga kamar yau ma yafi kyau koh ?
Ta jiyo wata daga bayanta tana fada
Se taji fateema bashir ta amshe d fadin
" bari kwae wlh guy din y hadu gashi d gani baya daukar raeni "
Wani dogon tsaki taja gabadaya se taji sun bata haushi
yah a matsayinsu na mata xasu xauna suna yabon wani namiji ?
wannan wane irin xubda mutunci ne
Bata ida tunanin ta b taji ajin y dauki shiru haka ne y alamta mata cewa malamin y shigo
A hankali ta dago daga kwanciyar d tayi ta maeda hankalinta gaba
Runtse idanunta tayi tana so ta tabbatar mafarki take ko kua gaske ne
" Baby !! Ta furta akan la66anta
Be dauki 5mins b y fara lecture cikin qwarewa d iyawa
kae b xaka ce ba malami bane kwae riqewa yayi na wucin gadi
Bayanin yake yi amma b fahimtarsa take b kwae kallansa take ta kaasa gasgatawa
toh meya kawo baby nan ?
Bata samu damar amsar tambayarta b taji wata tambayar d yayi ta xuwa ga en ajin gaba daya
cikin turanci yce
" duk wanda beyi attendance din jiya b inason ganin shi anan "
Ae bata san sanda ta faara kallan en ajin b
Sedae ga mamakinta babu wanda y tashi
kenan suna nupin dukkansu sun samu attendance din ita kadae ce bata samu b ?
" don't allow me 2 repeat it again " taji y fada
B shiri ta miqe tana takawa a hankali kamar me tsoron qasa
sedae ae taji gaba daya a tsarge take dan ko ba'a fada b tasan idon en ajin dukka a kanta yke
Da sassarfa ta qarasa wajen nasa
Se a lokacin ya dago ya kalleta tayi matuqar kyau cikin shigar abaya kamar yanda ta saba
yanda yaga ta masa kyau har yake san kallanta shakka babu suma en ajin kallanta suke
gabadaya wani takaeci y kamashi lokaci guda fuskarsa ta chanja yanayi
" yah sunanki " ya tambaya yana dauke kae
Muryarta har rawa yake tace
" Sanah Alqaseem Arab "
Bece komae b illah rubutu d yayi a wata er takadda y miqa mata
" U should submit it 2morrow "
Kar6a tayi tana sake kallansa
Sedae shi kuma be sake kallanta b ya dauki abubuwan daya shigo dashi y fice .
A hankali ta dinga takowa kamar me tafiya a iska ta koma wajenta ta xauna
takaeci haushi baqinciki kamar su kashe ta
wae shin baby me yake damunsa ne ? Anya ba'a musanta mata shi b ?
Wajen qarfe 3 ta daawo gida ranta gabadaya a cunkushe yake
tana shiga kua tayi sa'a mamama na xaune kan kujera tana kallo ta qarasa ta fada kan cinyarta tana sakin kuka
" Subhanallahi yah salaam ! Sanah me ya faru haka kike kuka tashi maza ki fadamin " mamama ta fada hankalinta a tashe ganin er lelenta ta na kuka
Seda tayi me isarta dan kanta sannan tace
" mamama kaena ke ciwo kamar xe cire "
Wata doguwar ajjiyar xuciya mamama taja tana hamdala a ranta sannan tayi murmushi
" sanah sanah yanxu ke kam ciwon kae kike wa kuka "
" Mamama sosae pah yke min ciwon "
" Toh ynx dae jeki wanka kiyi sallah kici abinci seki sha magani
daddynku baya nan amma nasan imam ko arman wani daga cikin su yana nan "
Da toh ta amsa tana miqewa ta shige dakin
ita kadae tasan meke damunta
Mamama ta bita d kallo tana girgiza kae.
Seda taci abinci tae wanka sannan ta fito d takardar assignment din d aka bata saboda yau tana fashin sallah.
Zama tayi a parlourn qasa ta cire hearing aid din saboda indae xatae karatu cireshi take dan bata son hayaniya
kana ta faara research akan assignment din
Tayi tayi tayi iya qoqarinta amma ta kaasa ma gaane inda assignment din y dosa
Kamar ta fasa ihu haka taji
Kamar wadda aka rada mata abu tayi zumbur ta miqe ta maqala hearing aid din ta dauki takadda d littafin ta fice
Seda ta dudduba car park amma bata ga motar yah imam b hakan na nupin baya nan kenan ?
Bata ida tunanin nata b motar daddy ta shigo gidan
Jiransa tayi seda y fito sannan ta qarasa tana murmushi ta kar6i brief case din hannunsa tana masa sannu d xuwa
Cikin fara'a daddy yce
" a'ah yana ganki a nan kuma ina xakije ?
Murmushin itama tayi tana cewa
" daddy yah imam nake nema xe koya min wani aeki "
" Eyyah ae kuwa ynxn muka gama waya dashi yau evening duty gareshi then in ya tashi daga nan hospital dinku ze wuce "
" Yah salaam " ta fada qasa qasa kapin a fili tace
" tohm "
Daddy yce
" toh ae dayan likitan yana nan koh ?
D sauri tace
" ehh daddy xanje y koya min "
A haka suka qarasa shiga part dinnasu suka haye sama
daddy y shige dakinsa dan yin wanka
Ita kuma ta wuce dakin mamama ta xauna kamar me tunanin wani abun
" A'ah sanah har ynx ciwon kan ne ? Mamama ta tambaya
" A'ah mamama y dena pah kuma naje neman yah imam baya nan da na kar6i maganin "
Mamama ta kalleta sosae kapin tace
" ohk toh maza kira yayanki yazo y baki magani kisha gaki nan gabadaya kin chanja lokaci guda "
Sanah ta 6ata rae
" mamama ni pah b wannan bane "
" Toh menene ? Inji mamama
" Toh b baby ne bah xe riqewa wani malaminmu class shine wae dan jiya ban samu attendance b y bani assignment kuma ni ban iya b " ta fada tana turo baki kamar me shirin yin kuka
Murmushi mamama tayi tace
" toh ae yasan me yayi tunda y baki aeki ae shi ze koya miki kamar yanda y saba "
Kallanta kwae sanah take bata ce komae b
Mamama tace
" ae seki je y koya miki tunda imam din baya nan "
Da toh ta amsa tana ficewa daga dakin
Mamama ta bita d kallan mamaki
Yau dan sanah xatayi wani abun a wajen arman seta tambaya ?
Ita yanda ta kula ma a kwana 2n nan kamar abubuwan d dama sun chanja
sedae amma bata fatan wata matsala ce babba kapin azo lokacin d take jira yazo din .
Da tunane tunane kala kala ta fito daga dakin mamaman ta wuce part dinsu arman
Seda tayi knocking se taga qofar ma a bude take
hakan yasa kwae ta tsaya tana saesaeta nutsuwarta kapin daga bisani kwae ta shiga dakin bakin ta dauke d sallama............
Mhiz Innocent ce......✍️
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent 😻
Page 12
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 😍
Shi kadae ne a dakin yana kallan wani indian film ya amsa mata sallamar amma be dago b
Yau b daban abu take nema a wajensa b babu abinda zesa ta kulashi
dan yanda ta kula wani baqin hali y tsuro dashi kwanakinnan.
Cikin rashin qwarin jiki ta qarasa ta xauna a qasa
seda ta dauki second ni sannan a hankali ta furta
" baby aeki na kawo ka koya min "
Yau karan farko taji dama tana d damar