Header Ads
Showing 36001 words to 39000 words out of 57539 words

Chapter 13 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

567

Ads at the middle of Article

_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*_27&28


**Washegari**


Safnah ba ita ta tashi bacci ba, se ƙarfe 10:00 tana yin sallar asuba ta koma bacci don bata kwanta da wuri ba.


Teemah kuwa tun asuba da ta tashi bata koma bacci ba, Kitchen ta shiga kasancewar ita take musu girki, bata tashi Safnan ba saboda tasan bata kwanta da wuri ba, ga jikinta har yanzu se a hankali bata samu ƙarfin jikinta ba sosai.


A ɓangaren part ɗin su Hindu kuwa suna tashi su ma kicin suka nufa don ɗora abin kari suna gamawa kuma suka shiga gyaran babban falon na su da harabar gidan kasancewar yau suna da babban taro wanda suke yi duk bayan wata biyu a Familyn su, ma'ana (Family meeting) kuma a part ɗin su ake gudanar da shi.


Ba su wani sha wahalar gyaran gidan ba, kasancewar kullum se an gyara shi dama, kuma su huɗu suka yi aiki, Meenal, Hindatu, se ƴan aikin su guda biyu.


Bayan sun kammala ne suka yi wanka tare da shiryawa suka nufo part ɗin su Teemah, kasancewar taron se Ƙarfe 12:00 na rana ne ake farawa har illah Masha Allah, wa su ma anan suke kwana musamman na nesa, haka taron nasu yake kasancewa kamar wani babban biki.


Lokacin da suka isa part ɗin su Teemah ƙarfe 10:40 a dining su ka samu Safnan tana ƙaryawa don tashin ta kenan ba daɗewa.


Dining ɗin suka nufa ko wacce ta samu kujera ta zauna.


"Hajiya Safnah an tashi lafiya?" Hindatu ta faɗa.


"Lafiya lau ya kuke"


"Lafiya lau, ina Teemah take"


"Teemah ta shiga wanka"


"Ok, Umma fa?"


"Umma tana ɗakinta"


"To bari mu gaishe da ita kafin Teemah ta fito" Meenal ta faɗa tare da miƙewa Hindu ma miƙewar ta yi suka nufi ɗakin da ya kasance na Umma ne.


"To shikenan" Safnan ta faɗa.


Mintuna 5 da shigar su ɗakin su ka fito tare da Umman Teemah sanye take cikin doguwar riga ta shadda blue colour.


Falon su ka nufa suka zauna, Safnan ma, ta koma falon don ta gama cin abincin suna hira ne da Teemah don ta fito wanka.


Kwalliya sosai ta cancaɓa a fuskar ta, kai ka rantse bikin wata babbar ƙawarta zata je, dama Teemah gwana ce wajen tsara kwalliya a fuskarta, har mutane ma tana mu su idan taga dama.


"Su Teemah irin wannan kwalliya haka, kamar ba za'a mutu ba!" Cewar Meenal


"Hm ai shine na gani nima, ko dai zai zo ne Teemah?"


"Kwa dai ji dashi! Mutum ba ze yi kwalliya ba, se ze tafi wani waje ko za yi baƙo?"


"Allah ya huci zuciyar ki amaryar Faruq!"
Cewar Meenal


Zaro idanu Teemah ta yi tare da kallon Umma, sannan ta juyo ta yi wa Meenal alama da kar Umma ta ji.


Amma aikin gama ya gama Umma ta riga da ta ji, don hankalinta yana kan abinda suke cewa, duk da idanunta na kan wayarta ne.


"Meenal waye kuma Faruq?" Cewar Umman


Gaban Teemah ne yayi mummunan faɗuwa da jin tambayar na Ummanta.


Shiru su ka yi daga Meenal har Teemah ba wanda yace komai.


"Ba ku bani amsata ba!" Umma ta faɗa


"Umm Umma abokin yaya Abdul ɗin nan, da ya zo gidan nan kwanaki" Hindu ta bata amsa don jin duk Sunyi shiru, don ita a tunanin ta ma, Teemah ta faɗawa Umma maganar Faruq.


"Wanda suka zo asibiti tare?" Umma ta sake jefo mu su tambaya.


"Ehh Umma shine"


"To menene tsakanin Teemah da shi?"


"Momy Saurayin Teemah ne" Meenal ta faɗa.


"Teemah maganar da su ka faɗa min hakane?" Umma ta faɗa tana kallon Teemah da ta sunkuyar da kanta ƙasa alamar jin kunya.


Gyaɗawa Umma kai ta yi alamar "Ehh"


Murmushi Umman ta yi wanda ka na gani kasan na farin ciki ne, sannan tace


"To Teemah ki na son shi ne?"


Gyaɗa kai ta sake yi alamar "Ehh" tare da sunkuyar da kanta ƙasa tana Murmushi.


"Masha Allah! Shine baki faɗa min ba Teemah, gaskiya na yi farin ciki da jin wannan lamari, domin na karanci yaron, daga ganin shi yaro ne mai hankali da sanin ya kamata, kuma burin ko wace Uwa ne ta ga ƴarta ta samu miji nagari, kuma aure shine cikar kamalar ƴa mace Teemah, amma da kin dage baza kiyi aure yanzu ba, bayan ga ƴanuwanki duk amsa ranar auren su"


Duk shiru suka yi ba wanda ya ƙara magana suna sauraron abinda Umman take faɗa.


Wayar Meenal ce ta ɗauki ƙara alamar shigowar kira, da sauri ta jawo wayar tare da ƙarawa a kunne,


"Assalamu alaikum Momyna ta kai na" Meenal ta faɗa fuskarta ɗauke da farin ciki da annashuwa.


Banji abinda akace a ɗayan ɓangaren ba naji dai Meenal ta ce


"Dagaske Momy!, To gani nan zuwa" tare da sauke wayar fuskarta ɗauke da tsantsar farin ciki.


"Lafiya ki kuwa?" Hindu ta faɗa ganin irin murnar da Meenal take yi


"Momyna ce take faɗa min gata nan har ta zo, tana ɗakin kaka" Meenal ta faɗa tare da miƙewa da gudu tana faɗin "Umma seanjima"


Murmushi kawai Umma ta yi, a zuciyarta kuma tace "Allah Sarki Uwa mai daɗi"


Su Teemah ma sallama suka yi wa Umma suka fita zuwa part ɗin su Kaka.




Meenal bata tsaya da gudun ba har ta shigo part ɗin na su, yaya Abdul ta tarar zaune kan motar shi, shi da yaya Sadiq duk sun ɗauki wanka sunyi masifar kyau duka manyan kaya su ka saka.


"Ke kuma lafiya kike faman gudu haka?" Cewar yaya Sadiq, shi ko Abdul bin ta kawai yayi da ido.


"Ina kwanan ku yaya Abdul!" Ta faɗa


"Lafiya lau, shi aka tambaye ki?" Yaya Abdul ya faɗa.


"Yaya momyna na ƙosa na gani wallahi"


"To shiga tana ɗakin kaka" Abdul ya faɗa.




Da sauri ta shige ɗakin, tsabar saurin da take yi be bata damar ganin mutanen da suke falon ba, kawai ɗakin Kaka ta nufa.


Tana shiga kuwa ta hango momynta zaune a kujerar, da gudu ta ƙarasa ta faɗa kan Momyn nata tare da cewa


"Momy I miss You so much"


Murmushi matar ta yi wanda kamar su ɗaya da Meenal kamar an tsaga ƙara, sannan tace


"To tunda kin yi kewata se ki karya ni ki huta!"


"A'a momyna bazan karya ki ba, ina su twinse da Zainab?"


"Suna falo baki gan su ba ne?"


"A'a momy ban lura ba ne"


Gaishe da mutanen da ke falon kakan ta yi tare da fita ta yi waje, wajen ƴan ƙannen nata.






"Abdul kwana biyu na rasa gane kan ka, kamar ka na cikin damuwa, amma ka ki sanar min" Cewar Abdul tare da saukowa a saman motar da su ke zaune tun ɗazu.


"Sadiq kenan!, Wallahi soyayya ce ta yi min mugun kamu"


Dariya Sadiq ya tuntsire da shi, sannan yace "ka ce maza an shiga hannu kenan, to kai ko wacce yarinya ce haka take ƙoƙarin baka wahala, kar ka manta kai fa soja ne"


Duka Abdul ya kai wa Sadiq tare da cewa "kai fa ɗan iska ne!, Shiyasa wataran gara na bar damuwata, har nayi solving ɗin ta ni kaɗai"


"Haba sorry babban yaya!, Yanzu faɗa min wacece?"


"Safnah ce!"


"Safnan da na sani dai"


"Ehh ita"


"To ka faɗa mata ne?"


"Shine abinda na kasa yi"


"To shikenan zanyi maka wani taimako akan haka in sha Allah!"


"To Allah yasa!"


Suna rufe baki su Teemah su ka shawo kwanan part ɗin, tun daga nesa Abdul ya kafe ta da idanu ba kwalliya ta yi ba, amma ta ƙara masa kyau sosai, ko dan ta daɗe be gan ta ba ne.




Abdul be san sun ƙaraso wajen ba don ya tafi duniyar tunani, se da ya tsinkayi muryar Teemah na faɗin


"Ina kwana yaya Abdul!" Da sauri ya ɗago kan shi tare da amsawa, Safnah ma gaishe da shi ta yi ya amsa.


"Yaya yaushe zaka Kaduna?" Teemah ta faɗa.


Shiru yayi bai ce komai ba se tsira mata idanu da yayi ma.


"Ki na da saƙo ne zuwa Kaduna?" Sadiq ya faɗa.


"Ehh ina da saƙo" Teemah ta faɗa tare da yin gaba don shiga part ɗin don ta ga fuskar yayan na su yau ba alamar wasa, hakan yasa ta shiga taitayinta.


"Safnah!" Sadiq ya faɗa lokacin har sun kusa shiga part ɗin.


Juyowa Safnah ta yi, alama yayi mata da hannu alamar ta zo.


Tahowa Safnah ta yi, Teemah kuma ta wuce part ɗin,




"Gani yaya Sadiq!" Safnah ta faɗa lokacin da ta ƙaraso.


"Babban yaya ke son magana da ke" Sadiq ya faɗa tare da ƙoƙarin miƙewa, jawo rigar shi Abdul yayi ta baya, alamun ya zauna, sannan ya kalli Safnah yace.


"Safnah ya ƙarfin jikin na ki?"


"Yayi sauƙi sosai yaya"


"Masha Allah!" Ya faɗa ba tare da ya sake yin wata magana ba.


Sadiq ne ya kalli Safnah tare da cewa


"Safnah akwai wata magana da nake son faɗa miki ne dama!"


Dum! Gaban Safnah yayi mummunan bugawa, dakewa Safnah ta yi tace


"To yaya ina jin ka!"


"Amma kafin nan ina so na tambaye ki, ki na da wani wanda kike so ne, kuma kin taɓa soyayya?"


Tara-tara kirjin Safnah ke bugawa, kamar ze fito waje, bata jin zata iya magana hakan yasa ta gyaɗa mai kai alamar a'a.


"To Safnah dama akwai wani wanda ya nuna yana son auren ki kuma mutumin kirki ne Safnah, ina fata zakiyi na'am da shi"


Shiru Safnah ta yi kanta a ƙasa don bata san me zata ce ba.


"Kinyi shiru Safnah!" Sadiq ya faɗa ganin shirin nata yayi yawa.


Kafin ya sake cewa wani abu suka ji shigowar motoci guda uku gidan, hakan yasa Sadiq cewa Safnah "ba wani bare ba ne Safnah, a cikin Familyn mu ne, kuma ze bayyana a gare ki anjima kaɗan, zan so ki ƙarɓi tayin soyayyar sa, domin idan ba haka ba, ze shiga wani hali, domin ya narke a son ki Safnah, ki je ciki se mun sake haɗuwa"


Sadiq ya faɗa tare da miƙewa don tarbo motocin don Abdul har ya tashi ya tafi wajen.


Safnah da gumi ya karyo mata sosai kamar ta shiga ruwa, jan kafarta ta fara yi don zuwa part ɗin don tafiya yana neman gagararta.




Mota ɗaya Baba Salihu ne da iyalan gidan sa, ɗayar kuma, Baba Mustapha ne, se ɗayan kuma Baba Sagiru.


Gaishe su Suka yi tare da nufar falon dukan su, kai tsaye ɗakin kaka su ka nufa don kowa ya zo can yake zuwa domin gaishe da tsohuwa mai ran ƙarfe.


Ƙarfe 11:45 kowa a dangin na su ya hallara, se mutum ɗaya ake jira gwaggon su Maryam, wacce take aure a Zamfara, amma ita ma ta kusa ƙarasowa don har ta shigo cikin garin.




Mota gudu uku ne su ka sake shigowa gidan, wanda na abinci ne da akayi odar su, dama duk idan za'ayi wannan taron odar abinci suke yi mai rai da lafiya, kuma mai kyawun gaske kala-kala.




Wani babban ɗaki da ya kasance anan ake gudanar da taron nan aka buɗewa masu kawo abinci, shiga dashi sukayi tare da shirya abinci su ka ɗauka akan kujerun da su ke zube a ɗakin masu kama da dining table, ko wanne mazaunin mutum shida6 ne, hakan yasa aka zuba abinci flate shida, da kuma sauran kayan tanɗe-tanɗe.




Ƙarfe 12:00 dai-dai aka buɗe musu ɗakin kowa ya shiga, duk Familyn ba wanda be zo ba, har da yara, amma kuma su yaran wanda ba su haura shekara 10 ba ɗakin su daban ne.




Kowa a mazaunin da ya saba zama anan ya zauna, Teemah, Sa'adatu, Meenal, Hindatu, Safnah da kuma A'isha kujerar su ɗaya, kamar yadda Abdul, Sadiq, Marwan, Umar, Mujahid da Majid su ma tasu ɗaya, haka dai har iyayen na su mata, da sauran su, amma Mazan kuma su ta su kujerar ita ce a gaba.


Kamar yadda suka saba, kowa se ya cika cikin shi kafin su fara gudanar da taron na su.


Bayan kowa ya gama cin abincin ne, aka fara da buɗe taro da addu'a wanda Baba Salihu ya gabatar kasancewar shi Babba, daga nan aka shiga tattaunawa akan matsalar da take damun Familyn da kuma yadda za'a magance ta.


Dai-dai nan kuma aka tsaya domin lokacin sallah yayi ƙarfe 1:45 kowa tashi yayi don zuwa ya gabatar da salla, za su cigaba ƙarfe 3:00.


Bayan anyi sallar ne kuma suka shiga yin hotunan, don dama duk inda dangi suka taru zaka samu suna hotuna domin tarihi.




Ƙarfe 3:00 aka dawo aka cigaba zuwa huɗu kuma za su tashi.


Baba Bashir ne riƙe da speaker yana magana.


"Kamar yadda suka sani abu na ƙarshe da zamu tattauna shine akan auren yaran mu da aka riga aka sanar da sa ranar wasu daga ciki yayin da wasu kuma ba su fito da wanda suke so ba, a zaman da muka yi kafin wannan taron, mun tsayar da cewa duk wanda be fito da wanda zai aura ba, za muyi haɗi ne".


Yana kai wa nan ya miƙa abun magana ga Baba Sagiru.


"Kamar yadda kuka sani, an sanar da sa ranar, Hindatu da Meenal se kuma Sa'adatu wanda sun dai-dai ta da ɗan uwanta Sadiq, se kuma A'isha, a mata wanda muke sa ran aurar da su a wannan shekarar Fatima da Safnah ne kawai ba su fito mana da wanda suke so, amma Mazan ma Baba Mustapha yace sun faɗa mai, in sha Allah nan da kwana biyu 2 za'a je neman mu su auren, yanzu muna son ganin Fatima da Safnah domin su gabatar mana da na su zaɓin"


Safnah tunda aka fara taron dama bata cikin hayyacin ta, tunda ya Sadiq yayi mata magana ɗazu ta birkice ta rasa nutsuwarta, hakan yasa bata samu damar jin me ake cewa ba, saboda hankalinta bashi wajen su, don duk shirme ta ɗauki wannan taro.


Teemah ne ta ɗan taɓa ta tare da faɗa mata abinda ke faruwa.


Miƙewa su kayi jiki ba ƙwari su ka nufi wajen suna ƙarasawa Baba Mustapha ya ƙarɓi abin maganar tare da cewa


"Muna sauraren ku, ku gabatar mana da zaɓin ku"


Wata irin kunya ne ta rufe su, sun rasa ma abin faɗa se zare idanu suke yi.


Ganin abinda ke shirin faruwa yasa Abdul-jabbar tashi ya nufi wajen da su ke


Ƙarasawa yayi tare da cewa


Ku biyo ni a kashi na gaba domin jin yadda za ta kasance.




Comment ɗin ku shike ƙara min ƙarfin gwiwar yi mu ku Update akai-akai.






Taku har kullum
Khadeejerh Ishaq ✍️ ce





??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*_29&30


Ganin abinda ke shirin faruwa yasa Abdul-jabbar tashi ya nufi wajen da su ke


Ƙarasawa yayi tare da cewa


"Baba dama akwai maganar da nake so mu yi da kai, kuma akan Teemah da Safnah ne"


"To Abdul-jabbar ina jin ka" Baba Mustapha yace


Murmushi yayi tare da sosai ƙeya sannan yace "a'a Baba idan an tashi zan sameka se muyi maganar"


Murmushi Baba Mustapha yayi tare da cewa "to idan an tashi ka sameni a gidana"


"To shikenan"
Abdul yace tare da zama a wata kujera da yake gaban, dama an tanade ta domin shi ne, kasancewar shi babban ɗa gaba ɗaya Familyn.


Baba Mustapha ne ya umarce su Teemah da su koma su zauna, ba ɓata lokaci su ka koma.


Cigaba akayi da gudanar da taron na su mai cike da burgewa da nishaɗi a tsakanin su, har zuwa ƙarfe shida 6:00 na yamma sannan aka rufe taro da addu'a.


Wanda suke kusa ne su ka fara haramar tafiya gida kasancewar magriba ta gabato, wanda su ke nesa kuma part ɗin suka koma don anan za su kwana.


Wasu ma duk da suna kusa amma a nan za su kwana cikin su har da A'isha da kuma ƙannen Hindatu da sauran su.




Su Hindatu part ɗin su Teemah suka nufa don gabatar da sallah sannan su huta.


Zaune su ke a ɗakin da ya kasance na mallakin Teemah ne, suna zaune a kujera 3siter dukan su, Meenal ne ta kalli Teemah tareda kwashewa da dariya kana tace


"Teemah kinsan menene?, Wallahil ɗazu na so yaya Abdul be je yayi belin ku ba, da na ga yadda za kiyi, ƙaryar rashin kunya ki ke yi"


Duka dariya su ka saka amma ban da Teemah da ta ɓata rai kallon su ta yi tare da cewa "ai wallahi kun san ba abu mai yuwa ba ne na fidda kai na, ko shi yaya Abdul ɗin da kuke magana yayi belin mu, wallahi ba don ni yayi ba, yayi ne don wata manufa tashi" Teemah ta faɗa Murmushi ɗauke a fuskarta.


"Ba wani nan kawai ya ga baku da mafita ne, kuma ya ga abokin shi ne yake son ki shiyasa" Hindu ta faɗa


"To yanzu miye na yin wannan maganar kuma?" A'isha ta faɗa


"Kyale su wallahi dai-dai nake da su, duk maganar da za su faɗa ina da amsarta, Ehem!"


Duk hirar da su ke Safnah ne kawai bata yi magana ba don kallon su kawai take, hankalinta bashi akan su.


"Yawwa kun ce saboda ni budurwar abokin shi ne, to ita Safnah fa?, Kawai abar maganar nan kar ayi tone-tone.


"To shikenan yafi muku dai" A'isha tace


Da haka suka bar zancen suka kama wata hirar.


Wajen ƙarfe 9:00 Meenal tace zata koma part ɗin su saboda tafi son ta kwanta a kusa da momynta, Hindu ma bin ta ta yi su ka koma, ya kasance saura A'isha da Safnah.




A ɓangaren Abdul kuwa, ana kammala taron su ka nufi part ɗin shi tareda Sadiq, wanka su ka yi tare da shiryawa, don a daren nan yake son ya samu Baban na su Mustapha akan maganar.


Wajen ƙarfe takwas 8:00 su ka kama hanyar gidan.


Kasancewar gidan ba nisa zuwa takwas 8:20 su ka isa gidan Baban na su.


Ƙaton gida ne sosai haɗaɗɗe, har falon su ka shiga kai tsaye kasancewar gidan ba baƙon su ba ne, domin matar baban na su A'isha akwai kirki da yi mu su mutumci, yana da yara biyar ne.


Kamar yadda ta saba tarba mai kyau ta yi mu su, duk da bata daɗe da dawowa gidan ba, kayan ci da na sha ta jere musu sannan ta shiga domin kiran mu su Baban na su.


Mintuna biyar da shigarta ya fito, sanye yake cikin

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads