Header Ads
Showing 24001 words to 27000 words out of 46028 words

Chapter 9 - YAR KWALLIYA COMPLETED Book by Husba'ahfama.txt

Ads the beginning of article before Image

Unknown   

03 Jul 2024

436

Ads at the middle of Article

kai hmm Allah ya temakeki mu kara haduwa saina zubar da hakwaran bakin ki


Yarin yar kuka kawai takeyi danta daku bakadan ba


Allah ya isa kuma saina turo muku yayana ainaga gidan da kuke


Shegiya wato binmuma kikeyi ko kufa yan birni kunada matsala Yasin sa ido ya muku yawa Wannan KWALLIYAR ne Baku taba ganiba


Niba KWALLIYAR Ku nake ganiba a bayan layin Ku gidan mu yake zakuga gatana cewar yarin yar


Binta tace kafin muga gatanki bari mubaki ladan gida sukai mata dukan tsiya ko tashi ma ta kasa


Abu tace barta haka mu koma gida sai anjima kuma zamu kara fitowa


To mutafi


Arif yana tuki yana waige ko ze gansu duk sun baza ido suna duba hanya ko zasu gansu


Abu da binta sukazo zasu tsallaka titi Abu kaitsaye ta tafi ko hanya bata duba ba motar su Arif ya taho da gudu ganin Abu da yayi yasa shi taka birki cikin sauri ya Tsaya


Aqeel ya Bude ya fiyo ya kaimata mari Abu ta gigice ta rasa inda zatasa kanta


Binta kura batama san anayiba me karas tagani yazo wucewa hanka linta ya koma gare shi


Arif Azuciye ya fusgota ya kaimata mari Gigi cewa tayi


Tana cewa gatan naki kenan badai kince abayan layi kikeba har gidanku zamu Yasin mudake ki


Jin haushin Abinda take fada yasa Arif ya kara marinta sai lokacin tagane wanda ya daketa


Ta fashe da kuka Abu ma kukan takeyi dan itama saida ta sake shan mari Amal takasa cewa komai kallon su kawai ta keyi tana kuka


Arif rai a bace yace Bakida hankali waya gaya miki haka ake tsallaka titi da kuka fito me kuka fito yi wakuka fadawa da zaku fito ke kuma kura daga


ganin A binci hankalinki yatafi dayanzu bamu bane wani dabanne yabita kanta ya wuce kiceme baki ganiba ko bakya gurin


Aqeel yadaka musu tsawa yace su shiga mota


Da sauri suka shiga suka zauna har lokacin basuce komaiba kuka kawai sukeyi
Arif ya kira hajiya ya sanar mata sunga Abu da Binta
hajiya taji dadin jin hakan


Arif fada kawai yake musu har suka isa gida


Amal da gudu ta tafi ta fada jikin hajiya tana kuka


Hajiya tace me kuka mata take kuka


Aqeel yace meze sata kuka inban da taba yaran nan da mukayi saboda ita kenan kar a musu fada idan sun yi laifi


Mommy dana sani ban bisu ba suna sane suka tafi dani dan su dakesu a ga bana nima tsoran su sukeso naji kuma naji tsoran naku Amal ta fada tana kuka


Hajiya tace Amal dolene Amusu fada idan sunyi laifi basuba harda ke kema yaiyan naki suna so su Abu su dena abinda sukeyi shiya Sa


Amal ta goge hawa yan fuskarta tace hakane to shikenan nina dauki nauyin gyara su Binta zasu dena duk abinda sukeyi insha Allah


Tana gama fada ta wuce dakin ta


Arif yace Lallai indan baki gyara suba su Sa koya miki hada sallah da rashin wanka wayan nan yaran kuma hmm


Hajiya taiwa su Abu fada sosai fadan yashige su sukai mata Alkawarin cewa bazasu sake ba


🤔 bari muga ko Abu da binta zasu iya cika Alkawarin da suka dauka🙄


Hajiya tace kuje kuci Abinci kuyi wanka malamin Ku yazo


Atare sukace to
Suna tafiya suna hararar nunar rana


Kwafa Aqeel yayi yace mommy duk sanda me KWALLIYAR Aljanu ta fado hannu na hmm ina tausaya mata


Hajiya tace yara ne sai hakuri


Amal na dakin Abu da Binta rai a hade sai Kada kafa takeyi


Sukazo zasu wuceta


Amal tace Ku Tsaya a koda yaushe ina zuwar muku da sauki saboda Ku ba kine amma kun kasa ganewa ko to


shikenan daga yau Anan tafiya ta daku ta canza salo muguwace ni banida kyau idan raina ya baci


Binta tace tomu ina ruwan mu canta matse miki


Amal ta daka musu tsawa tace haka kuka ce ko naji dadi kushiga kuyi wanka ko kuma ta zira hannun ta karkashin Gado ta Ciro wani shar beben kara tace idan na fara zaneku dashi saiya karye zan barku


Abu ta matsa kusa da binta take rada mata tace gaba daya yan gidan nan hawai niya ne kinga itama ta canza


Binta tace ya za muyi yanzu


Abu tace muyi abinda tace dankuwa bada wasa take ba


Amal tace kun gama shawara


Suka daga mata kai
tace dakyau waze fara shiga


Abu tace binta
Binta tace Abu


Amal tace ya isa nida kaina zan zaba Abu shiga ki fara yi kuma ki tabbatar kin goge baki Tsaya nafasa bari nakira Asibi ta Tsaya a kanku


Abu tace A'a karki kirata zamuyi tin rikon da tamin rannan haryau gurin zafi yake min


To shiga ki fito


Abu ta shiga tayi wanka ta goge baki tafito Binta ta shiga tayi ta fito dariya na kokarin kwacewa Amal ganin yanda suke tsoran ta saidai Ta dake taki dariya


Tabasu mai su shafa suka shafa suka dauki kayan da suka cire zasu maida


Amal tace mezan gani haka kayan zaku mayar sunyi datti gawasu kusa wayan can kuma za a kaisu wanki


Tab gaskiya a'a jiyafa muka sasu mudai kar a wanke mana muna sansu a haka to ko kayan mu se sunyi wata kafin mu wanke balle sabin Kaya hikuma saiya hekara


Ya isa Wannan a qauye kenan nan kuma birni ne dan haka kuyi abinda nace kafin raina ya baci


Haka suka dauki wanda ta basu suka Sa badan ransu yaso ba


Tace muje kuci abinci


Munkoshi baridai muyi KWALLIYA


Eh banyarda ba haka nake son ganin ku kuwuce muje malam kabiru na jirani mu


Abu zatai magana amal ta kafeta da idanu ganin haka yasa tai shiru har suka karasa gurin malam a waje suka ajiye mishi kujera sukuma suka zauna a tabar ma


Malam kabiru ya Bude Qur'ani yafara karan tawa Amal ce kawai take jinshi Abu da Binta hankalin su na wani gurin ji sukai garin ba dadi


Arif da Aqeel suka fito suka zauna gaba dasu kadan suna ganin su


Abu da Binta ganin su Aqeel yasa suka maida han kalin su gurin malam


Haya niyar me gadi da wasu mutane da basu san kosu wayeba Arif da Aqeel suka jiyo


Arif yace malam karka damu zamuji da komai kucigaba da karatu


Lokacin mutanen suka tunkude me gadi suka shigo


Arif yace lpy kuka shigo mana gida


Tan gadi yakeyi hannun shi rike da taba


Yan ra konsa na mai busa da kirari


Kanshi sai fasuwa ya keyi


Yana tangadi yace ina suke


Aqeel yace qaura meya kawoka gidan mu


qaura yace daliline ya kawo ni kubanisu na fidesu harni qaura za a samu wayanda zasu budewa qanwata idon da raina da lpy ta yakarashe maganar yana layi


Dan koranshi yamishi kirari


qaura ya zaro wuka yana gogawa a jikin shi


Aqeel yace qaura ban gane abinda kake nufi ba fa


qaura yace qanwata ce ta tafi talla wasu daga gidan nan suka mata A kuya kotashi bata yi


Haya niyarda hajiya da Alhaji sukaji yasa su fitowa


Hajiya tace ba a gidan nan ba kasake tam bayan ta


qaura yace Na tam bayeta saboda me bayan qanwata bata karya


Alhaji yace idan a nanne to waye


qaura yace yeeeehu harni za a kawowa rainin hankali aiya maza jada baya ga rago ba tsoro bane yanzu zanyi fata fata da mutum na kwana lpy


Abu da Binta suka taho gurin
Suna kallon qaura yana yiwa kanshi kirari


Abu tace qaryar banza kaje an disashe kaifin wukar kazo kana mana burga dashi mune nan muka daketa me zakayi


qaura yabude ido yana kallon Abu da Binta yace gaskiya bintu ta badani wayan nan dabefi ta murde musu kaiba amma ba komai


Ya sun kuya yana saita wukar ya saito gurin su Abu da Binta


Arif ya Tsaya a gabanshi yace qaura a'a karmuyi haka dakai wayan nan bakine fa


Ina ruwa na kabarni na fedesu Susan wadda suka taba


Alhaji yace qaura kayi hakuri muje naga yarin yar na kaita Asibiti


Abu tace Kawu tsimina na tahi dan'uwar makocin kishiyar kakan su binta qaurane ya jika ya bamu mu bama rike wuka ko gora namu salon na da banne matsa ka gani


Nanfa Alhaji hajiya Aqeel Arif da Amal suka shiga ba qaura hakuri qaura yaki hakura


Arif yace shi kenan gasu nan na bar ka dasu


Binta ta Ja da baya tace kawu matsa karma ya hakura abinda nake jira kenan


Suka sun kuya Suka debo kana nan duwatsunda aka baza a filin gidan suka fara jifan qaura da muta nansa tako ina daga me fashashan baki saime goshi a fashe


Koda qaura da mutanan Sa suka ga Abu da Binta na ji musu jiwo nan fa suka Sa gudu kofar ma ta musu kadan qaura da yake a bige nanfa ya watsa ke yana gudu


har waje Abu da binta Suka rakasu da jifa








































New writer's


Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋




👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝
👠👠
👝


💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄


👝
👠👠
👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠




Written by *husba'ahfama*




33-34




Ko da Abu taga sun tafi tasa ihu


Hankalin kowa ya dawo kanta


Tace saini Abu yar gidan Inna karwar yaya Nura saini Abu me qanhin da babu irin hi saini Abu kawar Binta gagare sarkin kwadayi kura kyaci da gahi


Kai Abu cin fuskar naki harda ni nice ma kura


Abu tace karkiga lai fina tsimi nane ya motsa kome nayi bana cikin hankalina yeeeehu saini qadan garen bakin tulu akarni akar tulu abarni na bata ruwan tulu


Binta tace wayace damu bamuba muma muce dashi bashiba


Aqeel yace daddy mata kenan fa kalli wana jahilin ne ze kwashi Wannan qaura fa suka kora


Alhaji yayi murmushi yace Zasu de na insha Allah


Amal tace yaya kune kuka yiwa qaura wata fassara ta daban kuma abin ba haka bane qaura ragone na bugawa a jarida yan


Koran sane masu karfi kuma suma bakoda yaushe ba dankuwa dasunga anfi qarfin su sai gudu basa tsayawa


Hajiya taceTab amma anfadi ba nauyi qaura yayita birga a unguwa Ashe duk bogine dan iskan karya ne


Arif yadaka musu tsawa yace su rufe mishi baki suwuce suje su cigaba da karatu
Suka tafi fuska ba walqala


Alhaji yace Nina kasa cewa komai Arif zoka rakani gidansu qaura


Eh Alhaji me nake ji kana kallon abinda Abu da Binta suka musu shi ne zaka gidan ka bari dai sai gobe shima idan qaura baya nan


To shi kenan Allah ya kaimu




SU WAYE Aqeel da Arif


Abdussamad Aqeel
Abdulmalik Arif
Yarane nutsatsu kamu lallu sunyi karatu a America a yanzu haka suna Aiki a America hutu suka zoyi gida miskilaine su basosai suka fiya dariyaba


kuma basa son raini basa son haya niya sunada saurin fishi Aqeel baya iya boye fishin shi Arif kuma yana boye fishin shi


Arif da Aqeel sun yanke shawarar cewa matan da zasu aura dole su zama yan2 masu irin halin su basa son mace me


surutu da rashin kamun kai shiyasa basa shiri dasu binta A yanzu haka basuda matar aure suna dai dubawa sune na nafari a gurin Alhaji Nasir sai Amal autar su


Malam kabiru na karatu Abu ta daga hannu


Tace malam inada tam baya


Yace Allah yasa na SANI


Tace kama sani cewa nayi a ajiye karatun a kama wani kawani zaunar damu kana mana karatu kamar munje masallaci


Binta tace kema dai kya fada sukinsan An kwankwadi karatu bakiga ko hutawa baya yiba


Amal ta kalle su sukayi shiru


Malam yace to mun Ajiye karatun Qur'ani sai gobe idan kuka kawo na yau sai a kara wani


Malam ya shiga yi musu wa'azi Abu da binta sukayi shiru kamar ruwa ya cinye su wa'azi yake musu akan sallah da tsafta suka nutsu sunaji harya gama


Yace antashi yau sai kuma gobe


Abu da Binta jiki a mace suka kasa cewa komai Amal ce tace Allah ya kaimu suka tashi suka shiga gida dakinsu suka wuce


Abu tace na kasa hakura Binta ni nunar rana ya mara saboda wani Abu da be taka kara ya karya ba


tace naki kika gani bakiga irin Marin dana shaba dan kawai nabi me karas da kallo


Abu tace haka zamu barsu


Tace injiwa ramuwa ya zama dole ai tsaka ninmu da nunar rana ba yafiya


Abu tace naji dadin jin haka nadauka zakice mu hakura wa'azin malam ya shigeni saidai bazan iya yafewa nunar rana ba


Binta tace yanzu za a kira sallar juma a idan suka fito zasu tafi kizuba ido Kiyi kallo


Allah Binta


Nice fa kema kinsan komai basena fada ba


Hakane sekinyi kai Abu komai naki yayi matsalar ki1 rak kwadayi shine kawai matsalar ki


Au dama saboda ki zageni kika kodani to shi kenan nafasa Kiyi da kanki


Haba Binta ni dake ba yar haka taso muje naga Abinda kika shir ya


Binta ta mike Suka fita kitchen su kaje Binta tace natab bata yau manyan Kaya zasu Sa dan haka muna bukatar manja


Allah qawata ko Anan kika Tsaya na gane inda kika do Sa saidai ina tsoran shan mari


Kinji ai tsoro ya miki yawa Abu kinga ki faki idon Sa ki shiga ki zuba mai a kaya nikuma nasan yanda zanyi nawa


Gaskiya hakan be kwanta minba Binta ki sake min wani


To shikenan biyoni Binta da manja a hannu Suka fito


Amal suka gani ta nufi Sa shan su Arif


Da sauri Abu tatsaya a gaban ta


Amal tace lpy


Lpy bana son ganin ki kina aiki Amal Wannan na waye


Lemo ne yaya Aqeel ne yace na kai mishi yasha kanya tafi masallaci


Abu da Binta suka kalli juna sukace da kyau


Amal tace da kyau kamar ya ban ganeba


Abu tace gurin su za mu basu hakuri akan abinda mukeyi ko zaki bani na kai mishi


Amal tayi dariya tace meze hana gashi kukai Nina koma ciki


To suka ce
Amal na tafiya
Suka sheke da dariya suka tafa hm baki san Meyeke faruwaba


Binta tace kinga nizan Tsaya Anan keki shiga


To Abu tace harda sallah Marta ta shiga
Tace ga shi inji Amal


Kallon banza ya mata yace ana aiken mutane tana aikomun wata halitta ita ba mutum ba itaba Aljanba


Shigo ki ajiya


Bazan iya shigowa ba


Azuciye ya taho ze ansa itama ta taho tana kara sowa ta juyar da kofin lemon ya zube a kayan shi daya gama shiryawa


Abu ta fara kukan karya tace Yazube yanzu me zanje na cewa Amal

Cikin takaici Aqeel yace nida kika batawa kaya bakya tani sai wata Amal


Batace komai ba ta fita tana kukan karya


Aqeel takaici ya ishe shi


Zuwa tai gurin binta tana dariya


Binta tace yi shiru karya jiyomu muje daki
Suka tafi


Binta tace nasan zasu kawowa hajiya kara lokacin zanyi nawa zokiji Binta ta radawa Abu yanda zatayi a kunne


Sukayi dariya suka


Tafa bajimawa Arif ya rako Aqeel gurin Hajiya


Lokacin Abu ta biyo Binta da gudu suna tsere tana karasowa gurin Arif tayi kamar zata fadi ta juye mai manjan hannun ta a Kaya


Abu kinga laifin kiko meyasa kika biyoni da gudu yanzu kinga abinda yafaru


Ni laifi nane kenan karyar banza bawani kece da laifi


Binta tace Kece ba niba


Abu tace Kece baniba


Binta tace Lai fin kine


Abu tace Nakidai


Arif ya daka musu tsawa yace karku sake magana laifin kine ko nata be sha feniba kinsan me yanzu zanje na cire na kawo muku kuwan ke


Abu ta kalli Binta tace wanki


Bakomai kawo zamu wanke


Abu tace haka bari na bika na anso


Aqeel Yace Arif wayan nan zakaba wankin riga kafella musu mari kamusu dukan tsiya a wuce gurin dan gaskiya ban yarda da yaran nan ba


Binta tace karka damuda nunar rana dan bakin cikine idan katashi kawowa ka taho da nashi


Arif yayi dariyar mugunta yace zanbaku bari na Ciro kuwanke ya fita tas
Yakarasa magana yana kallon Aqeel


Aqeel yace duk Abinda ya biyo baya ba ruwana karka nemeni


To naji
Arif ya tafi
Aqeel yabi bayan shi


Abu da binta dariya kawai su keyi


Binta tace Abu yakika gano rigar nan a hannunmu


Kibari kawai harna kasa jure wa nakagu sukawo hmm


Allah yasomu dan hana ruwa gudun nan be rinjaye shiba


Arif ya taho yana dariya yace Gashi harda na Aqeel kuwanke Ku goge mun tafi masallaci


A dawo lpy suka ce gaba dayan su


Suna fita Abu da Binta Suka ajiye kayan a kasa suna tsalle akai saida suka gaji suka zauna


Abu tace hifa nunar rana jiyake da kanhi jihi fari tas koda yake yan gidan ma haka suke


Tace jankosai zakice duk abinshi munzama ciwan ido mu i na ruwanmu ma yanzudai yaza muyi da kayan nan
































New writer's


Hakan Take *husba'ahfama*🌹🌹💋




👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads