Header Ads
Showing 33001 words to 36000 words out of 46028 words

Chapter 12 - YAR KWALLIYA COMPLETED Book by Husba'ahfama.txt

Ads the beginning of article before Image

Unknown   

03 Jul 2024

439

Ads at the middle of Article

zoki bude mana mu fita dinda ke bazaki jeba ita zaka mayar ba muba


Abu tace bazata Bude mana bafa bari kiga


Abu da Binta suka danno kofar da jikin su danya Bude Amal na kallon su ta bude kofa ta fito daga gidan gaba rai a hade tabude kofar tasu sukuma suka fado kasa


Waiyoo kin gama karya mu Amal Wannan ai mugun tane kice zaki Bude mu matsa mana cewar Abu


Ko kulasu bata yiba tawuce ciki suka mike suna binta ajinda za a musu bita Amal ta shiga suma suka shigo suna shiga aji suka fashe da dariya Amal ta kuma hade rai Abu da Binta suka sake tafiya


Malam yace Ku tsaya banan bane


Abu tace banan bane kamar ya mufa munsan a binda mukeyi matsa mu wuce


Yace da ganin Ku gudowa kukayi yanzu haka suna can suna neman Ku


Binta tace suwa ye suke neman mu da wani wandonka a yake daganima a bola ka tsinta


Yace Injiwa shi ake yayi kunsan nawa ake siyar wa kuwa koda yake bazaku saniba saboda a can babu


Abu tace can ina


Yace gidan mahaukata mana barina kirasu suzo su tafi daku kafin Ku fara duka


Abu da binta suka Ja baya suka dunkule hannu suna shirin kai mishi duka


Amal ta taso da sauri tace ko zan iya magana dakai


yace to ba matsala meye inajin ki


Tace ba mahau kata bane su kanne nane kabarsu su zauna inba hakaba hmm tsaf zasu dakeka wlh bakaga sun dunkule hannuba


Ya dago ya kalli hannayan su yagani adunkule "nagani amma meyasa kika barsu suna irin Wannan KWALLIYAR da shiga haka Wannan ai shigar qauyene


Zazu dena komai lokacine suje su zauna


Eh suje amma karsu sake Susa baki a abinda zan koya muku harna gama


Bokamai Abu Binta kuje Ku zauna


Binta tace Kibarmu mu hada mihi jini da majina muze wani cewa mungudo daga gidan mahaukata hi da yasa yagaggen wando ba mahaukaci bane sai mu








































New writer's


Hakan Take *husba'ahfama*🌹🌹💋


👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝
👠👠
👝


💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄


👝
👠👠
👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠




Written by *husba'ahfama*




43-44




Amal tace beyi karya ba ai shi gayu ne kukuma haukane


Abu tace Binta gyara kiga da alama harda ita zamu hada tintini nakeso na koya miki hankali kunyar hajiya nakeji shiyasa nake shiru


Yace Dan Allah ki bari na kirawo gidan mahaukata ina tantaman hankalin su wlh


Abu da Binta sukayi kukan kura sukayi kan malam bashiri Muta nan gurin suka rike Abu da Binta


Abu tace bakomai muna nan ai zaka kuma fadan wani abin mara dadi kaga yanda zamuyi dakai ke kuma zamu koma gida


Allah ya kaimu nima so nake na koya muku hankali kucakai kawai
Amal ta koma ta zauna
Abu da Binta suka zauna suma suna huci


Malam dayayi karatu saiya juyo ya kalle su sukuma kwafa kawai sukeyi Abu na Sosa hannu Amal rai a hade hararar su abu da binta take ta yi


Amal ta jiyo wata a bayan su tana cewa basuda hankali inba hakaba mezesa suyi yinkurin dukan namiji


Ta kusa da ita tace yan qauye ne bakiga shigar suba ba hankali bansan abinda zasu daukaba da waccan ta taho dasu ta nuna Amal


Amal tace ba laifinku bane laifin sune da basu kama Kansu ba har mata marasa aji irinku kuke gaya musu magana cemiki akayi bamu san komai ba mekalan dangi irinki


Ke banyi dakeba in banda shisshigi meye naki nasa baki dake nayi ni da yan qauyan can nake qucakai dasu nake kalan dangi kuma iyawane watama tayi mu gani


Amal ta girriza kai "a'a bada niba Wannan saiku dadinta nidai a gidan ubana nake ba wankewanke da shara nake yiba


Yarin yar ta fashe da kuka yanzu nizaki yiwa gori dan kinsan mahaifinki nadashi muma aibamu muka dorawa


kanmu talau Ciba dadinta ba a gidanku nake wanke wanke da sharaba balle kifada min magana


Abu da binta suka baro inda suke suka dawo kusada Amal dansu tabbatar da abinda sukaji


Amal tace Niban fada miki maganaba nadai tinatar dake ne idan kin manta koke wace shine kawai


Yarin yar tace wlh saigin gane koni wace da zaki fada min magana zakiga gatan me wanke wanke da shara


Abu tace Alhamdulillah naji dadin haka Wannan magana tamin dadi Amal matsa dan Allah kije ki turo duk wanda kika ga dama amma gashe da ki nuna mishi


Abu da Binta suka rufeta da duka duka bana wasa saida suka tara mata gajiya sannan suka barta


Malamin bita yayi iya yinshi akansu rabu basu rabuba saida suka gadama


Abu tasa i hu tace naji dadi wlh da wacce takeso itama mu Nada mata na jakine ko da wacca zata shigar mata


Kowa yace a'a


Binta tace shegu sunji tsoro dagun shigar mata dakun ga danyan kai


Yarin yar ta dago tana kuka tace ni kika yiwa haka ko bakomai kamar ni kucakan nan zasuwa haka gaskiya na fado idan bandau mata kiba


Abu tace dama dukan be ishe niba dan Allah kidau mataki ni zan iya sugun nawa akan kidau mataki


Base kin tsogun naba nariga nayi niya kuma sai nayi ta Ciro waya tana yauki jiki yayi tsami takira kannen ta tace su daho ta kashe waya


Malam dai abi mamaki yake gani "Allah yasa bani yaran nan zasu yiwa hakaba da an samu matsala ke ya nuna Amal yace zo


Amal taze

Yace wayan can yaran anyafe musu bita base sun zoba subari in anfara koyawa sazo


Amal ta jinjina maganar "nafada musu komai bazasu yarda su zauna agidaba indai ni ina zuwa karka damu hakan baze sake faruwa ba


Yace Nasani indai ta maganar ki zanbi amma sudinne kalli fa ki gani sun rabamin aji2 wancan nacan wancan nacan


kutsiri tsoma kawai sukeyi memakon su maida hankali a abinda ya kawo su kinga hakan be dace ba ko


Eh zan musu magana hakan baze sake faruwaba


Yauwa nagode meye sunan ki


Amal


Suna me dadi


Nagode Amal ta fada taje ta zauna


Abu da Binta sunsa 'yar mutane a tsakiya da tayi magana saisu dungure mata kai har aka tashi


Suna fita suka ga yan uwan yarin yar sunzo Abu ta kare musu kallo


A yasine "ni na dauka zanga wasu manya manyan mutane shine zaki turo min wayan nan da basufi nasa bulala na Zane suba


Yarin yar tace kibar rainasu barga ninsu sirara karfine dasu bana wasaba shiyasa na kira wosu


Binta tabisu da kallo 1bayan1 tazaga yesu ta tofar da yawu " nina dauka zanga rin dina guda shine zaki aiko saura yan nan


guda3 tomu maza ma 5 sun mana kadan a duka balle Wannan abin ta nuna kannenta mata da suka zo


Ke karki sake ki zage mu jikufa niba zan hada jiki da kuba Balle Ku goga min halin qauye da bulalana nazo na Zane ku


Gaskiya kin kyauta da kika rage mana aiki kika tahoda abinda zamu zaneki dashi cewar Amal


Yarin yar tace waime kuke jira Ku Dakar minsu indai kun cika kannena nane ku ciki1 muka fito daku kuramamin dan na tab batar da haka


Yaran sukayi kan su Amal Abu Binta
Abu da Binta tuni sukayi kukan kura suka rufar musu bayan sun gama dasu suka hada da yayar tasu Wannan karan harda Amal a dukan su


Abu tace Ku dena raina qauye duk abinda kuke takama dashi Akwai a qauye nasan ba zuwa wanke wanke da shara harna tsawon sati


Binta tace ba fita kice amuku ruwan zafi idan ba aso kujima a gida dan kar a kore Ku daga aiki


Suka je suka shiga mota suna dariya suka barsu a kwance


Haka suka jera sati1 suna zuwa bita wataran ayi dadi wataran kuma ba dadi dan kuwa su Abu ne suke nemo


fada wataran Amal ta tayasu wataran kuma tabarsu su cika aiki da kansu sun gama bita zasu shiga koya gadan gadan


Suka shirya tsaf dan tafiya Kaya iri1 suka saka


Abu tace nakagu naga munfara KWALLIYA kinga KWALLIYAR da nagani a wayar yar ajinmu irin na amaren nan yamin kyau sosai sai lokacin nasan asheni ba KWALLIYA nake yiba


Amal tace Alhamdulillah Gwanda da Allah yasa kika gane yanzu kya dena KWALLIYAR Aljanu ta bakin yaya Aqeel


Waaaa ba abinda zan dena harse na iya waccan tukun na kalan nayi saki na dafe Allah sarki nunar rana gidan ba dadi da basa nan wlh


Hmm yaya yace a siya muku waya ze tema kamuku sosai na fadawa daddy yace ze siya muku


Binta tace da naji dadi wlh dankuwa wayata cika zeyi da hotu nan abinci iri iri


Kura kyaci da Gashi sudai bazasu ciyuba saidai ki kalla da ido ki hadiyi yawu shine kawai
Amal ta fada tana dariya


Amal kenan lokacine da kanki zaki dena cemin kura niyanzu hanka lina ya kuma school wlh jibi zamu fara Exam


Abu ta zaro ido "hakane fa ni harna manta wlh idan mun dawo sai muyi karatu


Amal kallon su kawai take tana dariya "kaji student Allah ya te maka yasa Ku fito da saka mako me kyau


Suka ce Ameen


Binta tace mutafi karmu makara dan naga matar nan hakona kawai takeyi


Meyasa take ha konki baki ce mata tsaka ninki da abinci Akwai amana ba da zata ce miki haka Binta


Binta tace yauwa *point of correction* sunana *Fatima* ba Binta ba idan ya miki tsawo kice min *tima baby* zan amsa inata so na fada miki mantawa nakeyi


Amal ta zare ido ta saki baki ta zube kasa tana kallon binta " menake ji Binta kicemin bake kika fadi hakaba nidai banida matsalar kunne fa


Abu tace kunnan ki lafiyarsa kalau nima daga yau karki sake cemin Abu sunana *zainab* idan kuma zainab yamiki tsawo kice min *zee baby* duk1 ne Amal karkiyi mamaki *levels don change*


*Oh my God what a surprise* amma kun shammaceni Amal ta bisu da ido cikin mamaki






















New writer's


Hakan Take *husba'ahfama*🌹🌹💋


👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝
👠👠
👝


💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄


👝
👠👠
👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠


Written by *husba'ahfama*




45-46




Abu tace Shammata ba batun Shammata Anan makaranta fa muke zuwa taya zaki dinga gaya mana wani suna mara dadi ga namu na yanka


Binta tace Kalan yan ajinmu suji sufara kiran mu dashi ga yan makaranta da tsokana


Amal tace tab A she daddy beyi asarar kudin ba kukara kokari kufi haka Allah ya te maka


Suka ce Ameen mutafi


harlokacin Amal kallon su takeyi cikeda birgewa harsuka je suka dawo Abu baki falda maganganu taci Sa a hajiya na falo da sauri ta karasa gurin ta


Mommy kinsan me fuska nashan wuya Anan wlh kinga irin abinda A kanuna mana kuma wai duk a fuska ake amfani dashi


Binta tace kut fuska nashan wuya ko abinci nashan wuya mommy kinga irin kakalan da akewa abinci kuma idan angama ya tafi ciki


Abu tace injiwa kinga kayan KWALLIYAR da ta nuna nana ne shine zakice wani abinci karki damu idan aka siya min zaki gani


Binta tace ba wani nan ke kinga kayan banzan da aka zuba wa a girkin da mukayi yau ne tin ina fahinta harna dena saida aka gama naci tukunna na gane komai


Hajiya da Amal Suka sheke da dariya


Hajiya tace Allah binta da fatan dai yayi dadi


Sosai ma mommy zanmuku shi amma ba yauba


Amal tace harna kagu naga girkin daya tafi dake Binta saidai kinsan me yanzu kika fara ganin girke-girke iri-iri


Binta tace da naji dadi kinsan yanda nake son kirgin karyan nan kuwa idan na gama koya babban gidan abinci zan Bude fa kuma kuma zan koya muku


Abu tace nikuma gidan KWALLIYA kekuma Amal gurin dinki zaki bude amma muna kusa da juna kowa zekoyi abinda kowa ya iya


Hajiya tace insha Allah kumai da hankali a abinda kuke koya banda fada baruwanku da kowa


Suka ce to mommy


Abu tace mommy ai munyi sanyi sosai ma tambayi Amal a sati befi muyi fada da mutum 2 ko 3 ba aikin ga da sauki ko


Amal tace sosai ma yanzu dai gobe kushirya mu shiga kasuwa kowa ya siyo abinda akace musiyo naji kunyi shiru ko ba a ce Ku siya bane


Binta tace tafada mana yanzu na keso na fadawa mommy


Hajiya tace Amal idan kudin gurinki baze kaiba ki fada min na kara muku Abu Binta kuje kuyi karatu gobe jara bawa


Abu tace hakane bari muje


Amal tace kujirani muje kunayi ina jinku


Taho to suka tafi suna wasa da dariya hajiya ta kalle su tayi murmushi "Allah ya raya minku


Abu da Binta suka jera sati1 suna zuwa zana jara bawa sai su raba dare suna karatu Amal dakinsu ta dawo da kwana tana


temaka musu saboda ita jami'a take zuwa hankan yasa su Abu da binta suke fahintar abinda suke karan tawa hakan


besa sun dena zuwa koyan KWALLIYA da girkiba sun bawa komai lokacin shi jiran ranar da za a basu hutu da saka


makonsu suke jira duk sunbi sun hana Amal sakat daga sun tuno saisu ce mata na nawa zamuzo sai tace musu na 1


Binta tace Amal ni saina ga kamar ba gaskiya kike fada manaba


Amal tace ban fa himtaba kodai duk irin karatun da mukeyi yatashi abanza


Abu tace kamarya yatashi a banza bam fahim taba


Kin fahimta hankali kawai zaku raina min woto idan munyi karatu idan kunje makaranta sai kuyi wasa ko


Binta tace injiwa bakiga yanda muke cika paper ba


To idan hakane karku sake damuna kusa a ranku cewa zaku fito da saka mako me kyau kunga ne ko


To munji


Yau zamu gama namu jara bawar natafi


Saikin dawo Allah ya bada Sa a


Ameen nagode muku


Tashirya ta fita Amal na fita suka shirya zasu tafi makaranta dakin hajiya suka je suka sanar da ita tai musu addu'a Suka wuce makaranta


Suna shiga aji yan ajin suka Sa dariya Abu da Binta suka kule suka basar suka samu guri suka zauna duk wanda ya juyo ya kalle su saiyasa dariya abinya ishi Abu


me kuke nufi da mune dazaku kalle mu kusa dariya ko kungamu da wata makusa ne hannune daku muma muna dashi kuna da kafafu muma muna dashi to meye na dariya


Binta tace Rabi dasu DA alama sai mun dagargaza bakin su tukunna zasu gane naga dan rainin hankalin da ze kuma dariya Anan inbamu koya mishi hanka liba


Tana gama fada suka Sa dariya


A zuciye Abu da Binta suka yi Kansu zasu daka


Malamin su yace karku fara kutsaya tukun na


Binta tace amma malam tinda muka shigo suke ta mana dariya dube mufa kaga meye abin dariya a jikin mu


Yace kume yasa kuke musu dariya
Yan ajin basu ce komai ba sai dariya da sukeyi


Hakan ya kara konawa Abu da Binta rai


Malam matsa kar jini ya tabaka dan cikin ajin nan yau ba wanda ze fita cewar Abu


Yace meyasa kukeda saurin fishi ya fada yana dariya


Binta tace harda Wannan abin a kara bata mana rai Abu me muke jirane


Yace A'a ku Tsaya ni da kaina zan fada muku da lili an hada dika aji 2 a nan ne saboda wani abu


Meye shi ayi a fada mana hannuna na kai kayi wlh zan fasa baki cewar Abu


Yace Bakinwa dafatan dai ba nawaba a ss1A zainab kece kika dauki na1 A ss1B kuma Fatima kece ta 1


Yana gama fada yan haji suka tafa musu "suka ce Wannan shine abinda yasa muke muku dariya murna muke tayaku
Abu da Binta baki harkeya suka koma suka zauna


Yace ga result dinku kukai gida


Suka ansa suna murna baki yaki rufuwa


Ana tashi me mota ya daukesu ya maida su gida yana a jiyesu suka fella da gudu suka shiga gida suna shiga


suka samu hajiya da Amal a falo sai kuma suka canza fuskar jiki a mace suka zauna


Amal tace meya faru kardai kuce min kunfadi a jara

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads