Header Ads
Showing 42001 words to 45000 words out of 46028 words

Chapter 15 - YAR KWALLIYA COMPLETED Book by Husba'ahfama.txt

Ads the beginning of article before Image

Unknown   

03 Jul 2024

443

Ads at the middle of Article

Ku matan aure ne


Abu da binta sukayi dariya a tare sukace "mun fiki sani tinda igiyoyin na kanmu bari muje dakin mu muna zuwa


Amal tace to


Suka fita tabi su da kallo


Karfe 4 nayi suka shirya tsaf cikin material Ja sunyi kyau sosai suka fito falo suna kanshi tirare Arif Aqeel da
Hajiya na zaune a falo tinda


suka fito Suka dauke hankalin Aqeel da Arif duk wani motsin da Abu da Binta zasuyi akan idon su Abu da Binta suka gaida hajiya ta amma


Har kun fito ina ita Amal din


Abu tace tana ciki yanzu zata fito ta gama shir yawa


Hajiya tace bari naje gurin ta
Hajiya ta tafi ta barsu a falo


Aqeel yace ina zaku baku sanar da muba yanzufa ba kamar da bane kuna karkashin mu duk inda zaku sai da sanin mu idan mun amince kuje shikenan idan bamu aminceba kuma Ku hakura


Arif yace fada musu nasaki baki ina kallon ikon Allah Baku tam baye muba zaku fita da izinin wa zaku fita


Abu da Binta suka kalle su basu ce komai ba


Arif yace kuyi magana da izinin wa


Binta tace dan Allah bana son haya niya surutunka ze samin ciwon kai mun fadawa mommy shi kenan


Aqeel yace mommy ce take auren Ku da zaku tam bayeta ina zaku jema tukun na


Abu tace bikin kawar mu sannan kuma ba a gidan Ku muke ba balle kuce dole sai mun gaya muku a gidan mu muke


Arif yace tanan kuka fito to shikenan zamusa a gobe kutare sai muga idan kun tare kai tsaye zaku dinga fita


Binta tace tab babu inda zamu je muna nan Anan zamu zauna dakuke cewa mu tare qazamai kucakai damu zaku tare a gidan Ku a'a ajinmu bekai nan ba


Aqeel yace injiwa kunkai har kunyi yawa zamu yiwa mommy maganar tarewar dan Allah kuma Ku goyi bayan haka kunji


Abu tace waaa mu ba abinda zamuce kuda kuka baro zancen kusan yanda zakuyi yama za ayi kucakai masu warin mushe Susa baki a maganar Ku


Arif yace dan Allah Ku mance da Wannan maganar tsautsayine da subutar harshe yanzu kun wuce haka sai dai a jera Ku da manyan mata masu ji da Kansu


Binta tace kinajin dadin baki irin nasu ko maganar da kake fada bekai zuciyar kaba kafada ne kawai dan ka ganmu kuma maganar ka bazeyi aiki a kan muba


Aqeel yace ba maganar dadin baki Anan kufus kan cemu kuskure mun Riga munyi kumance da baya yanzu a kar ka shinmu kuke be dace muna fada kuna fada ba kunsan da haka tinda har sauka kunyi


Abu tace ko to shikenan kunga tafiyar mu idan ta fito kuce mata ta samemu a can dan kun bata mana rai bazamu jirata ba


Aqeel yace karku sake Ku fita bada izinin muba


Abu da Binta Suka kalle su


Arif yace bamu Baku izinin fita ba da ga yau Anan zamu fara gwada muku ikon mu a kanku


Ganin da gaske suke yasa Abu da Binta Suka kalle su suka koma ciki rai a bace dakin Amal suka je suka samu hajiya na dakin


Suka zauna rai a hade Arif da Aqeel Suka biyo bayan su dakin Suka shi ga rai a hade hajiya ta bisu da kallo daya bayan daya


Me kuka musu naga ransu a bace


Aqeel yace mommy kiji wani kwado fita zasuyi bada izinin muba mukace da izinin wa zasu fita sukace da izinin ki


Shine muka ce musu ke kike auren su mune nan maza jansu na aure ko sunki ko kunso ba a canzawa tuwo suna bazamu taba rabuwa da kuba


mutu karaba ko dan Wannan bazaku sassauta mana ba dan Allah Ku duba halin da kuke shirin jefamu mana Amal kince


mubar komai a hannun ki me kikayi a kai nayi zaton zanga sauyi Ashe wani sabon salon zasu fito dashi da ana tsaga zuciya damun tsaga kodan kuga gaskiya qaunar da muke muku


Arif yace irin qaunar da muke muku bamu taba nunawa wata mace ba dan'uwana yayi gaskiya Ku duba fusko kinmu shikadai ya isa ya gamsar daku


Hajiya shiru tayi tana jin ikon Allah a gaban ta suke furta Kalmar so da qauna


Kalaman nasu na faran tawa Abu da Binta rai "ko banza qauyawa kucakai sun kai matsayinda sonmu yake wa halar da Ku a zuciya gaskiya mun ciri tuta Abu ta fada a zuciyar ta


Abin kamar A film maza irinsu Arif ne suke qaunar mu mutanen da su kaje guri daban daban amma yanzu sun zabe mu sun kuma yi na am da zabin iya yansu gaskiya a jin-jina mana Binta ta fada a zuciyar ta


Dakin yayi shiru kamar ba mutane


Amal tayi matukar jin tau sayin yayyun nata cikin muryar kuka" Abu Binta lokaci na kurewa fa idan bamu jeba bazata ji dadi ba


Abu da Binta ko mutsi basu yiba


Hajiya rasa abin cewa tayi kallon su kawai takeyi


Arif yace da Alama Baku yarda ba ko to shikenan kuje sekun dawo duk abinda ya Sa memu kune sila


Jikin su Binta yayi sanyi
























New writer's


Hakan Take *husba'ahfama*πŸŒΉπŸŒΉπŸ’‹


πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ‘


πŸ’„πŸ’… *'YAR KWALLIYA* πŸ’…πŸ’„


πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ πŸ‘ 




NASADAU KARDA WANNAN SHAFIN GAREKU *mahaifana* bazan manta da kuba nagode da so da qauna hakika rayuwa bazeyi dadiba idan baku Allah ya kara muku lpy da nisan kwana Ameen πŸ’žπŸŽ‰πŸŽŠπŸ˜˜πŸ˜˜

YAN'UWA RABIN jiki πŸ’
Bazan manta da kuba


Alhaji Muhammad AUWAL
Anty hajara
Anty Aisha
Anty Fatima
Yaya ABUBAKAR
Anty halima
Kune jinin jikina rabin zuciyata ba abinda ze yiyu idan Baku Allah ya barmu tare🍾🍻😻



Written by *husba'ahfama*






55-60




Hajiya taja dogon numfashi "Aqeel Arif kum manta cewa ina gurin ne


Mommy Kiyi ha kuri gaskiyar zuciyar mu muke fada musu kila suyarda idan sunji cewar


Hajiya tace kuyi hakuri yanzu kubar su suje gurin bikin babbar qawar suce ita baza taji dadi ba idan basu jeba ina rokan alfarma a barsu


To mommy suje amma karsu dade saboda maza nasan baza su rasa maza a gurin ba koda yake suzo mu kaisu cewar Arif


Hajiya taci gaba da cewa Aqeel Arif zan yiwa su Abu magana zasu gyara insha Allah


Arif yayi wani irin murmushi "To bakomai Ku taho mu tafi


Abu Binta Amal Arif da Aqeel suka fito jiki a sanya ye suka shiga mota Arif ne yake tuka mota Binta a kusa dashi baya


kuma Aqeel da Abu sai kuma Amal da take gefen su suna tafiya suna satar kallon juna har suka karasa ba wanda yake


cewa komai suka fito harda su Aqeel suka je gurin Amarya taji dadin ganin su ta musu sauka ta mu samman Sukayi hotuna


Abu tace mata zasu tafi suka dauki kautar da Suka zo mata dashi suka bata Amarya taji dadin kyautar ta musu godiya


suka shiga mota suka dawo
gida suna dawo wa hajiya tayi kiran Abu da Binta tayi musu nasiha hakan ya kara kashemusu


musu jiki haka suka lallaba Suka shiga daki nasihar da hajiya ta musu na dawo musu
Suna shiga ana kiran sallah


sukayi sallah Suka kwanta wayo yinsu ya shiga kara ko da suka ga number ne ba suna suka ki dagawa saida number


ta damesu da kira tukunna suka daga sallama akayi cikin nutsuwa tareda kiran sunan kowan nen su hakan yasa suka kara gyara zama


Binta cikin mamaki tace dawa nake magana


Shiru yayi bece komai ba jin shirun yasa zata katse kiran yasa yace


Ni ne mosoyinki


Wa kenan dan sunada yawa
Sarai ta gane me magana


Mijinki Arif nakira ne na


Kafin ya karasa "ya wuce karka damu mune zamu baku hakuri


A'a Fatima mune muka jawo duk abinda ya faru da bamu furta irin kalaman da muka furta a kan kuba nasan daba za Ku mana haka ba kuyi hakuri hakan baze sake mai-maita kan shiba insha Allah


Dan Allah karka sake bamu hakuri mune ya dace mu baku hakuri baza mu sake fada kuna fadaba a matsayin mu na matan koba komai ya wuce zaku Sa memu yanda kuke so


Naji dadin jin haka yanzu yaushe kuke ganin ya dace Ku tare


Abu na gani a gefe daya tana waya harda dariya Aqeel sarkin zuciya yana ta tsara Abu


Aqeel yace zainab yaushe kuke ganin ya dace Ku tare


Abu da binta suka kalli juna
Kamar sunsan abinda aka fada mata shi aka fadawa Binta


Abu tace zamu fara waec da neko sai dai inmun gama tu kunna


Aqeel yace a'a zainab baza a yi haka ba kutare ba komai idan kuna gidan namu zamu barku Ku je Ku zana jara bawar Ku ba komai


Abu tayi dariya "na sani shiyasa nace Ku bari mu gama zanawa a gidan mu .mukanmu zamufi jin dadin haka


Aqeel yayi shiru "to badan munso ba dan dai kawai hakan ze faran ta muku shiyasa


Abu tace godiya Muke haka suka shafe a wanni suna hirar masoya kafin suka yi sallama da juna Suka kashe wayo yinsu suka kwanta bacci


Washe gari Usman ya sake kiran su Arif akan maganar Amal aqeel yace mishi karya damu Alhaji na kan hanyar


dawowa idan ya dawo zasu sanar dashi Usman yaji dadin jin haka sosai gurin hajiya suka je suka sanar da ita tayi farin


ciki da jin hakan bayan Alhaji ya dawo ya huta Aqeel da Arif Suka sanar dashi Alhaji Nasir ya yaba da hankalin Usman ya


kuma san mahaifin Usman shiyasa yayi saurin amincewa da su turo ayi maganar aure suna sanar da Usman Yaji


dadin jin haka dan haka ya turo iya yan Sa aka saka ranar aure wata1 Alhaji nasir yace baya son lokaci me tsawo


Hajiya na zaune a falo tareda su Abu Binta da Amal suna hira Aqeel da Arif suka zo suka zauna


Aqeel yace mommy me kuka fara yine akan maganar auren Amal dawani abinda zamu taya Ku


Hajiya dariya tayi tace munyi komai ranar kawai muke jira Da kuma fatan Allah ya kaimu da rai da lpy


Atare suka ce Ameen


Arif yace dama mun yanke shawarar kaisu su zabo abinda sukeso ne mommy shine mukazo muji ko kina da sako


A'a ni banida sako idan matan kune gasu nan Ku dauke su Ku tafi yanda kuke Sosa keyar nan nasan abinda ya rage ku tam baya kenan


Arif yace A'a mommy da bamuyi niyar tafiya da suba tinda kince suje shi kenan Ku taso ba komai


Hajiya tayi dariya "to shi kenan kuje Ku kadai su kuma Ku bar su Anan tinda badasu kukayi niyar tafiya ba


Aqeel ya za bura " mommy kinriga kin Sa musu rai ki barsu muje kawai idan kika hanasu baza suji dadi bafa


Amal Abu da Binta dariya sukeyi jin ga abinda suke so sai suce hajiya ce tace haka


Arif yace Ku taso mu tafi Abu da Binta kamar jira suke suka mike Aqeel da Arif na ganin su suka mance da hajiya da Amal


suka koma wa matan su suna tafe suna musu magana cikin rada suka yi hanyar fita ganin basu da niyar juyowa suyi wa Amal magana


Hajiya tace Amal din ta fita kenan


Aqeel a kun yace "kinga yarin yar nan ko mommy kina kallo ita na fara yiwa magana da magana nata da wan nan zaman da tayi yaci ace ta kai waje amma dube ta ki gani


Arif yace gaya mata wan nan san jikin naki ba inda ze kaiki gwanda ma ki dena gidan wani zaki yanzu idan kinje gidan Usman abinda zakiyi kenan


Amal baki ta saki tana kallon ikon Allah yanda suke shirin Dora mata laifi tana ji tana gani


Amal tace yaya dan Allah kun manta dani abinda zakuce kenan hasa Lima bada ni kuka yi niyar fitaba shiyasa suna tashi kuka tafi


Aqeel ya dawo kusa da ita ya zauna "Amal taso mu tafi zaki iya tafiya kona Goya ki abinda kike so mu muki kenan kadai


ba karamar yarin ya bace da zamu dinga yi miki magana cikin rarrashi idan zaki ki taho idan baza kiba gaba ta kaimu


Arif yace baza taba tace taho mu tafi tana bata mana lokaci


Injiwa yanda ba kwaso naje kamar naje na gama kome za ayi ko a siya nima a siya min


Arif yace kinga Usman Anan ne da zakice haka ba abinda zamu siyar miki idan kin bimu yarin ya kinje a banza


Bakomai nayi gaba Ku biyoni a baya


Amal ta bisu badan sun so ba haka Aqeel da Arif sukaita hade mata rai ko a kanta ita da Kansu suka gaji suka koma


yanda suke Kaya suka siya musu bana wasa ba daga Abu Binta har Amal suka biya ta gidan cin abinci sukaci Aqeel


da Arif sun zagaya dasu guri da ban daban dasu hakan ya kara saka sha kuwa tsaka ninsu da matan su suka fahimci junan su sosai


hakan yasa Amal ta dena jin kewar rabuwa dasu sai dare suka koma gida har dakin su Aqeel da Arif suka rakasu


suma suka wuce nasu dakin bayan sunyi sallah suka Ciro littattafan su suna karan tawa saura kwana 5 su fara waec




Bayan sun karan ta suka kwanta bacci saida safe suka Ciro kayan da maza jensu suka siya musu suna dubawa


Kayan nan sunyi kyau ko Binta


Sosai ma wai yau lpy kuwa Amal bata shigo ba ko duk baccin ne


Zo muje suna zuwa suka samu kofar dakin a Bude suka shiga kan gadon suka dira Amal a tsorace ta Bude ido


Abu da Binta suka Sa dariya suna ce mata matsora ciya


Cikin muryar bacci tace ba batun tsoro Anan koku nayiwa haka saikun tsorata ina nan lokacinda kuka zo dokan Ku su


yaya sukayi a kafa kuka ce barayi barayi Amal Allah ya Baku hakiri gidan Ku muka zo


Au abin yar Tina baya ne to ai shi kenan kije gaban yayyunki ki fadi haka Abu na gama fada tasa dariya daga ita har Binta


Binta tace dafa munyi hauka wauta iya san ranmu kunyi hakuri damu


Amal tace ni kanhin tiraren nan nafi so dama kunga biki ya maso yakamata kufara tanadin tirare na musam man danni da mutane tirare da ze fasa taro yasa a to she hanci


Suka kara fashewa da dariya
Abu tace wai na gode Allah na da na dena Wannan haukan koyan zu ya zanyi idan kanhin na Jikina


Amal tana dariya "gaskiya zan g
aya miki inda kina shiga suna to she hanci yanzu kam daki zasu miki su kulle ki saida mu Tsaya daga waje mu gaisa harda ke Binta


Bakomai tinda za kuzo mu gyai Sa meye a ciki kanhi rahamane ga Almiski a bakin mu


Tana gama fada suka Sa dariya


Amal tace dan Allah Ku barni haka kar cikina yayi ciyo kuzo muje muci abincin nasan kuma Baku Ciba


Yasin kuwa kamar kinsani ke muke jira mutafi


Amal tace Yasin din nan baze fita daga bakin Ku bako


Binta tace bama fada sai in munason Tina baya


To shikenan mu tafi


Suna tafe suna hira har suka karasa dining Suka ci abinci saiga Asibi da kande


Asibi tace Amal zamu fita bazamu dade ba zamu dawo ko zaku temaka kukula da girkin dana Dora


Abu da Binta kai a kasa


Amal tace Eh zamuyi sai kun dawo


Mun gode


Amal tace bakomai


Suna tafiya


Binta tace ni gaba dayama kunyar su nake ji wlh


Abu tace ke koni manya damu saboda qazantar mu su suka fara mana Wanka daga nan muka fara sabawa


Amal dariya takeyi "to meye a ciki kila masu sun manta da zancen kune dai Baku mantaba


Binta ta girgiza kai "ya zakice sun manta bayan muna tare saidai matan nan akwai karfi wlh wani riko da suka mana haryau mun kasa mantawa


Aqeel ne yakatse musu hirar su da cewa mommy gaskiya abinda ake mana a gidan nan be da ceba


Hajiya mariya fito warta kenan taji abinda yace saida ta samu guri ta zauna "da aka yi me fa


Suma zama sukayi
Arif yace mommy ya dace da auren mu da komai amma haryanzu muna tare daku kamata yayi ace muma muna gidan mu ko


Hajiya cikin jin kunyar maganar "Arif ban gane inda ka dosa ba fa ka fahim tar dani


Aqeel yayi gyaran murya "mommy kamata yayi wan nan abincin da muke ci Anan a gidan mu ake dafawa gaskiya ana hukun tamu da yawa


Sarai hajiya ta gane abinda suke nufi saita shashantar da maganar da cewa Amal Abu Binta horan yunwa kuke musu shiyasa naga suna rama amma a sanina ana dafa abinci kowa na samu garin yaya haka tafaru


Mommy bafa haka muke nufi ba fa muna nufin yakamata matan mu su tare a gidan mu horon ya isa haka


Ko to gaku gasu


Mommy ba haka ba fa munaso ki amince su tare yau


Hajiya tace yaushe kuka zama marasa kunya ne Aqeel Arif yanzu dan bakuda kunya ni kuke fadawa haka to kunjawa kanku bazasu tareba duk abinku


Aqeel a mairaice "mommy karkice haka mana ba dadi fa shikenan zamu zama masu biyayya a gareki duk sanda kuka ce keda daddy su tare dai dai ne


Arif yace amma

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads