Showing 21001 words to 24000 words out of 46028 words
Chapter 8 - YAR KWALLIYA COMPLETED Book by Husba'ahfama.txt
Unknown
03 Jul 2024
433
bace nunar rana tukun na ma Abu ta fada a cikin zuciyar ta
Amal tace yaya ya za ayi yanzu
Aqeel ya kasa cewa komai sai huci yake
Abu tace susha ruwa su tafi tinda abincin ba dole bane dama duk Wannan aboki akayi wa girkegirke haka Nina dauka sarkine ze kawo muku ziyara ruwanma karku baso tinda gidan bana gyatimi bane
A fusace Aqeel ya juyo yana huci shi tinda yazo gun bekula da itaba se yanzu mur yarta Yaji sai lokacin yasan tana gurin ya zari shar bebiyar wuka tana kyalli yabi Abu dashi
Dagudu suka wuce su Usman Amal na binsu a baya sukayi dakin hajiya
Gudun da taji yasata saurin mikewa tace lpy Aqeel mezan gani haka
Yace hajiya matsa ki bani ita ina abincin da aka dafawa su Usman babu shi ita kadai tasan inda ta kai shi
Abu tace hajiya karki yarda da abinda zece wana tabbaci yake dashi na cewa nina boye abinci
Inni naboye abincin ina nakaihi
Yace mommy ita kadai ce zata aikata haka Nina sani
Abu ta fito daga bayan hajiya tana murguda baki zatayi magana Aqeel ya dauketa da mari
Abu ta gigice takurma ihu ta zube kasa tana birgima
Yaya meyasa meyasa ka mareta kome ta maka ka dinga hakuri mana cewar Amal
Yimin shiru yadaka wa amal tsawa kema yanzu nahada dake nakula tinda sukazo kike goyan bayansu bakyaso aimusu fada kuma kina ganin irin abin da sukeyi bedaceba
Hajiya tace Aqeel karka sake dukanta kome ta maka ka sanar dani ni nasan mezan mata
Amma mommy
Tadaga mishi hannu tace ya isa bana son jinkomai
kanta karasa maganar ta tuno maganar da Abu tace mata Binta kurace taci ta koshi
Waiyoo Aqeel temako zoka temaka ka dauko Binta mukaita asibiti Abu karkicemin duk yawan abincin nan ita ta cinye
Hajiya Nifa ba tsoran nunar rana na keyiba maganar gaskiya hine Binta taci iya cinta sauran kuma na rabawa mabu kata
Mommy kina jiko kinajin abinda take cewa
Wlh zan karkarya yarinyarnan
Nidai Aqeel yar mutane katemaka mu kaita asibiti
To naso ace ke kikaci ba ita ba saidai dani kike magana
Yafita daga dakin rai abace
Arif ya shigo hannun shi dauke da leda guda2
Aqeel dasauri ya karasa gurin shi yasanar dashi abinda Abu tayi seyai murmushi yace
Nasan wani Abu me kamar haka ze faro tinda na gane cewa indai ta fadi Abu saitayi yasa na ke fadada tina Nina karka damu ga Wannan nabi ya na siyo abincine masu dadin gaske
Kai naji dadi Amma hakan baya nufin na hakura dan yau raina ya baci sosai
Yace karka damu muma zamu hukunta su
Su kayi dariyar mugunta
Arif yaje suka gaisa da Usman
Aqeel ya jera abincin da Arif ya siyo Aqeel ya fita kunyar Abokin shi dan Abincinda Arif ya siyo kamar a gidansu akayi
Saida yamma Usman da kannan Sa suka tafi
Lokacin ne Aqeel ya maida hankalin Sa ga Abu hukuncin da ze mata kawai yake Tina ni
Aqeel Tina ninme kakeyi haka
Kabari kawai Arif zo muje
Arif yabi bayan shi suka tafi kitchen sukaje
Arif yace me za muyi Anan
Zuba ido ka gani
Aqeel ya Dora ruwa yana ta fasa yasa taliya yana laushi kadan ya sauke ya kwashe yasa miya
Aqeel yace nagama mu tafi
To amma ka hada mata da giyarta ta dazu
Haka ne jeka dauko ka sameni a kofar dakin su
Arif yace to yaje ya nauko lema yanufi dakinsu Binta
Atsaye a kofar dakin yaga Aqeel
Aqeel na ganin Arif yazo yabude dakin ya shiga bacci kawai Abu da Binta sukeyi han kali kwance
Arif da Aqeel sukayi dariyar mugunta
Arif ya tsaya a bangaren da binta take
Aqeel ya Tsaya a bangaren Abu
Atare suka daga hannu suka Kai musu duka me shiga jiki a gigice suka mike suna ihu
Aqeel ya daka musu tsawa
Suka yi shiru suna kallon su Arif
Arif yace kun kyauta a binta kukayi kunbirgeni sosai Ku zonan
Binta tace nan ina muyi me kuma banda Wannan cin zalin da kuka mana
Aqeel rai ahade yace cinzali ko to bari namuku dukan kawo wuka muga abin da zaku kira Wannan kuma
Abu tace nuna karmuyi haka mana bari muzo
Agabanshi so ka Tsaya
Aqeel yace ku zauna a gaban kwanan dana kawo
To sukace sukayi kamar yanda yace
Arif yace Ku Bude kuci
Binta tace dandai ci gidan kazo ta Bude kwanon tana ganin abinda ke ciki tasa kara
Aqeel ya zaro wuka yace kokiyi shiru kona caka miki ba ina nufin hakan zan farayiba saina fara gunduwa gunduwa daku tukun na
Binta ta rufe baki
Abu tace nunar rana bama cin sutsa fa kukawo mana wani abin banda Wannan yai dariyar mugunta
Arif yace Ko lokacin da kuka rabar da abincin kunyi shawara dani
Abu ta girgiza kai alamar a'a
Aqeel yace Yauwa dan haka Ku cinye sutsar nan gaba1 banaso naga komai a cikin kwanan nan
Baza mu iyaba harni har kwada yina ban taba cin sutsa ba yasin cewar Binta
Balle ni Abu bazan iyaba dan Allah kuyi hakuri
Aqeel yace Hakuri Sam bazamu hakuraba har sai kun cinye sutsar nan gaba1 ya daga wukarshi yana sha fawa
To za muci Abu ta juya kai tasa hannu ta debo taliya jitayi yana mata motsi a hannu ta zubar dashi
Aqeel ya hade rai yace 'YAR KWALLIYA kinjawa kanki bayan kuncinye taliya ga lemo kushanye shi tas shima
Giya dan Allah kayi hakuri malam Rabi'u yace ba kyau shan giya fa
Tinda kika kirashi giya kekadai zaki shanye cewar Arif
Lokacinku ya fara daga yanzu inba Ku cinyeba ga Aqeel a kusa dani
Aqeel ya daga wuka ya nuna musu
To shi kenan zamuci haka Abu da Binta suka rufe ido suna cin sutsa ta bakin nasu
Suna hawaye serige ciki suke kamar zasuyi amai
New writer's
Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋
👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝
👠👠
👝
💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄
👝
👠👠
👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠
Written by *husba'ahfama*
29-30
Harsuka cinye Abu da Binta sai rike wuya sukeyi
Arif yace kun gama da Wannan saura lemo
Gaskiya Ku barmu haka
Aqeel ya wasa wuka
Binta tace Abu yi shiru bamu
Arif ya zuba ya basu
Suka ansa suna sha
Binta Kura kyaci da Gashi tana sha taji dadi ta kafa kai ta shanye ta mika mishi Kofi
Arif yace Me zanyi dashi
Tace Wani zaka zuba min
Arif ya zuba mata takuma shanyewa ta miko mishi Kofi shikuma yabata gaba daya ta ansa tashanye
Binta tace bawani Ku karo min Yasin giyar badai dadi ba wai kaf qauyen mu idan za a zagaye bana tinanin za a samu ya Wannan
Arif da Aqeel suka kalli juna
Aqeel yace ke harkin shanye
Abu tace Eh na gama tafada tana hawaye
Aqeel yace Yauwa ita dai waccan wani hanyar zamu sake dan na kula Wannan kura ce yanuna Binta
Kiran salla sukaji suka mike zasu tafi masallaci
Aqeel yaga su Abu ba a daniyar tashi kwanciya ma suke shirin yi a gurin ya daka musu tsawa yace meye haka bakuji kiran sallabane kuke shirin kwanciya
Abu tace munyi tin a *DARAUDAU* ba a binmu bahin salla
zaro ido sukayi atare suka hada baki sukace mekukace sukace mun shiga UKU Akwai bamban aiki
Arif cikin mamaki ya dawo ya zauna yana fukan tarta yace ban ganeba
Binta tace sallar sati1 muke hadawa muyi a rana1 kaga sauran ranakun mun huta Ku kuna salla mukuma muna hutu ta fada tana dariya
Aqeel yace hauka zalla bana tinanin kan yaran nan a kwai kwakwalwa wlh kai kaji wani Abu ko yaro bazeyi shir mannan ba
Arif yace kuna zuwa islamiya a qauye
Abu tace muna zuwa malam rabi'un ne dan rainin han Kali Abu kadan duka hine muka dena zuwa ban fada makaba
har bokoko a wuta munyi sau1 mukaje shima ya raina mana hankali muka hukuntashi bamu sake komawaba sai gamu a barni tafada tana dariya harda tafawa
Aqeel kaji magana gangariya nakula jahilcine kawai yake dawai niya dasu amma komai yazo karshe
Aqeel yace shi malam rabi'un ne ya ce Ku dinga hada sallah
A'a mune mukaga hakan yafi dacewa saboda bamuda lokaci zama muyi akan lokaci saboda dasafe mu debo ruwa darana naraka Binta tallar gurjiya da yamma muje dandali tafada tana rawa
Aqeel ya kalli Arif yace a kwai matsala ke dena mana rawa ko kinji kidane nibana tinanin kawunan yaran nan zasu dau karatu
Arif yace koma meye sunan Ku ban damu na saniba kutashi kuyi Alwala kuyi sallah yanzu sannan Ku sani ba a hada sallah kowacce ana yinta akan lokacinta kunaji
Allahu'akubar kaji malamai munji kuma mun gane zamu gyara wai bazaku kaimu dandali bane natara rawa masu yawa Ku kaini na juye yanbirni su gani su sani mu yan qauye hmm tatashi tana rawa
Aqeel yace yarin yarnan a bace take bata gane komai zomuje masallaci kaga har an tada sallah
Suka tafi sukabar Abu na rawa binta na zaune tana shafa ciki
Binta tace Abu zoki rakani gona nayi kahi sunan basuda shadda Gashi a matse nake waiyoo
Abu ta dena rawar da take cikin mamaki tace binta kefa ki kace yan birni basa kahi ya haka kuma keza kice na rakaki gona
Kinga su wayanda aka Haifa a birni nake nufi banda mu kinga aimu zuwa mukayi ko
eh hakane kinga yanzu yamma tayi kihiga inda aka yi mana wanka ina randar nan ta ruwa Wannan farin
Binta tace Eh na ganeta
Kije Kiyi a ciki
Abu ba komai
bakomai jeki na Tsaya miki
Binta ta shiga tayi ta fito tana rike ciki tana yamitse fuska
Abu hanci a toshe tace Binta duk warin kahin kine haka kamar mushe
Bana son wula kanci lafiyace da bani dashi bazan yiba
Amal ta Bude ta shugo tana shigowa warin ya daki hancin ta tace meye haka warin meye Wannan
Binta tace ji wani Abu da takeyi kamar bata taba yin kashi ba wayasanima ko naki yafi nawa wari
Amal tace a ina kikeyi
Binta tace shiga nan ta nuna ban daki zakiga randar ruwan nan a ciki nayi karki damu sanda na Debi ruwan tsarki a randar tukunna nayi
Randa Amal ta mai maita cikin ban dakin tashi ga tasamu binta batayi shirmeba korawane kawai bata yiba ta kirata ta nuna mata yanda akeyi
Abu tace Tab saura kiris mu fita waje Neman Gona da zatayi a can Ashe Gwanda da bamu fitaba da munsha wa halar
Banza
Shiyasa nace kome kuke so Ku tam bayeni
To ai mun gane yanzu kuma
Bari naje gurin mommy ina zuwa
Tabude ta fita su Aqeel ta samu a dakin
Aqeel yace mommy gaskiya a nemawa yaran nan malamin da ze dinga koya musu karatu a gida idan suka fara hankali a kai su makaranta
Arif yace mommy yaran nan naki da girman su hada sallah sukeyi
Hajiya tace Eh hada sallah bangane ba
Aqeel yace hmm dazu suka fada mana waisu sallar sati1 sukeyi a tare rana kunda zezo kuma sun huta
Hajiya tace tab Allah ya rufa asiri yakamata musamo musu malami yanzudai malamin da ze dinga koya musu Qur'ani da sauran littattafai na addini shine malam kabiru dama shiya ke koyawa Amal
Arif yace hakan ma yayi idan suka ga amal kila su zauna mommy boko fa
Eh to Wannan dinma kabiru ze iya koya musu tinda tsohun malin makaranta ne
Arif yace to mommy zan Kirashi na sanar dashi daga gobe zasu fara inba hakaba abin nasu lalacewa ze karayi
Hajiya tace yauwa Aqeel idan malamin yazo kuja musu kunne karsu yiwa malamin halin nan nasu dan naga suna
tsoron ku sosai Niko yakayi da Usman duk kunya ta hanani fitowa koda muke Salama Akunyace nake wlh
Aqeel yayi dariya yace mommy Arif ya findake kunya shiya siyo abinci ya kawo bazama kice a waje aka yiba kannen Usman sunce suna godiya da yautar da kika musu
Alhamdulillah amma naji dadi Allah ya muku Albarka
Ameen mommy tafiyar mu zuwa America na kara matsowa fa
Hakane fa harna fara kewar Ku
Mommy karki damu ga *'YAR KWALLIYA* da *KURA* za su debe miki kewa suka fada suna dariya
Hajiya tace yaran nawane kuraye lallai inajiye muku wlh ranar jinkunya musammanma Aqeel kafi kushe su
Tab indai wayan nan ne ranar bazata zoba nida zan dauko miki sirika a America me zanyi da wata yar qauye
Allah yaya to shi kenan zamu gani cewar Amal
Mommy saida safe mu zamu tafi
Allah yatashe mu lpy
Washe gari da safe Abu ko karyawa basu yiba suka fice daga gidan
Abu na tafiya tana mita
Kai dan Allah ki Tsaya Abu mitar me kikeyi
Binta tinda mukazo basu kaimu sun nuna mana gariba sun barmu a guri1 sannan gasu nunar rana gidan ma ba dadi ko dandali basu kai muba
Binta tace shine abin damuwa to ba Gashi mun fitoba muga gari iya san ranmu daga nan muje muga dan dali
Hakane kuma saida sukayi tafiya me tsawo sukayi nisa da gidan sosai
Duk wanda ya gansu mamaki yakeyi ganin KWALLIYAR dake fusko kinsu duk wanda ya kallesu baya karawa
Abu ta jabe a kasa tace daga nan babu inda zani
Meyasa
Saboda yunwa nakeji indan banciba bazan iya tafi yaba
To bari naga ko zamuga abin siyar wa
Wata yarinya ta wuce ta ga bansu tace zaku sai waina
Binta tace waina Abu kinji waina tab shegu yan birni nasani ai duk abinku saikun hada da qauye sauke mu gani
Yarin yar ta sauke sukace na nawa ne a ciki
Tace dubu1
Abu tace Yarinya kingama ciniki yidari
Yarinya tayi dariya
Abuda binta suka Sa hannu a robar waina suna ci
Can gida kuwa ne mansu kaiwai a keyi suzo suci a binci gashi kuma malamin da ze koyar dasu yazo
Amal tace yaya Aqeel bangan subafa
Baki gansuba kamarya ina zasuto cewar Arif
Amal tace nima ban saniba
Hajiya ta daga hannu sama tana cewa Allah kasa muga yaran nan Allah kakaresu a duk inda suke
Aqeel yace mommy dan Allah karki damu zamu nemo su duk inda suke bari mu tam bayi me gadi koyaga fitar su
Dukan su suka je gurin megadi
Arif yace kaga fitar kannen mu guda2nan da sukazo
Eh nagani sunce min suntafi bude ido
Alhaji yace Bude ido kai Arif Aqeel kuzo muje Neman su
Aqeel rai a bace yacewa megadi tin yaushe kake aiki a gidan nan dasuka ce maka haka saika zo ka tam baye mu kafin ka barsu su fita
Ayi min Afuwa insha Allahu hakan baze sake faruwaba
Arif yace daddy karka damu kukoma ciki zamu nemosu da kanmu mu kawo su
Amal tace yaya zan biku
Arif yace taho mu tafi
Hajiya tace saikun dawo Ku kula da kanku idan kun gansu Ku kira Ku fada mana
To mommy
Me gadi ya bude musu suka fita Neman su abu
Saida su kaci suka koshi sukace taje ta siyo musu ruwa da kudinta tajeta siyo ta kawo musu suka sha
Alhamdulillah Allah na gode maka yanzu naji dai_dai dauki wai narki ki tafi Allah ya kawo ka zuwa
Yarin yar tace kubani kudina saina tafi
Binta ta kaiwa yarin yar duka tace rashin kunya zaki mana bazamu biya ba Kiyi abinda zakiyi
New writer's
Hakan Take *husba'ahfama* 🌹🌹💋
👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝
👠👠
👝
💄💅 *'YAR KWALLIYA* 💅💄
👝
👠👠
👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠
Written by *husba'ahfama*
31-32
Yarin yar tace hakama zakice wlh Baku isaba duk abinda kuke takama dashi Nina fiku bala'i yanzu zan dakeku na daki kudina na kaiku gurin yan sanda
Binta tace Ko to bisimillah mafashi keda kinsan komu suwaye tsayawa ma baza Kiyi a nan ba
Yarin yar ta kai wa Abu duka
Abu rai a bace takai mata wani mugun naushi saigata a kasa Abu da binta suka rufar wa yarin yar sukai mata duka
Abu tace Banza a banza kemu zaki nunawa taurin