Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 46028 words

Chapter 5 - YAR KWALLIYA COMPLETED Book by Husba'ahfama.txt

Ads the beginning of article before Image

Unknown   

03 Jul 2024

430

Ads at the middle of Article

bude musu mota yace su fito


Koma gana Abu da binta sun kasa Tsaya wa sukayi suna kallon gidan babban gidane tsayawa fadan haduwar gidanma qauyan cine


Amal da hajiya mariya matar Alhaji nasir da gudu suka fito


Amal da gudunta ta taho zata rungume su tana zuwa taji kanhin tiraren jikin binta da Abu a haka ta rungu mesu tana murna


Amal tace sannunku da zuwa tinda nasamu lbr zuwanku na sa aka gama komai da wuri kuzo mushiga ciki kuyi Wanka kuci abinci


Abu tace Wanka tab bakiji kanhin tirarena bane


Amal tace banjiba saidai naji wari


Abu ta dunkule hannu zata kaima amal duka binta tarike hannun


Tace Abu gidansu kika zofa kiganar da ita idan taki ganewa saiki ragargaji bakinta nida kaina zan tayaki


Abu tace kinci sa a kufa yan bin tsiyata daku hirme warin da kikaji ba wari bane qanhine zokiji Amal ta matso Abu tace rabona da wanka harna manta


Hancin Amal ha toshe har Abu ta gama magana


Amal tace naji kuma na gane kuzo mu shiga ciki




























New writer's


Taku *husba'ahfama*🌹🌹💋


👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝
👠👠
👝


💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄


👝
👠👠
👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠



Written by *husba'ahfama*




17-18

Abu da binta suka kalli hajiya mariya suka ce ina wuni


Hajiya mariya tace lpy kalau


Abu tace naka gu naga cikin gidan nan yasin binta gani nake kamar na higa haljan na Yasin Wannan yayan Inna dan


bakin cikine yasan da Wannan gidan a duniya yaki yazo ya daukeni sai yanzu dana Riga na girma a qauye datini bansan kiba Binta

Binta tace nikuma naji dadi dabe zo ya daukeki da kina karamaba daya daukeki da kinmin bakin cikin zuwa binni dubafa kiga girman gidan nan bantaba Tina nin zanzo hiba yausaiga Binta a ciki


Abu da binta na tafiya suna hirar gidan Hajiya da Alhaji suka shiga Amal na bayan Abu da Binta

Amal tace kushiga mana


Abu da binta suka kalli juna tiles ne baje a falon gidan Binta tasa kafa Abu matasa suna tafiya santsi na jansu suka zube kasa


Abu tace daga nan bazan dara ko inaba


Binta tace nima haka muna tafiya yana janmu dan hihigi


Abu tace gaya mata dai Binta kalli kiga hoton ki a nan tanuna mata tiles din dake kusa da ita


Binta tace hi Wannan banda tafiya da mutane har hoto yana dauka laaaaaa kalli kiga kema gaki a nan


Amal tace dan Allah Ku bari tiles ne baya tafiya da mutane kutashi kuga


Abu tace Yasin daga nan bani zuwa ko ina bayan a gabanki yatafi damu bakice komai ba


Amal tace to shi kenan zan mishi magana yanzu kutashi


Binta tace kai Nifa jinake kamar nakawo kaina inda zan sha wuya daga zuwa naci karoda Wannan abin ze tafi dani gaba kuma mezan gani


Amal tace ba abinda zaki gani kuma nadau Alkawarin yiwa komai na gidan nan fada


Abu tace dagaske


Amal tace dagaske mana nidaku yanzu kawaye ne kutashi


Abu da binta suka tashi suka tsaya Cak ganin basuda niyar tafiya yasa Amal ta shiga tsakiyar su ta rike Hanna yen su tafi dasu ta zaunar dasu a kan kujera ta kunna musu kallo


Amal tace ga kallo na kuna muku kuyi ina zuwa bari nakai muku kayanku dakin ku yanzu zan dawo


Binta sukayi da kallo basu ce komai Ba suka maida hanka linsu kan kujera suna daddan nawa suka shafo tiles din


Binta tace Abu kinsan me Wannan shine Aljan nar duniya da malam rabi'u yake fada mana kintuno


Natuno mana saidai kinsan me yanzu kanhin titaren jikin mu zeyi Amfani sosai ma cewar Abu


Binta ta kalli TV tasa ihu tana nuna shi da dan yatsa


Abu ma ihu tayi


hajiya, Amal, da yan aikin gidan Asibi da kande suka taho gurin su da gudu


hajiya tace Abu Binta lpy meya faru


Abu tace hajiya Aljanune suka Bude mana ido muna kalla mukaga wani gabjejen kato ya kaiwa wani nauhi sai
dukansu yake daga karshe ya


dunkule hannu zekai mana nauhi kamar haka Abu ta dunkule hannuta tayo saitin hajiya hajiya ta sunkuya Abu ta samu kaiwa Asibi naushi a baki


Amal tace Abu kinfasa mata bakifa


Hajiya tace nashiga3 alhaji kakawo mana aiki


Binta tace ba laifinmu bane laifin Aljanun canne susuka Ja komai harmu har doke doken mu munga wayanda suka fimu


Amal tace Asibi muje ciki yi hakuri


Hajiya tace ku bata hakuri


Sukace yi hakuri


Hajiya tace ba aljanu bane kuje Ku zauna


Binta tace tab babu inda zani sun dunkule hannu zasu nau hemu mun kauce kice mu koma


Abu tace fada mata dai ga hican yana kallon mu da alama mu yake jira muna zuwa hi kenan ba lbr


Hajiya taje ta kashe TV tace kuzo kuzauna nakoresu sun tafi


Binta tace gaskiya a canza mana gurin zama sabo aljanunnan zasu dawo inada tabba cinhaka


Amal tazo tace kuzo muje
Amal ta kaisu dining


Abu tace ina ne nan kuma nasaba ganin idan za ayi tafiya sai anhau mahin Ku kuma da kafa a ke zuwa nan


Amal tayi dariya tace bawani tafiya bane me tsawo shiyasa kika ga haka


Binta tace Abu Yasin idan Akazo rabani da Wannan Aljannar za a shawuya dan nahigo kenan ba inda zani nida *DARAUDAU* sai ziyara


Abu tace ke kenan ni ko ziyara bazan jeba duk wanda ya matsu yazo ya ganni damuwata 1 yaya Nura,inna da baba


Amal tace Ku zauna muci abinci bayan mungama na zagaya daku kuga dakin Ku da gidan gaba 1


Abu tace bayan nan akwai wani unguwar da zamu tab ba inda zani idan bada jirgin yan binni ba


Amal tace shikenan dai Ku zauna zansan abinyi
Amal ta zuba musu taliya da miya da na man kaza


Tinkan Amal ta gama zubawa Binta take hadiyan yawu tana gamawa Binta ta danki naman kaza tana ci Amal kallon su kawai takeyi tana dariya


Abu taliyar take kalla fuska a yamitse tace yan binni da kwada yintsiya tsutsar ma cikuke


Abu ta kalli binta dake danbe da naman kaza


Amal tace Abu ba tsutsa bane taliyane yanada dadi sosai cikiji


Kai bada niba ko a qauyan mu daga akuya sai kaji zabo tantabara agwagwa sune Abinda nasan Anaci banda


tsutsa kikawo min tuwo danmalele ko dan bagalaji waiyoo dadi saikin bani lbr cewar Abu


Amal tace kici Wannan yanzu kafin nasa a dafa miki abinda kika lissafo


To bari na gwada
Tasa hannu ta debo taliya takai baki ta fara tauna ta furzar da shi


Tace tab Yasin bazan iyaba kibani tsutsa da ranhi da komai inaci yana motsi gaskiya yan binni bakuda tausayi


Abu Wannan fa ba tsutsa bane kamar yanda kike Tina ni amma Bakomai muje kisami Asibi kifada mata abinda kike so a dafa miki


Sai lokaci binta ta dawo cin hanka linta bayan ta cinye kaf kajin gurin tana gyatsa tace dadi binni wai bani komawa


ko ina zama dis saita fashe dakuka waiyoo umma tana can tana fama da tuwo tafada da muryar kuka


Ta kalli abincin da kyau ta fasa kara ta koma bayan Amal
Binta tace gaskiya bazan iya cin tsutsa ba nadai ci kaza zan iya zama daku amma abinda nake ci kubakwa ci shine kawai matsala


Amal tace karki damu shima zaki saba dashi zo muje


Takaisu gurin Asibi suka fada mata abinda zasuci tace su bata lokaci kadan zata dafa ta kawo musu suna fitowa daga kitchen


Amal tace kujirani Anan karkuje ko ina ina zuwa nazo na za gaya daku

Amal ta tafi


Abu tace mutsaya kar muje ko ina karya ma kenan binta biyoni


Suka fara tafiya suna Kalle kalle
Abu kinsan me fasa har kawunki a dakuna ta kare kalli kiga irin dakunan dake gidan nan nasani mutanan garin nan


gaba1 Anan suke kwana sun fita Neman abinci anjima zakiga gidan nan yacika da mutane


Abu tace Yasin be birgeniba dayabar su Anan daya musu a wani guri daban sukuma su zauna Anan


Binta tace Abu kinji abinda nake ji kuwa


Abu tace naji wakar daga daku nan nan2 suke fitowa saidai ba irin wakarda mukeyi a dandali bane Wannan yafi dadi Yasin
Tana fada tana rawa


Binta tace sosai ma bazaki hadaba binni yafi qauye kalli gidan nan kamar gidan sarki hiko me gari gidan muma yafi nahi kyau


Abu tace nidai zan higa dakin nan naga waye a ciki ke kuma ki duba dakin nan


To hi kenan
Abu ta Bude tana lekawa da bataga kowaba saita shiga sautin wakar nashigarta tafara rawa


Binta kaitsaye data Bude ta shiga lemo ta gani a ajiye a cikin Kofi ta dauka


Tace giyar yan binni barina sha abina meyafi raina ba yaya Nura balle yamin fada cewar Binta takafa kai tana sha tace dadi gaba daya zan shanye takai baki tana sha


Me zan gani haka yadaka mata tsawa yace me kikeyi Anan cewar Arif


Binta najuyowa saboda tsoro ta fesa mai lemon bakinta


Kai keee ni kika fesawa lemo wacce ke tukun nama dahar zaki fesa min lemo kinsan koni waye kuwa cewar Arif


Binta tace kokai waye be dame niba wa yace ka tsora tani


Arif yace haka zakice ko


Binta tace kwarai da gaske


Arif ya nufo inda take yace ke warin me kikeyi


Binta tace kut Yasin yanzu bakinka zeyi jini indai kasake cewa wari kudama yan binni kwai rainin han Kali


Arif cikin tsawa yace fita kona dakeki kowaye ya kawoki gidan nan ma oooho


Abu rawarta kawai takeyi tsabar dadin wakar yasa ta danne danne harta kara sautin wakar


Waye waye a nan Yaji ba a amsaba yace sister ba a amsaba yace Amal shiru saiya fito da kanshi


MaMaki yakeyi yanda akaita shigo yaje ya kashe wakar yace me kikeyi Anan fuska kamar Aljana kifadamin Aqeel ya fada cikin tsawa


Abu tana rawa dukda ya kashe wakar take cewa duk inda ake kida da waqa kirana ake dan haka wakar kace ta kirani


Aqeel ya toshe hanci kinga dadawar cikin gida zaki kai sune masu amfani dashi ba niba


Abu tace a ina kaga dadawa kuma kanhi dai gaskiya kanada babban sa'a tinda kaji kanhin tirarena


Aqeel yace tirare karkice daga jikinki warin nan yake fitowa


Wari Yasin karka bari na fara dakai karka sake cewa wari kanhidai


Wari ko kanshi beda meniba fita daga dakina kokuma na yankaki


Eh yankani zaka aikata dantinda naganka naji tsoronka Ashe kisa kake


Aqeel ya dauko wukarda ya yanka lemo dashi ya rike a hannu


Arif yace bazaki fitaba ko duka nakeyi kuma dukana yana karya mutum koma ya mutum


Eh karka kasheni zanfita


Arif yace fita cikin sauki kona dauko abinda nake duka yanzu na fasa miki jiki


Abu tace kakasheni a kasheka amma dai kabarni darai zan fita


Aqeel ya biyo abu da gudu Abuta fito
Arif yabiyo Binta da gudu Binta ta fito


Abu ta kalli Arif
Binta ta kalli Aqeel


Atare suka kurma ihu mai kara suka rungume juna

Abu na nuna Arif
Binta na nuna Aqeel




































New writer's


Taku *husba'ahfama*🌹🌹💋


👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝
👠👠
👝


💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄

👝
👠👠
👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠




Written by *husba'ahfama*




19-20






Gaba daya yangidan suka fito sukazo gurin


Amal tace Abu Binta lpy


Abu cikin muryar tsoro tace kalli kiga


Amal tace nagani yaya Arif ne


Binta tace gaskiya bazan iya zama a gidan nan ba gida ya cikada Aljanu biyoni yayi yakoro ni ina fitowa na ganhi a Wannan daki


Harlokacin suna kankame da juna


Amal tayi dariya tace laifinane daban gaba tar muku da suba kutashi kugansu dakyau


Abu tace kinga bazan iya hada ido da nunar rana ba kinsan meya cemin kuwa


Amal tace kome yace miki yafada ne kawai ba da gaske yakeba kutashi mana


Aqeel yace karma su tashi beda meniba Aljanu mutane duk yanda suka dauka dai daine


Arif yace yarin ya bakai lemo na ajiye naji wayata tana ringing naje dau kowa nasamu ta dauki lemon tana sha


Amal tace yaya dan Allah kubari ya wuce Gashi yanzu kun tsora tasu


Aqeel yace Dama atsorace suke inba hakaba meye abin tsoro dan Arif yafito daga dakin nan Nina fito a Wannan daki


Hajiya tace amma saiku duba cewa basu sanku yan2 bane yaba zasu tsorata ba kamar ku1 kayanku iri1 sannan kuce meye abin tsoro


Amal tace Abu Binta wayan nan yayyu nane su yan2ne Yaya Aqeel da yaya Arif kuma yanzu sun zama yayyinku


Abu tace tab bahi kuka dauka tinda kuka tsorata mu saina rama yasin


Aqeel yace aikin gama ramawa Wannan kwalliyar taki kadaima abin tsorone dana ganta fa sanda na tsorata saina dake kwai nai mata magana


Amal tace haba yaya Aqeel meye abin tsoro a Wannan kwalliyar kuma


Arif yace bazaki ganiba ai tinda ancika miki burinki ankawo miki qawaye ko saida kawayan naki wari sukeyi dan haka Akwai aiki a gabanki


Binta tace kut da alama yanzu baki zeyi jini suwaye suke wari


Abu tace barsu dani nice nan daidai kai nunan rana dani kake magana bawai kai makahiba ko a kaina dakai zan rife ido namaka abinda nakewa maza a qauyen mu Yasin


Aqeel yace Amal kinyarda cewa kinada aiki wacce macace zata Tsaya yin fada da namiji inba kucakaba dawani fuskarki dayaci wuwar kwalliya kamar wata Aljana


Arif yace maza kuce zakuyi abinda kukeyi a qauye ne idan kukayima dariya zasu muku masu fada da maza Anan abuhu ake sasu a kulle aba kura


Abu tace Amal kike kowa sudai wayan nan nunar ranar babu wata magana me dadi a bakinsu inaso ki fada musu cewa karsu bari nafara dasu banida kyau


Aqeel ya hade rai yace kifara damu kigani kucaka qazama kawai kika kara ce mana nunar rana saina zubar miku da hakori


Yana gama fada suka shiga daki suka rufe


Abu tazube kasa tana tumami tana dukan dakin Aqeel tana cewa Yasin zan samu lokacin ka tinda kace min kucaka mun kullada kai Yasin


Amal tace yi hakuri Abu baze sakeba daso kiji


Binta tace haba Abu kinbani kunya wayan nan zaki Tsaya kinawa haka sekace bakece Abu ba


Abu tace hakane kuma natahi


Amal tace kokefa kuzo muje dakin Ku


Suna tafe suna hira harsuka karasa qanhin jikinsu na dukan hancin ta tin tana daurewa harta kasa ta koma toshe hanci


Amal tace ga dakin Kunan amma gaskiya kusamu kuyi wanka kanshin tiraren naku yana damun mutane kusamu kuyi wanka koda ya ragu


Binta tace tab waikinji Abu


Abu tace munfiso kanhin yafi hakama tinda mun higo binni baraini tsaka ninmu daku


Amal ta zauna akan kujera tace kuyi wanka nikuma zan kawo muku tirare ma kanshi wanda idan kunfesa kunje guri kanku karasa tiraren yarigaku karasawa


Binta tace bar abinki bama so kanhin tiraren mu basemun fesaba kukuma kince saikun fesa na mune na gaskiya naku kuma jabine


Yanzudai Ku zauna Ku huta ina zuwa cewar Amal


To sukace gaba dayan su


Binta ta tashi tana kalle kalle ta Bude bandaki ta shiga tana kalla wanda ya mata kyau kuma ta taba


Binta tace Abu kinsan me su yan binni basa kahi


Abu Tataso tazo gurinta tace meyasa kika ce haka


Binta tace kalli kiga daga randar yan binni sai madubi da baho ba gurin kahi muma daga yau munde na kahi


Tace tab gayu hikenan dai binta kinga


Binta tace bakin gurin ne kina tabawa ze fara magana hiyanzu Ankulle bakin hi bazeyi maganaba


Abu tace Niko zanso naji abinda zece ta danna gurin


Ruwa ya fara zubowa daga sama binta tasa kara
Amal ta taho da gudu


Tace lpy


Abu tace kinga bada munaba amma ana ruwan sama


Amal tace tabawa kukayi Wannan da kuke gani idan zakuyi wanka zaku kunna shi
Tanan ruwan ze Zibo


Wannan kuma abin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads