Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 65672 words

Chapter 12 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt

Ads the beginning of article before Image

11 Jun 2024

560

Ads at the middle of Article

Sabah tayi wanda ya qara fito da ainihin kyawunta


Suna nan zaune afrah na sanya mata abin hannu yayin da amrah take daura mata sarqa , suma duk sunyi shiga me kyau a matsayin su na aminan amarya kuma en uwanta sunsha ado dan suma duk sunyi lalle d fulawar .




.......Kallan kayan ya sakeyi a karo na barkatai sannan yaja tsaki yana tunanin yadda ze saka wadan nan kayan , hadda wata babbar riga , toh ko shine angon ai se haka


Yasan yanzu haka souban ya shiga busy daze sameshi ne seya fada masa baze saka ba


Toh sedai tun dazun daya fita taho da abokansa har yanzu be shigo ba , shiyasa kawai ya yanke shawarar saka rigar kawai banda babbar riga


Seda ya taje kwantacciyar sumar kansa dake ta tashin qamshi sannan ya saka kayan , ya dakko hula zanna ya dora ta akansa


Turaren san nan dai na ko yaushe ya dakko ya saka , se kuwa dakin ya gauraye da qamshinsa me sanyi , sannan ya sake kallan kansa a mirrow , yayi matuqar kyau kyau me suna kyau , kai badan kar ace yabon yayi yawa ba da se nace " daga kyau aka nuna arman an tashi "


Kasancewar shi din ba ma'abocin saka manyan kaya bane se hakan yasa ya fito wani daban dashi yayi mugun kyau , sedai fuskarsa sam babu walwala dan a dinke take tsaff kamar wanda akama mutuwa


Madaidaicin agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa ya kalla qarfe 1:00pm ya nuna


Dai_dai lokacin da wayarsa tayi twuwwa , da Saudi ya daga yana Neman waje ya zauna


" Slm Alaik daddy "


Can 6angaren daddy y amsa kafin yace


" Kana ina ne yanzun ?


" Ina cikin gida " ya fada a ladabce


" Toh ka fito mu hadu a masallaci ana idar da sallah za'a daura auren " daddy ya fada


" Toh " kawai ya iya furtawa yana miqewa


Wayar tasa kawai ya dauka ya fice daga part din nasu


Yana shirin fita shi kuma imam na shirin shiga


Seya dakata suka gaisa kafin imam yace


" Pls ka jira ni mana yanzu zan fito nayi mantuwa ne "


" Ohk " arman ya fada yana yin gaba ya wuce parking lot


Mintuna 3 sega imam din ya fito , suka tafi a motar imam din shi yake driving yayinda arman ke zaune a wajen me zaman banza


Tunda suka fara tafiya ba wanda yace uffan


Se can imam ya katse shirun ta hanyar fadin


" Ashe ka dawo ?


Se yaji tambayar kamar rainin hankali amma se yace


" Yeap ! Jiya da dare "


Jinjina kai imam yayi yana cigaba da driving har suka isa masallacin na B.U.K .




Qarfe 2 dai_dai aka idar da sallah sannan aka fara shirye_shiryen daurin aure


A hankali y sulale daga cikin masallacin zuwa waje dan ya samarwa kansa peace of mind .


Har yanzu mamaki yaqi barin Abba na ganin har qarfe 2n souban bezo masallacin ba


Dan haka ya dauki wayarsa ya kira , sedai tana ta ringing ba'a daga ba


A'ah tunfa yana daukar abin a matsayin shiriritar souban har ya fara mamakin abinda ya hanashi zuwa har yanzu , dan kuwa biyu da Rabi ma ta kusa ( Allah yaso akwai wasu daurin auren se aka fara daurawa )


Toh abba na nan sega kiran souban din


Abba ya daga da sauri kuma yana fadin


" souban wane irin shashanci ne wannan da zesa har yanzu baka iso ba ?


Can 6angaren souban ya numfasa cikin sanyi yace


" Abba abinda yasa na kaasa zuwa wajen daurin auren nan , Abba bansan da wane irin ido zan kalleku na fada muku na faasa auren Sanah ba !


Abba ayi haquri a gafarceni amma bazan iya auren sanah ba bisa wasu dalilai na "


Suman tsaye Abba yayi kaana ya sauke wayar daga kunnensa ya duba , gashi nan dara_dara sunan souban ne akai amma danya qara tabbatarwa se yace


" Souban ?


" Na'am Abba ! A gafarceni don Allah "


Shikenan souban din ne kenan


" Ya salam " Abba ya furta yana Neman waje ya zauna cike da zullumi bayan katsewar wayar


Baba,daddy suka qaraso wajen suma sunsha bluen shadda duk iri 1 da babbar riga sun fito sakk iyayen amarya da ango


Baba yace


" Abban souban wai me yake faruwa ne ? Lafiya dai koh ?


Seda ya dawo daga shock din da maganar souban din ta jefa shi sannan ya fada musu abinda ya faru


Shiru duk sukayi kowa da abinda yake saqawa a ransa kafin daddy yayi qarfin halin fadin


" Kaaga baze yiwu a biye ta yaran nan ba ! Ai ba dole se yana nan za'a daura auren nan ba , kawai muje a daura in munje gida se asan yadda za'ayi "


" Me ? Inji Abba


" Ni souban ze maida qaramin mutum ? Toh wlh yayi was kansa tun farko shiya nemi auran sanah yanzu kuma yace baya so saboda haka an soke maganar nan !


Baba yace


" Ayi haquri dai a duba lamarin "


Abba ya dawo da dubansa wajen baba yace


" Wai baka gani ba saboda raini ni ya kira a waya ake fadawa ya faasa auren wai a bisa wasu dalilansa , dalilansa na banza , dalilan da basu tashi bayyana ba se ranar daurin aure ? Toh kuwa souban ze gaane wanene ni bama shi kadai ba wlh ! INA IMAM ???


saga haka suka dunguma zuwa wajen brigadier general Yusuf Arab da yake waje shima saboda wani daurin auren da ake gabatarwa a ciki


Sojoji a zagaye da baffan riqe da bindigu a hannunsu suka qarasa


Sosai Abba yayiwa baffa bayani sannan suka tattauna sosai dan kuwa seda suka kai wajen qarfe 3 kafin suka gama



Daurin auren da aka saka qarfe 2 se bashi se 3 za'a daurashi ,


Seda suka shiga wajen limamin daze daura auren shima sukayi magana sannan .


6angarensa kuwa tun yana haquri harya qosa haba ya gaji , qarfe 3 na shirin yi amma Abu yaqi ci yaqi cinyewa ? Se kace masu shirin aurar da duk en danginsu


So yake ya sulale yabar masallacin amma hakan baze yiwu ba tunda akwai idon daddy .


Qarfe 3 dai_dai dubban mutane suka shaida daurin auren SANAH ALQASEEM ARAB da ANGONTA akan sadaki naira dubu 100 .


****6angaren amarya kuwa yanzu haka tana cikin wani rantsatstsan less ne me kyau aji da tsada tayi matuqar kyau tamkar ka sace ta ka gudu


Dai_dai lokacin da agogon dakin ya harba qarfe 3:30 kuma a dai_dai sanda wata er uwassu daddy ta shigo dakin tana guda


" Aure ya dauru , sanah ta zama matar souban ?!


Se kuwa gidan dama dakin ya dauki shewa da guda anayi ana qarawa cikin farin ciki yayin da dubban en uwa aka fara sanya alkhaeri akan auran .




....Zagaye dakin kawai yakeyi dan kuwa tun dazu ya qagu ya dawo gidan


Mintuna 10 sega mama ta shigo dakin cikin wani dandasheshen less me arnen kyau


Da wani irin kallo Abba ya bita dashi


Cikin fara'a tace


" Ahh Abba Ashe kun dawo......"


Kafin ta qarasa ya katseta da fadin


" Ya isa haka ! Kinyi abinda kikeso akan danki , kinso ki wulaqantamu a idon jama'a ! Toh na barki da ikon da kika nuna akan danki , amma sedai ki sani nima zan nuna miki iko na akanki saboda haka ki jira sakamakonki da zarar an qare bikii ! Sannan ki dauki waya ki kirashi yazo taron da za'a gabatar yanzu haka a parlourn baffah "


Daga haka ya fice


Ita dai tunda ya fara magana kallansa kawai take Sam ta kasa fahimtar inda zancen nasa ya dosa , haka ta bishi da kallo kamar wata sokuwa harya fice .




..........Gaba 1 duk Wanda yake ko take a cikin zuria'ar Arab toh yana cikin parlourn baffan




Mutane da dama sunyi mamakin hada wannan taro haka bagatatan ana tsaka da taro


Abba ya kalli mutanan dake parlourn yanzu ma babu souban , girgiza kai yayi cike da fushi


Imam ne ya gabatar da addu'a kana duk aka shafa


Kapin baffah ya fara magana


" Toh dalilin daya saka aka shirya wannan taro cikin gaggawa haka shine akan wata 6araka data taso yau din nan a cikin zuri'ar na


Shiyasa a matsayinmu na manyanku sannan ga iyayenku nan zaune , a matsayinmu na wadanda zasu iya za6a muku abinda baze cuceku ba shiyasa muka magance abin tun a wajen "




Nan yayi musu taqaitaccen bayani akan abinda ya faru sedai yaiwa wasu abubuwan kwaskwarima gdun lalacewar zumunci sannan ya qaare da fadin


" Toh ahmadu ya kaawo maganar a bawa imam auranta sedai kuma bamu ta6a ji imam yayi zancen yana qaunar sanah na , toh ni kuwa na riga nasan soyayyar da arman yakewa sanah a dalilin hakan ne yasa na yanke wani hukunci !
!




Imam kallan baffa kawai yake , anya kuwa wannan tsohon be faara shan qwaya ba ? Ya tambayi kansa yana qara tattara duk nutsuwarsa zuwa wajen baffan dan jin cigaban bayaninnasa


" Saboda haka shi souban muna masa fatan samun wata yarinyar ko a cikin familyn nan ko kuma a waje amma yau kam an daura auran SANAH ko kuma nace an riga an bawa ARMAN auranta !!


Besan sanda y dago yana kallan baffa ba ido cikin ido


Wai meyasa mutanan gidan nan suke neman haukata shi ne ?


Don Allah a dena masa irin wannan wasan wlh baya so sam , Idan ba so suke su tarwatsa masa xuciya ba




Sake kallan duk en wajen yayi


" ehh tabbas iyayensa ne kuma yasan babu wasa tsakaninsu amma tabbas yau kam sunyi masa wasa wasan da idan basuyi sauri sun fada masa cewa wasa bane xiciyarsa na dab ta tarwatsewa....


Tabbas tasan kunnuwanta ne basu jiyo mata daidai ba


kawai ta saki wani murmushin gefen baki kapin ta maida hankalinta wajen manyan gidan dan jin wanda suka xa6a mata a matsayin miji tunda ga abinda souban yayi mata


Se kuwa tajiyo baba yana fadin


" Qwarai kuwa an daura auren ARMAN da SANAH !!




Ji tayi kunnuwanta suna barazanar dena ji gabadaya duk da hearing aid din dake kunnanta


Idanuwanta sun makance , qwaqwalwarta tana neman tarwatsewa , zuciya ta tsaya cak ta yadda ta dakata da aikinta na wucin gadi


ji tayi numfashinta na barazanar daukewa ta yadda seda taja wani irin numpashi kapin ta faara dawowa hayyacinta




Dama yaya ze iya auran qanwarsa ne ? Ko kuwa dama can ana iya yin hakan ?


Toh ae ko maguzawa banjin xasu aikata hakan ? Me yake faruwa ne ? Me yake shirin faruwa ? Suna cikin garin musulunci cikin musulmaei shine aka aikata wannan kwamacalar ? Ta yaya ? Ta yaya ma dan uwa ze auri wadda suke uwa 1 uba 1 ? Wae menene haka ne ?


In mafarki take zataso ta farka daga wannan mahaukacin mafarkin da bashi da kae ballantana qafa .






Tun daga zancennan bata sake fahimtar komae ba


tabbas tasan magana sukeyi amma ji take kamar wani yaren da bata fahimta sukeyi.


Shin wannan wace iriyar rayuwa ce da za'ayi haka ? Anya ba xata daga ido ta saka masa kwalli ta fada wa iyayennata hakan da suka aikata ba daedae bane ? hakan ya wuce maguzanci ?


Tabbas tasan duk cikinsu suna da ilimi amma ko ba'ace komae ba tasan yau sunyi fatali da wannan ilimin nasu akan wannan son xuciyartasu ,


Wani dumm taji kanta yayi a hankali ta faara ganin wani duhu na gitta wa ta saitinta se kuwa ta tafi luuuu cikim ficewar hayyaci ta fadi a wajen sumammiya ...........


Zuciya tah ke tayyo za6i so ya wuce wasa , zo mu zauna tare kizam abokiyar tarayyata πŸ˜ΉπŸ’ƒπŸ’ƒ


Toh ya update din yau ?Ina jiran comment naku 😻


Daga alqalamin mhiz Innocent........✍️






*β™‘β˜†A ZURI'AR ARABβ™‘β˜†* An amazing and heart touching story

By Mhiz Innocent 😻


πŸ’–THE TALENT TROUPE WRITER'SπŸ’–


Page 30


Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES πŸ˜πŸ‘Œ Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻


( Baby WhatsApp group link ) πŸ‘‡πŸ‘‡


https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e




..........Ba Sanah kadai maganar ta ta6a ba , kafatanin en dakin in ka cire manyan mazan gidan


Cikin mamaki kowa ke kallan baffahn dake magana


Mamama kuwa da wani irin sauri bugun zuciyarta ya qaru


Cikin wani irin yanayi dana gaza fahimtar farin ciki ne ko akasinsa ?


Wasu sanyayan hawaye ne suka zubo a kumatunta " ita kam me zata cewa Allah ? Babu abinda zatayi se godiya ga Allah buwaya gagara misali , dan kuwa shi kadai ke iya chanja abu a lokacin da yaga dama "


Hannu ta saka ta goge hawayen ,wani sassanyan murmushi na bayyana a fuskarta .




......Kansa gaba daya ya kulle , komai ya xakude masa , ya rigada ya gama tabbatarwa kansa wani yaudararran mafarki yake yi , mafarkin da yake neman yaudararsa , ya qagu ya farka kafin abin yayi nisa ta yadda inya farka baze iya jurewa ba


Kai zeso ace akwai wanda yake a kusa dashi ya bashi hot slap ko ze farka ! Sedai har yanzu shiru , yaqi farkawar sannan wani yaqi tashinsa


" Oh my god " ya fada yana dafe kansa kuma a dai_dai lokacin ne sanah ta zube a wajen a sume .






******8:40pm


Kuka take tamkar ranta ze fita dan tun dazun take so ya fito amma se yanzu ta samu wannan damar


Mamama kuwa shafa kanta kawai take ba tare da tace komae ba


Dan kanta ta gaji ta dago ta kalli mamama tana sheshsheqar kuka


" Mamama dama yaya ze iya auran qanwarsa ne wadda suke uwa 1 uba 1 ?


Mamama se tambayarku nake kunqi bani amsata bansani ba koni banda wannan ilimin ko ilimi na bezo wajen ba shiyasa bansani ba


amma nidae a islamiyyar da kuka sakani mamama yaya baya auran qanwarsa " ta qarasa maganar tana sake fashewa da kuka me cin rai


Janyo ta mamama tayi jikinta muryarta a sanyaye tace


" Kiyi shiru haka sanah kukan ya isa haka ko se kin sanyawa kanki ciwo ne ?


Bata iya cewa komae ba illah kukan dake fita a hankali


Mamama ta cigaba d fading


" Ki tashi kije kiyi wanka kiyi bacci anjima in Allah ya kaimu xamuyi maganar ohk ?


Da kanta mamaman ta hada mata ruwa me dumi tayi wanka bayan ta cire hearing aid dinta sannan ta zura doguwar riga Mara nauyi da hula ta kwanta


Mamama taja mata blanket tana cewa


" Bana son kuka kinji koh kiyi bacci cikin nutsuwa uhmm ?


Gyada mata kai tayi wasu kyawawan hawaye na xubo mata kan fuskarta


Tayi sauri ta goge su tana kwanciya duk da tasan qarya take bacci ya iya daukar ta a irin wannan lokacin .




Mamama ta koma wajen baqin ta da basu gama watsewa ba wadanda suke en uwa na kusa kenan .




....Tunda akayi taron nan Maman souban bata sake samun nutsuwa ba , gashi dai tana da baqi amma ta rasa wane tunani ma ya kamata tayi ? Abba da souban suna neman su haukata mata qwaqwalwa ! Ita kam ya zatayi ???




************** " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un "


Shine kawai abinda zuciyarta keda qwarin furtawa


kallan Mamama kawai take da take mata magana


" Mamama ba itace mahaifiyarta ba ? Mamama yaya ce a wajen mahaefiyarta ? How ? Can't believe cewa ba Mamama ce ta haefe ni ba


Duk wata kulawa daya kamata uwa ta bawa erta ta bata


Duk wata hidima d uwa zatawa erta Mamama ta mata


Duk wata soyayya da uwa xata nunawa erta Mamama ta nuna mata !


Daddy pah ? Yanzu daddy bashi ne mahaifi na ba ? Shin wannan wane irin 6oyayyen sirri ne da yake a cukurkude be warware ba se yanzu ?


Shin gaskiy ne abinda ke faruwa ko kuwa har yanzu bata farka daga shashashan mafarkin da take ba ?


" Nop ! dis is reality fah sanah ya kamata ki gaane cewa duk abinda ya faru yau gaskiyane ! Xuciyarta ta raya mata hakan


A hankali ta tashi ta qarasa kusa da Mamama ta kama hannunta


" Mamama kin dauke ni kamar erda kika haifa , kin bani duk wata kulawa data kamata uwa ta bawa erta


Mamama ban ta6a kuka a dalilinki ko daddy ba ku din har abada zaku cigaba da kasancewa a matsayin iyayena ne "


" Shttttttt !! Mamama ta fada tana dora yatsanta kan bakinta


" Bana son shashanci sanah ! wannan maganar ba dan zancen aure ya biyo ba baza'a ta6a tona ta ba har abada


kuma wato yanzu da kika gano gaskiyar lamarin shine zaki daukemu a matsayin iyaye ? Bama a iyayen ba ?


Sanah tace


" A'ah Mamama abinda nake nupi kenan "


Seda ta numfasa kadan kapin ta cigaba d fadin


" Mamama ku din na daban ne a rayuwata ina matuqar qaunarku " ta fada tana fadawa jikin mamaman tare d@ fashewa da kuka


Daddy dake tsaye tun dazun ya qaraso ya zauna gefen kujera yana murmushi yana kallansu


Seda tayi me isarta sannan ta taaso ta zauna gaban daddy ta kaamo hannunsa kana a hankali muryarta a shaqe saboda kukan da tayi tace


" Daddy a dukka rayuwata bani d kamarku nagode Allah ya saka da alkhae.... "


" Y@ isa haka mana sanah " daddy y katse ta


" Shin har yanzun baki ji me mamanki ta fada bane ? karki sake gode min kinji koh ? har yau har gobe ke 'ya ta ce kuma hakan baze ta6a chanjawa ba sedai Idan ke kika chanja ”


Da sauri ta girgiza kai wasu hawayen na sake xubo mata


Daddy yace


" Kiyi haquri Sanah nine na bawa baffah amanna akan wannan auren , ba dan haka ba da yanzu baki zubar da hawayenki ba !




" Don Allah daddy ka bari ! Daddy in kana bani haquri se naga kamar ka cireni a sahun 'ya'yanka ne ! Don Allah ka bari " ta fada cikin kuka


" Shikenan toh ya isa haka kinji koh bana so na sake ganinki kina kuka uhmm ?


Gyada kai tayi tana murmushi hade da share hawayenta .


Daddy ya miqe mamama ta rakashi da addua ya fita


Ita kuwa sanah komawa tayi kusa d mamama ta dora kanta kan cinyar mamaman tana sauke numfashi a hankali


Itama mamaman se yanzu ta samu damar zub da hawayen ta dan tuna er uwatta da tayi tana kuma sake godewa Allah akan wannan al'amari


a hankali itama take kukan tana me shafa kan sanah dake kwance shiru ta fada duniyar tunani


Cewa fah akayi an daura aure na da baby ? Ta yaya ma zata iya rayuwar aure

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads