Showing 39001 words to 42000 words out of 65672 words
Chapter 14 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt
jinsa take b .
Yana nan xaune kan gadon har can cikin dare sannan y tashi y fito daga bedroom din
Can y hangeta tsakiyar parlourn d alama ma tayi bacci
D sauri y qarasa y yaye bargon daga fuskarta
Kyakykyawar farar fuskarta ta bayyana numfashinta na sauka a hankali tayi wani irin kyau na musamman
A hankali kuma akan la66ansa y furta
" Sleeping beauty " yana sakin wani qayataccen murmushi
Kapin y kae hannu d nupin daga ta gbdy se kuma y faasa
A hankali y fara buga pillown da take kae yana lura d kunnenta , abin mamaki ko hearing aid din bata cire b kenan tana nupin dashi xata kwana ?
A hankali ta fara bude idanun nata kapin ta bude su tarr akan fuskarsa , cikin Sauri ta miqe xaune
Ganin ta miqe y sanya shi fadin
" Tashi ki koma kan gado "
" Bana so " ta fada tana turo baki
Maaze wa ya kuma yi yce
" Ki koma kan gado nace koh ?
Kauda kanta itama ta kumayi tana fadin
" Nace bana so "
Miqewa yayi kapin y faara tattare hannun rigar jikinsa sannan y nupota gadan gadan
D sauri ta miqe tana yayimar blanket din tayi cikin bedroom din tana harare harare d murguda baki
Binta yayi d kallo har seda ta shige sannan y bita dakin
Tana tsaye harya shigo bata d niyyar kwanciya
Bece mata komae b y janyo wani blanket din y haye kan kujerar dake cikin dakin y lullu6a abinsa .
Seda ta tabbatar ya kwanta din sannan ta qarasa kan gadon ta kwanta tana sake karanto addu'oi .
Washe gari d safe kusan tare suka tashi , sedae shi ya fita massallacin dake dan nesa kadan d gidan d suka sauka .
Hakan ne y bata damar tashi tayi duk wani abu d xatayi , ta gyara gidan ma gaba daya ta shirya dae cikin hijab din sannan ta koma kan gadon , sedae ba bacci take b .
Se wajen 8 y shigo gidan kae tsaye kitchen y wuce dan yunwa yke ji
sedae me ? Babu abinda y gani alamar matar gidan bata tashi bane kome ?
Toh amma dae yaaga gidan a gyare Fes fes toh me hakan ke nupi ?
Kae tsaye y wuce bedroom din
Hango ta yayi a kwance mamaki y kamashi y qarasa cikin dakin
Idon ta 2 kwae dae ta kwanta ne
Tabbas taji shigowarsa amma bata dago b bare ma ta kalleshi
Ransa a 6ace yce
" Baki yi breakfast b ?
Kamar ba xata amsa b se kuma taga rashin dacewar hakan hakan yasa tce
" Bansan me zan dafa b "
Shafa kansa yayi dan harga Allah yunwa ykeji sosae
" Ki tashi kije ki sarrafa mana abinda xamu ci otherwise..."
Se kuma yyi shiru y fice daga dakin
Seda ta qara wajen 5mins bayan fitarsa sannan ta tashi ta fito ta wuce kitchen din
Tea ta fara hadawa sannan ta soya musu qwae ta ajje kan dinning , ta koma parlourn ta kunna kallo mbc Bollywood takae akayi sa'a ynxn suka shigo mujhse dosti karoge , tana son film din sosae hakan yasa ta xauna tana kalla
Can se gashi y shigo d leda a hannunsa y wuce d ita kitchen sannan y fito y wuce kan dinning din
Hankalinta gaba daya yana kan T.Vn sedae taji shigowarsa amma bata dago ta kalle shi b
" Oh yah taso kixo muci " y fada yana kallanta
" Ki taso muci koh " y fada a karo na 2
Haushi y kamashi ya tashi y matsa gaban T.Vn yana cewa
" Aou ashe pah kurma ce let's off d television yanda xaki ji "
Kallansa ta tsaya yi xuciyarta na neman karyewa
" Kurma ? Ta fada akan la66anta
Sedae yaji ta hakan yasa yce
" Ohh ashe kina jina tun farko amma baki amsa min b ! kin maeda ni shashasha wato inyi d bango koh ? Y fada yana kashe t.vn
" Ki tashi ki wuce muci abinci "
" Na qoshi "
" Wlh se kinci " y fada cikin tsare gida
Tashi tayi ta qarasa dinning din ta xauna , sannan shima y xauna y miqa mata plate d cup wanda y xuba tea a ciki
Ba dan tana jin yunwa b ba abinda zesa taci ko abu 1 ne dan ji take kamar ta rusa ihu
Tea din tasha shima ko rabin cup bata sha b ta ajiye sannan ta miqe tana Jan numfashi da sauri d Sauri alamar kuka take shirin yi
Binta yayi d kallo harta shige dakin
Yasan be kyauta b amma wannan itace kadae solution din d zesa ta daawo hanyar dae dae ( Amma pah a ganinsa )
Se da yaci yayi hani'an sannan y miqe y shiga bedroom din , tana kwance ynxn ma sedae ynx ajiyar xuciya take ajjewa akae akae abinda xe alamta maka cewa kuka tayi
Wanka yayi y fito y shirya cikin qana nan kaya sannan y juya y kalleta
" Ki tashi ki shirya xamu wuce hospital ! yau xaki fara kar6ar treatment "
Yanxu kam batae musu b dan so take dama ta fita daga gidan , ta wuce toilet din tayo wanka ta shirya a ciki sannan ta sake fitowa sanye d hijab sedae ta chanja wannan din
Kallanta yayi y kauda kae se kuma yce
" U know what ? Ki cire wannan hijab din ki nemi mayafi kinsan dae dubaki xa'ayi koh ? Ko kuwa in mukaje xaa dubakin cire hijab din xakiyi gaba daya ? Kije ki chanja " y fada yana ficewa daga dakin.
A hankali take takowa xuwa cikin qatuwar harabar gidan , kasancewar gidaje ne d yawa a cikinsa
sanye take d Marun din abaya d mayafin ta fuskarta babu komae se kwalli da ta saka
Motar data dakkosu jiya ta hanga arman a tsaye daga jikin qofar driver hakan yasa ta nupi motar
Ganin ta da yayi ya sanya shi shigewa cikin motar d alama shi xeyi tuqin
Kae tsaye ta qarasa wajen motar sannan ta bude gidan baya ta shiga ta kulle qofar
D mamaki yke kallanta ta jikin mirrow , sedae ita kanta ma yana gefe ne tayi kicin kicin d face
Gyara xama yayi ya janyo wayarsa ya fara daddannawa har suka kwashe kusan 20mins
Ganin in dae shirun y mata ba xata ta6a gane yaren d yake nupi b ya sanya shi kallanta
" Ni drivern ki ne ?
Bata juyo b har ynx dae kanta na gefe
Y sake maemaeta mata tambayar still dae tana kallan gefen
Seda y juyo sosae yana kallanta y sake daure fuska sannan yce
" Wae ba kya jina ne "
Se a lokacin ta juyo tana kallansa cikin dakewa tce
" Aou wae magana kke ? Kasan pah kurma ce seka daga murya " ta fada a dake tana dauke kae
Wani qayataccen murmushi y saki yana juyawa
" Ohh wae abinda y fada mata jiya ne y 6ata mata rae ? uhmm wae yarinyar nan ni take fadawa magana haka ? Soon xanyi maganin ki baby "
Sake waewayowa yyi yce
" Ynx dae b wannan b muna 6ata lokaci kar mu makara , plsss ki fito Ki daawo gaba in mun daawo se a dora daga inda aka tsaya uhmm ?
Seda ta gama shan qamshinta sannan ta fito ta koma gaban har ynx dae fuskarta a haden take.
Ba suyi tafiya me tsayi b suka isa asibitin , kasancewar ansan d xuwansu kuma shima likita ne yasa basu sha wahala b kae tsaye suka wuce ganin likita
A ranar aka bata magungunan d xata faara amfani dasu kapin ayi mata aekin d kuma shawarwari d suka bata .
Seda suka daawo ta samar musu abinda xasu ci dan b qaramar yunwa take ji b har wani jiri jiri take dan tun tea din d tasha d safe bata sake cin komae b
Tana gama cin abincin a kitchen ta jere masa nasa a dinning , sannan tayi wanka tae sallah ta kwanta cikin blanket dan wani sanyi d taji yana shigarta alamar xaxxa6i na shirin kamata .
Bata Dade d kwanciyar b baccin y dauketa .
...Yana kan dinning din bayan y gama cin abincin y cigaba d xama yana danna waya
Kira ne y shigo wayar tasa dauke d wata sabuwar number ta qasar
Cike d mamaki y kalli number kamar baxe daga b se kuma y daga tana dab d tsinkewa
Cikin karyewar murya tace
" hey Lurv ! Its Catherine ! Har na saare na dauka b xaka daga b !
Ashe ka daawo ? Kuma kana los Angeles amma baka fadamin b why ? Kasan kuwa yadda nayi missing naka ? Kuma nima na daawo gida "
" Toh pah ! Y fada akan la66ansa dan harga Allah shi kam y manta d wata Catherine in banda ynx data kirashi
Cikin dakewa yce
" Yeap ina qasarku !
" Ohk lurv ka bani address gobe se in shigo , though dae naso maka surprise ne kwae sedae ka ganni , but bansan inda xan samu address din b dole seta wajen ka ".............
Tohhhh pah readers ga fah Arman a qasarsu Catherine , ga kuma sanah a can gefe π₯ΊπΉ
Ko ya xata kaya ?π
A next page dina In Sha Allahu xakuga sunayenku en amanatah π masu min comment π₯Ί
Mhiz Innocent ce.............βοΈ
*β‘βA ZURI'AR ARABβ‘β* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent π»
πTHE TALENT TROUPE WRITER'Sπ
Page 33_34
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES ππ Mhiz Innocent luv u owl ππ»
( Baby WhatsApp group link ) ππ
https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e
...........Seda ya lumshe ido kamin a hankali ya furta
" Not now plss ! Akwae aekin da nake in na gama i will let u know "
" Uhmm memakon ka bani kawai inzo , ko aekin ma ae sena tayaka " ta fada wai ita ala dole shagwa6a zata masa
" Plss...."
" Ohk..Ohk lurv ! Duk yadda kace , but k dinga tunawa cewar I luv u to d extent " ta katseshi kafin takae ga jin abinda zece
" Its Ohk " Kawae ya fada yana katse kiran cike da qosawa
Wannan Catherine din tana neman ta jagula masa lissafi.
*_Nigeria_*
" Kin bani mamaki sadiya , kin shayar dani mamakin da ban ta6a tunani ba , ashe har akwai abinda zance kiyi ki saka qafa kiyi fatali dashi ?
Kukan ta sake fashewa dashi kanta a qasa
Abba yace
" ki bar wannan kukan , magana zaki bude baki kiyimin "
Cikin sarqewar murya tace
" Wlh wlh abban souban bani na saka souban ya aekata abinda ya aekata ba , hasalima ni tun ba yau ba na fawwalawa Allah komae akan auran nan ! Wlh abban souban bani da masaniya akan komae "
" Toh idan baki da masaniya ina souban yake har tsawon kwana 4 ?
" Wlh bansani ba ! nima shine bansani ba , amma don Allah ka yadda da abinda nake fada maka abban souban "
Se kuma ya nemi waje ya zauna zuciyarsa fall cike da tunani kala kala ' toh meya faru souban ya chanja ra'ayinsa haka a lokaci guda ? Bayan ga wadda yake zargin zata sakashi aekatawar tana rantsuwa akan ba itace ba ?
******* Yana qarasawa cikin dakin y zare hular kansa samfurin face cap yace
" Momsy ina kwana ?
Aunty dake zaune kan kujera tana kallo tace
" Lafiya qalau Khalid ! Kwana 2 duk ka daukewa gidan nan qafa ? Ae ko baka zo dan kowa ba kaazo danni "
Murmushin gefen bani yayi yace
" Hajiya momsy ni zuwa nayi inyi muku jaaje "
" Jaaje kuma ? Ta fada tana kallansa
" Ehh manager ae jaaje za'ace , ace wae ranar daurin sure ango ya faasa aure ? Ae an tozarta gidan nan "
Ta6e bani aunty tayi tana fadin
" Allah kyauta ! Kasan ni ban fiye Shiga damuwar da ba tawa ba "
Dariya sosae ya sheqe da ita yana buga hannayensa
" Allah koh momsy na ? Ni zuwa nayi In share muku hawaye , Dan kuwa xuwa nayi in nemi auren er taku !
Kallansa aunty tayi sosae kafin ta girgiza kae
" Allah ya shiryeka Khalid ! Halin en gidan nan ne baka Sani ba ? Ko da take bama wannan ba
Kae yanzu kana tunanin ko da basu aura mata wani ba zasu Bka ita ne ?
" Momsy meye laefi na ? Ya fada yana kallan kansa "
" Uhmm toh seka samawa kanka salama Dan kuwa tun a ranar suka daura mata aure da arman !
Cikin gigecewa ya zabura ya miqe yana fadin
" What ? Arman ? Garin Yaya ?
" Meye naga ka zabura ne ? Aunty ta fada tana nazarinsa
" Momsy arman fa kikace ? Yanzu ina suke ?
" Meye naka da inda suke Khalid ? Toh sun bar wasar ma gaba 1" ta fada cikin halin ko in kula
Seda yayi yadda yayi yasan qasar da sukaje da satin da taji ance zasu dawo duk seda ya sani sannan ya bar gidan cikin tashin hankali .
......Tun kafin ya kae ga Shiga parlourn ya faara qwallawa black kira
Da sauri ya fito yana fadin
" Oga lafiya kuwa ? Wannan Kira haka ?
" Oh yah Ku saki wancan garan ! mun gama dashi , aekin ya tashi daga kansa yya koma kan Dan uwansa "
Saga kafada black yayi yana fadin
" Duk yadda kace "
Kafin ya qarasa wani daki , ya bude
Souban na zaune kan kujera 1 sitter hannunsa dauke da counter , sedae ya jingina kansa kan kujerar da yake kae kamar me bacci
Black ya qarasa yace
" Kae lokacin fitarka yayi , se kazo ka fice "
Seda yakae qarshen zancen sannan souban ya dago ya kalleshi , kaana a hankali ya miqe yana fadin
" Yah salam " dafe da Kansa dake saara masa , sannan yayi gaba black na bite dashi
Babu kowa a parlourn haka zalika a filin gate din ma , sa6anin kullum da take jin hayaniyarsu a parlourn
Yabi gidan da kallo sannan yayi gaba jikinsa a matuqar sanyaye
Black dake ankare dashi ya sheqe da dariya .
Seda Khalid ya tabbatar souban ya fita ya fita sannan ya fito yana fadin
" Black mene next target namu ??????
*_Los Angeles_*
.............Washe gari harya daawo daga masallaci bata tashi ba , so yae assuming ma bata sallah ne shiyasa be tashe ta da asuba ba .
Sedae yanxu kam abin y bashi mamaki ganin har ynx babu alamar ta fito dan ko gidan ba'a gyara b
Qarasawa bedroom din yayi d sallama dauke a bakinsa yana tsammanin ze ji ta amsa masa
Sedae me ? hangota yae har ynx dae akan gadon kamar yadda y batta
Cikin sauri hade d sassarfa y qarasa gadon y yaye blanket din dan ganin yanda take rawar sanyi
" Yah salaam ! Y furta yana qarasa yaye bargon , sannan y ta6a goshinta xafi zau , abinda y tabbatar masa xaxxa6i ne y rufe ta
D sauri y hau kan gadon yana daga kanta ya dora a cinyarsa
" Baby ! Baby !!
Da qyar ta bude idanunta da suka yi mata nauyi ta sauke su akan fuskarsa
Qoqarin miqewa ta farayi ya riqota sannan ya taemaka mata ta miqe gaba daya
Kae tsaye y wuce da ita toilet ya hada mata ruwan zafi tana xaune kan kujera
Tsayawa tayi tana kallansa
Ya gaane me take nupi , toh shi kuma ynx baya son musu hakan yasa y fice y bata waje dan tayi wankan.
Mintuna wajen 15 sannan ta ta6a qofar tana qoqarin fitowa
D sauri ya qarasa y riqota
Ba tae musu b dan tana da buqatar taemakon
Y qarasa d ita gefen gadon sannan ya koma wardrobe y ciro mata doguwar riga mara nauyi d hula y ajjiye a gabanta yace
" Dauki ki saka "
Bata motsa ba kuma bata kalle shi ba
Ya sake maemaeta mata
Nan ma tayi shiru
Ganin bata da alamar kulashi y sanya shi daukar kayan ya faara warewa yana matsowa kusa da ita
Ba shiri ta miqe tana turo baki ta kar6i kayan
Shi kuma ya dauki wayarsa yana dannawa , yayinda tayi amfani d wannan damar ta saka kayan sannan as usual ta kima wannan uban hijab din ( wae nikam nace makinkimi ππ)
Ranar haka ta wuni akan gado daga tabi wannan waje se ta chanja waje .
Tana nan kwance y shigo dakin d sallama hannunsa dauke d Leda d bansan ta meye b
Y qaraso yae switching light din dakin blue colour sannan y qarasa gefen gadon kan side drawer y zauna
A hankali ya furta
" Tashi kisha magani "
" Innalillahi " ta fada a hankali se ta maaze as in bacci take
Ya san sarae idonta 2 kuma tana jinsa hakan yasa yace
" Ki tashi tun kapin na 6ata miki "
Tashin tayi tana sake turo baki tana kallan gefe
Murmushi ya saki yana janyo drawer da yake kae ta qara kusanci da gadon
Shawarma ya fito da ita daga cikin ledar sannan y fara gutsura a hankali ya kae bakinta
" Ni bana ci " ta fada a taqaece
" Se kinci " ya fada cikin nuna isa
Ba dan tana jin dadin bakin ta ba tace
" Toh ka bani inci da kaena "
Kallanta y cigaba dayi dan yanda take maganar cike d shagwa6a wanda ita bata san tana yi ba kawae dae a nature dinta ne hakan
B musu y miqa mata
Ta kar6a taci kadan sannan ta ajjiye
Nan ya ciro maganin ma y bata tana 6ata rae , yayinda shi kuma ya hade mata girar sama data qasa yadda bama xata ga fuskar d xatayi masa musu b
Tana gama sha ta fara qoqarin kwanciya tana ajjiye numfashi
D sauri y riqota
" A'ah kwanciyar ta isa haka ! bari na shafa miki maganin can kapin nan se ki huta "
Xamewar dae tayi sannan d sauri kuma d gudu taji wani vomiting ya taso mata
D sauri ta fara qoqarin janye hannunsa daga jikinta , yayin da shi kuma be fahimci abinda take nupi b y sake riqota
Aekuwa ta shararo vomiting din a jikinsa
" Yah ilahee ! Sannu kinji baby ! Y fada yana miqar da ita gaba daya y qarasa d ita toilet din ta wanke fuskarta dan jikinta be 6aci ba , sannan ta fito ta koma cikin blanket din
Shi kuma yayi wanka ya fito y shirya yae duk wasu abubuwan d yake d buqata sannan y daawo
Tana kwancen dae sedae yanzu babu rawar darin da take in ta kwanta
A hankali ya qarasa kan