Showing 1 words to 3000 words out of 46028 words
Chapter 1 - YAR KWALLIYA COMPLETED Book by Husba'ahfama.txt
Unknown
03 Jul 2024
427
'YAR KWALLIYA
Bismillahirrahmanir Rahim
Wannan kirki raren labarine nayi shi dan fada karwa da nisha dan tarwa ban yishi dan wani ko wata ba
Written by husba'ahfama
1-2
Wata yarin yace 'yar shekara 15 kafa fururu komai babu fuska kuma tasha Jan baki da hoda harda gazal ta fallo da
gudu kanta daukeda tulo tadebo ruwa a guje ta fada gida Tana shiga ta saki tulun yafadi ya fashe
Nidai gaskiya bazan yar daba hikenan ni banda kata bus hine fa ya bini har inda zan debo ruwafa inna yana cemin
*YAR* *KWALLIYA* kafa ba mai fuska tasha ado hine nakamahi da danbe na fasa mihi baki hine dan bahida kunya ya biyoni gida
Yasin bazan yarda ba inna kalli yanda bakina yake zubar jini inna Abu muguwace wlh
Kayi hakuri kaji kaima da naka ina ruwanka da tsokanar ta kuma kasani sarai bazata barkaba
Au abinda zaki ce kenan to shi kenan zan turo me rama min
Kayi hakuri mana kai baka jin hakurine
Ina kotsayawa beyiba yatafi
Inna ki barhi ki barhi nace kaje ka kawo bindiga karhe kenan
Yanzu Abu Wannan rayuwar kika zaba to shikenan zandena tsare miki wlh tinda ke bakida hakuri yanzu Wannan gabjejen kato kika kama da fada
Inna hinefa ya nemi tso kanata fa
Yanzu ruwan da kika debo ma gashi kin fasa tulon kaini inna ina zansa kaina
Inna Wannan fa laifin tulun kine ina ruwanhi dani nan naso na ajiye hi hine ya fadi ya fahe sai hakuri
Kamarya sai hakuri Abu girkifa zan Dora yanzu ya kikiso ayi
To ni kome ma za ayi ayi tuludai yafahe nikuma na gaji bazan iya komawaba
Kin isa komawa kamar kinyi kin gama ga wani tulun can jeki dauka kidebo wani ruwan
Kai inna kinemo wani ya debo kinga janbaki da hudana ya kare sonake na zagaya baya na siyo
I dan har baki debo ruwan nan ba ba inda zaki Abu kin jini da kyau
hikenan zan debo
Abu ta dauki tulun tatafi
Rake yauwa bari naga
maya finda ke daure a kugunta ta kwance ta Ciro Hamsin ta mika wa me rake
Yabata rake da canji tana tafe tana sha harta karasa rafi
Yauwa wana kama wato jiya kika watsa min kasa kika gudu ko yanzu wana kama cewar Abu
Ke Abu kinga diban ruwa aka turoni ba fada ba matsa na wuce cewar binta
Ke binta me kike nufi ni wasa aka turoni kenan bari kiga wasa cewar Abu
Hannu tasa ta ture tulun dake kan binta yafadi kasa yafashe
Yauwa kinga wasa nan nafasa banza ko kinada abinyi ne
Kaiiii ni kika fasawa tulu wallahi kinyi karya saina rama Abu kome kike takama dashi kin tara kin samu ni binta saina gyara miki zama
Binta na gama fada tasa kafa ta daki tulun Abu yafashe
Nanfa Abu ta daka tsalle ta dire ta kamo wuyan Binta suka kama fada da kyar aka rabasu
Aina fada miki Abu ni Binta nice dai dai ke saina gyara miki zama
Tohi kenan idan baki gyara min zamaba nizan gyara miki kuma saikin biyani tuluna kona daka ki a gurin nan wlh
Allah ko Abu bazan biya ba kiyi abinda kika gadama koda me kika zo ni Binta na fiki
haka kikace ko to hikenan
Kallon ta Abu take tana gyada kai da buga kafa
Banga wanda ze fi karfinaba ni Abu wai saiwata banza bazara iskar damuna binta wlh kintarowa kanki aradu da ka
Hannun ta Abu ta kama ta sakar mata cizo dagudu tabar wajan
Binta tabi bayanta da gudu haka suka yanka cikin unguwa dagudu harzuwa gidansu Abu
Abu ta boye a bayan inna
Inna ki matsa Wannan fadan ba naki bane kimiko min Abu na nuna mata abinda binta zata iya ni kika ciza dai ko cewar Binta
Yar gidan marasa tsoro mekikeyi a bayana aina fada miki ni nadena bada hakuri kinga Binta gata nan zoki mata abinda kike so cewar inna
Gadan gadan Binta tataho
Kinga Binta tsaya Abu ina ruwan dana aikeki kidebo cewar inna
Inna asara kika aika dankuwa ni Binta nice nan na fasa tulun *'YAR KWALLIYA* tafasa min nawa shine nima na rama wata tsiyarce cewar Binta
Ahh babu bakomai kinyi daidai yanzudai kiyi hakuri Binta kibari idan tafito kuyita takare mutuwama tana tsoron idon ma haifi cewar inna
Inna kenan kince haka ko to ina waje ba inda zanje kekuma Abu zaki fito kisameni hoda bawanka kidinga Wanka idan zakiyi kwalliya
Binta tajuya ta fita
Inna ki matsa kibar ni da ita kina jin metake cemin
Karya tayi Abu gaskiya tafada yau kwananki nawa rabonki da kwanka
Inna batun wankan nan kibarhi aikyan kwalliya kayihi batateda wankaba gawani kamhin turare na musamman
dayake tahi a jikina gahi turaren babu a kasuwa me yafi raina shine zan tsaya inta batawa kaina lokaci wajan yin kwanka
Dalla rufemin baki kazamar banza kazamar hufi ina kyau Anan *HODA BA WANKA*
Baki tabude ta gir_giza kai ta dunkule hannu
inna harda ke yasin duk wanda yasake ce min hoda ba wanka na dena raga mihi yasin cewar Abu
Yanzu da kika dunkule hannu damben zakiyi dani nima cewar inna
Jifa tayi da takalmin kafarta ta debo kayan Kwalliya ta zube a gabanta tadauki Wannan tashafa ta ajiye takalli kanta a madubi tayi dariya
Inna jiya da naje dan dali aka dinga tambaya waye yafesa turare nayi shiru tsabar kanhin turaren jikina hanci suka toshe
Niko kayan nan ma bacanzasu zanyi ba Wanka kuwa nadena
Kaza kankida motsi afakaice suka zageki baki saniba ba abinda kikeyi sai bugawa kitemaka ki ajiye kayan kwalliya kiyi Wanka kekanki zakiji dadi
Tab tab aaah waii saidai wata Abun badai niba wanka nida hi munyi hannun Riga inna kifara sabon lissafi daga nan harranar sallah nida Wanka
Haka kikace to Allah yashigoda yayanki da malam su insun isa dake Sa saki kiyi tinda ni kin rainani dan Allah ji yanda kika cika mana gida da tsami cewar inna
Kinji ko inna kinji irin kamhin turarena ko hakama wani saurayi yajiyo kamhin yace yana sona nace bana son hi ni fako inna har bana son fita dik inda nabi ansan nice saboda turturarena cewar Abu
Waiyoo waiyoo tasa kafa tayi koli da kayan kwalliya
inna ban fada mikiba yau ake cin kasuwar gangare natafi
Tayi fice warta
Badan Allah yasa akwai sauran ruwa agidan nan ba da Abu ta gama dani cewar Inna
Tafiya take a hankali tana tafiya tana yanga acewarta tafi kowa haduwa ga turaren jikinta yafi na kowa kanshi tana tafe tana cin gyada hannun takuma rikeda sandar rake ga wuwar danmara tasha a kugunta
binda na labe tana kallon ta Abu nakara sowa inda Binta take Binta tariketa
Wana kama yasin saina dagargaza bakinki zan kyaleki yanzu ina inna take balle kibuye a bayanta cewar Binta
Yasin Binta kanki baya aiki kalli yanda kika rike min Riga a gaban mutane gasamari a gefe kalan ki zubarmin da mutunci a idonsu haba kidena abinda kuda zebiki
Karsan kuda nice mangoro kobakijiba cewar Binta
Janyota tayi zata daka bashiri ta saketa tatoshe hanci
Abu dagaskene abinda ake fada kenan Wannan warin daga ina lallai kinci sunan ki huda ba Wanka sammin raken mana
Abu taraba shi2 ta bata
Yauwa nagode gyadar fa
Tadiba tace Gahi kibarni zaki rakani cewar Abu
Eh ni yanzu kawarkice gaskiya kinada hankali Abu
Dariya tayi tace ko nasani
suna tafe suna shirme harsuka siyo suka dawo
Atare suka shiga gidan
Inna na ganinsu ta fara salati
Abu mekika kuma yiwa Binta cewar inna
Inna ai yanzu Binta tazama kawata cewar Abu
Ina baze yiyuba ban yardaba wlh dama ya kike bare ankaraki da binta waye besan bintaba cewar inna
Kinga Binta jeki gida zanzo na same ki cewar Abu
To inna sai anjima cewar Binta
Sallama Alaikum inna ina wuni
Lpy kalau Nura sannu dazuwa kaga Abu tayi sabuwar kawa mara aji irinta
Ke Abu yatoshe hanci inna meya yake bugawa haka cewar Nura
Wacce inbanda *'YAR KWALLIYA*
Fari Abu tayi da ido tareda juyawa
New writer's
Taku husba'ahfama馃尮馃尮馃拫
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼
馃憹
馃拕馃拝 *'YAR KWALLIYA* 馃拝馃拕
馃憹
馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
Written by *husba'ahfama*
3-4
Yaya Nura a hekaima kaji kanhin tiraren nawa
Dalla kanshi ko wari kazama kawai dubi yanda gidan nan yadauki warin jikin ki
Wari karyama kenan Yasin kanhi kaji cewar Abu
Yau sai kinyi Wanka bazan iya zama dake kina wariba wlh inna bani ruwan nan na kusa dake cewar Nura
Banga abinda zesa nayi wanka ba Yasin kalan kanhin turarena ya tafi
Nura ya dauki ruwan yasa a bandaki yakai mata soso da sabulo ya karyo bulala yarike
Shiga kiyi wanka
Yaya Nura ina ganin gir manka fa cewar Abu
Yadaga bulala bashiri ta fada bandaki tayi zamanta
Kayi ka gaji yaya ba wankan da zanyi cewar Abu
Tana tawasa da ruwan kamar tana wanka tawanke fuska da kafa da hannu
Kate makeni ina fitowa zan cika fukata da KWALLIYA na raka Binta tallar gurjiya hahhh
Tabude ta fito ta harareshi tashige daki tayi KWALLIYA ta tafi gidansu Binta taje tasamu Binta ta fito tallar gurjiya
A hanyarsu na tafiya Abu tayi ido4 dawata taci ado da KWALLIYA tayi kyau sosai harta bace Abu na kallon ta
Ke mekike kallo cewar Binta
Kinga yanda tayi kyau tafi yanta kayanta komai yayi
Nanfa Abu tashiga yin irin tafiyar
Kibar Wannan abin Abu kinsan daga ina take cewar Binta
A'a cewar Abu
Daga birni take haka suke tasu KWALLIYAR dasa kaya ba irin nakiba HODA BA WANKA
Yasin yanzun nan bakinki zeyi jini Binta nizaki cewa haka nifazanyi fada da duk wanda ya kirani da Wannan sunan kowaye hi cewar Abu
Maida wukar nataba zuwa birni sau1 yanada kyau ginin su ba irin namuba kinga baze yu nabaki lbr ba saikin gani da idon ki cewar Binta
Kai nima inaso naje zaki kaini dan Allah cewar Abu
Inna inna ce matsala Abu damunje yasin cewar Binta
Kinga bawata matsala ki kaini kawai inzaki kaini ya kika ganni zanyi kyau a birni ko cewar Abu
Ehhh to ban saniba saikinje tukunna saboda gaskiya tsoro zaki basu kalle kifa tab cewar Binta
Waike hikenan bakida magana sai kice na kalli kaina me zan gani kodai ciki baki kike min ne cewar Abu
Ko daya KWALLIYAR takice abin tsoro ga kafarki Fari fat gaskiya bazan kaikiba saikin waye cewar Binta
Abinda Binta tafada yabatawa Abu rai yasa tayi gaba ta barta a baya
Wani yarone yazo siyan gurjiya gun binta
Binta zuba min gurjiya
Karki zuba mai cewar Abu
Tinda na ganka nadawo mekace min jiyama
Meka ce mata Eh cewar Binta
Shiru yayi yakasa cewa komai saida ya gano yayanshi
yace ' *YAR KWALLIYA* nace
Ohh me dadtin dankwali itace *'YAR KWALLIYA* cewar Binta
Barshi dani yanzu nanuna masa kalata Yasin harni zaka tsokana ka gudu anhi kudin nahi Binta cewar Abu
Binta ta ansa tace kuma bazan siyar maka da gurjiyan ba na karfine
Gaya mihi binta waihi Wannan dame yake dakama ne naga saiwani jijjidakai yakeyi cewar Abu
Kasa ta diba ta watsamai a ido Binta tasamai kafa ya fadi suka rufeshida duka abin mamaki kato a kasa mata na duka abinda mutane ke cewa kenan
Yayan shina kara sowa ya daka musu tsawa
Suka bar dukanshi suna Harar shi
Lpy kaikuma meya kawo ka kasan muko suwaye cewar Abu
Suwaye Ku inbanda kucakai marasa hankali dalla dubeki kafa furu furu komai be ganiba dubi kayan jikinki fuska saikace Aljana waike kinyi KWALLIYA
Ap abanza yafi na tsohuwa kaga ka gaggauta barin gurin nan inba hakaba kuma hmmm cewar Binta
Karkusake suce zaku yimin haukan da kuka saba danni bazan daukaba wlh
Ko Binta mu gwadamai aiki dan nakula saimun koya mishi hankali cewar Abu
Waige Binta tafara can ta gano dutsa tace haryanzu bakinka be mutuba ko tsaya ka gani
Dutsen ta dauko da buga mishi a kai
Banza a banza cewar Abu
Jini ya fara zuba a kanshi
Abu da Binta suka zuba a guje suka wuce gidansu Binta
Umma ga gurjiyar ki yau an hana talla inji me gari cewar Binta
Ke Binta waya fada miki cewar umma
Umma Nifa ganauce ba jiyauba Gashi can ya baza yan *DOKA* A gari cewar Abu
Kunga bana son shegan taka waca tsiyar kuma kukayi na sanku da kyau cewar umma
Wani ne ya nemi tso kanar mu hine muka fasa mai kai cewar Binta
Eh banjiba naji kamar kince fasa kai Allah na gode maka daka bani Binta nidai shikenan bakina baze zauna shiru ba saboda inada Binta cewar umma
Kofar gidan su Binta aka siga duka da karfi
Kufito mana dasu ko mushigo yara sun gagari kowa wlh yau zamu sharewa kowa hawaye kufito dasu cewar mutanan da suka zo
Kuna jiko yara kunzama dan kuka mejawa uwarsa jifa
Umma kinga jeki kiji dame suka zo idan da sulhune kusulhunta idan kuma akasin hakane kikira womu katkenan cewar Abu
Kushiga ciki bari naji dasu
Wai baza a fito dasu bane Eh mumafa yan zama nine kofar suka bude suna kokarin shiga
Haba dan samari gidan matan aure ne fa
Nasani ina 'ya'yan Allah banin nan suke Binta da Abu
Basa nan sun fita
Karyama kenan ina ganin su suka shiga gidan nan dan haka ki fito dasu kawai mu baza mu hakuraba dan uwanmu suka fasawa kai gashinan sai zubar jini yakeyi yanzu haka yana Asibiti
Allah yabaku hakuri kuje idan sun dawo nida kaina zan kawo muku su cewar umma
Eh to na yarda dake saidai be kamata mu tafi haka ba bari mu bar miki sheda idan sunzo ki nuna musu
Yadaga gora ze sauke mata dagudu tabar gurin ta shige gida tarufo kofa
Yauni umma naga ikon Allah ina kuke
Umma sun bar miki sheda banzaye sokaye sun yarda ba ma nan gamunan muna jinsu kuma cewar Binta da Abu
Au kujin dadin kune a bar min sheda saboda kun amsa sunan Ku Binta da Abu ko Allah yate makeku suna nan suna jiranku kuna fita sai abinda hali ya yiwu cewar mama
Basu isaba yanzuma ba barinsu zamuyiba narike muryar su zan ne mesu 1 bayan 1 cewar Abu
Umma kawo mu kai miki dan dali cewar Binta
Gashi nan kutafi amma dan Allah karku nemi tso kanar kowa kuma Ku canza hanya karsu ganku cewar umma
To sai mun dawo suka fada gaba dayansu suka fita
Suna fita umma taji wani hadeden wari
Umma taja dogon nun fashi Wannan wani sabon yayi ne kuma Abu irin Wannan bugawa haka nida Allah yasa kar Binta tadau Wannan halin na rashin Wanka
Suna tafiya suna waka suna ciye ciye suna neman tso kana
Abu ta gano bishiya
tace Binta ajiye gorjiyar nan muhau bishiya kinga yanzu basu fara zuwaba zuwa anjima sai muje dan dali
To muje suka tarar da yara a jikin bishiya suna wasa
Kubar gurin nan Abu da Binta sunzo ko sokuke jiki yayi tsami cewar Binta
Tinkan Binta ta karasa magana yaran suka bar gurin dan sunsan halin Abu da Binta
Suka cire takalmi suka haye bishiya suna wasa kamar yara
Wasu yan mata suka zo wucewa suka gano Binta da Abu suka kwashe da dariya
Abu na ganin su ta sauko Binta ma sauko wa tayi
Wakuke wa dariya Eh daku nake magana Abu ta fada tana dungure musu kai
Karki sake dun guremin kai kinsan kowaye babana kuwa A garin nan
koma waye hi beda meniba abinda yasa kika kallemu shine yanzu ze Ja miki dukan tsiyama kuwa cewar Binta
Jiki ko kayama baki iya sawaba ji hodar fukarki janbakin ma tsohon yayi ne amatse ciki asai sabo cewar Abu
Kaji wai harkurace zata ce da kare maye jiki kalli kafarki kalli fuskarki ji wani wari mara dadi da kikeyi gaskiya kinci sunan ki HODA BA WANKA
Nanfa Abu tayi kukan kura ta rufesu da duka Binta nadukan daya Abu ma na dukan 1
New writer's
Taku *husba'ahfama*馃尮馃尮馃拫
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼
馃憹
馃拕馃拝 *'YAR KWALLIYA* 馃拝馃拕
馃憹
馃憼馃憼