Showing 39001 words to 42000 words out of 57539 words
Chapter 14 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
farar jallabiya, zama yayi a kujerar.
Gaishe da shi su ka yi sannan yace "Abdul har kun zo?, Na zaci ai se gobe"
"Ehh Baba har mun zo" Abdul ya faɗa
"To inajin ku!"
"Baba dama akwai wani abokina ne da ya nuna yana son auren Teemah, kuma mun gama magana dashi, idan anyi mai izini ya fito?"
"Masha Allah, naji daɗin wannan maganar, amma a ina yake?"
"Shi ɗan Kaduna ne, Zaria"
"To yayi kyau zamu bincika mu gani, idan ya cancanta se a bashi izini ya turo, duk da nasan ba zaka yi wa ƙanwar ka zaɓen tumin dare ba, saboda na san waye kai Abdul"
Murmushin jin daɗi Abdul yayi tare da cewa
"Nagode Baba"
"Bakomai, se kuma ita ɗayar wato Safnah na ji baka yi maganar ta bane?"
Sunkuyar da kai Abdul yayi yana Murmushi ba tare da yace komai ba, se ɗan taɓa Sadiq yayi alamar yayi magana.
Ai ko Sadiq kamar yana jira yace
"Baba wannan ai tashi ce, ku kawai yake jira ku ce kun bashi"
Murmushi Baba Mustapha yayi tare da cewa
"Masha Allah naji daɗi sosai da wannan haɗin, nasan kowa idan yaji ze ji daɗi, wato Abubakar kai ne rasa kunya ko?, Haka kazo ka shaida min abinda ke tsakanin ku da Sa'adatu"
Murmushi Sadiq yayi tare da cewa "ba haka bane Baba, gani nayi barin kashi a ciki ai baya maganin yunwa" Sadiq ya faɗa yana sunkuyar da kan shi ƙasa.
"To yayi kyau, zan samu Yaya na shaida mai, za'a san yadda za'a yi"
"To Baba mun gode sosai" Abdul ya faɗa tare da miƙewa su ka nufi kofar fita falon.
Washegari
Misalin ƙarfe 10:00 Safnah ta baro part ɗin su Teemah don zuwa ɗakinta, don rabonta da ɗakinta tun ranar da ta fara rashin lafiya.
Ɗakin su Hindu ta nufa domin tambayar mulkin nata, a falo ta same su suna hira, ƙarasawa ta yi tare da cewa.
"Barkan ku da safiya"
"Yawwa Safnah barka ykk?"
"Lafiya lau, an nace key ɗin ɗakina yake?"
"Yana wajen yaya Abdul"
"To shikenan" tace tareda fita waje, a ƙofar ɗakin ta tsaya tana saƙe-saƙe a zuciyarta, ta je ɗakin shi ne, ko kuma ta kira a waya ne.
"Safnah me kike yi anan?"
Ta ji an faɗa lokacin da ta dannawa yaya Abdul kira, hakan yasa ta yake kiran bayan ya fara ringing.
Ɗago da kanta ta yi "ina kwana Baba" ta faɗa lokacin da fuskarta ta yi arba da Baba Mustapha.
"Lafiya lau Safnah, ykk?"
"Lafiya lau Baba"
"Masha Allah, Safnah na ji abinda yake tsakanin ki da Abdul, kuma nayi farin ciki sosai da hakan, Allah ya baku zaman lafiya"
Dum! Gaban Safnah yayi wani irin mugun bugawa da jin maganar Baban na su, wanda bata san inda ya dosa ba.
Dogon tunani ta shiga wanda yasa bata san ya tafi ba ma, dama kaka ya zo gaisarwa.
Ringing ɗin wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin da take yi, ko da ta duba yaya Abdul ne, kaman kar ta ɗaga wayar, se kuma dai ta ɗaga tare da karawa a kunne.
"Assalamu alaikum" ta ji ya faɗa, daurewa ta yi ta amsa tareda gaishe da shi sannan tace
"Yaya key ɗin ɗakina fa?"
"Ki zo ki amsa yana wajena"
"To" kawai tace tare da yanke wayar, har yanzu bata shiga nutsuwarta ba, ɗakin nashi ta nufa, da sallama ta shiga.
Yana zaune yana kallo a Computer shi, "yaya ina key ɗin?" Safnan ta faɗa.
"Ki zauna Malama" Abdul ya faɗa ba tarda ya kalleta ba, zama Safnah ta yi a kujerar ta sunkuyar da kanta ƙasa, yayin da zuciyarta ke dukan tara-tara.
Kusan mintuna biyar 5 ya ɗauka kafin yace "Safnah me kika fahimta akan maganar da Sadiq yayi miki jiya?"
Bugun zuciyarta ne ya ƙaru da jin tambayar nashi, bata samu damar bashi amsa ba, don bata da amsar.
Duban shi ya kai wajen da take, tsura mata idanu yayi na wasu sakonnin sannan yace "Safnah bansan yadda zaki ɗauki abun ba, idan nace miki ni ne wanda Sadiq yayi miki magana akai, sannan na ƙara miki da cewa ina matuƙar ƙaunar ki Safnah!"
Da sauri Safnah ta ɗago kanta jin abinda yaya Abdul ɗin yake faɗa, ba dai maganar da Baba Mustapha yayi mata ɗazu bace take ƙoƙarin zama gaskiya, in dai hakane kuwa akwai matsala domin bata jin akwai wanda zuciyarta zata amshi tayin soyayyar shi.
Mayar da kanta ƙasa ta yi ba tare da tace komai ba
"Safnah ina so na ji daga bakin ki shin kin amince da soyayyata?"
Gyaɗa kai Safnah ta yi alamar a'a yayin da bugun zuciyarta ya tsananta yanzu.
"Safnan ban gane me kike nufi ba, kimin magana, idan ba so ki ke yi zuciyata ta tarwatse ba!"
Safnah ta rasa amsar da zata ba Yaya Abdul, hakan yasa ta yin shiru yayinda har hawaye sun wanke mata fuskantarta na jin takaicin abinda ya faɗa mata.
"Kin yi shiru Safnah!" Yaya Abdul ya faɗa ganin shirun nata yayi yawa.
Daurewa Safnah ta yi tace "Yaya Abdul ka yi hakuri"
Tashi tsaye Abdul yayi don maganar Safnah ta bashi mamaki, daurewa yayi yace "Safnah ban fahimci me kike nufi da nayi nakuri ba, baki so na kenan?"
Miƙewa tsaye itama tayi tare da cewa
Ku biyo ni a kashi na gaba don jin yadda zata kaya.
More comment
More typing
Khadeejerh Ishaq ✍️ ce
??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*_ 31&32
Miƙewa ita ma ta yi tare da cewa "Yaya Abdul kayi hakuri, akwai wanda na mallakawa zuciyata"
"Safnah waye shi?" Abdul ya faɗa cikin tashin hankali.
Shiru ta yi ba tare da tace wani abu ba, takawa yayi har zuwa wajen da take tsaye tare da cewa
"Safnah yanzu har akwai wanda zaki so sama da ni ɗan uwanki, nasan ki na faɗa ne kawai, amma rannan ai kin cewa Sadiq baki da wanda kike so!"
Juyawa Safnah ta yi ta nufi hanyar fita ɗakin ba tare da ta yi wani magana ba, shi ma Abdul be yi ƙoƙarin dakatar da ita ba yana gani har ta fice daga ɗakin.
Hankalin shi ya matuƙar tashi da amsar da Safnah ta bashi, ya rasa ma abunyi yanzu, zama tayi tare da jawo wayar shi.
Ita kuwa Safnah kai tsaye part ɗin su Teemah ta nufa, don bata tsaya karɓar key ɗin nata ba ma.
Ba kowa a falon hakan yasa ta nufar ɗakin Teemah kai tsaye, a falon ta sameta ta na waya, zama ta yi tana kallon ta.
Kimanin mintuna biyar 5 Teemah ta ɗauka sannan ta kammala wayar, kallon Safnah ta yi tare da cewa "Safnah ya naga kin dawo?, Yanzu nake shirin zuwa part ɗin ai"
"Teemah akwai matsala fa!"
"Subhanallahi!, Wacce irin matsala kuma Safnah?"
"Teemah yaya Abdul ne yayi min wata magana da take barazanar tarwatsa zuciyata"
Murmushi Teemah tayi sannan tace "Safnah ko baki faɗa min ba, nasan menene, kuma dama na daɗe ina sauraren zuwan wannan rana"
Kallon mamaki Safnah ta bi Teemah dashi sannan tace
"Ban fahimce ki ba Teemah"
"Safnah maganar gaskiya na daɗe da fahimtar yaya Abdul yana son ki, kuma kema da zaki nutsu ki lura zaki gane, a kwayar idon yaya Abdul kaɗai zaki iya hango tsantsar ƙaunar da yake miki Safnah, ranar da ki ka faɗa min cewa akwai wanda ki ke so a can Zaria, yaya Abdul kawai ya faɗo min, kuma na tausaya mai, amma da naji cewa ba tabbatacciyar soyayya ba ce a tsakanin ku naji daɗi sosai, saboda ni kai na nafi son ki da yaya Abdul"
Safnah mayar da hankali ta yi sosai kan abinda Teemah take faɗa, kuma ya shiga jikinta.
"To yanzu me ki ka ce ma yaya Abdul ɗin?" Teemah ta faɗa ganin Safnan bata da niyyar yin magana
"Na faɗa mai ba na son shi" Safnah ta faɗa cikin halin ko-in-kula.
"What! Safnah dagaske kike yi don Allah " Teemah ta faɗa cikin tsantsar takaici
"Ehh Teemah, kinsan ba wasa a tsakanin mu ai"
"Safnah don Allah kar ki ɗaukarwa yaya Abdul wannan ɗanyen hukuncin, ki tausaya masa Safnah, yaya Abdul be taɓa furta kalmar so ga kowa ba se ke Safnah, duk da tarin ƴan matan da suke son shi, don Allah ki kira shi kice mai wasa ki ke yi Safnah"
Ita kan ta Safnah ta ji ba daɗi na abinda ta yi wa yaya Abdul, amma abinda ke zuciyarta ne ta faɗa mai.
"To Teemah zan kira shi na bashi hakuri, ko na tura mai text" Safnah ta faɗa.
"To shikenan, ta so mu tafi part ɗin akwai inda zamu je da su Meenal ne dama"
"To" kawai safnah tace tare da miƙewa suka fita.
Kai tsaye part ɗin su Hindu suka nufa, a falo suka same su suna ta hira, harda yaya Abdul.
Gaban Safnah se da ya faɗi da ganin yaya Abdul ɗin, sanye yake cikin shadda army green yayi masa Bala'in kyau sosai, hira su ke yi kamar ba abinda ya ɓata mai rai ɗazu.
Ƙarasawa su ka yi suka zauna "a'ah! yaya Abdul irin wannan wankan se kace yau ne ranar" Teemah ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin zama.
"To sannu ƴar sa ido, ke baki iya ganin abu kiyi shiru ko?" Abdul ya faɗa tare da kai duban shi inda Safnan take, kanta a ƙasa yake hakan yasa be samu damar ganin kwayar idonta ba.
"Kun shirya kuwa?" Teemah ta faɗa tare da kai dubanta wajen da Hindu take.
"Ehh mana ke muke jira dama" Hindu ta faɗa.
"To sarakan yawo ina zaku? Abdul ya faɗa yana kallon Teemah
"Yaya za muje rabon cingam ne na sa ranar su"
"Se ki jira idan an saka naki se ku raba gaba ɗaya, amma ba inda zaku?"
"Haba yaya Abdul, don Allah ka barmu mana!" Meenal ta faɗa
"Yaya don Allah!" Hindu ma ta faɗa
Murmushi Abdul yayi tare da cewa "wato ku baku da kunya ko?, Zaku rabon cingam, to Allah ya shirye ku, ku bari jibi za'a kawo na Teemah se ku tafi gaba ɗaya"
Gaban Teemah se da ya buga da jin maganar Abdul ɗin, amma bata nuna ba, se cewa ta yi "to yaya tunda wannan fitar ta gagara se ka barmu muje mu sha ice cream"
"Ku je ku ɗauko a fridge, ai akwai a gida" Abdul ya faɗa
"Ai kuwa dai yaya don Allah ka barmu mu je"
Murmushi Abdul yayi a zuciyar shi tace "lallai wannan yaran da son yawo su ke, ko don ba'a barin su fitan ne yasa haka"
"Yawwa tunda kuka ga yana murmushin nan ya amince wallahi, ku dai kawai ku taso muje mu sake shiri don shirin zuwa shan ice cream daban yake" Teemah ta faɗa tare da miƙewa su ma suka rufa mata baya da gudu se kace wasu ƙananan yara.
A hankali Safnah ma ta miƙe domin bin su,
"Safnah!" Taji yaya Abdul ya kira sunanta
Tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba, "Safnah abinda kika faɗa min ɗazu shine gaskiyar abinda yake cikin zuciyar ki?"
Juyowa Safnah ta yi tare da kallon shi sannan tace "yaya Abdul ka yi hakuri da abinda ya faru ɗazu"
"To Safnan ba komai ni yanzu abinda nake son ji a ina ki ka ajiye ni Safnah"
"Yaya zan turo maka ta waya" Safnah ta faɗa don bata son ƙara ganin ɓacin ran yaya Abdul ɗin.
Murmushi Abdul yayi sannan yace "kije ki shirya zamu fita, sannan kice su kira Sa'adatu ma ta shirya mu tafi"
"To yaya" Safnah tace tare da nufar hanyar ɗakin nasu.
"Safnah!" Ta ji ya ƙara kiran sunanta
Juyowa ta yi don ganin ko dai ba yaya Abdul ɗin ba ne, tsaye ta gan shi yana kallonta.
Sassanyar Murmushi ya sakar mata tareda cewa "Safnah ina jiran amsar ki, don Allah ki amince min kin ji ƙanwata ta kaina"
Jikin Safnah sanyi yayi sosai da jin maganar yaya Abdul ɗin saboda cikin sigar tausayi yayi maganar tashi.
Ɗaga mai kai ta yi alamar "to" sannan ta shige ciki.
Da sallama ta shiga ɗakin, "Safnah kiyi sauri ki shirya mu wuce" Teemah ta faɗa bayan ta amsa sallamar ita kaɗaice a falo su Meenal sun shiga ciki don canza kaya.
"Ba shirin da zanyi, a haka kawai zan tafi ma"
"Ok kun tsaya soyewa kenan da mutumin naki ko?" Teemah ta faɗa Murmushi ɗauke a fuskarta.
"Ke dai kin cika neman magana wallahi" Safnah ta faɗa
Murmushi Teemaah ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba.
Dai-dai lokacin su Meenal suka fito sunyi kyau sosai amma fa hijab suka saka.
Jerowa suka yi suka fito, ba su samu Abdul a falon ba, hakan yasa su fita tsakar gidan.
Can suka hango Sa'adatu da yaya Sadiq sun nufo part ɗin na su, suna tafe suna hira cikin nishaɗi gwanin burgewa.
"Idan kun gama kun gama surutun ku taho mu tafi"
Su ka jiyo muryar yaya Abdul daga cikin motar shi da take nesa da su kaɗan.
Wajen motar suka nufa tare da buɗewa su ka shiga su huɗun.
"Ɗaya ta dawo gaba" suka ji yaya Abdul ɗin ya faɗa.
Teemah ce ta taso ta koma gaban ta zauna, dai-dai nan su Sadiq su ka ƙaraso.
Baya Sa'adatu ta shiga, shi kuma Sadiq ya shiga gaba.
"Sannu Anty Sa'adatu" Hindu ta faɗa tana murmushi.
murmushi Sa'adatu ta yi tare da cewa "kema sannu Anty"
Dariya su kayi sannan Teemah tace "su yaya Sadiq manya, ko kunyar mu baka ji, ka wani jero da ita kuna tafe juna hira ko? To kadai menene ƙawar mu ce ai"
"Lallai Teemah rashin kunyar na ki har ya kai ki yi wa matar da zan aura, itafa Antyn ku ce yanzu" Sadiq ya faɗa cikin sigar wasa.
Dariya suka kwashe da shi dukan su.
Jan motar Abdul yayi ya nufi hanyar fita gidan.
Haɗaɗɗen wajen shakatawa su ka je irin na ƴan gayun ƙarshen nan, sun ji daɗin fitar sosai domin sun ga gari kuma sun shaƙata sosai.
Se gabanin magriba sannan su ka dawo gidan, duka a part ɗin su Hindu suka sauka har Teemah saboda Ummanta bata nan, ta tafi garin su ɗazu har da ƙannenta ma, hakan yasa ta rufo part ɗin su ta dawo nan, saboda kwana Umman zata yi.
Sa'adatu ne kawai ta nufi part ɗin su, yayin da Sadiq suka nufi ɗakin Abdul tare.
Safnah ɗakinta ta nufa domin ta yi nasarar ƙarɓar key ɗin a hannun Yaya Abdul ɗazu.
Wanka ta yi ta canza kaya tare da dawowa falo ta kwanta tana ta danna wayarta.
Knocking ta ji daga bakin ƙofar ɗakin nata kasancewar ta rufe shi ne dama.
Miƙewa ta yi ta nufi ƙofar tare da buɗewa su Hindu ta gani tsaye a kofar.
"Bismillah ku shigo" ta faɗa tare da shigewa ciki.
"Safnah kice kina hutawa ne abunki" Meenal ta faɗa
"Ehh wallahi naji ina jin bacci ne sosai na gaji"
"Yawwa Safnah ana ta kirana a waya wai wani Khalil daga Zaria kuma yace Safnah yake nema"
Zumbur Safnah ta tashi kamar an tsunguleta tare da cewa "don Allah dagaske? Ina Number?"
Miƙa mata wayar Hindatu ta yi tare da cewa"nayi saving da Khalil.
Da sauri Safnah ta karɓa tare da kwashe number a wayarta, ta fara kira, amma kashhh! Number a kashe take.
"Nagode sosai Hindu" Safnah ta faɗa tare da miƙawa Hindu wayarta, hira suka cigaba da yi har tsawon wani lokaci ba tare da sun kwanta ba.
****Washegari****
Misalin ƙarfe 12:15 Safnah ne kwance a kujerar falonta hannun ta riƙe da wata, number nan take ta gwadawa amma taƙi shiga.
Tsaki ta yi tare da da yin jifa da wayar kan kujerar, bayan wasu mintuna ta ƙara gwada number.
Kira ɗaya ta yi sa'a ta shiga, wayar tana gaf da katsewa aka ɗaga.
"Assalamu alaikum" ta ji an faɗa da wata murya wanda kana ji kasan ta yara ce.
Amsawa Safnah ta yi tare da cewa "Khalil Safnah ce"
"Ba Khalil ba ne abokinshi ne" ta ji an faɗa.
"To don Allah ina yake shi?"
"Yana gidan su"
"To kai a ina kake?"
"Ni ina kusa da gidan su ne"
"Aminu ne?" Safnah ta tambaya.
"Ehh shine"
"Don Allah Aminu ka kira shi, amma kar kace waya za muyi kasan Anty bazata bari ba"
"To ki kashe bari na kira shi, zamu kira idan ya zo"
"To don Allah ka kira shi Aminu"
"To zan kira shi yanzu" ya faɗa tare da yanke wayar.
Aminu ya kasance abokin Khalil ne kuma kusa da gidan su take, Islamiyyar su ɗaya.
"Ko a ina Aminu ya samu waya?" Safnah ta tambayi kanta, sanin bata da amsar tambayar ne yasa ta juya akalar tunaninta zuwa wani wajen.
Ƙarar wayarta ya dawo da ita daga tunanin da take yi, koda ta duba number Aminu ce, yankewa ta yi sannan ta kira.
"Assalamu alaikum Anty Safnah ya kike?" Ta ji muryar Khalil ya faɗa
"Lafiya lau Khalil ya Anty da kawu?"
"Lafiyar su ƙalau, Anty kaka fa bata da lafiya tana gidanmu da zama ma yanzu haka"
"Subhanallahi! Khalil me yake damunta?"
"Wallahil Anty ban sani ba"
"Baka ji kawu na faɗin abinda yake damunta ba?"
"Ehh Anty"
"To Allah ya bata lafiya" Safnah ta faɗa cikin tsantsar tashin hankali.
"Anty jiya na ga yaya Safwan, amma ban bari ya ganni ba, saboda kullum maganar ki yake min, to ƙaryata ta ƙare bansan me zan ce mai ba, shiyasa nake ɓuya idan na ganshi"
"Khalil meyasa to baka bashi Number ta ba?"
"Anty wallahi Momy tace kar na sake na bashi wani bayani da na sani akan ki"
"Ya su Halima?"
"Suna lafiya, Anty yaushe zaki zo?, Ko se bikin yaya Safwan?"
Dum gaban Safnah yayi wani irin mummunan bugawa cikin tashin hankali tace "Khalil wani Safwan ɗin ne ze yi aure"
Cikin halin ko ina kula Khalil yace "Anty yaya Safwan dai da kika sani, saura kwana goma ma yau"
Zama Safnah ta yi don ta ji kafafunta baza su iya ɗaukanta ba, cikin rawar murya tace "Khalil kasan bana wasa da kai ko? Ka faɗa min dagaske kake yi ko ƙarya"
"Anty kinsan bana miki ƙarya wallahi bikin yaya Safwan saura kwana goma kuma Daddy na ji yana faɗa"
Wasu zafafan hawaye ne suka wanke wa Safnah fuska daurewa ta yi ta riƙe kukan da yake shirin zuwa mata tace "Khalil gobe za muyi waya, ka kashe"
"A'a Anty idan Momy tasan muna yin waya wallahi