Showing 42001 words to 45000 words out of 65672 words
Chapter 15 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt
gadon ya yaye bargon
Gumi sosae take d alama xaxxa6in y saukar mata
A hankali ya kae hannunsa ya faara janye hijab din dake jikinta
Da sauri ta riqe hijab din tana bude idanunta da sukayi rau rau
Hade rae yayi ya qaara kae hannunsa kan hijab din ita kuma tana sake riqewa
Be bi ta kanta ba ya cire hijab din y ajjiye shi gefe , sannan ya faara qoqarin tashi daga kan gadon
Ita kanta dama xafin take ji amma duk da haka seda taja blanket din ta sake lullu6e jikinta har kanta
Cikin kausashshiyar murya yace
" Malama in zaki yaye blanket din ki yaye karki kashe kanki "
Ta jishi sarae dan bata kaega cire hearing aid din ba amma se cewa tayi
" Kasan pah kurma ce se ka daga murya "
Yau kam seda yayi dariyar me isarsa bayan ya fita daga bedroom din
Wato dae har yanxu bata manta ba ? Ya fada yana girgixa kae
Kitchen yaje y hada tea ya sha sannan y koma bedroom din
Kae tsaye kan gadon ya nupa yaja pillow y faara qoqarin kwanciya
Sedae duk ta babbake gadon dan wata iriyar kwanciya tayi amma kuma ta nannade waje guda
Matsawa yayi kusa da ita a hankali gudun karta tashi ya fara qoqarin gyara mata kwanciyar , ita kuma tayi juyi sannan hannunta ya koma bayan kansa
Kawae seya rabu da ita dan kar ta farka yaja pillownsa wajen ya kwanta , yana sake janta jikinsa dan da alama baccin ya mata dadi
Ya kae idanunsa kan kyakykyawar fuskarta wadda in tana bacci ma qara kyau take
A hankali ya lumshe ido yana budewa a lokaci 1 ya kae hannunsa kan ta da hular ta zame , kyakykyawar sumar kanta me sul6i d santsi ta bayyana
Cikin rashin sanin abinyi yakae bakinsa goshinta dinta ya bata light kiss
Kamar a mafarki taji alamar motsin mutum a kusa da ita
Ba shiri ta bude ido
Sedae me ? Jinta tayi kane kane a jikin wani abu seda ta gama bude ido sannan ta fuskanci a jikin mutum take
Cikin sauri ta fara qoqarin tureshi danta tashi daga jikinsa , amma ya sake riqeta sannan cikin sanyayyiyar murya yace
" Shttttt ! kiyi baccin ki bana son musu , in kuma wani abin kike so u should let me know "
Bata sake cewa komae ba , amma ta cigaba da qoqarin tashi , sedae hakan ya gagara dan ya zagaye tane da hannayensa a cikin faffadan qirjinsa , dan haka kawae ta haqura tayi shiru tana jiran 6arawon ya sace ta.
Suna nan zaune a haka har ya faara ji tana sauke numfashi a hankali hakan ya alamta masa cewa bacci ya dauke ta
Ajiyar xuciya ya sauke sannan a hankali ya furta
" Baby rigima dae " yana murmushi ............
Godia a gareku masu min comment team fb and team whtsp π₯Ίπ₯° heart u all π
Yau kam page din naku ne ku kadae , banda masu la6e , kuma In Sha Allah yau xanyi mentioning sunayenku π₯Ίπ₯°
*_Team FB_*
Salma salisu
Ummin Abba
Imane mousa
Salma sulaiman
Fateemah Muhammad bukarr
Aminu usman
Uwar alkhaeri tawa ni kadae π₯Ίπ₯°
Call mhie hussy musa
Fatima Ahmad Muhammad
Ummi ihsan
Hannatu habibullah
Asabe ezakiel
Jamilu sani Abubakar
Sa'adatu Abdullahi
Princess husna autarh masoyiyatah π₯Ίπ₯°
Maryam mrym
Kareemat Ibrahim
Teema Abubakar
Ruqayyah Muhammad
Husna alameen
Zainab usman
Hawwa abdullahi
Maimuna isa Umar
Nawal abdulwahaf
Fatima Muhammad
Ummusawwama saeed
Aisha Sani sule
Khadija musa
*_Team whtsp_*
My lop abar qauna π₯Ίπ₯°kinsan kanki
Call mhie apple
Dr khulsum
Hindu
Hussy
Ummu ashraf
Walida bint sadeeq
Maryam Ahmad (Ummu affan)
Gilimah
Meerah0214
Maleekatue
Hafsat
Naja'atu Isma'il
Oum areef
Ameenam
Maryam
Asma'ou
Big bby
Bilkeesu Muhammad
Call mhie shalelen mijinta
Fateemah
Fatima
And a huge and special thanks goes to Aunty zuby and Amina caps and more π₯Ίπ₯°
Ina godia sosae d yadda kuke qaramim qarfin gwuiwa d addu'oinku gareni Allah y saka muku d alhaerinsa π€²π₯Ί
Wadanda banyi mentioning sunansu ba kuma suna min comment sumin afuwa next page In Sha Allah xakuga sunanku π₯Ί ragowar kuwa dama bakwa comment sedae ku karanta kwae Ku wuce ππ shiyasa ma baku ga sunayenku b dan wadannan sunayen masu comment ne π
Mhiz Innocent ce............βοΈ
*β‘βA ZURI'AR ARABβ‘β* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent π»
πTHE TALENT TROUPE WRITER'Sπ
Page 35
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES ππ Mhiz Innocent luv u owl ππ»
( Baby WhatsApp group link ) ππ
https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e
Not edited π«
.............Bata dauki kwanaki masu yawa b xaxxa6in y tafi sedae abinda ba'a rasa ba , kuma har ynx tana shan magani d kuma na shafawa a kunnenta dan se tayi 2weeks tana shan maganin sannan xa'a mata aekin.
*******Yau garin aka tashi dashi a lumshe ga iska me dadi da take kadawa
Ba dan yanxu baasa wani gud tym dashi b dah ba xata bari y fita y barta ita kadae a gidan b , musamman d taga alamar hadari y hado sosae .
Tana kitchen tana sarrafa musu abinda xasu ci da dare ne
Lokacin da hadarin y hado gadan gadan
Gudu gudu sauri sauri ta qarasa girkin sannan ta koma bedroom ta xauna can qarshen gadon dan lokacin ma har an fara tsawa alamar ruwa xe iya sauka kowanne lokaci gashi garin yayi duhu sosae .
Tana nan xaune tana addu'ar duk da taxo bakinta dan a matuqar tsorace take taji an turo qofar bedroom din
Cikin gudun da bata san tana dashi ba ta tashi a guje ta fada jikinsa tana qanqame shi sosae
Cikin rikicewa yace
" Wah happen ?
Ita dae ta riqe shi sosae tana Jan shashsheqar kuka
Y tsaya y kalli fuskarta yace
" Share hawayen ki fadamin me ya faru ? Y fada yana daga ta daga jikinsa
Kamar jira take dama ta faara kukan sosae kamar wadda aka yiwa wani abu
Janta yayi xuwa kan gadon ya xaunar d ita
" Relax relax mana baby fadamin meya faru ?
Cikin kukan dae tace
" Toh ba kaene k tafi k barni ba kuma pah tsoro nake ji "
" Oh my god ! Y fada yana dafa kansa
Ynx wannan dalilin ne kawae y sakaki kuka ? Y fada aransa a fili kuma yace
" Is ohk is ohk ynx ba gashi na daawo ba ? ya isa haka kinji koh ? Y fada yana goge mata hawayen
Ranar duk inda y saka qafa seta mayar ko toilet da zeyi wanka ma a qofar ta tsaya harya fito
Shi abinma har dariya yake bashi , duk da dae yasan dama gwana ce a fannin tsoro , shi kuma da gayya yake janyo wani abun dan tayi ta naniqe masa shi kuma yana biye mata .
Har dare ana ruwan kuma irin me qarfin nan
Tana biye dashi harya gama shirin baccinsa yazo ze kwanta , yana sane yau ya nemi kan kujera yae kwanciyarsa a binsa
Kamar ta rusa ihu haka taji aekuwa tayi xamanta a qasan kujerar daya kwanta din
Shi kuma ya mata shiru har wajen mintuna 15 yaga dae bata d alamar tashi , hakan y sanya shi miqewa y nupi kan gadon
Itama binsa tayi ta hau kan gadon
Ya ja blanket ya kwanta
Ganin hakan y sanya itama ta kwanta tana kallansa
" Madam kallan pah ? Ya fada yana dage mata gira
Kauda kanta tayi tana murguda baki
" Ni meye xan kalla a jikinka " ta fada qasa qasa
" Me kikace ?
" Ni bance komae b " tae maganar cikin basarwa
Hannu ya miqa mata
Ita kuma ta kauda kanta gefe
Se ya ture bargon y faara qoqarin tashi
" Baby !! Ta fada kamar xatayi kuka
Juyowa yayi yana kallanta ,dan rabon da ta fadi sunansa har ya manta se yau , sannan se kuma ya hade rae
" Bake kika nemi inxo in kwana akan gadon ba ?
Gyada kae tayi kamar xatayi kuka kana ta matsa kusa dashi a hankali
Shi kuma ya mata masauki a jikinsa yana kallan saman kanta
Sun shafe more than 10mins a haka kowa d abinda yke tunani kapin yace
" U better sleep otherwise xanyi tafiya ta in barki a dakin ke kadae "
Da sauri ta runtse ido tana fatan Allah yasa baccin y dauke ta
Aekuwa addu'arta ta ta kar6u dan kuwa bata dade b baccin y dauketa har shi kansa ma ogan .
Sati 2n ya cika ciff
Qarfe 6 dae dae tayi musu a asibitin dan qarfe 7 xaa mata aekin .
A tsorace take matuqa , ji take kamar mutuwa zatayi dan har seda tayi kuka shi kuma yana rarrashinta
A hankali ta daga idanunta da sukayi jajir ta kalleshi tace
" Baby ! Ka kiramun mamama da daddy in gansu "
Wata uwar harara ya jefa mata
" Wato so kike ki tayar musu da hankali koh ?
" Ni dae ni dae k kiramun su ! Ta fada kamar tana shirin sakin kuka
Seda y sake jefa mata hararar sannan y dauki wayarsa y kira mamama
Seda suka gaesa dashi sannan y miqa mata wayar
D farin ciki ta kar6i wayar cikin kewar mamaman suka gaesa kana ta dora d
" Mamama wae aekin pah xa"amin kuma ni Allah tsoro nake ji "
" A'ah sanah tsoron na menene ? In Sha Allah xa'ayi komae cikin sa'a da yardar Allah muna nan muna miki addu'a kinji koh " mamama ta fada cikin son kwantar mata d hankali
" Ehh mamama naji " ta fada cikin sakalcin data xame mata jiki
Shi ko kallanta kawae yake harta gama wayar dasu , kapin ta miqa masa wayar tasa
Kar6a yayi idansa cikin nata yace
" Wato ni b xaki fadamin abinda ke damunki b se mamama koh ?
" Toh ina ruwanka ? Ta fada akan la66anta
Ya bude baki zeyi magana wayarsa ta dauki qara
Ya dauka ma ko mamaman ce ta sake kira se yaga wata number , kasancewar be gane number da Catherine ta ta6a kiransa ba yasa besan ita bace
Ya daga wayar kana ya kara a kunnensa
" Hello lurv !
Ya jiyo muryarta ta and daedae lokacin da yaga sanah ta fara qaramin kuka tanayi tana matse idanu
A hankali ya janyo ta jikinsa yana dora hannayensa akan gadon bayanta yana shafawa a hankali sannan cikin sanyayyiyar murya yace
" Catherine !
" Yes lurv ! Har mun cinye 3weeks baka bani address din b , so koma wane aeki ne plsss zanzo na taya ka but kayi expecting dina a cikin week din nan "
Gyara xamansa yayi yana gyarawa sanah xamanta itama kafin yace
" Don't ever try dis , in na gama aekin ni da kaena xan fada mk "
" Plss lurv ! Nidae I have already decide it , zan ajje waya kayi expecting dina kawae couz ba zaka gane yanda nayi missing naka ba se nazo" ta fada tana ajje wayar daga 6angarenta amma bata katse kiran b
Shiru yayi yana nazarin maganganun ta bayan ya katse kiran
Komae mutuncin Stephen da yake gani anzo wajen daya kamata ya taaka wa diyarsa burki , ya yana so ya lalla6a abarsa tana neman hanyar da zatayi fatali da hakan ?
Amma fah Stephen ? Idan yayi hakan kuwa ya kyauta ?
6angaren sanah kuwa dukda taji yana waya , bata kaawo komae a ranta ba dan kuwa fargabar ma da take ciki kadae ta isheta .
Wae me yake faruwa a Nigeria tun bayan fitar souban daga gidan nan ?
"""""""""Abba da tunda ya fara magana yake kallansa yace
" Souban ka bude baki kayi mana bayani me kyau wanda zamu fahimta dan kuwa wannan kwane kwanen ba gaaneshi mukeyi ba " Abba ya fada dukda cikin zuciyarsa a karye take na ganin souban din wani iri haka
barrister souban saurayi me jini a jika amma yau duk se yake ganinsa wani iri kamar bashi ba
Souban ya gyara zama yana kallan wadanda ke xaune a dakin , kasancewar ranar juma'a ce yasan duk wani dan gidan yana cikin dakin
A hankali ya fara zagaye da idanunsa ba tare da yasan hakan ba yana Kallan mutanen dake zaune a dakin
Se dae me ? ya zaga idanunsa ko ina amma be hango ta b , Yayi mamakin yadda yaga babu Sanah a dakin !
Tana makaranta ne ? Ya tambayi kansa
A'ah tabbas yasan tun kafin bikin aka tafi strike ,
Toh ko an aeke ta ne ? Ya sake tambayar kansa ! Dukda yasan hakan ba dabi'ar gidan nasu bace
Wata amsa ce ta fito daga zuciyarsa wato " may be bata da lafiya ne " Wanda lokaci guda yayi na'am da hakan dae dae lokacin da ya sake fahimtar Arman ma baya dakin
Cikin sakannin da basu wuce 2 ba amsar tazo masa cewa " Ya koma Cyprus tunda dama biki ne kawae ya kawoshi.........
Kuyi manage da wannan pls yau qwuiwa nake ji wlh π«
Mhiz Innocent ce..............βοΈ
*β‘βA ZURI'AR ARABβ‘β* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent π»
πTHE TALENT TROUPE WRITER'Sπ
Page 36
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES ππ Mhiz Innocent luv u owl ππ»
( Baby WhatsApp group link ) ππ
https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e
............Souban ya gyara zama sannan a hankali ya fara fadin
" Abba lokacin dana fita da safe zanje in taho da abokaena da sukazo daga abuja , da yake safiya ce babu mutane sosae a titin , kawae wata mota tayi over taking dina sannan wadanda suke ciki suka fito da sauri zuwa cikin mota ta
Cikin sakannin da basu wuce 5 ba black ya shaqawa souban wani abu dake jikin handkerchief din dake hannun sa
Tun souban na qoqarin kaare kansa har yaji gaba daya jikinsa ya mutu , be sake sanin inda yake ba se farkawa yayi ya ganshi a cikin wani bedroom a kwance
A hankali ya tashi yana dafe kansa dake saara masa kamar ze cire yana tuno abinda ya faru
Wajen mintuna 5 sannan wani ya shigo ya kalleshi bece komae ba ya fita , se can suka dawo su 2 shi da wani qaton mutum baqi sidiq dashi babu alamar annuri a fuskarsa ( black kenan ) riqe da bindiga a hannunsa
Kallansu yake sosae yana so ya gane ko ya sansu ? Su waye su ? Me yake a dakin nan ? Shi da ya kamata ace yanzu haka yana can yana shirye shiryen tafiya daurin auren sa
Cikin karyewar murya yace
" Bawan Allah me nake anan ? Meyasa kuka kawo ni nan ? Me nayi muku ? Ko da yake be kamata in tambayi abinda na muku ba couz na san a cikin wadanda nayi case dasu ne ! So plss Ku bari yau ranar farin ciki ce a gareni ranar daurin aure na , Ku bari bayan daurin auren se mu dora daga inda aka tsaya , wannan ba lokacin wata maganar bane "
Dariya black ya sheqe da ita kana yace
" Toh mu kuma wannan lokacin ne kawae damu ! Kasan meyasa muka kawoka ka nan ?
Souban ya karkata kansa alamar yana ji
" So muke ka faasa auren matar da zaka aura yau din nan "
Dariya souban yayi kana yace
" Sorry wace mata kenan ?
" Sanah ! Black ya bashi amsa da sauri
" Impossible ! Wait a cikinku ma wae waye ne yake so in bar masa ita ?
Dayan dake kusa da black yace
" Ogammu ne , karka bari ya bayyana a wajen nan ba tare da ka amsa wannan buqatar ba "
" And so ? Souban ya fada yana kallansu su duka
" Kaaga barrister ! Rashin kunyar ka ta faara yawa fah , ka sani wani matsayin ka ba zeyi amfani a wajen nan ba , kawae kayi biyayya shine abinda ze ceceka in kuma ba haka ba zakayi nadama " black ya fada a kufule dae_dae lokacin da wancan ya fita daga dakin
Wajen minti 2 se gashi ya dawo riqe da wayar souban din a hannunsa dae_dae lokacin da Abba yake kiransa lokacin da suna masallaci
Black ya kar6i wayar ya miqawa souban yace
" Kar6i ka daga wayar ka fada musu cewar ka faasa auren !
" Baze yiwuwa ba ! Souban ya fada
A fusace black yayi kansa da kan bindigar ya kwada masa a gefen kansa ya qara fadin
" Kar6i ka fada musu Cewar ka faasa auren nan "
Souban ya sake girgiza kae yana riqe da gefen kansa
Dayan da suke tare da black ya kaewa souban naushi a hanci and lokaci guda yana kae masa a ciki
Haka suka hadu su duka suka dinga dukansa kamar wadanda aka aeko sannan black ya sake cewa
" Zaka fada yanzu ko kuwa sena fasa qwaqwalwarka ?
Shiru souban yayi yana nazari , yasan idan be fada din ba zasu iya kashehi a banza , toh kuma idan ya fada din yasan daga can 6angaren za'a fasa auren ne
Toh wannan ce kawae mafita in yaso idan ya koma seya fada musu abinda ya faru , yasan idan hakan ta faru toh za'a daura musu auren su a nutse
Daga nan kuma seya binciko wadannan shashashan yayi maganinsu
hakan ce ta sanyashi fadin
" Ehh "
Black ya danna number abban kira 1 ya daga
Nan ne inda souban yake fadawa abba ya faasa auren , toh abinda yasa souban yace ya faasa ne a bisa wasu dalilansa , yasan wannan kadae ya isa abinda zesa a jirashi aji menene dalilan nasa ????
Daga nan basu sake azabtar dashi ba , yana dae zaune a cikin dakin , zasu kawo mishi abinci da ruwa da sauran kayan buqata
Se kuma ranar da sukazo suka bude masa qofar ya fito daga gidan zuwa gida....
Shiru dakin ya dauka na wajen mintuna 10 babu wanda ya iya cewa komae , kowa da abinda yake saqawa a ransa
Cikin matuqar tausayi gami da mamaki kowannensu ke kallan souban din sanda yake baada wannan labarin
Abba dake zaune a qaramar kujerar parlourn yayi shiru hannayensa riqe da juna a ha6arsa
Be ta6a tunanin haka abin yake ba , be kawo ba haka zalika beyi zaton haka al'amarin ya kasance ba , meyasa yayi gaggawa ? Ya tambayi kansa
Baffah yayi gyaran murya cike da dattako shima muryarsa a hankali da alama labarin ya tsuma shi yace
" Souban !
Souban ya daga kae ya kalli baffah sannan ya maeda kan nasa qasa kafin baffah ya cigaba da fadin
" Wato duk abinda kaga ya faru da dan adam toh dama can rubutacce ne a cikin littafin qaddararsa , saboda haka ka riga da kaasan cewa daya daga cikin cikon imani hadda yadda da qaddara ta alkhaeri ce ko akasinta "
Duk souban yasan wannan hakan yasa ya gyada kae , amma se yaji kamar ba zancen kenan ba , dan yaji kamar maganar tayi ta kumayi alaqa da kuma