Header Ads
Showing 12001 words to 15000 words out of 57539 words

Chapter 5 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

551

Ads at the middle of Article

ba shi, tun da ta fito ta ke jin gaban ta na fad'uwa sosai wata jibgegiyar mota ga kuma motar kawu shima a wajen ta gani a 'kofar gidan na su shiga ta yi bakin ta da sallama Anty da ta ke kicin ta amsa mata, "Sannu da gida anty" "yawwa Safnah".


Safnah d'aki ta shiga ta aje jakar ta ta fito don kamawa anty aiki don yau ba ta gama ba, fitowa ta yi tace Anty kawo na 'karasa", "a'a Safnah ba ki ga ma munyi ba'ki ba ne", se yanzu Safnah ta kalli d'akin ba'kin ta ga takalma se kuma ta tuna da motar da ta gani a waje "anty waye?" shiru anty ta yi "anty kin yi shiru", "Safnah Baba Salihu ne ya zo tafiya da ke katsina", wayar Safnah da ke hannun ta ne ta fad'i kasa ta ke ta tawarwatse har layin se da ya fita, tace "anty da gaske ki ke?", kafin anty ta yi magana, Baba Salihu ya fito daga d'akin, Cikin rawar murya Safnah tace, "ina....wuni... Baba", "lafiya lau Safnah shiga ki had'o kayan ki Katsina za mu wuce", "Baba don Allah ka barni anan jarabawa za mu fara fa, Next week don Allah ka bari mu gana", tsawa ya daka mata yace "kije ki shirya nace ko ba ki d'auki kaya ba zan aiko a kwasan miki", d'aki Safnah ta nufa yayin da wasu irin zafafan hawaye su ka wanke mata fuska rasa me ma zata yi ta yi se kawai ta zauna kan gado ta fara rusa kuka ga kanta har yanzu kamar ze fashe, Inna Aisha ne ta bud'e kofar tace "Safnah me ki ke yi ne haka muna jiran ki" se yanzu Safnah tasan ma da ita akazo, wato su biyu ne, "Inna don Allah ki ba shi hakuri ki ce ya bari na gama jarabawa" fita ta yi ta kyaleta, Kawu ne ya shigo yace "Safnah ki shirya ki bi su kinji kar ki saka komai a ran ki, Safnah na so na zauna da ke har kiyi aure don idan na ganki ina jin farin ciki kamar 'yar uwata na gani amma Safnah dangin mahaifin ki ba za su yarda ba, tun da na d'auke ki kullum cikin cewa ki dawo su ke bansan me yasa ba su son zaman ki anan ba Safnah, ko da sun ce an barki haka ba aure se karatun boko, kinsan su basu yi ba shiyasa ba su san mahimmancin shi ba, sun ce aure za su miki, Safnah ki yi hakuri amma ni na gama rike ki, ko inna tace nabar musu ke kawai tun da itama ta hakura da ke d'in Safnah ina miki fatan alkhairi kin ji Allah ya miki albarka" Safnah da tun da Kawun nata ya fara magana kukan ta ya tsaya cak, ta na sauraran shi, yanzu dagaske tafiyan zata yi wani marayan kuka ne ya kwace mata kuka take sosai anty ma juyawa ta yi ta bar d'akin don ta fara kwalla itama irin sabon da su kayi da Safnah yanzu idan ta tafi ai zata yi kewar ta sosai.
Baba Salihu ne ya dawo yace "ke Safnah ba nace ki fito ba ne ina jiran ki", mi'kewa ta yi ta fito don ba abun da take jin zata iya d'auka anty na tsaye a kofar d'akin ta, Gaban anty Safnah ta zo ta tsaya ta na kallon ta ido cike da kwalla, "Anty... Anty.." Safnah ke fad'i ta kasa yin magana ma rungume ta ta yi nan ta ci gaba da kwalla, anty ma hawaye ne ya fito mata saurin sharewa ta yi, Kawu ne yace "Safnah kukan me ki ke kamar ki na Ban kwanan mutuwa", kasa magana Safnah ta yi se juyawa ta yi ta nufi wajen harta ta fita waje ta dawo da gudu, tace "Anty wayata" da sauri Anty ta d'auko mata, "Anty layin fa?" na duba wajen ban gani ba amma zan duba miki" "to anty" tace sannan ta fita har zata shiga mota ta ga mai napep ya sauke su khalil da sauri ta 'karasa wajen su rungume su ta yi ta na kuka, Khalil ne yace "anty ina za ki?" "Katsina zan ta fi Khalil" "to yaushe zaki dawo?" "bazan dad'e ba zan dawo", "to anty meyasa ki ke kuka?" cewar Halima "ba komai zan yi kewar ku ne kawai, Khalil kace wa Safwan ya yi hakuri d'azu munyi fad'a da shi, sannan kuma kace mai ya ri'ke min al'kawari na, sannan kace mai ina... Ina..." Bata 'karasa ba Inna Aisha ta zo ta kama hannun ta suka nufi motar, Safnah na kuka haka nan ta saka ta amota, su ka nufi katsina, a mota in banda kuka ba abun da Safnah ta ke yi, yayin da su ka kyaleta, har bacci ya kwashe ta.







_‍♂️ƘADDARAR SAFWAN♂️
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍YAFI TAKOBI️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*13&14


Gaf da magrib su ka isa katsina gidan su yana nan inda ta sani se de an mai gyara sosai ya 'kara masifar kyau horn su ka yi a bakin gate d'in, masu gadi su ka bud'e mu su, su ka shiga ciki, su na perking su ka bud'e su ka fito, wa su 'yan mata da baza su gaza sa'ar Safnah ba naga sun zo da gudu had'e da rungume ta, "sannu da zuwa Safnah" su ka had'a baki su ka ce, Safnah da ta ci kuka har ta gode Allah ta yi shiru, bata ce musu komai ba, hannun ta su ka kama su ka shiga gidan.


"Masha Allah" na furta lokacin da na ga falon don katon falo ne sosai ya had'u ya ji kujeru had'ad'd'u sosai, Safnah d'akin su su ka shiga zama ta yi a kujerar da ke d'akin d'ayan ce tace "Safnah kin manta mu, ko magana kin ƙi mana ko?" "banajin dad'i ne" cewar, Safnah.


Abinci 'yan matan su ka zubo, Hindatu da Amina, su ka zauna tare da cewa "Safnah ki sauko muci, kai kawai ta d'aga musu don ba su san haushi su ke bata ba idan su na mata magana.


Bayan sun gama cin abinci su ka yi Sallah Safnah ta shi ta yi ta fita a d'akin kai tsaye d'akin momin ta ta nufa don baza ta manta da shi ba, murd'a wa ta yi taji a rufe, dai-dai nan kuma Baba mustapha ya zo, yace "Safnah a she har kin zo, yau Su yaya su ke cewa za su d'auko ki ashe har sun dawo", "Ehh" Safnah tace tare da gaishe shi, don tana mutukar son Baba mustapha don shi akwai son yara sosai gashi ya fi sakar musu fuska, gashi kuma shine ke tsantsan kama da Daddyn ta har muryar.


"Zaki shiga d'akin ku kenan?" Baba Mustapha ya tambaye ta "Ehh, amma naji a rufe", "Ehh yana rufe ne dama, mukullin na wajen yaya Babba, ki bari gobe zan karban miki, kinje kin gaida Kaka kuwa? Nima wajen ta nazo", 'ta dawo nan ne?" Safnah ta tambaya da muryar ta da tafi kama da ta masu jin bacci, "Ehh, zo muje" cewar Baba Mutapha miƙewa su ka yi zuwa can ciki zuwa wajen kakan na su, a wani d'aki na ga sun tsaya sallama ya yi aka amsa sannan ya shiga, wata 'yar tsohuwa ce wacce a kalla zata kai shekara 87 zaune a kan sallaya da alama sallah ta idar, gaishe ta Yayi ta amsa sannan Safnah ma ta gaishe ta kaka ce tace "wannan wace ce?"


"Ai 'yar wajen Abdallah ce" "oho kace Safnatu ce, zo nan Safnah mu gaisa Allah sarki auta na, ka gama wahalar ka tafi gashi se mu muke ci, Allah ya jikan ka" se kuma kuka, Baba mustapha ne yace "Don Allah ki bari kar ki ta so ciwon ki, addu'a za ki cigaba da yi mai muma munanan muna yi".
Share hawayen ta yi, sannan su ka d'an yi hira sannan su ka yi Sallama, Safnah ma sallama ta yi mata duk da batasan taka-maiman inda zata kwana ba. ko ina ta shiga kuma kwanciya zata yi, d'akin su Hindatu ta wuce "sannu" kawai tace musu sannan ta hau kujera ta kwanta, Amina, wacce su ke cewa meenal ce tace "Safnah idan Bacci za kiyi ki shiga Bedroom" "to" kawai tace sannan ta nufi uwar d'akan.


Masha Allah gaskiya ya had'u sosai Manya-manyan sif ne irin masu guda goman nan masu tsada ne guda, uku a d'akin ga drawer su, ga kuma wasu manyan gado guda biyu ko ba'a fad'a mata ba tasan kowa da gadon shi kenan d'aya ta za'ba tare da hawa ta kwanta, hawaye ne su ka fara bin fuskar ta don tun da ta shigo gidan nan ba abinda ya fad'o mata se Iyayen ta, sabo mutuwar su ta zaman ma ta, se juyi ta ke ta kasa bacci ga tunanin su anty da kawu da su khalil da acan ne ta tabbatar yanzu su na can suna hira, ga uwa uba tunanin Safwan ga kuma irin rabuwar da su ka yi, d'azu a makaranta kuka ta dinga yi har bacci 'barawo ya d'auke ta.




A bangaren Safwan tun da Safnah ta tafi, se ya koma Class zuciyar shi a cunkushe, don ya rasa meke yi mai dad'i ma a duniyar, ko da ya shiga shima kifa kan shi ya yi a kan benci, tunani ne su cika mai zuciya har ya rasa wanda ze yi, ana tashi ya hau motar shi se gida, yana perking ya fito da sauri ya nufi d'akin shi, ya kwanta, yana kallon sama yayin da idanun shi ke rufe, Juyo wa yayi laptop d'in da ke ajiye a drawer gefen gadon shi ya jawo tare da kunna ta, shige-shigen shi yayi wajen hotuna na gani ya shiga, hotunan ya tsaya yana gani, hotuna ne da yawan gaske don sunyi d'ari uku300 ko wanne da rubutu a kai, wani hoto ne ya zo kan shi Safna ce, a makaran tasa ka riga da wando ta ɗaura after dress akai ta yafa wani gyale dariya sosai kuma take yi wanda ya fito da tsantsar kyau ta, kallon hoton ya tsaya yi, se da na ƙura ido sosai sannan na iya ganin rubutun dake jikin hoton, "MY LOVELY FOREVER" na gani an rubuta da manyan ba'ki a saman hoton rufe system d'in yayi ba tare ma da ya kashe ba, sannan ya juya ya kwanta wayar shi ya jawo number Safnah ya kira a kashe sosai ya yi mamaki kan shi ya d'aure don Safnah bata barin waya a kashe, se idan ba lafiya, ba, to me ya faru, ko ciwon kai d'in ne, nan da nan tashin hankalin shi ya sake dad'uwa, tunani fal ran shi, bacci ne ya d'auke shi batare da ya zaci zuwan shi bama.


A gidan kawu kuwa tun da aka ta fi da Safnan su khalil su ka shigo gida su ka ce "momy ina anty Safnan za ta je?"


"ta tafi garin su hutu", "to kukan me take yi", "ba komai kawai dai, ku je ku cire kaya ku zo ga abinci kuci", "to momi" su ka ce, sannan su ka nufi d'akin, Anty cigaba ta yi da neman layin Safnah amma ba ta gan shi ba hakan ya sa ta barshi bayan sunyi Sallah ta zu bo musu abincin su ka zauna su ka ci sannan ko wa ya zauna shiru, Afrah ne ta nufi d'akin Safnah tana fad'in "anty! anty Safnah", anty ne ta rike ta tare da d'auko key ta saka ma d'akin, tace, "Afrah na anty ta tafi anguwa" "to yaushe zata dawo?" "Ta kusa" "kince ta kawo min tsaraba ko", "Ehh",


Littafan su su ka d'auko kowa ya duba wanda aka yiwa Assignment anty ta yi nu na mai.


A bangaren Safwan be tashi ba se 'karfe 4:30, wanka ya yi sannan ya ya yi Sallah, shirin shi ya yi cikin baƙin wando da kuma jar riga wanda ya yi bala'in yi masa kyau sosai, jikin shi ya feshe da turare mai masifar ƙamshi, falon gidan ya fito ya zauna, tare da kunna tv, tashar kwallo ya kamo kasancewa shi mayen kwallo, Momin Mansur ce ta fito cikin wani dakakken leshi purpule and Blue, se kuma adon ba'ki ajiki, sosai ya yi mata kyau, wajen Safwan ta nufa ta na dariya, "my son har ka fito da yanzu zan aika Mansur ya taso ka naga tun da ka dawo school shiru", mamaki sosai ya kama, Safwan ganin wannan abu, Daddyn shi ya ga ya fito, murmushi ya yi sannan a zuciyar shi, yace "lallai matar nan makira ce", da sauri ya nufi gurin Daddyn shi da ke saukowa daga step rungume shi ya yi, yace "wellcome Dad shine baza ka fad'a min zuwan ka ba se de na ganka", "to ayi min Afuwa my son" "shikenan Dad" jerowa su ka yi su na tahowa falon yanda kasan Hassan da Hussaini don Safwan tsantsar kama ce tsakanin su da Dad shi, se dai Safwan ma ya fi Daddyn shi tsayi da kad'an, Zama Dad ya yi sannan Safwan ya zauna ku sa da shi, "Ya karatu" Dad ya tambaye shi "Alhamdulillah Dad", "yayi kyau to, ya kuma maganar aure" dariya Safwan ya yi yace "Dad aure kuma?" "Ehh mana, Safwan ni nafi son ka yi aure da wuri yanzu shekarun ka ashirin da bakwai fa ka kusa talatin, ya kamata ka yi aure Safwan ka cika min gida da jikokin ka", "to Dad dama ina da budurwa ma" "to masha Allah se ka fad'a min ita sannan naje nema maka auren ta" "to Dad" yace Sannan yace "Dad na tafi kwallo" tare da mi'kewa ya nufi waje, murmushi Dad ya yi yace "to adawo lafiya ka kula dai", "to Dad" Sannan ya fice ya bar su su na hira da momin Mansur.


Safwan ko da ya fito tsayawa Yayi jiran wucewar Safnah, se yanzu ma ya tuna da cewa biyar ta wuce, don Safnah ba ta latti, hakan yasa ya wuce filin kwallon kasancewar a hanyar makarantar su ta ke yana yi amma hankalin shi na kan bakin hanya ko ze ganta amma shiru har su ka tashi, lokacin kuma yaga 'yan makarantar an tashe su tsayawa ya yi har su ka wuce amma be ganta ba, ko su Khalil be gani ba gida ya nufo zuciyar shi cike da tunani, kala-kala lokacin an fara kiran Sallar magrib d'akin shi ya wuce da sauri ya d'auko wayar shi ya sake kira amma har yanzu Layin Safnah a kashe sosai hankalin shi ya tashi, to ko ciwon kan ne wata zuciyar ta fad'a mai, abun da be sani ba Safnah ta sauka a katsina a wannan lokacin.




Masallacin ƙofar gidan su ya nufa domin yin Sallah Bayan yayi Sallah zama ya yi har se da akayi isha'i sannan ya dawo gidan afalo ya zauna kasantuwar yunwa da yake ji sosai hakan ya sa ya shiga kicin, mai akin su ya gani ya tambaye ta abincin don Safwan ba ya wasa da cikin shi, tace mai ai ta gama ta aje kan dining, dining d'in ya nufa, abincin ya gani kala-kala wanda ze ci ya d'iba ya nufi d'akin shi da shi, ko da ya isa d'akin ajiye abincin yayi Saman gado sannan ya zauna ya fara ci, wayar shi na hannun shi numbar Safnah ya sake kira, har yanzu a kashe, Bayan ya gama cin abincin ne ya koma ya kwanta, to me yake damun Safnah ya zama dole gobe ya je gidan su, ga kuma abun da Dad shi yace, magana ce yake yi a zuciyar shi, "kai lokaci ya yi da zan bayyana wa Safnah sirrin zuciya ta duk da nasan itama tana so na amma ba irin matan da su ke cewa su na so na bace ita baza ta ta'ba fad'a ba, domin Safnah daban take cikin mata, ga kuma wannan fitinanniyar Salma", tunani ya dinga yi har wajen 'karfe biyu sannan bacci ya d'auke shi.


Bara mu waiwayi mutan katsina


Safnah ko da gari ya waye da ciwon kai ta tashi mai tsananin gaske Sallah ta yi kawai ta kwanta, har wajen 9:00 tana kwance su Hindatu ne su ka zo su ka tashe ta wai Baba babba na kira, mi'kewa ta yi ta fito falon ta gaishe shi Sannan yace "kin ƙarya ne?" "a'a" "to kije dining ga abun karin ki can" "to" kawai tace "sannan idan kin karya kije ki gaishe da mutanen gida don yanzu gidan akwai wasu" "to" tace sannan ta nufi dining d'in su Hindatu ma binta su ka yi, don suma ba su karya ba tana ganin su seda suka cika filet sosai da abinci kuma kada'n su ka rage sun sha ruwan tea da chips na Dankalin turawa kuma, ita ko Safnah tea d'in kawai ta sha sannan ta zuba Dankali d'an kad'an shima bata cinye ba, sannan su ka mi'ke su ka nufi cikin gidan, Hindatu ne tace


"Safnah kin ga tsarin gidan ya canza ko, da ku kad'ai ne aciki, amma yanzu an kara part biyu ma wannan da kike gani ta nuna wanda su ka fito, shine akwai d'akin ku na da, to se d'akin mu se kuma d'akin kaka se d'akin ya Abdul d'an Baba Babba ne kuma shi d'in soja ne, sauran d'akin ma ba kowa a ciki, se wancen part d'in ta nuna mata wani part da suke nufa shine na Baba Bashir, d'aya kuma na Baba mudansir, na hannun daman su ka fara shiga wanda shine,

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads