Header Ads
Showing 51001 words to 54000 words out of 57539 words

Chapter 18 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

563

Ads at the middle of Article

halartar wannan taro, amarya ma ta na cikin fili ta na rawa, ango kuwa ya fita tun ɗazu, dama Kamal ne ya jawo shi cikin filin don yace ba ya rawa, amma Safwan gwanin rawa ne.


A ɓangare guda kuwa Abdul ne da Faruq da kuma Sadiq sun jingina a jiki wata mota suna hira idon su na kan filin, dai-dai lokacin kuma su Hindu su ka fito, Abdul se watsa ido ya ke don ya ga wankan Sahibar shi, amma be gan ta ba, be kawo komai ba, a tunanin shi ko ta riga yin gaba ne began ta ba, don wajen da taron jama'a, su na ƙarasawa kuwa Amarya Salmah ta jawo Teemah ta saka ta a filin rawar fisgewa Teemah take yi amma Salmah ta riƙeta ba don ta so ba ta hakura, saitin kunnen Salmah Teemah ta je tare da cewa "don Allah kar ki faɗa mu su ni ce budurwar Faruq"
Don tun ɗazu ta na ji wasu na tambayar ina surukar ta mu?.


Dariya Salmah ta yi su ka cigaba da rawar su Hindu ma ba'a bar su a baya ba sun shiga fili kasancewar ƙawayen amarya ne a filin yanzu.


Komai da ya ke gudana akan idanun Abdul ake yi da Faruq don Sadiq ma ya bar wajen ya na can wajen ƴan mata, idanun Abdul har yanzu ba su hango mai Safnah ba, taɓo Faruq yayi tare da cewa "zo ka rakani wajen can!"


"Ni ma yanzu dama zan je" wajen su ka nufa, Abdul Hindu ya kira tare da tambayarta Safnah, ta faɗa mai ita su ka bari a ƙarshe, shi kuma Faruq wajen mai dije ya nufa.


Da sauri Abdul ya nufi ɗakin don ganin abinda ya hana Safnah fitowa, kai tsaye ɗakin ya nufa kasancewar a buɗe ya ke, can ya hangi Safnah ta kifa kai a kujera, zuwa yanzu ta daina kuka se sheshsheƙar kuka ta ke yi.


"Safnah!" Abdul ya faɗa cikin ɗaga murya, a firgice ta tashi don ta tsorata sosai, hanjin cikinta se da ya kaɗa.


Shi kan shi Abdul be san da karfi ya kira sunanta ba.


"Safnah kin ce min ba komai ɗazu, amma yanzu kuka fa ki ke yi"


Safnah shiru ta yi, don ta rasa me za ta ce.


Ƙarasawa yayi wajen da ta ke yana faɗin "Safnah me ya ke faruwa ne"


"Yaya Abdul bakomai kawai kai na ne ya ke ciwo!"


"Subhanallahi! Shine ba ki faɗa min tun ɗazu ba, da mun je ko chemist ne ai"


"Yaya yayi sauƙi ma yanzu!"


"Za ki iya fita wajen yanzu?"


Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh


"To tashi ki shirya ina jiran ki a wajen idan an tashi taron se mu je chemist!"


"To!" Safnah ta ce tare da miƙewa, shi kuma Abdul ya fita waje.




Kayan Safnah ta saka sannan ta ɗauki gyalen ta yafa, ji ta yi ba za ta iya fita a haka ba, cirewa ta yi ta ɗauki wani farin hijabi a cikin kayan ta ta saka.
.
Zama ta yi ta na sake-sake a zuciyarta don ba ta so Safwan ya gan ta ko kaɗan, gashi idan ta ki zuwa, Abdul ze tambayeta dalilin hakan, bata da wani zaɓi da ya wuce ta fita, miƙewa ta yi ta nufi wajen, ta na buɗe kofar ta ga Abdul a tsaye


"Masha Allah wallahi duk kin fi su kyau ma da ki ka saka hijabi, dama wallahi kishin ki fito da gyalen na ke yi!" Safnah ba ta ce komai ba se ƙaƙaro murmushi ta yi.


"Mu je to!" Abdul ya faɗa, gaba Safnah ta yi Abdul ya na bin ta a baya.




Faruq kuwa ce wa Dj ya yi yace kowa ya bar filin amarya ake son gani da kuma Antyn amarya Fatima.


Cak! Kiɗan ya tsaya Dj ya bayarda sanarwar da aka bashi.


Teemah har za ta gudu Salamah ta riƙo ta, ba ta da wani mafita se tsayawa ita ma jawo Meenal ta yi, su ka zama su uku ne a filin, Teemah ji ta yi kamar ta nitse a wajen jin mutane sun fara faɗin


"ita ce Fatima wanda aka yi mu su baiko da Faruq!"


Dai-dai lokacin Abdul ya fito shi da Safnah, tun kafin su ƙaraso wajen Faruq ya je tare da ce mu su "dama ku na ke jira!, Ku shiga fili mu yi rawa!"


"Lallai ne, ni ka ga na yi maka kama da mai yin rawa, ita ma ba ta rawa kuma ba ta jin daɗi!"


"Kai Mallam kar ka rai na min wayo!, Kai ne ba ka rawa? Kai fa ka koya min fa!"


"To amma ka san dai ba zan shiga filin rawa ba ga Teemah, idan akace waccan kuma fa?, Se ace yayanta ne!, Kai ka ga abin yayi dai-dai" dariya Faruq tare da cewa


"Gaskiya ne babban yaya!, Antynmu Allah ya baki lafiya"


"Ameen Safnah ta faɗa" sannan su ka jero zuwa wajen lokacin har an saki kiɗa, su huɗu ne a filin yanzu da wata ƙanwar Momyn su Faruq (Maman Farida) riƙe da hannun Teemah ta na jujjuyata, Faruq ma filin ya shiga don takawa shi ma, kan kace me fili ya cika da ƴanuwa se takawa ake yi.


Abdul kuwa wani waje ya samar wa Safnah ta zauna, shi kuma ya koma daga can gefe in da su ke tsaye ɗazu.


Safnah se wurga idanu take yi, amma bata sake ganin Safwan ba, ta na ji dai Dj na faɗin ango ya shirya za'a sake dawo dashi filin.


A ɓangaren Safwan wani waje aka tanadar mu su shi da abokan shi gefen filin kaɗan, duk da mutane ma a wajen amma su su na can daga ciki ne.


"Safwan ka ɗan ƙara haƙuri mana, an kusa magriba na san yanzu za'a tashi!"


"Ni wallahi na gaji kuma tafiya zan yi, na gaji da wannan haukan na su, se wani kiɗe-kiɗe ake yi da raye-raye mara ma'ana!"


"To ya mu ka iya zama za muyi dole!"


"Gashi wallahi na ji jikina kamar zazzaɓi ne ze kama ni, ga zuciyata se bugawa take yi!" Safwan ya faɗa


"Ko ma miye dai zama za ka yi!"


Safwan ya na rufe baki Dj ya fara kiran ango da abokan shi, tsaki ya ja tare da miƙewa ya nufi wajen, har ga Allah ya ƙosa ya tafi gida ma.


A ɓangaren Safnah kuwa hijabinta ta jawo ta rufe fuska don kar Safwan ya gan ta, ta kusa da ita ya zo ya wuce, ji ta yi kamar ta kwala mai kira ya zo gareta, amma bakinta yayi mata nauyi, kuma zuciyarta ba ta umarce ta da hakan ba, amma idanunta se zubar da kwalla su ke yi.




Salmah da Teemah ne har yanzu a filin, ko da Safwan ya ɗora idanun shi akan Teemah se da gaban shi ya yi mummunar faɗuwa.


"Safnah!" Ya furta a zuciyarshi lokacin ɗaya kuma duk nutsuwar shi ta rabu da shi, Teemah fita ta yi ta bar su daga Safwan se Salmah don hoto za su yi.




A ɓangaren Safnah zuciyarta kamar za ta fito daga ƙirjin ta, tsabar baƙin ciki da ta ke ciki ba ta taɓa tsammanin ganin wannan rana ba ko a cikin mafarkinta.




Taro yayi taro an ta shi taro cike da farin ciki a ɓangaren wasu kuma cikin baƙin ciki su ke musamman ma Safnah.


Ɗakin da su ka sauka su ka je su ka gabatar da sallar Magriba sannan su ka zauna domin hutawa, ba daɗewa kuma Salmah ta shigo ta kawo mu su abinci mai rai da lafiya, sun cika cikin su sosai, amma banda Safnah don ko kallon abincin ma ba ta yi ba.




Misalin ƙarfe 8:25 Abdul ya shigo ya kira Safnah don ya kai ta Chemist, duk da ɗazu ciwon ƙarya ta yi mai, amma zuwa yanzu kan ta kamar zai tsage biyu tsabar ciwo.


Wani babban chemist su ka je da ya ke Gaskiya layout Zaria, magunguna aka haɗo mata sosai, sannan ya biya wani super Market yayi mata siyayyan kayan ciye-ciye, sannan su ka nufi gida.




Ɗakin da aka sauke su ta nufa, Abdul da Faruq kuma su ka nufi na su ɗakin, ko da Safnah ta shiga kwanciya ta yi bayan ta sha maganin, su Hindu ne su ka cinye duk kayan ciye-ciyen don Safnah ko ta kan shi ba ta bi ba.








*****WASHEGARI*****


Misalin ƙarfe 2:00pm aka ɗaura auren Muhammad M. (Safwan) da kuma Ummu Salmah Ahmad akan sadaki dubu ɗari biyar 500'000 wanda ya samu halartar dubban Jama'a tun daga kan manyan mutane da kuma ƙanana ma.


Zan tsaya a nan


Ku cigaba da kasancewa da ni don jin yadda zata kaya a cikin wannan ɗan littafin nawa, Nagode sosai Allah ya bar zumunci, ayi hakuri na ji na shiru kwana biyu2.


Ta ku Khadeejerh Ishaq ce ✍️









??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*_39&40


Biki yayi biki, domin an narka Naira a wannan bikin duka gida biyu, ba zan ce ga wanda su kafi rawar ƙafa a bikin ba, kowa ka gani fuskar shi ɗauke da farin ciki da annashuwa, an ci an sha, ƴan uwa da abokan arziki kamar ƙara watso su ake yi.


Yau ne kuma ƴanuwan Momyn Safwan su ka zo, Safwan ya ji daɗin zuwan su sosai, don har ga Allah ya na son ƴanuwan Momyn shi fiye ma da na Daddyn shi.


Ɗunguma su ka yi duka su ka nufi gidan da za'a kai Amarya don akwai kwarya-kwaryan Walima da aka shirya misalin ƙarfe huɗu a gidan lokacin kuma za'a kawo Amarya.




**********


A ɓangaren gidan su Amarya ma shirin kai Amaryar ake yi domin yanzu ƙarfe 3:00 ne, kuma zuwa ƙarfe huɗu za'a kai ta, su Hindu ma ba'a bar su a baya ba don sun sha wanka iya wanka, amma ban da Safnah da tun wankan da ta yi da safe ta saka kaya bata canza ba, su kuwa kayan jikin su shine na huɗu ma da su ka saka yau don duk Anko ɗin da aka fitar se da Momyn Faruq ta saka aka ɗinka mu su kusan kala biyar.


Se misalin ƙarfe 3:45 sannan Safnah ta tashi ta canza kaya shi ma don Abdul ya kirata ya shaida mata gashi nan zuwa za su tafi Walima ne, yau tun safe ba ta gan shi ba ma saboda zirga-zirgan da su ke yi.


Wata shadda blue colour ta ɗauka ta saka, duk a cikin Anko ɗin ne, se baƙin takalmi da baƙin jaka, sannan ta ɗora pink ɗin gyale, ta yi masifar kyau duk da ko hoda ba ta shafa ma fuskarta ba.


Fitowa daga ɗakin ta yi zuwa babban falon, ba wasu mutane sosai don duka sun tafi wajen Walima se ƴan kaɗan su ma shirin tafiya su ke yi.


Ɗakin da ta tabbatar su Hindu na can ta nufa, ɗakin ya kasance na Salmah ne, a can kuwa ta same su su ma su na shirin fitowa har da amarya Salmah.


Ƙasa Salmah ta yi da idon ta duk da dama ta na cikin lulluɓi ne, saboda ba ta son su haɗa ido da Safnah don kunyar ta take ji kuma jikinta se yayi sanyi.


"Safnah ya jikin na ki?" Hindu ta faɗa tare da kamo hannun Safnah.


"Da sauƙi!" Safnah ta faɗa.


Sauran ma ya jiki su ka yi mata sannan su ka fito waje, su na fitowa kuwa aka ɗauki guɗa, kai tsaye motar da aka tanada domin Amarya da ƙawayenta aka buɗe mu su su ka shiga amma ban da Safnah don Abdul ya ce kar ta bi kowa shi zai zo su tafi, ta na tsaye a wajen motar ta tashi ta nufi gate ɗin gidan.


Motar na fita wata mota ta shigo, har wajen da Safnah ta ke motar ta perker, buɗe glass ɗin motar aka yi, Abdul ne fuskar shi ɗauke da murmushi, alama ya yi ma ta da ta zo, zuwa ta yi tare da buɗe murfin motar ta shiga, kunna motar yayi tareda barin gidan.


"Safnah ya jikin na ki!" Abdul ya faɗa tareda kallon Safnah.


"Da sauƙi!" Ta ba shi amsa.


"To amma kin sha maganin ko?"


Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh, sannan ya ƙara cewa "Shiyasa na ce da kai na zan zo na kai ki, saboda ba na son ayi min gudu da ke a hanya!"


"Da nisa ne wajen walimar?"


"A'a Samaru ne wai can za'a kai Amaryar"


Mummunan bugawa ƙinjin Safnah ya yi jin ya ambaci Samaru "wato gidan su Safwan Salmah za ta zauna ma lal....."


"Kin san kuma ban wani sanin wajen ba, karanbani zan yi!, Don mun zo jiya kila na gane" maganar Abdul ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi.


Murmushin yaƙe Safnah ta yi, don ta gaji da surutan da Abdul ya ke yi mata.


Tafiya su ke yi har Samaru Safnah na hangen gidan Anty don ta kusa da wajen su ka wuce, har gidan su Safwan se da aka wuce, don gidan ya na can cikin anguwar ta su ne.


Gidan yayi masifar haɗuwa sosai da sosai, a can ta samu su Hindu har sun isa, har ma an fara Walimar su na wajen, su ma wajen Walimar su ka nufa Safnah a gaba Abdul na biye da ita.


Kan ta a ƙasa ta ke tafiyar ta na jan ƙafa, kamar an ce ta ɗago kai su ka haɗa ido da Safwan, zuciyarta se da ta buga, da sauri ta juwo don duk rintsi ba za bari Safwan ya gan ta ba, da alama be gan ta ba, don ko murmushi ne ta san ze yi da ace ya gan ta.


"Ya aka yi kuma?" Ta ji Abdul ya faɗa, ita ta ma manta tare su ke tafiya, dabara ce ta zo mata, duƙawa ta yi tare da riƙe ciki tace "yaya Abdul cikina ke ciwo!"
"Subhanallahi!, Sannu, za ki iya tafiya kuwa?" Abdul ya faɗa cikin tashin hankali.


"Ehh zan iya!" Ta faɗa


Mota ya mayar da ita ta zauna sannan ya juya ya na faɗin "bari na kai ma Faruq wannan se na zo mu koma chemist ɗin!"


"Yaya Abdul!" Ta kira sunan shi, juyowa ya yi tare da cewa "ya aka yi?"


"Yaya don Allah ka bar ni na je gidan Anty mana!"


"Wacce Anty?" Ya tambaya


"Gidan Kawuna!"


"A'a ban yarda ba!, Yanzu ba ki da lafiya ki bari gobe se na kai ki!"


Kuka Safnah ta fashe da shi tare da faɗin "yaya Abdul don Allah ka bar ni wallahi na ji sauƙi"


"To shikenan kin iya driving ne?"


Da sauri ta ce "Ehh na iya!" Tare da share hawayen da su ka wanke mata fuska.


Shiru Abdul ya yi ya na tunanin ya rasa gane kan Safnah tun da su ka zo garin nan.


"A'a ba ri na kai ki kawai se na dawo!" Abdul ya faɗa bayan ya dawo daga tunanin na shi.


Motar ya shiga shi ma tare da kunnawa ya bar gidan.


Mintuna biyar 5 ya kawo su gidan Kawun na ta, perking ya yi da sauri Safnah ta ɗauki jakarta za ta fita.


"Ba za ki yi min sallama ba ne!"


"To se anjima yaya!" "Haka ne sallamar!, To ki gaishe da su, gobe zan zo na ɗauke ki se na shiga na gaishe da su, yanzu Faruq se kirana ya ke yi"


"To yaya nagode!" Safnah ta faɗa tare da buɗe motar ta fita.


Abdul juyawa ya yi ya koma gidan, Safnah kuwa da mugun sauri ta shiga gidan ta na kwala kiran Anty.


Anty da ke tsakar gida ta na aiki da sauri ta ɗago jin muryar Safnah na kwala mata kira, ta na ɗagowa su ka haɗa ido da Safnah, ita a zaton ta gizo kunnuwanta su ke yi ma ta.


Da sauri Safnah ta ƙarasa ta rungume Anty tare da fashewa da kuka.
"Safnah kukan na miye kuma, ya isa mu shiga ciki" Anty ta faɗa tare da jan hannun Safnah su ka nufi falon, da saurin yaran ma su ka ta so su ka rungume Safnah su na faɗin "oyoyo!, Anty Safnah ta dawo"


Cikin farin ciki da Safnah ta manta rabon da ta yi irin shi ta rungume yaran su na murnar ganin juna.


"Anty amma ba za ki sake tafiya ki bar mu ba ko?" Afrah ta faɗa.


"Ehh ina tare da ku" Safnah ta faɗa da Addu'ar Allah ya sa hakan.


"Anty kin je bikin yaya Safwan kuwa?"


Halima ta tambaya.


Gyaɗa ma ta kai kawai Safnah ta yi alamar a'a don shine kawai amsar da za ta bayar.


"Anty bari na ɗauko miki key ɗin ɗakin ki ma!" Khalil ya faɗa tare da miƙewa ya nufi ɗakin shi.


Cikin ƴan sakonni ya dawo hannun shi ɗauke da key ɗin, miƙa mata ya yi, da sauri ta ƙarɓa.


"To Khalil uban azarɓaɓi ka bari ta huta ai ko!" Anty ta faɗa


"A'a Anty ni kai na na yi kewar ɗakina da abinda ya ke ciki!" Safnah ta faɗa tare da karɓar key ɗin ta fita da sauri.


Anty kuma uniform ɗin su ta kwaso mu su na Islamiyya su ka saka don lokaci ya yi tun ɗazu ma, se da su ka leƙa ɗakin Safnah su ka mata sallama sannan su ka wuce makarantar ba don son ran su ba, don sun yi kewar Antyn su Safnah sosai.


Safnan ko da ta shiga ɗakin fes! Ta gan shi, kamar akwai mutum a ciki, tsayawa ta yi ta ƙare wa ɗakin kallo kafin daga bisani ta shiga uwarɗakar ɗakin nata, fitilar ɗakin ta kunna kasancewar akwai wutar nefa, durowar da ta ke ajiye kayan karatun ta ta nufa tare da buɗewa, computer ta ta fara cin karo da ita a sama, ɗaukowa ta yi tare da komawa ta zauna a kan madaidaicin gadon na ta.






Kunnawa ta yi ta dinga shige-shigenta a ciki, hawaye na bin fuskarta na baƙin cikin karatunta da aka daƙile mata, wani ɓangaren na zuciyarta kuma Safwan kawai ta ke tunawa haɗe da jin kishin sa a zuciyarta.




Ta yi mintuna 15 ta na kuka a ɗakin na ta kafin ta ji

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads