Showing 51001 words to 54000 words out of 65672 words
Chapter 18 - A ZURI'AR ARAB COMPLETE BY MHIZ INNOCENT .txt
ya sure ta be tsaya ko ina ba se cikin motarsa dukda wutsil wutsil din da takeyi tana
" Ni ka saukeni kar wasu su gammu "
" Toh menene ? Ae kinga ma se hakan yafi bada citta " ya fada a dae_dae lokacin da yake ajjiyeta a kujerar me zaman banza
Sannan ya qaraso ya zauna a wajen driver ya tashi motar ya fice daga gidan gaba 1.
Kae tsaye suya spot ya tsaya ya siya gasassun kaji, sannan ya dawo ya tashi motar, ya sake tsayawa a wani supermarket din ya siyi yoghurt da sauran kayan sha sannan kae tsaye ya qarasa gidan nasu dake Nasarawa G.R.A
Shiya sauka ya bude gate din gidan sannan ya kutsa motar cikin madaedaeciyar harabar gidan
Ita dae tunda suka fara tafiya ba tace komae ba se cika kawae take tana batsewa ta cika tayi fam qiris take jira ta fashe dan haka sam bata lura ma da abinda ya sissiyo din ba .
Seya qaraso 6angaren da take ya bude da murmushi kan fuskarsa yace
" Madam barka da zuwa gidanki " ya fada yana ware hannayensa na hannun dama
Dauke kae gefe tayi ba tace komae ba
Se ya sake murmushi yace
" Ohk an sake bani dama kenan in shigar dake ciki ? Well ! Hakan ma yayi " ya fada yana qoqarin fara daukarta
Da sauri ta fito daga cikin motar, se a lokacinma ta tuna ko mayafiko hijab babu a jikinta .
Qaton parlour ne with well furnished ya hadu iya haduwa dan kuwa an zuba dukiya irin sosae din nan, akwae kitchen a ciki se two bedroom duka dae a cikin parlorn,
Ya nuna mata 1 daga cikin bedroom din yace
" Ki shiga ciki kiyi wanka, bari nima naje nayi "
Ba tace komae ba ta wuce dakin shima da ya gaji da kyau kamar a qasar waje
Mintuna wajen 20 ta dauka tana wankan sannan ta fito daure da towel tana tunanin kayan da zata saka tunda dae tasan ita ba tazo da komae ba
Tana bude wardrobe taga saetin dogayen riguna masu kyau kalar wadanda takeso
Kawae se taji murmushi ya su6uce mata ta dauki 1 daga cikim rigunan ta saka, sannan tayi sallah ta nemi gefen gadon ta zauna kafin bacci ya dauketa .
Wajen qarfe 9 se gashi ya shigo hannunsa dauke da wani plate da jug da robar yoghurt, ya qaraso ya ajjesu sannan ya kalleta
" Madam tashi muyi sallah koh ?
Kallansa tayi cikin rashin fahimta tace
" Ae nayi "
" Yes na sani, wannan ta daban ce "
Jiki ba qwari ta tashi ta gyara zaman mayafin ta sannan suka tada sallar bayan ya shimfida musu dadduma .
Ita dae haka kawae taji jikinta yayi sanyi da al'amarin babyn, haka ya tilasta mata seda taci kazar da yoghurt din kadan taci sannan ta miqe taja blanket ta shige ciki tana fatan bacci ya dauketa a lokacin
Sedae addu'arta bata kar6u ba dan kuwa tana kwancen harya gama cin kazar ya tashi ya fita ya dawo baccin be dauketa ba
A hankali taji ya hawo kan gadon sannan ya yaye bargon data rufa dashi ya janyo ta jikinsa yana kishingida akan pillow
Bugun zuciyarta ne ya qaru amma ta dake tana sauke ajiyar zuciya
A hankali ya fara magana cikin taushi hannayensa akan sumar kanta me santsi
" Baby ! Kinsan kuwa tun sanda nake qaunarki ? Ina qaunarki ne tun kina qaramarki, da sonki na tashi tun ina qarami, bansan sanda soyayyarki ta shigeni ba nidae kawae abinda nasani shine na tashi ne naji ina qaunarki , na kasa fada miki ina qaunarki ne saboda karki gane basu Mamama ne suka haefeki ba, dan kuwa bazan ta6a yafewa kaena ba indae ta dalilina kika shiga wani hali, meyasa kike ganin 6acin raena duk sanda na ganki da wani ? Ko kikae zancen wani ? Kishinki nake baby , ina jin zuciya ta tamkar zata faso qirji na a lokacin, baby ki tausayawa wannan zuciyar me matuqar qaunarki dan kuwa ta azabtu shekaru da dama ya kamata ace yanzun ta sami salama, baby ina sonki sosae pls kice kina so na kema " ya fada a raunane
Bata iya cewa komae ba, sedae zancen nasa ya shige ta sosae ta yadda seda taji wata qwalla ta zubo mata
Seya shagala da rarrashinta wanda daga nan zancen ya sauya.......
Daga haka na kamo hannun Ummulkhaer, dama Fateema bashir ke dauko rahoton ina rubutawa ta tsaya zata qarasa daukowa, Maemuna ta janyo hannunta muka fice daga dakin muna kullo musu qofar.. Daga haka se ince seda safenku Arman wa Sanah .
.......Bamu sake komawa dakin ba se da safiya wajen qarfe 12..
*****A hankali ya tura qofar dakin hannunsa dauke da tea
Tana kwance har yanzun kamar yadda ya batta ya qarasa yana jan side drawer ya zauna sannan yace
" Pls baby ki tashi kisha tea ne "
Maqe kafada tayi tana juya masa baya
" Ohh shet ! Ya fada sannan ya dora da
" Don Allah ki tashi karki qarawa kanki ciwo " ya fada yana kae hannu ya dagota sannan ya ta6a goshinta wanda yae zafi zau alamar zazza6i ne a jikinta
" Yah salam ! Zazza6i ne a jikinki " ya fada yana tunanin yadda ze sama mata magani dan kuwa kwata kwata babu magani a cikin gidan
Ya kalleta with matsananciyar qauna a idanunsa sannan yace
" Lem me get medicine 4 u " ya fada yana gyara mata kwanciyar , ita kuma ta sake Jan bargon dan yadda take jin wani sanyi na ratsa jiki da 6argonta
Kae tsaye ya janyo wata jallabiya ya saka sannan ya dauki key din motarsa, harga Allah bata son barinta ita 1 a cikin gidan amma babu yadda zeyi dole ya samar mata maganin
Yana dab da fita ya daawo ya sake kallanta sannan ya bata light kiss yana fadin
" Yanzu zan dawo In Sha Allah "
******Kae tsaye chemist din dake kusa dasu ya nufa sedae akayi rashin sa'a baya nan , dan haka ya wuce wani chemist din dake dan nesa kadan da gidan nasu,
A dae_dae yazo wani jection yana shirin karya kwana motar da tun dazu take binshi ta samu damar bugarsa, motarsa tayi taga_taga tana karya kwana sannan suka sake bugar motar tasa
Se da sukaga motar tayi gefen titi tana juyi sannan suka juya suka fara qoqarin guduwa , wata qatuwar motar en sanda tazo tai blocking nasu kafin en sandan suka fito suka cafke mutanen dake cikin motar data gogi ta Arman din
Daya daga cikin en sanda ne ya dauki waya yayi dialing din wata number ya kaara a kunne yana fadin
" Yalla6ae aeki ya kammala, mun samu damar cafke 2 daga cikinsu "
Bansan da wanda yake magana ba amma naji yace
" Ohk sir "
.....Da qyar aka samu aka fito da Arman wanda sudae en sandan suka riga suka tabbatar cewar ya rasu.....
*****Ita dae tun dazu take jin hayaniya a a compound din gidan, amma batae magana ba, seda Umman amrah tace
" ni fa run dazu nake jin hayaniya "
Mamama tace
" Qwarae Nina naji ! Ya kamata muje" ta fada tana miqewa suka fita compound din duka su 2n
Haka kawae mamama taji zuciyarta na bugawa sanda taga mutanen dake a tsaye a harabar gidan nasu
Ganin fitowarsu ya Sanya 1 daga cikinsu matsowa yace
" Pls muna Neman mahaefi ko mahaefiyar Arman Alqaseem "
Cikin tashin hankali da firgici Mamama tace
" Nice mahaefiyarsa " ta fada sanda wasu hawaye masu dumi suka sakko mata a kunci, tana fatan ba abinda take tunani bane ya faru
" Ohk tohm bismillah " ya fada yana yin gaba
Umman amrah data kasa shiru tace
" Pls ya kamata musan meya faru koh ?
Seya dakata ya juyo garesu kafin yace
" Toh hatsari ne dae ya ritsa da Arman kuma muna da tabbacin Allah ya masa rasuwa !!
Da sauri mamama ta lalubi ginin dake gefenta sannan ta sulale akan kujera tana jin kamar a mafarki ne take jin wannan al'amari
" Arman ya rasu ? Innalillahi wa inna ilaehi raji'un " ta furta sanda wasu zafafan hawaye suka silalo akan kuncinta
Duk yadda taso taqi yin kukan hakan ya citira .
*****Tunda taji zancen mae gadin gidan nasu taji hankalinta yaqi kwanciya , cikin rashin sanin abinyi da qwarin jiki ga zazza6in dake jikinta har yanzun ta dauki hijab ta saka sannan ta fito
Gashi baby baya nan ballantana su taci tare, bata masan inda ta jefa wayarta ba ballantana ta kirashi dan haka kawae ta hau motar suka dauki hanyar gidan nasu na Arab
Duk wasu tunane_tunane da suke zuwar mata a qwaqwalwa haka ta watsar dasu ta cigaba da janyo duk wata add'uar neman tsari da tazo bakinta har suka iso gidan .
Ba baqon abu bane ganin sojoji a gidansu ba, amma yau ganin harda en sanda ya sanya haka kawae ta ji gabanta ya fadi
Can ta hango wani abu a kwance wanda zata iya kira da gawa a lullu6e , a take a lokaci guda jikinta ya soma 6ari tana tunanin wanda ya rasu a gidan nasu Daddy ne ? Ko mamama ?
Tunanin nata ya katse sanda ta hango mamama zaune a kan wata kujera
Jiki babu qwari ta qarasa wajen mamaman, ta zube akan gwuiwoyinta ta kamo hannayen mamaman fuskarta cikin wani iron yanayi dana kasa fahimtarsa tace
" Mamama waye ya rasu ?
Wasu sabbin hawaye ne suka sake zubowa mamama tana kallan Sanah cike da tausayawa amma ta kasa cewa komae
Sanah ta sake fadin
" Mamama pls ki fadamin wanene ya rasu ?
Umma dake gefe tace
" Kiyi haquri sanah arman...."
Kafin ta qarasa fada sanah tace
" Baby baya nan ! Ya fita, be masan na taho ba, nidae don Allah Ku fadamin "
Cikin kuka umma tace
" Kiyi haquri Sanah Arman ne ya rasu "
Seta saki hannun mamaman da sauri kamar wadda aka yiwa wani Abu, ta miqe a hankali ta fara ja da baya. tana girgiza kae fuskarta dauke d wani irin murmushi
Umma ta miqe da sauri dan riqota Sanah tace tana dakatar da ita da hannunta
" Karki Matso kusa dani ! Karki sake ki matso ! Ta yaha zaki cemin baby ya mutu ? Baby fah ? jiya fah ya gama fadamin ze kasance dani har abada, amma yanzu kinzo kina cewa wae ya mutu ? Kinsan abinda kike fada kuwa ? Ta fada tana sake girgiza kae tana hana hawayen da suke kwance cikin qwayar idanunta zuba
Aekuwa ta sake karyar musu da zuciya, Mamama dake zaune ta samu damar tasowa a hankali ta qarasa ta riqo sanah ta rungume a jikinta
Se a lokacin kukan da sanah take riqewa ya fito fili kafin cikin kukan tace
" Don Allah Ku tasheni daga wannan mummunan mafarkin da nake ! Meyasa abubuwa suke zuwa ba'a lokacin daya dace ba ?
Mamama tae sauri ta rufe bakin sanah din tana jin wasu hawaye suna tsere a kumatunta
" Mamama bafa baby ne ya mutu ba , ki fada musu , ya Riga da yamin alqawari fah mama....." Bata qarasa fada ba mamama taji nauyinta ya qaru wanda hakan ya alamta mata cewar ta suma.
Dae_dae lokacin motarsu daddy ta shigo gidan kasancewar basa nan duka Manyan gidan sun tafi wata gaesuwa
Jiki a sanyaye jikinsu suke saukowa daga motar
Kae tsaye wajen gawar suka nufa
Daddy ne ta fara tsugunnawa a hankali cikin wani irin yanayi na kidima ya yaye abinda suka rufeshi dashi , ba zakace ma hatsari yayi ba banda karcewar da gefen fuskarsa tayi
A hankali daddy ya kae hannunsa saetin zuciyar Arman din dan tabbatarwa kansa cewar da en sanda suke Arman dansa tilo, shalelensa, yaro 1 tamkar da dubu ya rasu....................
Daga haka se ince mu hadu bayan sallah In Allah ya kaemu da rae da lafiya, fatan zamuyi sallah lafiya
Nasan tambayoyi fall a cikin ranku, bari inyi shishshigi in fadi tambayoyin da nasan sune suka fi damunku a rae da zuci
Su waye suka kaewa Arman hari ?
Sgin Arman y rasu ?
Toh kuyi haquri bayan sallah duk zaku samu amsoshin tambayoyinku In Sha Allah
Mhiz Innocent ce..........✍️
*♡☆A ZURI'AR ARAB♡☆* An amazing and heart touching story
By Mhiz Innocent 😻
💖THE TALENT TROUPE WRITER'S💖
Page 41
Ina miqo gaesuwa a gareku INNOCENTIES 😍👌 Mhiz Innocent luv u owl 🌚😻
( Baby WhatsApp group link ) 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ETMx34eVVElHuSQDD3QH2e
_Wannan page din sadaukarwa ce a gareku team Arman_
..............Daddy y kulle idanunsa cike da fargaba gami da faduwar gaba ya qarasa da hannun nasa saetin zuciyar Arman
Cikin wani irin yanayi dana kasa fahimtar a wane fanni zan ajiyeshi daddy ya juya yana kallansu Abba dake tsaye a kusa dashi , In a lower voice me cike da sanyi yace
" Baffah akwae sauran numfashi a jikin Arman !! Ya fada yana kallansu su duka , sedae kamar a hanzarce yae maganar
Wata qatuwar ajiyar zuciya dukkansu suka ajjiye, dae_dae lokacin da Daddy ya miqe
En sanda dake kusa dasu suka kalki daddy cike da mamaki
Jinjina kae daddy yayi alamar tabbatarwa yana kallan 1 daga cikin en sandan
Tuni cikin hanzari aka fara kiciniyar daukar Arman din zuwa wata motar daban wadda ta cikin gidan na Arab ce
Mamama dake gefe a tsaye ita da umma da Maman souban wadda fitowar ta kenan suka bisu da kallo cike da mamaki dan basu san akan abinda sukae magana ba .
A hankali daddy ya qarasa wajen mamama da sanah ke kwance a kafadarta
Mamama ta bishi da kallo kana ganinsa kasan jikinsa a sanyaye yake sedae ba taga wata alamar da zata nuna yasan da mutuwar ba , bayan kuma yanzu ta Ganshi a wajen
Ya qaraso sannan ya sakarwa mamama murmushi me taushi yace
" Albishirinki ?
Wasu ajiyayyun qwalla ne suka kwaranyo mata a kuncinta tana Kallan daddy cike da tausayawa dan taga alamar har yanzu besan da mutuwar ba
Umma dake kallansu ta qaraso jiki a matuqar sanyaye ta kar6i sanah sannan ta qarasa da ita cikin gidan kafin a wuce da ita asibiti
Daddy yace yana murmushi
" Rahama ki bar kuka Arman be mutu ba !!
Seta tsaya da kukan tana kallansa ido cikin ido, abinda bata ta6a ba kenan
Ya jinjina mata kae alamar tabbatarwa sannan ya dora da
" Ki tashi yanzu mu tafi asibiti, za'a dubashi dan kuwa akwae sauran numfashinsa a duniyar nan "
Haka kawae kamar wata sokuwa seta miqe tabi bayansa har suka qarasa wajen motar
Kafin daddy ya koma cikin gidan suka fito tare da umma da sanah suka wuce asibitin baki 1.
****Kae tsaye emergency suka wuce dashi dan bashi taemakon gaggawa, Cikin mintuna kadan likitoci suka hadu a kansa suka fara aekinsu cike da qwarewa sedae ya shiga coma ne dan haka har lokacin da suka gama abinda zasu masa be farka ba , dan haka aka wuce dashi wani ke6antaccen daki dake Cikin asibitin wanda ake kae masu matsala irin taasa .
.........A hankali ta fara bude idanunta tana rufewa tana budewa hakan yasa dogayen gashin idanunta suka jiqe da ragowar hawayen dake kwance a cikin qwayar idanunta
Da sauri mamama dake zaune gefenta ta miqe ta qarasa bakin gadon tana kamo hannayenta sannan cikin taushi tace
" Sanah "
Seta sauke idanun nata akan mamama wanda a lokacin wasu hawaye masu dumi suka zubo mata a kumatunta cikin shaqaqqiyar murya tace
" Mamama ina baby ?
Murmushi me hade da kuka kuka mamama ta saki sannan a hankali tace
" Ki kwantar da hankalinki sanah, Arman yana nan qalau "
Seta fara qoqarin tashi zaune , mamama ta taemaka mata ta zauna din sannan tana kallan mamama tace kamar zatayi kuka
" Mamama don Allah ki fadamin inda baby yake ! Inason na ganshi ne don Allah "
Cike da tausayi mamaman ke kallan diyarta ta
" Ya isa haka ! Ba zasu bari ki ganshi ba yanzu haka sanah, sun shigar dashi wani daki ne "
Se ta saki wani murmushi tana qissimawa ranta lallae haqiqa kenan mafarki tayi babyn ya mutu tunda gashi mamama na fada mata yana daki
Seta fara qoqarin sakkowa daga kan gadon dukda rashin qwarin jikinta ga zazza6in data kwana dashi jiya
Mamama tayi saurin riqota , sedae wannan karon bata ce komae ba ta taemaka mata tana kallan ta cike da tausayawa
" Mamama don Allah inason na ganshi " ta fada kukan da take riqewa na fitowa
Mamama ta riqeta suka fita daga cikin dakin, kae tsaye wajen daddy suka nufa, kafin su qarasa daddy ya qaraso kasancewa yana waje baya cikin office dinsa
" Ahh rahama ya akae kika fito da ita ?
" Wlh daddyn Arman ta daage ne tana son ganinsa koda yadda za'ae "
Har zece a'ah seya kalli sanah din wadda idanunta sukayi rau rau gwanin tausayi dan haka yace
" Ohk muje "
Mamaman ce dae ta sake mata jagora har qofar dakin, daddy ya bude ya tura qofar sannan ta shiga ciki, mamama na komawa da baya ta zauna dan yadda taji zuciyarta ta karye
Wayar daddy ce tayi qara yana dubawa cike da mamakin ganin kiran , dan shi kam sam yama manta da maganar Dr Stephen
Ya kaara wayar a kunnensa bayan ya sannan accept
Daga 1 6@ngaren Stephen yace
" Dr ! Na jika shiru and yarinyar ce ta damu akan lamarin shiyasa "
Daddy ya dafe kansa cikin rashin sanin abinyi sannan ya tattara kalaman bakinsa yace
" Sorry dr, but abinda yasa ka jini shiru wlh Arman dinne ya samu hatsari yau din nan "
Dr Stephen yace bayan ya jajanta lamarin
" Zamu shigo ñigeria next month har momynta couz gobe ma zamuje qasarsu mom din nata ne semu taho tare da ita mu dubashi and muyi maganar auren nasu "
" Ohk then, Allah ya kaemu "
Stephen yace
" Amen, quick recovery I pray "
" Thanks " daddy ya fada yana katse kiran
Mamama ta kalleshi dan yadda taga damuwa ta bayyana qarara a fusarsa bayan hakan ba dabi'arsa bace tace
" Yalla6ae lafiya dae koh ?
Seya sauke numfashi kamin yace
" I hope so, but....." Se kuma yayi shiru dan baya son qara mata damuwa kafin yace
" Babu komae " yana sakar mata murmushi lokacin guda yana miqewa ya dora da fadin
" Bari na koma wajensu baffah, inta fito ta janyo qofar "
" Tohm " mamama ta fada tana bin mijin nata da kallo
A hankali ta qarasa bakin gadon nasa tana kallansa tun daga kan qafarsa harkan kyakykyawar fuskarsa wadda ke manne da oxygen amma dukda haka hakan be hanata kallansa ba
Sannu a hankali ta sake matsawa dab dashi sannan cikin sanyi ta kamo hannunsa ta saka cikin