Showing 48001 words to 51000 words out of 57539 words
Chapter 17 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
mata yana hanya dama shi ake jira a fara.
Wani ɗaki da aka tanada musamman domin su aka kai su sallah su ka fara yi kafin daga bisani aka gabatar mu su da abinci kala-kala.
Su na cikin cin abincin Salmah ta shigo fuskarta ɗauke da fara'a wajen Teemah ta nufa ta rungume ta ta na faɗin
"Barka da zuwa Anty Fatima"
Safnah kuwa gabanta ne yayi mummunan bugawa da ganin Salmah.
"Sannu ku ya hanya?" Muryar Salmah ya dawo da Safnah daga tunanin da ta tafi.
Ɗagowa Safnah ta yi tare da cewa "yawwa sannu!" Ita ma Salmah zuciyarta se da ya buga daurewa ta yi tace "Safnah ashe ki na nan"
"Ehh ina nan" Safnah ta faɗa daƙyar.
"Ku ci abinci se Farida ta kai ku ku gaishe da Momy, mutane sun yi min yawa ne, amma Farida za ta kawo mu ku kaya se ku saka ku fito wajen taron"
"To shikenan ba komai" Meenal ta ce.
Salmah kuwa juyawa ta yi ta na sake-sake a zuciyarta.
Safnan kuwa neman nutsuwarta ta yi ta rasa, hankalinta a matuƙar tashe ya ke, Salmah na fita ba daɗewa su Abdul su shigo ɗakin.
Gaishe da su su ka yi, zama su ka yi bayan sun amsa gaisuwar, Abdul idon shi yana kan Safnan ya karanci tsantsar damuwar da take fuskar Safnah.
"Ya hanya mutanen Katsina?" Faruq ya faɗa.
"Alhamdulillah! Yaya Faruq" Hindu ta faɗa Teemah kuwa sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tun lokacin da su ka shigo ɗakin, Abdul ne ya kalleta tare da cewa
"Ke kuma miye haka kamar wata munafuka kin shiga hijabi?"
Su Meenal kuwa dariya maganar shi ta ba su, Teemah kuwa haushi ta ji, da za ta nu na rashin kunyarta ta shine na farkon wanda ze mata magana.
"Haba Abdul, Teemah ce fa ka ke ce mata haka" Faruq ya faɗa.
Dariya Abdul yayi tare da cewa "to kai ba ka ga abinda ta yi ba ne?"
"Kunya ce fa!" Hindu ta faɗa.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa "ina Sadiq ɗin?"
"Tun da mu ka zo ba mu gan shi ba"
"To ku yi ku gama cin abincin ku shirya ku fito waje"
"To yaya" A'isha ta faɗa.
"Safnah ba ko magana?" Faruq ya faɗa ya na kallon Safnah.
"Kai kar ka takura mata fa mu je kawai" Abdul ya faɗa ya na jan hannun Faruq zuwa waje.
Sai da su ka kai ƙofar sannan Abdul ya juyo ya ce "Safnah zo nan!"
"Laaa! Laaa!!! Yaya a gabana ba ka jin kunyata ko?" A'isha ta faɗa,
Murmushi yayi tare da jawo ƙofar, Safnah tashi ta yi ta bi shi, su Teemah se tsokanarta su ke yi, don Faruq yana Fita Teemah ta buɗe fuskar ta.
A ƙofar ɗakin ta ga Abdul ɗin shi da Faruq, ƙarasawa ta yi tare da cewa "ga ni yaya"
"Safnah me yake faruwa ne? Na ga ki na cikin damuwa"
"Bakomai yaya"
"A'a ban yarda ba, ki faɗa min"
"Dagaske babu komai"
"To shikenan, amma ki saki ran ki kin ji!, Kin san ba na son na ga fuskar ki da damuwa"
"To yaya" Safnah ta ce
"To ki koma ku shirya se ku fito bari mu shirya mu ma"
Yana faɗin haka ya juya ya nufi ɗakin Faruq, don Faruq tun ɗazu ya wuce.
Safnah kuwa bata koma ɗakin ba se fitowa ta yi har zuwa babban falon gidan na su, babu kowa a falon, don duk su na tsakar gida, don har an fara gudanar da Fulani day ɗin.
Safnah har ƙofar falon ta zo can ta hango taron mutane sosai.
Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa har sai da ta kusa faɗuwa ƙasa, wata mata ce da ta zo wucewa ta riƙeta tare da ce mata "sannu" Safnan kasa magana ta yi se ɗaga kai.
Ba komai ya haddasawa Safnah wannan ba, face ganin Safwan riƙe da hannun Salmah a cikin filin rawa.
Ku kasance da ni don jin yadda za ta kasance,
Na ga addu'o'in ku sosai, kuma ina godiya, Allah ya bar zumunci, ayi min afuwa na ji na shiru, yanayin jikin ne da wasu abubuwan, amma na ji sauƙi sosai, zan cigaba da kawo mu ku.
Safnah fa ta ga Safwan! Shin me ze faru idan shi Safwan ya ga Safnan ze fasa auren Salmah ne ko kuma ya za ta kasance?
Amsoshin tambayoyin yana cikin wannan ɗan littafin.
More comment
More typing
Khadeejerh Ishaq ✍️ ce
??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*_37&38
Jingina Safnah ta yi da jikin wani window da ke falon, ka na iya ganin tsakar gidan ta Window kasancewar shi na glass, Kuka mai tsuma zuciya Safnah ta ke yi, ƙara kallon Window ta yi don ganin ko dai gizo idanunta su ke mata, tabbas idanunta ba gizo su ke ba Safwan ne ta gani.
"Innalillahi -wa-Inna ilaihi raji'un" Safnah ta furta a fili jin wani irin bugu da zuciyar ta take, muryar Abdul ta jiyo da Faruq alamun fitowa su ke yi, da sauri ta shige wani labule da ke gefe don kar su ganta.
Tsayawa ta yi da kukan da take don za su iya ji, sanye su ke cikin kaya irin na Fulani ya yi masifar yi mu su kyau, kamar ba su ba, sun saka hula irin ta Fulani.
Ta kusa da Safnah su ka wuce, Allah ya sa ta na cikin labulen da sun gan ta.
Jan kafafunta ta yi ta nufi ɗakin da su ka sauka, ta tarar da su duk sun shirya cikin kayan Fulani sun yi kyau sosai, gyale fari su ka ɗaura akan kayan don Abdul se da yayi mu su kashedi kar su fito haka, amma mutane da yawa idan su ka saka kayan ba abinda su ke ɗorawa a kai.
"Safnah idan kin gama soyewan se ki zo ki shirya ko?" Meenal ta faɗa.
Daƙyar Safnah da daure ta ce "Ku je gani nan zuwa!"
"Ai ko ba ki ce ba, don tafiya za mu yi, sahibin na ki se ya zo ya raka ki" Hindatu ta faɗa, Safnah ba ta tanka su ba, ta ƙosa su fita ne ma ta yi kuka ko raɗaɗin da take ji a zuciyarta ze yi sauƙi.
Fita su ka yi bayan sun nu na mata kayan ta, su na fita ta durkushe a wajen ta saki kuka mai tsuma zuciya, a hankali sautin kukan nata ya ke tashi.
A filin Fulani day kuwa Maza da mata ne su ke cashewa abun su, dangin amarya da na ango don su ma sun samu halartar wannan taro, amarya ma ta na cikin fili ta na rawa, ango kuwa ya fita tun ɗazu, dama Kamal ne ya jawo shi cikin filin don yace ba ya rawa, amma Safwan gwanin rawa ne.
A ɓangare guda kuwa Abdul ne da Faruq da kuma Sadiq sun jingina a jiki wata mota suna hira idon su na kan filin, dai-dai lokacin kuma su Hindu su ka fito, Abdul se watsa ido ya ke don ya ga wankan Sahibar shi, amma be gan ta ba, be kawo komai ba, a tunanin shi ko ta riga yin gaba ne began ta ba, don wajen da taron jama'a, su na ƙarasawa kuwa Amarya Salmah ta jawo Teemah ta saka ta a filin rawar fisgewa Teemah take yi amma Salmah ta riƙeta ba don ta so ba ta hakura, saitin kunnen Salmah Teemah ta je tare da cewa "don Allah kar ki faɗa mu su ni ce budurwar Faruq"
Don tun ɗazu ta na ji wasu na tambayar ina surukar ta mu?.
Dariya Salmah ta yi su ka cigaba da rawar su Hindu ma ba'a bar su a baya ba sun shiga fili kasancewar ƙawayen amarya ne a filin yanzu.
Komai da ya ke gudana akan idanun Abdul ake yi da Faruq don Sadiq ma ya bar wajen ya na can wajen ƴan mata, idanun Abdul har yanzu ba su hango mai Safnah ba, taɓo Faruq yayi tare da cewa "zo ka rakani wajen can!"
"Ni ma yanzu dama zan je" wajen su ka nufa, Abdul Hindu ya kira tare da tambayarta Safnah, ta faɗa mai ita su ka bari a ƙarshe, shi kuma Faruq wajen mai dije ya nufa.
Da sauri Abdul ya nufi ɗakin don ganin abinda ya hana Safnah fitowa, kai tsaye ɗakin ya nufa kasancewar a buɗe ya ke, can ya hangi Safnah ta kifa kai a kujera, zuwa yanzu ta daina kuka se sheshsheƙar kuka ta ke yi.
"Safnah!" Abdul ya faɗa cikin ɗaga murya, a firgice ta tashi don ta tsorata sosai, hanjin cikinta se da ya kaɗa.
Shi kan shi Abdul be san da karfi ya kira sunanta ba.
"Safnah kin ce min ba komai ɗazu, amma yanzu kuka fa ki ke yi"
Safnah shiru ta yi, don ta rasa me za ta ce.
Ƙarasawa yayi wajen da ta ke yana faɗin "Safnah me ya ke faruwa ne"
"Yaya Abdul bakomai kawai kai na ne ya ke ciwo!"
"Subhanallahi! Shine ba ki faɗa min tun ɗazu ba, da mun je ko chemist ne ai"
"Yaya yayi sauƙi ma yanzu!"
"Za ki iya fita wajen yanzu?"
Gyaɗa mai kai ta yi alamar Ehh
"To tashi ki shirya ina jiran ki a wajen idan an tashi taron se mu je chemist!"
"To!" Safnah ta ce tare da miƙewa, shi kuma Abdul ya fita waje.
Kayan Safnah ta saka sannan ta ɗauki gyalen ta yafa, ji ta yi ba za ta iya fita a haka ba, cirewa ta yi ta ɗauki wani farin hijabi a cikin kayan ta ta saka.
.
Zama ta yi ta na sake-sake a zuciyarta don ba ta so Safwan ya gan ta ko kaɗan, gashi idan ta ki zuwa, Abdul ze tambayeta dalilin hakan, bata da wani zaɓi da ya wuce ta fita, miƙewa ta yi ta nufi wajen, ta na buɗe kofar ta ga Abdul a tsaye
"Masha Allah wallahi duk kin fi su kyau ma da ki ka saka hijabi, dama wallahi kishin ki fito da gyalen na ke yi!" Safnah ba ta ce komai ba se ƙaƙaro murmushi ta yi.
"Mu je to!" Abdul ya faɗa, gaba Safnah ta yi Abdul ya na bin ta a baya.
Faruq kuwa ce wa Dj ya yi yace kowa ya bar filin amarya ake son gani da kuma Antyn amarya Fatima.
Cak! Kiɗan ya tsaya Dj ya bayarda sanarwar da aka bashi.
Teemah har za ta gudu Salamah ta riƙo ta, ba ta da wani mafita se tsayawa ita ma jawo Meenal ta yi, su ka zama su uku ne a filin, Teemah ji ta yi kamar ta nitse a wajen jin mutane sun fara faɗin
"ita ce Fatima wanda aka yi mu su baiko da Faruq!"
Dai-dai lokacin Abdul ya fito shi da Safnah, tun kafin su ƙaraso wajen Faruq ya je tare da ce mu su "dama ku na ke jira!, Ku shiga fili mu yi rawa!"
"Lallai ne, ni ka ga na yi maka kama da mai yin rawa, ita ma ba ta rawa kuma ba ta jin daɗi!"
"Kai Mallam kar ka rai na min wayo!, Kai ne ba ka rawa? Kai fa ka koya min fa!"
"To amma ka san dai ba zan shiga filin rawa ba ga Teemah, idan akace waccan kuma fa?, Se ace yayanta ne!, Kai ka ga abin yayi dai-dai" dariya Faruq tare da cewa
"Gaskiya ne babban yaya!, Antynmu Allah ya baki lafiya"
"Ameen Safnah ta faɗa" sannan su ka jero zuwa wajen lokacin har an saki kiɗa, su huɗu ne a filin yanzu da wata ƙanwar Momyn su Faruq (Maman Farida) riƙe da hannun Teemah ta na jujjuyata, Faruq ma filin ya shiga don takawa shi ma, kan kace me fili ya cika da ƴanuwa se takawa ake yi.
Abdul kuwa wani waje ya samar wa Safnah ta zauna, shi kuma ya koma daga can gefe in da su ke tsaye ɗazu.
Safnah se wurga idanu take yi, amma bata sake ganin Safwan ba, ta na ji dai Dj na faɗin ango ya shirya za'a sake dawo dashi filin.
A ɓangaren Safwan wani waje aka tanadar mu su shi da abokan shi gefen filin kaɗan, duk da mutane ma a wajen amma su su na can daga ciki ne.
"Safwan ka ɗan ƙara haƙuri mana, an kusa magriba na san yanzu za'a tashi!"
"Ni wallahi na gaji kuma tafiya zan yi, na gaji da wannan haukan na su, se wani kiɗe-kiɗe ake yi da raye-raye mara ma'ana!"
"To ya mu ka iya zama za muyi dole!"
"Gashi wallahi na ji jikina kamar zazzaɓi ne ze kama ni, ga zuciyata se bugawa take yi!" Safwan ya faɗa
"Ko ma miye dai zama za ka yi!"
Safwan ya na rufe baki Dj ya fara kiran ango da abokan shi, tsaki ya ja tare da miƙewa ya nufi wajen, har ga Allah ya ƙosa ya tafi gida ma.
A ɓangaren Safnah kuwa hijabinta ta jawo ta rufe fuska don kar Safwan ya gan ta, ta kusa da ita ya zo ya wuce, ji ta yi kamar ta kwala mai kira ya zo gareta, amma bakinta yayi mata nauyi, kuma zuciyarta ba ta umarce ta da hakan ba, amma idanunta se zubar da kwalla su ke yi.
Salmah da Teemah ne har yanzu a filin, ko da Safwan ya ɗora idanun shi akan Teemah se da gaban shi ya yi mummunar faɗuwa.
"Safnah!" Ya furta a zuciyarshi lokacin ɗaya kuma duk nutsuwar shi ta rabu da shi, Teemah fita ta yi ta bar su daga Safwan se Salmah don hoto za su yi.
A ɓangaren Safnah zuciyarta kamar za ta fito daga ƙirjin ta, tsabar baƙin ciki da ta ke ciki ba ta taɓa tsammanin ganin wannan rana ba ko a cikin mafarkinta.
Taro yayi taro an ta shi taro cike da farin ciki a ɓangaren wasu kuma cikin baƙin ciki su ke musamman ma Safnah.
Ɗakin da su ka sauka su ka je su ka gabatar da sallar Magriba sannan su ka zauna domin hutawa, ba daɗewa kuma Salmah ta shigo ta kawo mu su abinci mai rai da lafiya, sun cika cikin su sosai, amma banda Safnah don ko kallon abincin ma ba ta yi ba.
Misalin ƙarfe 8:25 Abdul ya shigo ya kira Safnah don ya kai ta Chemist, duk da ɗazu ciwon ƙarya ta yi mai, amma zuwa yanzu kan ta kamar zai tsage biyu tsabar ciwo.
Wani babban chemist su ka je da ya ke Gaskiya layout Zaria, magunguna aka haɗo mata sosai, sannan ya biya wani super Market yayi mata siyayyan kayan ciye-ciye, sannan su ka nufi gida.
Ɗakin da aka sauke su ta nufa, Abdul da Faruq kuma su ka nufi na su ɗakin, ko da Safnah ta shiga kwanciya ta yi bayan ta sha maganin, su Hindu ne su ka cinye duk kayan ciye-ciyen don Safnah ko ta kan shi ba ta bi ba.
*****WASHEGARI*****
Misalin ƙarfe 2:00pm aka ɗaura auren Muhammad M. (Safwan) da kuma Ummu Salmah Ahmad akan sadaki dubu ɗari biyar 500'000 wanda ya samu halartar dubban Jama'a tun daga kan manyan mutane da kuma ƙanana ma.
Zan tsaya a nan
Ku cigaba da kasancewa da ni don jin yadda zata kaya a cikin wannan ɗan littafin nawa, Nagode sosai Allah ya bar zumunci, ayi hakuri na ji na shiru kwana biyu2.
Ta ku Khadeejerh Ishaq ce ✍️
??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*_37&38
Jingina Safnah ta yi da jikin wani window da ke falon, ka na iya ganin tsakar gidan ta Window kasancewar shi na glass, Kuka mai tsuma zuciya Safnah ta ke yi, ƙara kallon Window ta yi don ganin ko dai gizo idanunta su ke mata, tabbas idanunta ba gizo su ke ba Safwan ne ta gani.
"Innalillahi -wa-Inna ilaihi raji'un" Safnah ta furta a fili jin wani irin bugu da zuciyar ta take, muryar Abdul ta jiyo da Faruq alamun fitowa su ke yi, da sauri ta shige wani labule da ke gefe don kar su ganta.
Tsayawa ta yi da kukan da take don za su iya ji, sanye su ke cikin kaya irin na Fulani ya yi masifar yi mu su kyau, kamar ba su ba, sun saka hula irin ta Fulani.
Ta kusa da Safnah su ka wuce, Allah ya sa ta na cikin labulen da sun gan ta.
Jan kafafunta ta yi ta nufi ɗakin da su ka sauka, ta tarar da su duk sun shirya cikin kayan Fulani sun yi kyau sosai, gyale fari su ka ɗaura akan kayan don Abdul se da yayi mu su kashedi kar su fito haka, amma mutane da yawa idan su ka saka kayan ba abinda su ke ɗorawa a kai.
"Safnah idan kin gama soyewan se ki zo ki shirya ko?" Meenal ta faɗa.
Daƙyar Safnah da daure ta ce "Ku je gani nan zuwa!"
"Ai ko ba ki ce ba, don tafiya za mu yi, sahibin na ki se ya zo ya raka ki" Hindatu ta faɗa, Safnah ba ta tanka su ba, ta ƙosa su fita ne ma ta yi kuka ko raɗaɗin da take ji a zuciyarta ze yi sauƙi.
Fita su ka yi bayan sun nu na mata kayan ta, su na fita ta durkushe a wajen ta saki kuka mai tsuma zuciya, a hankali sautin kukan nata ya ke tashi.
A filin Fulani day kuwa Maza da mata ne su ke cashewa abun su, dangin amarya da na ango don su ma sun samu