Showing 1 words to 3000 words out of 49839 words
Chapter 1 - UMARNIN SAURAYI Complete BY SUMMY M. NA'IGE.txt
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata,Burinmu mu faɗakar da Al'umma Domin Ribantar Duniya Da Kuma Lahira.}_
'''🎐G•W•A🎐'''
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 1📑*
*__________📖* Wayar tace ke rura, tana son ta tashi ta ɗauka amma ta kasa, saboda irin yadda ya manne ta a jikinsa.
Sosai wayar ke rura aƙalla anfi yin miss call goma amma tana ji ta kasa tashi ta ɗauka.
Ba dan komai ta kasa tashi ba sai dan kada ta ɗan mutsa ta ta da shi,abinda bata so ita kuma.
Wayar ce taƙi dai na ƙara,kuma gashi bata son ƙarar data ke, dan bata son ƙarar ta dame shi yana baccin sa,dan haka ta fara tafiyar da hannuta slow-slow har ya kai kan wayar.
Ɗauko wayar tayi lokacin kuma wayar ta sanya wata ƙara.
Da sauri ta sanya ta silent, duba miss call ɗin tayi taga wake kiran ta.
Fara dubawa tayi aikuwa gaban ta ne ya yi munmunar faɗuwa da taga wanda ya kira ta.
Tana cikin wannan fargabar sai ya fara mutsi alamun zai tashi,jikinsa ya ƙara jawuta kana ya ɓuɗe idonsa waɗan da bacci basu gama sakin shi ba.
Ahankali ya fara mata magana akunne yace, "My Sweet nah, ki tashi ki haɗemun abunda zan karya saboda yanzu na ke son tafita office dan jirana akeyi".
Ba musu tace, "yanzu kuwa Hayateena".
Kumatunta ya shafa haɗe da kai ma kiss kana yace, "shiyasa nake ƙara sonki".
Murmushi tayi mai ɗan sauti kana ta tashi taje kitchen ta haɗa masa abunda yake buk'ata.
Har takusa kammalawa wayar ta tasake ƙara,da sauri ta ɗauku waya tana mai duba sunan dake yawo saman screen ɗin wayar.
Gabanta ne yaba da dummm hannuta na karkarwa ta kara akunninta.
Kafin tayi wata magana har anfara magana cikin faɗa-faɗa.
"Hafsa ina kikaje?ina kika kwana?miyasa kikeso kijamin abun magana da mahaifinki, ehh!".
Muryar ta narawa tace, "Mama wallahi karutune yayimin yawa kuma kinsan munkusa Fara exams kuma wannan karun mai zafice zamuyi shiyasa nayi bacci na a hostel,amma ki bashi hak'uri anjima kaɗan zan dawo".
Sai Mama tace, "to naji amma kirinƙa faɗamin idan zaki kwana saboda nasamu natsowa kinji ɗiya ta".
Tace, "tau Mama sai nazu anjima".
Bayan sunyi sallama da Mamar ta,tashi tayi ta haɗe masa komai na breakfast,bayan ta kammala taje toilet ta haɗa masa ruwan wanka,bayan ta gama haɗe masa taje ta faɗa masa yazo yayi wanka.
Bayan yayi wanka ya fito,da kanta ta shirya sa ta fesheshi da turare mai ƙamshi kana ta kaishi dining Yayi bearkfast.
Bayan ya kammala ya tashi zai fita office,jikin sa ya jawota kana ya kai mata kiss a baki,ido cikin ido ta dubeshi ciki da shagwaɓa tace,"Hayatee nah, anjima zanje gida dan Mama takirani tana faɗa dan ma nace mata ina hostel ne ta ƙyaleni".
Tunda ta fara Magana ya heɗi fuska har ta kai karshe.
Yace,"bawani Mama ta kiraki kina dai son kitafi dan yanzu naga alamun kin daina sona".
Kamar tayi kuka tace, "kadaina faɗin haka wallahi inasonka sosai,amma tunda bakaso naji na fasa zan san me nace mata.
Aikuwa tana faɗin haka wani murmushi ya bayyana afuskar sa,lokaci ɗaya ya fara kiss ɗinta.
Abun ne yaga zaifi ƙarfinshi kuma anajiran sa a office dan haka yasake ta ya ɗau jikar sa ya fice batari da ya saki waiwayo wa ya dube taba......
_*Idan kunji daɗi mucigaba idan ko bakujiba na aje na huta*😁_
*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*UMARNIN SAURAYI°*
*1441H/2020M.*
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER'S ASSCIATION.*
~_Wattpad~@ ~GaskiyawritesAsso_~
*SHAFI NA 2📑*
*__________📖* Saman kujerar parlour ta faɗi tana maida numfashin ta ,dan sosai ya taso mata da sha'awar ta, dan ita bata masu yafita ba, taso ya tsaya ya cikaga ba da abunda sukeyi ko ba komai zata samu natsuwa.
Ta jima kwance saman kujera kafin ta tashi, ko shi lokaci taga ya tafi kuma bata son ya dawo bata gama aiki ba dan haka ta tashi ta fara aiki, cikin ƙan-kanin lokaci ta gama gyaran gida da abunda zai ci idan ya dawo.
Bayan ta kammala komai tayi wanka ta shirya cikin shigar da tasan yana so, dressing ɗin english wears kenan .
Jikin ta ta feshe da turarukka masu masifar ƙamashi bayan tagama shafe jikin ta da humra ta ƴan sokoto wanda akayi ma haɗi na musamman.
Tayi kyau sosai dan idan ka ganta bazaka ce ita ba haushiya ce ba.
Bayan ta kammala gyara jikin ta,zama tayi saman kujera haɗi da ɗauko wayar ta ta kunna kana ta kira Mamar ta dan tagaya mata yau ma ba zata samu damar zuwaba sai gobe.
Ringing ďaya Mama tayi picking call ďin ďiyar ta.
Kafin tayi magana sai Mama tace, "kina kan hanya ne?".
Hafsa tace,"a'a Mama yau ma bazan dawo ba sai gobe dan munada Lectura da safe kuma Babane damu kin san tsohon ba dai fitina ba,amma da mungama zan dawo".
"Tau ba komai amma naso ki dawo gida,amma gobe da kun gama ki dawo".
Tace, "tau Mama ki gaida Abbana".
Sallama sukayi ta aje wayar,sai jin tayi ana mata knocking,tashi tayi taje ta buɗe masa ƙofa.
Tunda ta buɗe ƙofa ya kifeta da ido dan ba karamin kyau ta masa ba,lokaci ɗaya ya jawota jikin sa,haɗi da kai mata kiss a goshe.
Kallon dressing ɗin da ta masa ya shigayi dan tunda yake da ita bata taɓa yimasa irin wannan shagar ba kuma sosai yake son irin wannan shigar.
English wears ɗin data ke sanye da su ya bi da kallo,jan riga ce da wani matsatsin wando wanda ya kamata sosai, ahankali ya kai hannusa ya fara shafar jikin ta yana shaƙar ƙamshin dake fita ajikin ta.
Tunda ya fara shafar jikin ta tafara jin yarrrr......sosai ta ƙara manne jikin ta da nashi.
Tsayuwar ce ta gagaresu dan haka cak ya ɗauke ta ya ƙarasa bedroom ďinsa da ita.
Sosai yayi romances ďinta kafin ya ƙyaleta.
Itako haka tabiye masa ya yi duk yadda ya keso da ita duk da bawani son abun take ba amma bazata iya nuna masa bata so ba saboda bata son ransa ya ɓaci.
Bayan ya gama abunda ya ke so kana ya dube ta yace,"kije ki haɗe man ruwan wanka dan fita nake son yi".
Ba musu taje tayi yadda yace,bayan ya yi wanka ya ci abinci kana ta dubeshi cikin kwantar da murya tace,"Hayatee nah".
Idonsa ya ɗago ya kalleta kana yace, "ya dai sweet nah".
Sai da ta kwantar da kanta ajikinsa kana tace, "dama-dama amma kayi haƙuri ba dan na ɓatama zanje ba please Hayatee ka fahince ni"...tana faɗa kamar zatayi kuka.
Kallon ta yayi kana yace, "inajiki ki faɗa zan fahince ki.
Murmushi tayi haɗe da kai masa kiss agoshi kana tace, "ina son naje gida na faɗama Iyayena zan kuma hostel da zama kaga sai na dawo nacigaba da zamana anan hankali kwance,amma fah acan zanyi weekend,amma sai ina ka yarda"...tafaɗa haka kamar da tsoro aciki.
Sai da akayi ƴan seconds kana yace, "banyarda har kiyi weekind ba sai dai kije da safe da yamma ki dawo amma ban amince kije har kiyi kwana biyu acan ba".
Haƙuri ta fara bashi haɗe da masa alƙawar idan zaije Plateau zata rakashi ,dan kwannan zaiyi tafiyar dan awajan akin da aka turashi can dan yayi wani bin cike,ko dama yace zai je da ita amma bata amuntaba saboda alokacin ne zasu fara exmas amma yanzu ta amince masa.....to kuma ban san wani za'ayiba tsakanin exmas da tafiya.
Da safe da zai fita aiki ya ajeta kan hanyar gidan su,itako ta ƙarasa da ƙafa dan banisa da wurin da ya aje ta.
Da sallama ta shiga aikuwa ƙanninta najin muryar ta suka fara mata oyoyo,sosai suka ji daɗin gani Yayar tasu.
Bayan sun gama gaisawa da ƙannenta kana ta ƙarasa wajan iyayinta wanɗanda tunda ta shigo gidan fara'arsu ta bayyana musamman Abbanta.
Gaishesu ta farayi suka amsa ciki da kulawa da son ƴar tasu ƙwaya ɗaya mace.
Bayan sun gama gaisawa suka shiga firar yaushe gamu haɗi da basu labarin karatunta.
Sai da fira tayi daɗi take gaya musu zata koma hostel da zama saboda yanzu karatunsu ya ɗau zafi kuma tana buƙatar tana tsu tayi karatu.
Sosai iyayinta suka gamsu da abunda tace kuma suka amince mata da haka.
Dan haka tace musu zatayi weekind anan sai Monday ta tafi ,amma data tafi sai bayan exmas zata dawo.
Ba abunda suka ce da ita sai fatan alhairi.
Bayan sungama fira da ita tashi tayi taje ɗakin da ya ke mallakin tane dan tana son ta ɗan huta dan jiya bawani barci yabar ta tayi ba,dan iya wuya yabata.
Tana shiga tayi kwanciyar ta dan ɗakin ko da yaushe Mama sai ta gyarashi sosai,dan haka bashi da wani datti.
Bata jima da kwanciya ba, bacci yayi awun gaba da ita.
Tajima tana bacci dan ko sallah bawace tayi tsaka nin azahar da la'asar dan ita Mama ta ɗauka ɗiyar ta ta na fashin sallah shiyasa bata tashe taba.
Aikuwa ba ita ta farkaba sai biyar saura,lokaci taga yatafi dan haka da sauri ta tashi taje tayi sallah.
Da dare har ta kwanta dan tana son tayi bacci da wurin dan ta tashi da wuri,sai ga wayar ta tafara ƙara,ɗan tsaƙi ta ja kana ta ɗauko wayar daniyar ta kashe,sunan da taga yana yawo saman screen ɗin wayar ne yasa da sauri tayi picking ďin call ďin haɗi da faɗin, "Hayateenah".
Ba abunda yace da ita sai ki fito gani aƙofar gidan ku.
Lokaci ɗaya jikin ta ya ɗau karkarwa muryar ta na rawa tace,"kayi haƙuri yanzu Abbana yana gida kuma bazai barni ba".
Tsawa ya daka mata yace, "minti biyu nabaki kifito dan bana son yawan magana".
Haƙuri ta fara bashi kafin ma ta ida faɗa har ya kashe waya sa.
Jikinta na karkarwa ta ɗau hijab tasaka kana tayi ɗakin Mamar ta.
Da sallama ta shiga tace Mama zanje gidan su Safiya na karɓo wani book ɗina ina son karatun shi a daren nan".
Mama tace, "a'a ba zaki jeba kibari nasa ƙaninki yaje ya karɓo, amma bake ba".
Mama tana ce baza taje ba ita ko Hafsa tana ce sai taje dan har kuka sai da tawa Mama.
Itako Mama tace taje amma da ƙaninta zasuje,ban dan taso ba haka ta aminta tace tayar da suka fita ita da ƙaninta Marwan.
Har zasu fita tace, "Marwan kaje ɗakin ku ka kwanta dan naga bacci kakeji".
da yake ɗakin nasu asoron gida yake.
Yace, "eh Aunty bacci nakeji".
Sai da tabari ya shiga ɗakin su kana ta fito ta sameshi amota.
Ahankali ta buɗe marfin motar ta shiga,haƙura ta bashi na jimawar da tayi bata fito ba.
Komai bai ce mata ba yaja wota jikinsa ya fara kissing ɗinta haɗe da sanya hannusa cikin rigar ta yana shafar dukiyar fulanin ta,sosai yayi romance ɗinta acikin motar kan ya ƙyaleta.
Wayar sa ya ɗauko ya shiga gallery ya kamu wani videos yayi playing ďin ɗaya yaba ta yace ta kalla yadda sukeyi haka zata mishi yanzu.
Jikinta na karkarwa ta karɓa ta fara kallo,dan har tasu tayi masa magana taga ba fuskar yin haka ɗin.
Bayan ta gama kallon abunda ya bata itama tamishi yadda taga sunayi,sosai yake jin daɗin abunda take masa dan sun kusan kai sha biyu bai tafiba.
Kuka ta fara yi masa kana ya yarda ya ƙyaleta amma bandan ya gajiba.
Abunda yasu mata ya bata yace kafin ta kwanta tashi zata ji daɗin bacci.
Amsa tayi jiki na rawa tayi masa sallama ta shige gida.
Koda tashiga gidan Mama batayi bacci ba tana nan tana safa da marwa atsa kar gida.
Kallonta Mama tayi da kyau kana tace, "me ya tsaidaki?ina kuma Marwan yake?".
Alamun rashin gaskiya suka bayyana afuskarta amma sai ta wayen ce tace,"Marwan ya shige ɗakin su yanzu,dan bacci ya fara shiyasa na kaishi ɗakin su.
Mama tace, "tau ina book ɗin da kika karɓo?".
Jikin tane ya fara karkarwa sai kuma ta nuna mata ledar da ya bata tace, "gashi".
Har Mama zata karɓa sai sukaji mutsin Abban Hafsa dan haka da sauri Mama tace ta wuce ɗaki dan bai masan ta fitaba.
Koda ta shiga ɗaki zama tayi tana mai dafe gaban ta saboda ta tsallake rijiya da baya.
Ledar da ya bata ta buɗe,kaza ce da wasu ƙwayoyi,kazar kawa tace ta aje ƙwayoyin dan tunda yake ba tasu bata taɓa shaba sai indai tana gabansa take sha,koshi dan bata son gani ɓacin ransa.
Da safe wajan ƙarfe goma bayan ta tashi daga bacci tayi wanka tana zaune tana shafe jikin ta da Vaselin,sai jin tayi ana mata sallama abakin ƙofar ɗakin ta.
Kanta ta ɗago dan taga wake mata sallama.
Aikuwa suna haɗa ido tace, "shin wai kece bangane muryar kiba?waya cemiki nazo hala ?".
Tace, "amma kya bari ko gaisuwa muyi kafin ki fara jerumin wannan tambaya.
Kallon ta safiya tayi tace,"yaushe kika dawo gida ai na ɗauka kin tare ne gabaki ɗaya a gidansa".
Sai da Hafsa tama ta kallon sama da ƙasa kana tace, "zan dai tare dan ko yanzu weekind ne nazu nayi natafi sai wanda yagani bari ya yaɓamin magana.
Safiya tace, "har yanzu bazan gaji da baki shawara ba,kice inda gaske yake yana sonki ya fito kuyi aure abunda yafi kenan dan wallahi ni ke nake tausayi nan gaba.
Aikuw rigama sukayi sosai dan duk lokacin da zasu haɗu da Safiya haka ne dan ita Safiya ba abunda ta tsana kamar yadda ƙawar ta kebin *UMARNIN SAURAYI*.....
*#Vote*
*Comment*
*Shere*
*© SUMY NA'IGE.*
*°🔘°UMARNIN SAURAYI°🔘°*
*1441H/2020M.*
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*
*NA MARUBUCIYA:-*
*SUMY M NA'IGGE✍🏼•*
```Ga masu buƙatar complete ɗin wannan book za iya nemanshi a wattpad👇```
~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~
*SHAFI NA 3📑*
*__________📖* Wacece Hafsat?.
Alhaji Usuman haifaffin ɗan garin sokoto ne shi ne mahaifin Hafsat, matar shi ɗaya Hajiya Fatima mutane ne musu haƙuri da jama'a dan tunda suke ba'ataɓa jin su ba,bare da maƙutan su, kowa lafiya suke dashi sai wanda ba'arasa ba.
Suna da yara shidda maza biyar mace ɗaya.
Hafsat itace ƴarsu ta fari kuma ita kadai ce mace,ta taso cikin gata da tarbiya mai kyau, yarinya ce mai natsuwa da kamun kai,sosai ta keba mutane girman su, bata damu da kowa ba dan ko tarin ƙawaye batayi, sosai mutane ke ganin girman ta,tana da ilimin addini dana zamani dai-dai gwar-gwado.
Tun tashin ta ƙwarta ɗaya ce ita ce Safiyya, koshi abunda ya ƙara ƙarfafa ƙawan cin su saboda school ďin su ďaya da Safiyya.
Sunyi primary school da secondary school duk atare kuma class ďaya islamiya ma haka,dan shi suka shaƙu sosai dan idan ka gansu za kace ƴan gida ɗaya ne,ko kayan sawa iri ɗaya ake musu sosai suke son junansu.
Lokacin da suka gama secondary school gidan su safiyya ba'abarin yaro ya ƙara gaba sai yayi aure amma saboda Hafsat zata ciki gaba Baban Safiyya yace ya barta itama sutafi tare.
Ba'a ɗau wani lokaci ba aka samar musu admission a Usumanu ɗan Fodiyo Unversity sokoto.
Inda kowa ce burinta ta zama doctor ta mata, dan ta taimakama ƴan wunta mata, kowa ce shine burin ta.
Haka suka ci gaba da karatu cikin kwanciyar hankali ko wace na karatu dai-dai gwargwado.
Ba wata matsala akaratun su har suka kai UG 3 going to 4 Hasfat ta haɗu da Anwar ,sosai ya nuna so gareta amma taƙi kulashi,ya sha wahala kafin ta kulashi dan yana nuna mata so bana wasa ba har ita Safiyya takan mata faɗa akan ta daina masa haka ta kulashi ko kaɗan ne.
haka dai aka samu ta fara sake masa fuska har soyayya ta kullu tsakanin su mai tsanani.
Abun har mamaki ya dawo ba Safiyya dan yanzu yadda Hafsat ke nuna ma Jawad so abun yana bata tsoro.
ana cikin haka ya kwanta ciyo sosai yake jin jiki dan haka Hafsat tagaya ma Safiyya tace ta raka ta su dubashi gidan sa.
Da ƙyar Safiyya ta yarda zata je duba sa.
Bayan Safiyya ta amince Hafsat takira shi tace za su zo duba shi.
Address ɗin gidan ya basu yace sai sun zo.
Bayan sun zo school sun gama lecture safe suka kama hanyar gidan sa dake arƙirla.
Basu sha wuya ba wajan gane gidan,dan maƙocin sa sanan ne ne agarin sokoto.
Tun kafin su ƙarasu ya faɗama maigida zai yi baƙi dan haka suna ƙarasuwa maigida ya kaisu har part ɗinsa.
Godiya sukayi ma maigadi kana suka ƙarasa ciki.
Kwance suka same shi anɗaura masa drip a hannun sa.
Da sauri Hafsa ta ƙarasa gareshi,irin yadda ta ganshi ai bata san lokacin da tafara hawaye ba.
Alama yayi mata da hannu ta daina kuka ,amma sai ƙara kukan takeyi.
Safiyya ce tayi mata magana tace ita kam sauri takeyi dan haka ta daina kuka su gaisa su wuce gida.
Dakyar ta daina tayi masa ya jiki ,Safiya ma ta masa kana suka ɗan zauna kaɗan har drip ɗin da aka sama sa ya ƙare,Hafsa da kanta ta cire masa kana sukayi masa sallama suka wuce gida ba dan ran Hafsa ya soba.
Bayan kwana biyu da zuwan su takira sa tayi masa ya jiki yace jiki da sauki amma har yanzu bai daina shan drip ba.
Sosai ta tausaya masa har tace zata zo ko da yamma ne idan sun gama lecture.
Haka kuwa akayi tace Safiyya ta rakata tace itakam bazata koma dubin saba tunda taje.
Komai Hatsat bata ce da itaba dan ranta ya ɓaci akan abunda Safiyya ta mata dan haka tace ita sai taje amma idan taje gida ta faɗa musu sai yamma zata dawo dan tana da lecture ƙarfe huɗu.
Komai Safiyya bata ce da ita ba kowa ya kama gabansa.
Ita Safiyya tayi gida ita ko Hafsa tayi gidan saurayin tah.
Koda taje doctor na duba shi har yana bashi shawara yarinƙa cin abinci kuma ya rinƙa shan magani.
Bayan doctor ya fita Hafsat ta ƙarasa gareshi kamar zatayi kuka tace, "yanzu Hayat baka cin abinci,to ya kake so nayi, ko so kakeyi na kwanta?".....tana faɗa tana fitar da ƙwallah
Ahankali ya taso daga kwanciyar da yake kana ya ƙaraso gareta, handkerchief ya bata dan ta goge hawayen ta.
Bayan ta gama kana yadube ta da kyau yace,
"My sweet heart,bawai bana son cin abunci bane, a'a abinci sayarwa ne bana so ko da na hotel ne, shiyasa ban cika cin abinci ba".
Kallon sa tayi da kyau kana tace,
"yanzu meza kaci?".
Yace, "zan sha lemo sai nasha magani dan bazan iya dafa wani abinci ba bare nadafa".
Tambatar sa tayi inada kitchen yake ya nuna mata bata ce dashi komai ba, ta tashi tashiga kitchen ɗin ta kunna gas ta ɗura masa jallof ďin taliya wadda taji kayan haɗi.
Tana cikin aikin ya shigo,bata masan ya shigo ba dan baka jin mutsin ma tafiyar sa har yazo kitchen ɗin.
Tunda ya ƙarasu ya ƙife bayan ta da kallo yana ayyana wani abu aransa.
Kamar ana kallonta taji dan haka da sauri ta juyo dan taga wake kallonta.
Ido biyu sukayi dashi da sauri ta ɗauko mayafinta dan tasaka amma yayi sauri ya rikeshi kana yace,
"miye afanin rufewa tunda watarana yazama mallaki na".