Showing 9001 words to 12000 words out of 57539 words
Chapter 4 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
yasa Safnah yin dariya sosai sannan tace "Kai ka girma ai dole momy tabar ji da kai" "kina so muyi faɗa ko" "a'a kayi hakuri to"
"Shikenan, amma gobe ki tabbatar wayan ki a kunne take" "baka da matsala zaka same ni" "to anjima zamu yi waya kar na kira ban samu ba"
"Baza ka samu bama, kai fa ka cika naci tunda nazo kullum se ka kira yafi sau biyar, to kiran na miye, baka gajiya ne kai" shiru taji yayi hakan yasa ta yin dariya "se na kira kawai yace tare da yanke wayar.
To a cigaba da labarin mu
Kamar kullum bayan su Safnah sun gama cin abinci su ka kwaso littafan su, wanda aka ba su Assignment se Safnah ta ko ya musu, har lokacin Islamiyya ta yi su ka ta fi.
Washe gari Safnah ta shirya kamar kullum ta shirya yaran su na zaune kasancewar yau kawun su shi ze kai su don yanzu ya sayi mota kwanan nan Bayan ya kimtsa ne ya fito su ka wuce Safnah ya fara aje wa ya bata d'ari biyar ta yi break Sannan ya ce Idan be zo d'aukan ta ta dawo a napep "to kawu Allah ya tsare", "Ameen Safnah".
More comment
More typing
Ku cigaba da kasancewa tare da ni
Taki Khadeejerh Ishaq ✍️
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*11&12
Safnah sauri take dom ta kusa yin latti ta zo dai-dai shiga ajin su su ka ci karo da wata za ta fito kallon kallo su ka tsaya yi ba lefi yarinyar kyakykyawa ce fara ce kuma, Safnah ce tace "yi hakuri ban gan ki ba" yarinyar da baza ta wuce sa'ar Safnah ba tace "bakomai"
Sannan ta mi'ka mata hannu su ka gaisa tace "sunana Salma daga jushi ni sabuwar zuwa ce" "Safnah Daga Samaru" kawai Safnah tace mata tare da wucewa don kawai ta ji yarinyar bata kwanta mata ba, ta na shiga kuma Safwan ya shigo Salma ta ga ni ta shigo ajin kujerar bayan su ta zauna ta na kallon irin kallon da Salma ta ke yi wa Safwan ran ta ba 'karamin 'baci ya yi ba.
Bayan an ta shi makaran ta Safnah ta na tsaye ta na jiran shi se hango shi ta yi shi da Salma sun fito se wani yamutsa fuska ta ke kamar ta ga kashi, har ya zo wajen motar shi shiga ya yi Salma kuma ta yi gaba tare da d'aga mai Hannu ta na murmushi, fitowa ya yi dai-dai in da Safnah ta saba jiran shi ya zo ya bud'e mata tare da cewa "ranki ya dad'e amin hakuri na shanya ki ko?, ayi hakuri" ko kallon shi ba ta yi ba ta shige motar su ka fara tafiya juyowa ta yi ta kalle shi tace "yau ne fa" "mene?" Murmushi ta yi tace "oho! ai ka fini sani wallahi kuma kaje ko, hm", dariya sosai Safwan ya yi don har ga Allah ma shi ya manta da wani party da za su, yace "yawwa nagode da tunamin da ma kuwa na manta, na biyo ta gidan ku ne muje", "Ehh mana" Safnah tace, "to 'karfe shida dai zan biyo miki", "to shikenan"
Hirar su su ka cigaba da yi har aka iso gidan su Safnah ya sauke ta ya wuce, perking d'in motar shi ya yi ya shiga falon sauri yake domin anty bata falon don yanzu baya son ganin ta ma, d'akin shi ya shiga yayi wanka sannan ya ya bud'e frige ya d'auko lemo da snak ya ci duk da haka yunwa ya ke ji sosai hakan ya sa shi fitowa zuwa kicin Lami mai musu aiki ya samu yace mata "me ki ka dafa?" mamaki ne ya kama Lami ganin Safwan ya zo neman abinci, bayan rabon shi da cin abincin gidan ita kan ta ta manta Idan ba Dadyn shi yana nan ba ne ya kira shi dole ya ci, zubo mai ta yi d'akin shi ya koma don ya ci tsakurar abincin kawai ya yi ya ajiye shi don ya ji ya 'koshi. Sallamar Kamal ya ji daga falon shi, fitowa yayi ya bud'e mai su ka shiga, Kamal ne yace "haba Boss na ji shiru baka yi wata magana ba ne kasan kuma anjima ne fa" murmushi Safwan ya yi sannan yace "Kamal kenan yau bazan samu zuwa ba ka gaishe da kowa a madadi na",
"Haba Boss kasan fa idan baka je ba wajen baya dad'i fa", murmushi Safwan ya 'kara yi yace "Kamal yau fa ba zan je ba gaskiya" kud'i ma su yawa ya d'ibo ya bawa Kamal yace ayi komai godiya Kamal ya yi sannan ya fita.
Safwan Baccin shi ma ya sha sosai don da ma ya gaji sosai ba shi ya tashi ba se 'karfe5, Cikin sauri yayi alwala yayi Sallah, sannan ya shiga ya 'kara yin wanka, ya fito ya shirya cikin shaddar shi maroon colour da ya yi matu'kar yi mai kyau, sannan ya d'aura agogon shi shima maroon colour mai tsadan gaske, sannan ya Saka takalmin shi shima maroon ne Idan kagan shi yayi masifar kyau sosai fitowa ya yi yaje inda su ke ajiye motoci guda ya zaba wanda sabuwa ce ma ya shiga idan ka gan shi kamar wani sabon ango, kai tsaye gidan su Safnah ya nufa, perking ya yi ya fito wani yaro ya aika gidan yace a kira mai khalil, don yasan yau Juma'a ne ba su da Islamiyya.
Su na zaune duka suna hira aka shigo wai khalil ya zo anty ta za ci ma Wani abokin shi tace "to saura a wuce yawo", murmushi khalil ya yi sannan ya fita, yana fitowa kuwa ya ga Safwan murna ne ya kama shi kasancewar su na yi sosai da Safwan zuwa ya yi ya mi'ka mai hannu su ka gaisa don dama sun sa ba, Safwan ne yace, "Anty tana nan?" "Ehh", "kace mata ta yi ba'ko amma kar ka ce ni ne", "to" khalil yace sannan ya nufi gidan da gudu, Yana zuwa yace momi kin yi ba'ko murmushi anty ta yi sannan ta ce "waye?, "ban san shi ba", "ok, kace ya shigo", "to momi" yace sannan ya nufi wajen ya fad'a wa Safwan ya shigo.
Safnah da ke zaune kusa da anty jin ance ta yi ba'ko ta mi'ke ta shiga d'akin ta don a tunanin ta 'yan uwan antyn ne
Safwan ne ya yi sallama ya shigo gidan anty murmushi ta yi tare da amsawa tace, "Safwan Idon ka kenan?", murmushi ya yi ya na sunkuyar da kai, don shi kan shi kunyar anty ya ke don ya rabu da zuwa gida, d'akin anty ya shiga ya zauna anty ta kawo mai kayan motsa baki ci ya yi sosai don gidan ba bakon shi ba ne, hira su ke yi yayin da Safnah har yanzu bata fito ba, Safwan ne yace "anty wai ina mutuniya ta?" dariya anty ta yi tace "dama wurin ta ka zo kenan?" "wane ni rufa min asiri anty ni ke na zo gaishewa" "to nagode, khalil je ka kira anty Safnah" fad'in anty, da sauri khalil ya mi'ke ya nu fi d'akin Safnah don kiran ta.
Akwance ya sameta ta na game a wayar ta, yace "anty ya Safwan na kiran ki" Safnah ta shi ta yi tace "ina yake?" "yana d'akin momi," murmushi ta yi sannan ta ce "ka ce ina zuwa to anty ya ce tare da fita, Riga da wando ne ajikin Safnah hakan ya sa ta d'auko after dres d'inta ta sa ka, ta d'auko hijab d'in ta wanda ya d'an wuce gwiwar ta ta saka sannan ta nufo d'akin Sallama ta yi Safwan da ke facecing ɗin kofar d'akin ya amsa tsayawa ta yi kallon shi don yanda ya had'u sosai don Safwan ba ma'abocin sa ka manyan ka ya ba ne se ta d'auro mai, kuma kyau su ke yimai sosai, sassanyar murmushi Safwan ya sakar ma ta ita ma Murmushin ta mayar mai, har yanzu bata bar kallon shi ba shi ma ita ya ke kallon, anty ce ta tsaya kallon ikon Allah sunyi minti1 a haka sannan Safnah ta shigo d'akin ta zauna tare da cewa "d'an rainin wayo na zaci ai ka ta fi ne ma?" Murmushi ya yi yace "yanzu zan wuce bakin ce na biyo miki ba?" Dariya Safnah ta yi tace "Wannan ba wankan Party ba ne ba", "to ke ai kin yi na Party ke" "to ana zuwa da hijab ne?"
"Ehh ma na Idan an je se ku cire a waje ba" "Allah ya tsare ni" "ke kad'ai ban da mu ko?" dariya ta yi tace, "har da ku mana da duk Musulmai" Ameen, Safnah ne ta juya tace "anty kin yi shiru ki na jin mu", murmushi anty ta yi tace "to ba kyale ni ku ka yi ba", "a'a anty ba mu kyale ki ba" cewar Safwan, anty murmushi kawai ta yi, Wayar Safwan da ke Aljihun shi ce ta fara ringing hannu yasa ya fito da wayar, cikin zafin nama Safnah ta kwace wayar ta fita da gudu ta na fad'in "'yan partyn ne ba, to wlh baza ka d'auka ba ma" shi dai Safwan murmushi ya yi kawai su ka ci gaba da hirar su da anty da su khalil da Halima.
Ita kuwa Safnah d'akin ta ta shige sannan ta duba sunan mai kiran, SALMA ta ga ni a rubuce, sosai ta yi mamaki kamar baza ta d'auka ba kuma se ta d'auka, shiru ta yi bata yi magana ba, daga can ta juyo muryar Salma na fad'in, "haba Safwan abun da ka ke min ya da ce kenan tun da aka ta shi school na ke kiran ka amma ka'ki d'agawa, hakan na cutar da zuciya ta ga shi baka ba ni amsa ta ba, nace Ina matukar kaunar ka amma kai baka fad'amin ba, zuciyata na azaftuwa da son ka sosai don Allah ka tausaya wa zuciya ta, ka yi magana mana ko zan ji dad'i a raina",
Safnah bushewa kawai ta yi awajen don ta yi danasanin d'aga wayar kar ta yi magana tace ta ji mata sirrinkan ta ta yanke kuma tace ya mata wulakan ci, ta na tunanin ne ta ji wayar ta yanke, Hamdala ta yi sannan ta koma d'akin tace "ga wayar ka Sweetyn ka ce ta kira", dariya ya yi yace "wayace to ki d'aga", "babu na yi ra'ayin hakan ne" "ya yi kyau", hira su ka cigaba dayi har gabanin magrib sannan Safwan ya mi'ke don tafiya gida yace wa khalil ya zo ya 'kar'bi tsarabar su, kayan za'ki ne su biskit, coculate, alawa da dai sauran su duk Safwan ya had'a musu, su ka yi sallama Safwan ya nufi gida,
Bayan Sati biyu da zuwan Salma makarantar, se faman shigewa Safwan ta ke don son shi ne ya kamata, kuma har ta fad'a mai ta na son shi yayin da shi be bata amsa ba ma amma ta ke ta haukan ta ita budurwan Safwan ce, Salmah irin yaran wa su kud'in nan ne sangartattu ga shi bata da kunya ko kad'an, soyayya ta ke nuna wa Safwan sosai wanda zuwa yanzu Safwan ya fara biye mata yayin da Safnah ke jin haushin hakan.
Hakan yasa Safnah ta rage shiga Safgar Safwan shi ma sosai ya shiga tashin Hankali.
Kanar kullum Safnah na zaune ita kad'ai don maryam kwana biyu bata zuwa makarantar Safwan kuma ta wuce shi da Salma su na hira, Salma ce tace "wai Safwan har yanzu ba ka ce min ka na so na ba" banza Safwan ya yi da ita, ta cigaba da cewa "Safwan da ace akwai yanda zan cire son ka a raina da tu ni na cire amma wallahi na ka sa don Allah ka tausa ya min", kallon ta Safwan ya yi sannan yace "na fad'a miki amma ina da budurwa ko", "na yarda Safwan ai namiji an bashi damar ya auri mata hud'u ma, duk da bani da ra'ayin zama da kishiya amma indai da kai ne na amince na yarda", shi Safwan abun ma ya fara ba shi mamaki don be iya wulakan ta mace ba da se ya mata wukakan ci ko zata kyale shi, muryar ta ya ji ta na cewa "Safwan ka ba ni soyayyar ka don Allah, ka ba ni dama" "to shikenan", "Nagode" tace sannan ya mi'ke yace "na tafi wajen bestyna", "to a gaishe ta" tace, sannan ya nufi wajen Safnah.
kamar daga sama ta ji Sallamar shi Zama yayi ku sa da ita yace "my lovely Besty na kwana biyu kin bar ni cikin damuwa ba ki kula ni", dariya Safnah ta yi tace "to ba kyale ni kayi ba nima", dariya Safwan yayi yace "kodai kishi ki ke na yi budurwa" Murmushi safnah ta yi ta ce, "Allah ya kyauta me ye abun kishi anan yarinya kamar aljana ga shi kamar ka hure ta fad'i 'kasa, se wani jan fuska kamar kosai" dariya sosai Safwan ya yi yace "Kin rai na min budurwa ko to zan ne mi wata" "ya fi maka dai".
Tun daga ranar kuma su ka had'e su ka cigaba da abotar su yayin da bangaren Salma ma ta na nan ta li'ke mai kamar manya.
yau Safnah ko da ta dawo makaran ta ta samu Kawun ta a gida kallo d'aya ta yi mai ta san ran shi a'bace ya ke, "sannu kawu" tace mai da'kyar ya amsa yace "ki shiga ki shirya ki zo ina da magana da ke" gaban ta yayi mummunar fad'uwa tace "to kawu", cikin sauri ta shirya ko abinci bata ci ba ta zo kallon ta yayi yace "Safnah Allah ya ga ni ina son zama da ke har na ga na aurar da ke amma kuma gaskiya dangin mahaifin ki baza su yarda ba don yau Baba Salihu ya kira ni ya na min wa su maganganu da ba su kamata ba abun ya ba ni haushi ne sosai Safnah", hakuri Safnah ta ba Kawun nata, don ya d'auki zafi, a haka har ya huce, "ba komai Safnah je ki", tashi ta yi ta koma d'akin ta
Bayan wata biyu2 su Safnah su na ta karatu sun ku sa fara Exam ma sati me zuwa za su fara Safnah ta dage da karatu sosai Safwan ma ba ba ya ba, Salma ma an dage don Safwan ya had'a su da Safnah ba lefi su na d'an mutunci sosai, amma idan ta ganta da Safwan haushi ta ke ji sosai a ran ta, amma bata bari Safwan ya lura da haka, shi kuma Safwan yanzu gaba d'aya ba ya jin dad'i ya rasa dalilin ba ya son Salma amma kuma yanzu biyayya ta ke yi mai sosai ya lura kuma ta na tsantsar kaunan shi, shiyasa yake ɗan kulata na wani lokaci.
Kamar Kullum Safnah na zaune ita da Maryam Salmah ta zo Sallama ta yi musu sannan tace "Sannun ku" Maryam kawai ta amsa mata, ta samu gurin ta zauna tare da cewa "besty ba magana" murmushin ya'ke Safnah ta yi tace "Sannu ina wani tunanin ne daban"
"ok"
Bayan sun koma aji Safnah can baya 'karshen ajin ta samu ta zauna sa'banin wajen da ta ke zana kusa da Safwan, hakan ya sa Salmah zuwa wajen ta zauna, Safwan ne ya kalleta yace "anan kike zama ne?" "ka yi hakuri na ga ta koma baya ne shiyasa", ta shi ya yi ya koma baya sunan ta ya kira, "Safnah! Safnah!!" d'ago kai ta yi da'kyar don kan ta da yake mata ciwo sosai yace "lafiya?" "kai na ke ciwo", "to ki dawo wajen ki mana" "a'a ka bar ni anan ma" yayi-yayi ta taso amma ta 'ki hakan yasa ya koma ba don ya so ba, Salma da ma ta koma wajen ta kallon ta ya yi ya mata alama da hannu alamar ta zo, tasowa ta yi ta na murmushi ta zauna don ta ji dad'i kallon ta ya yi yace "kinsan bana son surutu ko?" "to ranka ya dad'e", murmushi ya yi dai-dai lokacin kuma Safnah ta d'ago kan ta ba'kin ciki ne ya cika ta wato ya je can har da murmushi be da mu da Ciwon ta ba, shi ko Safwan murmushin ya yi na mamakin Salmah duk class d'in ta ta zu bar ita ce har da fad'in ya yi hakuri.
Safnah mi'kewa ta yi ta nufi waje Safwan da tun d'azu hankalin shi na kan ta shi ma ta shi ya yi ya fito office ya ga ta nufa, excuse da ba da akan za ta gida don baza ta iya zama har ta shi ba, fito wa ta yi da sauri ta nufi gate Safwan ne ya biyo ta yana ta kira amma ta yi banza da shi, bin ta ya cigaba da yi ya sha gaban ta yace "Safnah ya akayi ina ta magana kin kyale ni?" "gida za ni" kawai tace, sannan ta juya za ta tafi cikin zafin nama ya ri'ko hannun ta, cikin sauri ta juyo ta kalle shi da mamakin shi, kallon shi ta tsaya yi ko dai baya cikin hayyacin ne,
Safwan da se yanzu ya lura da Abun da ya yi da sauri ya saki hannun ta yace "kiyi hakuri Safnah muje na kai ki gida" "ba na so" kawai tace ta juya har da 'karawa da gudun ta, ta na fita kuwa ta samu napep ta tsayar ta mai kwatan ce har gida ya kawo ta ta bud'e jakar ta ta ciro d'ari biyu ta