Header Ads
Showing 63001 words to 65672 words out of 65672 words

Chapter 22 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

569

Ads at the middle of Article

sanah din take tana kamota sannan itama cikin kidima tace


" Yah salaam, haehuwar ce " tana gama fada ta fice daga dakin


Se gasu sun dawo ita da Umma da Maman souban, kafin su qarasa shigewa dakin nata sega aunty ma ta shigo, su suka taemakawa Sanah din aka sakata a mota dan bama ta cikin hayyacinta se nishi kawae take saki, mamama na riqe da diyarta ta cike da tausayawa halin da take ciki har suka isa asibiti.




.....Dukkansu suna harabar asibitin wasu a zaune, wasu a tsatstsaye kowa da addu'ar da yake karantowa,


Bayan shudewar wasu awanni, wata er farar midwife ta fito dauke da baby a hannunta, gaba 1 suka nufeta da sauri,


da murmushi kan fuskarta ta qaraso wajen nasu sannan ta miqa musu babyn dake lullu6e cikin farin haddaen towel tace


" Congratulations, ta haehu lafiya, an samu da namiji "


Dae_dae lokacin da Arman ya qaraso, ya tsinci maganar da take, besan sanda wani qayataccen murmushi ya qwace masa a kyakykyawar fuskarsa ba, sannan ya qarasa ya saka hannu ya kar6i babyn, ya bude towel din da aka rufe shi dashi, kyakykyawar fuskarsa jajawur da ita ta bayyana, lallae wannan babyn shine kyau da kansa, Dan kuwa shi ba'a sama ya dakko kyaun ba, kyau ne daya gajeshi a wajen uwa da uba


" Wow, Masha Allah, Alhamdulillah " ya fada yana bawa babyn light kiss a kumatu, sannan ya masa huduba yana miqawa mamama shi, ta kar6a cikin wani irin farin ciki daya kaasa 6oyuwa a fuskarta, ta kalleshi sannan a hankali taji wasu hawaye na sakko mata ba, ta saka hannu ta goge tana fadin


" Alhamdulillah "




Arman ya kalli midwife din yace


" Ina matata ? Ya fada yama manta mamama na wajen


Midwife din tace


" Cikin ikon Allah ta haehu lafiya amma tasha wahala dan har jijjiga taso ta farayi, se Allah ya taemake ta, amma yanzu tana dakin hutu "


" Ya salaam " suka hada baki wajen fadar hakan, Arman yayi gaba, yayinda duk suka bishi da kallo


A hankali ya tura qofar dakin ya shiga shi 1, abinda yasa be nemi suje da kowa ba dan yasan hakan ya sa6awa tsarin asibitin, shima dan likita ne shiyasa ya shiga,


Kamar yadda ya tsammata tana kwance tana bacci, ya qarasa yaja kujerar dake ajje a gefen gadon ya zauna sannan cike da qauna kulawa ya kamo hannunta ya sanya a cikin nashi yae kissing din hannun, Sannan ya miqe ya bata kiss a goshinta kana ya koma ya zauna yana fadin


" Sannu kinji baby, Uban masu gida ya bawa wannan mummyntasa wahala, Allah ya miki albarka ya baki lafiya "




.........Seda tayi kwana 3 sannan aka sallameta daga asibitin, kae tsaye gidan na Arab aka wuce da ita kuma part din mamama, Wata irin kulawa take samu daga wajen mamaman uwa Uba kuma daga wajen abin qaunarta Arman, ga sauran en gida ma da suke bata wata shahararriyar kulawa.


Ana saura kwana 1 suna, en Maiduguri suka iso da tawagarsu, wata kulawar ta sake qaruwa a wajen sanah da babynta, dan kam har yanzu bata san menene raeno ba, indae ba abinci yaron ya nema ba, toh yana wajen wata daga cikin en gidan, yanzu ma hakan ce ta kasance,


Tana zaune a dakinta kan gado waya take da Arman yana tambayarta lafiyarta dana babynsu tace


" Muna nan lafiya baban baby "


Dae_dae lokacin wata yarinya Ameerah da sukazo daga Maiduguri ta shigo da babyn a hannunta, ta qarasa ta miqa mata shi tace


" Aunty umma ce tace a kawo miki shi, wae yunwa yake ji "


Kae kawae ta daga mata tana kar6ar babyn


Arman da yaji abinda yarinyar tace yace


" Maza a bawa babynmu abinci "


Seta turo baki kamar yana wajen tace


" Fisabilillahi ayi mutum kullum cikin cin abinci yake "


Dariya Arman yayi yana fadin


" Toh ko se nazo ne an sake yin irinta ranar farko ?


Seta murguda baki kamin tace


" Zan ajje way..... "


Bata qarasa ba babyn ya tsandara kuka yana wuwwulga hannu


Arman yayi dariya


" Awwnn, kingani koh ? Baya so ki ajjewa daddynsa waya "


Turo baki ta sakeyi sannan ta kalli babyn nasu daketa wawurar rigarta.


_____Ranar suna ta zagayo, babyn yaci suna Alqaseem ( sunan daddy ) sedae za'a dinga kiransa da junior, Daddy yayi matuqar farin cikin jin takwarasa ne dan haka akwati daban daddyn ya hadawa takwarannasa alqaseem jr ,


Sanda suka dawo gida da asuba Arman na shirin shigewa baffah ya janyoshi yace


" Malam aena dauka yusuf za'a saka ! Shine aka wani saka sunan wancan tsohon, ga suja me jini a jika ?


Murmushi Arman yayi sannan ya shafa sumar kansa yana fadin


" Ahh ae babu damuwa baffah, In sha Allah Brigadier general yusuf na nan zuwa wata shekarar " ya fada yana dariya gami da wucewa


Baffah ma yayi dariya yana kae masa duka.


....Me jego tayi ado kala kala, anci ansha, sannan anyi rabon memo, sticker hadda cotton bag me dauke da sunan jaririn 6alo_6alo wato ALQASEEM ARMAN ALQASEEM ( Junior ), haka mamama ma tayi shigarta me kyaun gaske a matsayinta na uwar taro, shi kam Arman yau throughout bega matartasa da junior ba dan kuwa bema shigo gidan ba kwata kwata saboda baqin dake cikin gidan.


Bayan suna, haka Arman ya cigaba da kasancewa a 6angaren mamaman kullum sedae idan baya nan, amma indae yana nan indae yazo toh baze fita ba sedae idan zeyi sallah ko dare yayi sannan yake komawa part din mazan gidan, dama ya dade da dakko kayansa ya dawo dasu gidan dan baze iya zama yana can wata unguwa sanyin idaniyarsa na wata unguwar ba, gwara ya zauna inda duk sanda yake son ganinsu ze gansu.


....Yana zaune a dakin riqe da junior a hannunsa wanda yakewa wasa, shi kuma yana ta 6a66aka dariya, yayinda ita kuma tana toilet, mintuna wajen 10 ta fito, yana ganin ta fito ya ajjiye junior yana fadin


" Kwanta kayi wasa, dad ze taemakawa mom " ya fada yana qarasawa wajen sanah dake qoqarin saka riga, seya fara taemaka mata da zuge zip bayan ta saka din yana fadin


" Kinsan aeki na ne meye na wahalar da kanki ?


Daya gama zuge zip din, seya dora kansa a kafadarta yana qoqarin magana mamama ta shigo dakin, se tayi turus kafin ta faara sallallami tana tafe hannu


" Zo ka fita " ta fada tana nuna masa hanya


Se yaji duk kunya ta kamashi, yayi qasa dakae sannan sum_sum ya fice daga dakin, be sake cewa komae ba,


Mamama ta juyo ta kalli sanah dake wasa da gefen hannun rigarta tace


" Ke kuma kin kyauta kinji, toh karku damu dukkanku na kusa tarkataku Ku barmun gida haka nan "


Ita dae sanah ba tace komae ba, dan kuwa Arman ya gama muzantata a wajen mamaman.


____Seda sanah tayi kwanaki 42 a gida sannan mamama da kanta ta dauketa ta maedata gidanta bayan tasha gyara na musamman, shi kam Arman Allah ma ya gani haqurinsa ya qaare dan haka yau daga asibiti kae tsaye gida ya wuce part din mamama


Da sallama ya shiga dakin mamama na zaune akan kujera tana karatun qur'ani, Seda takae qarshen ayar da take karantawa sannan ta dago ta amsa sallamar tana kallansa yanda yake wani sum_sum da kae kamar munafiki, ya nemi waje ya zauna bayan sun gaesa seya shafa sajensa amma ya kaasa cewa komae, Dan haka mamama ta tari numfashinsa da fadin


" Matarka ? Na kaemaka ita gida dazun nan, dan haka ba seka 6ata yawun bakinka ba tashi ka tafi "


Besan sanda ya saki wani murmushi ba sannan ya miqe yana fadin


" Angode, Angode mamama, Allah ya qara girma "


" Ameen_ Ameen " ta fada tana binsa da kallo lokacin da yake fita daga dakin, mamama ta saki murmushi tana girgiza kae sannan ta janyo qur'anin ta cigaba da karantunta.




Cikin matuqar farin_ciki yake driving sanda ze koma gidan nasa, a haka harya qarasa.


___Tana tsaye bakin mudubi bayan ta fito daga wanka tana mulke hannayenta da wata humrah da aunty ilham ta bata ya shigo dakin, Seda ya tsaya ya qare mata kallo yadda yaga ta qara wani fadi tayi kyau abinta, se kuma a hankali ya taaka zuwa Indi take din ya rungumota ta baya, bata san da shigowarsa ba dan haka tana shirin saka qara, kyakykyawa kuma sassanyan turarensa ya bugi qofofin hancinta, seta lumshe ido tana shaqar qamshin


" Nayi kewarki sosae matata "


" Nima haka mijina " ta bashi amsa wadda ta fito tun daga qasan zuciyarta


Seya juyo da ita yana kallanta kamin ya lumshe ido yace


" Kinga yadda kike ta qara kyau kuwa baby ?


Seta saki murmushi tace


" Kaema haka ae "


Tare suka qarasa bakin gadon, ya qarasa yana kallan junior dake ta bacci hannunsa 1 a cikin bakinsa


" Ae dole kayi bacci tunda ka gama zuqemin mata " ya fada yana murmushi gami da lakuce kumatun junior


Itama murmushin tayi, tana tayashi daukar junior din suka maedashi kan gadonsa dake ajje gefen nasu gadon.


Seya janyota jikinsa yana shaqar sassanyan qamshin dake tashi daga ko'ina na jikinta yace


" Kinsan kuwa yadda nayi kewarki ?


Bata iya bashi amsa ba dan kuwa yana kae qarshen zancen nasa ya hade bakinsu waje 1, sannan ya fara aeka mata da wasu zafafan saqonni dake nuna yadda akayi kewar wanda ake aekawa da saqon, itama kuma ta zage tana maeda masa martani dan ba shakka tayi kewarsa sosae kuwa, Haka suka sha soyayyarsu ba kama hannun yaro.




_5years later_


Abubuwa da dama sun faru a cikin wadan nan shekarun, ciki kuwa hadda haehuwar afrah da amrah wadanda duk suka haefi 'ya'ya maza, dan gidan Afrah yaci sunan baban yah imam, dan gidan amrah kuma abban souban. Sannan Khalid ma ya fito, kuma yayi nadama sosae dan kuwa bayan fitowarsa seda yaje qàfa qafa wajen duk wadanda yayiwa kaefi nemam afuwarsu kuma Alhamdulillah duk sun yafe masa din.




_______Wani cute baby boy na hango an saukeshi daga bus din wata makaranta, Haka kawae naji inaso insan wanene wannan yaron dan kuwa kyaunsa kadae abin dubawa ne, gate din wani gida ya nufa ya tura a hankali sannan ya qarasa cikin gidan har zuwa parlourn gidan, Cikin muryarsa me zaqi yace


" Babyyyyyyyyyy " ya fada yana jan qarshen sunan sannan ya yadda jakar daya shigo da ita gefe


Arman da yaji shigowarsa ya qaraso cikin parlourn yanawa yaron kallan irin baka jin magana, seya tsuguna a gaban yaron yace


" Wae bana hanaka cewa babyn nan ba ? Ka kirani dad sannan ka kirata mom uhmm ?


Seya daga kae yana turo baki yace


" Toh amma kaema haka zaka dinga fada koh ?


Arman ya juya kansa yana sauke ajiyar zuciya yace


" Yeap, In Sha Allah "


" Yawwah dad " ya fada yana tsalle


" Mum " ya fada yana qarasawa wajen Sanah da fitowarta kenan daga daki ya rungumeta, tayi wani irin kyau da ita tayi fresh alamar kwanciyar hankali ta zauna mata,


Itama rungumeshin tayi tana fadin


" Oyoyo junior "


" Mum, yunwa nakeji fah " ya fada yana shafa cikinsa


" Ohk, jeka dad dinka ya taemaka maka ka shirya se kazo kaci abincin uhmmm ?


" Nidae pls daku zanci abincin " ya fada yana turo baki


" Ohk,Ohk ba matsala "


" Yeah ! Ya fada yana tsalle sannan ya wuce dakin, kafin yakae ga shiga dakin ya juyo yace


" Dad, ina jiranka "


Arman da tun dazu yake kallansu yace


" Ohk " se kuma ya maeda dubansa ga sanah yace yana riqo ta


" Wato junior duk wani surutu da shagwa6arki ya dakko, kin kula da hakan ?


Seta turo baki tace


" Ni din ? Allah kuwa ban yadda ba, surutu naka ya dakko, ae naga kaene ka koyamin surutun "


" Nima ban yadda ba, amma dae nasan junior kama ta ya dakko sakk "


" Kaaga kaje ka shiryashi karya fito ya gammu a haka


Seya saketa yana fadin


" Ohkkkk " ya shige cikin dakin junior din,


Shiya taemaka masa yayi wanka sannan ya shirya cikin riga da wando jeans, yana shiryashi yana ta zuba masa surutu da hirar abinda ya faru a makaranta, tun yana amsa masa har seda ya gaji yace


" Junior "


" Yes baby " inji junior


"Oh my goodness " arman ya fada yana dafe kae


Seya kama baki yana fadin


" Aou dad, sorry plss " ya fada yana kama kunnensa


" Ahnn, dats my boy, oyah gimme five "


Seya miqa hannunsa suka tafa sannan arman yaja hannunsa suka wuce masallaci, seda sukayi sallahr maghrib da isha'i sannan suka dawo.


Kae tsaye dinning suka wuce suka zauna, seda sukayi wajen mintuna 10 sannan sanah ta fito ta nemi waje ta zauna


Junior ya kalleta jin batace komae ba yace


" Mom, mun dawo "


" Sannunku da zuwa, Abban junior kun dawo lafiya "


" Lafiya qalau " ya fada yana karantar yanayinta kafin ya Dora da fadin


" Are u okay ?


Seta yamute fuska


" Wlh zazza6i ne kesan rufeni "


Junior da yaji abinda tace yace


" Sorry mom, dad ya dubaki ya baki magani " ya fada kamar zeyi kuka


" Ehh zansha maganin, but yanzu dae kaci abincinka uhmm ? Ta fada tana murmushi


Seya gyada kae yana janyo plate din da Arman ya zuba masa abinci a ciki


Haka dae suka ci abincin suka gama sannan junior ya miqe


" Dad, mom, bacci "


" Ohk ayi addu'a sosae " inji arman


" Ohk dad " ya fada yana wucewa wajen arman din, ya bashi kiss a goshi sannan sanah taja hannun junior din suka wuce dakinsa


Ita ta taemaka masa ya kwanta sannan tayi masa addu'a sosae kana taja masa blanket, tana shirin tashi yace


" Mum, gim me a kiss "


" Ohhh, kaaga harna manta " ta fada tana murmushi gami da bashi light kiss a goshinta ta miqe tana fadin


" Asuba ta gari "




Kae tsaye bedroom ta wuce dan tasan can ya nufa shima, yana zaune kan gadon da alama ita yake jiraz kafin ta kae ga zama ya janyota yana rungumeta kana yace


" Zo ki fadamin, kodae mun sami qani ko qanwar junior ?


Seta turo baki tana fadin


" A'ah nifah babu wani nan, kawae dae normal rashin lafiya ce "


" Nidae ban yadda ba, inada tabbacin junior ya kusa zama yaya, mu kuma mun kusa zama iyaye a karo na 2 "


Shiru tayi dan kuwa ta yadda hakanne, dan duk wasu alamomi data dingaji a lokacin cikin junior su takeji yanzun, bata qarasa tunanin ba ya katse ta da fadin


" Gaskiya keta musamman ce a rayuwata baby, ina matuqar qaunarki, Allah ya qara mana zaman lafiya da zuri'a ta gari "


Seta saki murmushi tana amsawa da


" Ameen mijina "




___Haka rayuwarsu ta cigaba da kasancewa cikin farinciki, kwanciyar hankali da qaunar junansu, kullum ji suke kamar ana sabunta musu soyayyar junansu, kowanne ji yake yaci dan uwansa qaunar 1, A haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya.


GAME OVER !!!🔥🔥


ALHAMDULILLAH !
ALHAMDULILLAH !!
ALHAMDULILLAH !!!


Anan na kawo qarshen wannan littafin nawa me suna A ZURI'AR ARAB (BABY) Allah na gode maka daka bani wannan dama na fara littafin nan lafiya na gamashi lafiya, abinda na fada dae_dae Allah ya hadamu a ladan, abinda nayi kuskure Allah ka yafemin.


Ina matuqar godiya a gareku masoyana masoyan wannan littafi musamman masu min comment, Allah ya barmu tare ya qara mana haquri da junammu, I heart u all 🥹🥰




Tambayoyi


*ME YAFI BURGEKI A CIKIN LITTAFIN NAN ?*


*WAYE STAR DINKI A CIKIN LITTAFIN ?*




*WANE WAJE NE YAFI BURGEKI A CIKIN LITTAFIN ?*


*MEYE SAQONKI ZUWA GA MARUBUCIYAR ?*




*****Godia ta musamman a gareku aminaena....


Fateema Bashir
Ummulkhaer Yusuf
Maemuna Abubakar
Kudin na dabanne a rayuwata 🥰


Ina miqo gaesuwa a gareki Hajaratyy 🥰


Gaesuwa me yawa a gareku Husnatyy and Faridah 🥰


Ina qaunarku sosae 😍


Gaesuwa ta daban a gareki Yaya tah Sa'adatu Yusuf 🥰 ina qaunarki sosae


Godia a gareku sisters of myn...


Fateema Aliyu and Ruqayyah Umar 🥰 base na fada ba kunsan kudin na daban ne a wajena


Gaesuwa a gareku en uwana...


Abdoul
Mubarak
Faruq
Khausar


Allah ya qara mana qaunar junammu 🥰


Gaesuwa da godia ta musamman ga en Team dina na 💖THE TALENT TROUPE WRITERS💖


Mum sayyid
Aunty sadiya
Aunty Zarah
Aunty Aisha
Aunty meemah
Aunty azeemah


Allah ya barmu tare ya qara mana basira da hazaka Ameen 💗




And daga qarshe nake miqa gaesuwa zuwa ga Mamana da Abbana 🥹😍 Allah ya qara muku lafiya da nisan kwana 💖


Semun hadu a next book dina In Allah ya yadda 🥺😍




Subhanakallahumma, wa bi hamdika, ash hadu anla ila ha illa anta, astagfiruka wa atubu ilaeka...




Mhiz Innocent.........✍️

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads