Showing 42001 words to 45000 words out of 57539 words
Chapter 15 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
zata iya dukana musamman ma Daddy, ki bari bayan kwana biyu zan kira ki"
"To Khalil wayar waye ne wannan?"
"Wayar Aminu ce, yayan shi ya bashi ƴar ƙaramace ma"
"To shikenan se anjima" Safnah ta faɗa tare da yanke wayar.
Wani marayan kuka Safnah ta fashe da shi na takaici da tsantsar damuwa, yanzu ace Safwan aure ma ze yi, ya manta ma da ita kenan, amma ya barta da tunanin shi ba dare ba rana, lalle bai kyauta mata ba, abinda.
Safnah take ta saƙawa kenan a cikin zuciyarta.
Ta ci kuka sosai har ta gode Allah, daga bisani bacci mai nauyi ya kwashe ta.
Yaya Abdul ne zaune shi da Sadiq suna hira, don indai Abdul na gari to zaka same shi da Sadiq, domin suna bala'in yi dashi, kusan sa'anni suke amma Abdul ya ba Sadiq wata shida6.
"Abdul baka faɗa min yadda kuka ƙare da Safnah ba, kace ka faɗa mata"
.
"Ni kaina amsar nake jira, tace zata tura min ta waya amma tun ɗazu nake zuba idanu shiru"
"Hm kace kana cikin jiran tsammani, ai nasan zata amince maka ma babban yaya"
"Allah yasa haka" Abdul ya faɗa.
A ɓangaren Safnah kuwa knocking ɗin da ake yi a kofar ɗakin nata shi ya tashe ta.
Ƙofar ɗakin ta nufa domin buɗewa idanunta gaba ɗaya sun kumbura fuskarta ta yi ja, abinka da jar fata.
Teemah ta gani a tsaye lokacin da ta bude ɗakin, shigowa ta yi tare da cewa "Safnah lafiyan ki kuwa?, Tun ɗazu nazo amma ban gan ki ba, har sun gama cin abincin rana, amma sunce ba ki fito ba, gashi yanzu ƙarfe 3:30" ta ƙarasa maganar tare da zama a kujera dake ɗakin.
Safnah ma zama ta yi tare da cewa "wallahi bacci ne ya ɗauke ni"
"Amma ya naga idanun ki sun kumbura Safnah kamar kinyi kuka?"
Duk inda Safnah ta kai ga son riƙe kukan da yake shirin zuwa mata ta kasa, se da ya fito.
"Subhanallahi! Safnah kuka? Me ya faru?"
Cikin kukan Safnah tace "Teemah wani mummunan labari ne ya sameni ɗazu"
"Innalillahi -wa- Inna ilaihi raji'un waye ya rasu Safnah?"
"Teemah ba rasuwa akayi ba, wanda na baki labari ina so, shine ze yi aure Teemah"
"Gaskiya bai kyauta ba, amma kema ya kamata ki kyale shi, idan yana son ki baze taɓa yin aure ya barki ba"
"Hakane Teemah, amma Allah ya gani ina son Safwan sosai, se dai na roƙi Allah ya yaye min son shi a rai na"
"Ameen!, Kin ba yaya Abdul hakuri kuwa?"
"Ehh, amma ya ƙara cewa na bashi amsar shi, shine nace zan rubuta mai"
"To kin rubuta?"
"A'a" Safnah ta faɗa tana goge kwallar da take zubo mata da zarar ta goge wasu se wasu su fito.
"Safnah ni dai shawarar da zan baki ki amince da soyayyar Yaya Abdul, kin ga wanda ki ke so ɗin ma aure ze yi ya barki, kila ya manta da wata Safnah ma"
"Teemah nagode da shawarar ki, kuma zan yi aiki da shi"
"To shikenan, yanzu ki tura mai saƙon amincewa da soyayyar shi"
Miƙawa Teemah wayarta ta yi tare da cewa "Gashi ki tura mai"
Ƙarɓa Teemah ta yi tare da rubuta saƙo kamar haka:
"Assalamu alaikum yayana, farin cikina da fatan kana lafiya, yaya Abdul ka yi hakuri da abinda ya faru jiya, amma maganar gaskiya itace na karɓi soyayyar ka hannu bibbiyu, kuma na amince zan aureka idan Allah ya so, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, Ameen!"
Abinda Teemah ta rubuta kenan, ba tareda ɓata lokaci ba ta tura.
"Duba ki gani na tura" Teemah ta faɗa tare da miƙawa Safnah wayarta.
Karɓa Safnah ta yi tare da da dubawa "Kai! Teemah duk wannan kalaman haka, wallahi har kinsa na fara jin kunyar shi kafin na gan shi"
Murmushi Teemaah ta yi tare da cewa "lallai ma! su kunya anji jiki!"
"Wallahil Teemah da gaske nake bansan ya zanyi ba wajen ganin na mayar da yaya Abdul masoyi, saboda na riga na ɗauke shi a matsayin yayana, kuma ban ji son shi ya shiga rai na ba"
"Dama ba lokaci ɗaya soyayya ke shiga zuciya ba, amma akwai wanda lokaci ɗaya zaki ga ya shiga zuciya ya zauna, kamar dai Soyayya ta da Faruq, tun ranar da ya furta min yana so na, na kamu da ƙaunar shi, don a ranar ma kasa bacci nayi se tunanin shi, ki bada lokaci zaki ji kin fara son shi Safnah"
"To shikenan Teemah ya na iya zan ɗauki hakan a matsayin ƘADDARATA wacce take bibiyata a kullum"
"Kuma kinsan yaya Abdul har ya faɗawa su Baba maganar tsakanin ku, don na ji Faruq yace min gobe iyayen shi za su zo neman aurena, kuma za'a saka ranar ne tare da na yaya Abdul, da na tambaye shi da waye? Shine yace min da Safnan"
"Don Allah da gaske kike yi Teemah?"
"Wallahi kuwa!"
Kafin Safnah tace wani abu ta ji shigowar kira wayarta, ko da ta duba sunan yaya Abdul ta gani.
"Teemah yaya Abdul ke kira da!"
"To ina ruwana! Idan zaki ɗauka ma ki ɗauka, kinga tafiyata ki sameni a ɗakin su Hindu.
Teemah ta faɗa tare da barin ɗakin, lokacin kiran har ya yanke.
Wani kira ne ya sake shigowa wayar, se da ya kusa yankewa sannan ta ɗaga.
"Assalamu alaikum gimbiyar mata!" Ta ji muryar yaya Abdul ɗin ya faɗa, amsa sallamar ta yi tare da cewa "yaya Abdul ya kake?"
"Lafiya lau Safnah, naga saƙon ki, kuma naji daɗi sosai, kin sani farin cikin da na daɗe rabon da nayi irin shi, amma da kinsa zuciyata tana barazanar tarwatsewa"
Shiru Safnah ta yi tana sauraren yaya Abdul ɗin yayin da take cike da mamaki, wai yaya Abdul ne ke faɗin irin waɗannan kalaman.
"Kin yi shiru!"
Ta ji muryar shi yana faɗa "yaya to me zance?"
"Ke kike da abin faɗa kuwa, kina ina ne?"
"Ina ɗakina"
"To ki fito ki sameni a falo yanzu"
"To" kawai tace, sannan ya kashe wayar, miƙewa ta yi ta nufi falon.
Can ta hango shi a kan kujera shi kaɗai ne a falo, ƙarasawa ta yi har wajen.
"To ki zauna mana" Abdul ya faɗa, zama ta yi a kujeran kanta a ƙasa don wani irin kunyar shi take ji sosai.
"Ki ɗago ki kalleni mana!"
Dan ɗago da kanta ta yi suna haɗa ido ta sunkuyar da kai, murmushi yayi tare da cewa "wai kunyata ki ke ji ne?, To shikenan tashi ki je kimin girki, kinsan nayi kewar daddaɗan girkin ki, kuma baki tambayeni inda nake cin abinci ba ko?"
Miƙewa Safnah ta yi tare da cewa "to yaya bara naje nayi maka girkin"
Tans faɗa ta nufi ɗakin su Meenal da sauri don ta ga surutun na Abdul bashi da ƙarshe.
Zan tsaya a nan se mun haɗu a page na gaba.
Ina miƙa gaisuwata ga duk wasu masoya wannan littafin nawa, fatan alkhairi gare ku.
More comment
More typing
Khadeejerh Ishaq ✍️ ce
??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*_ 33&34
Da sallama safnah ta shiga ɗakin su Meenal ɗin.
Amsa mata su kayi sannan ta samu wuri ta zauna tarada cewa
"Yau mai aiki ta yi har da girkin dare ne? Naga har ta tafi"
"A'a Safnah!, Na rana kawai ta yi, dama ina jira muyi sallar la'asar ne se mu shiga kicin ɗin" Hindu ta faɗa.
"Ok, dama yaya Abdul ne yace nayi masa girki se kawai na haɗa nayi da na daren"
"A'a Safnah ki je ki yi mai, ƙila yanzu yake buƙata, dama girkin kashi biyu ne, Meenal za ta yi wa kaka na ta, ni kuma se nayi namu, ke kuma ki je ki yi wa Habibin ki girki kawai"
Meenal ta faɗa
Hararar wasa Safnah ta jefawa Meenal tare da cewa "se dai mijina ba Hubbina ba!" Ita kan ta Safnah bata san lokacin da maganar ta fito ba.
Dariya suka sa duka, Teemah ce ta ce "to kwana nawa ne ya rage ya zama mijin naki Safnah!"
"Ai kuwa dai faɗa mata!"
Su Meenal su ka faɗa a tare.
Safnah shiru ta yi don ta rasa abin cewa ma,
"tashi mu je na ta ya ki aiki"
Teemah ta faɗa tare da miƙewa tsaye
"Ai kwa-bari dai ayi sallar la'asar ko?" Hindu ta faɗa
"Ehh!, Kuma hakane, gashi ana kira.
Tashi su ka yi duka don zuwa gabatar da sallar.
Bayan sun gama ne kuma su ka shiga kicin ɗin dukan su, kasancewar da wuri su ke fara girkin daren su, kasancewar abubuwa da dama suke yi, wataran ma kowa nata za ta yi.
BAYAN WASU AWANNI
Zaune su ke gaba ɗaya a dining table don cin abinci, kasancewar da sunyi sallar Magriba su ke fara cin abinci, Hindu, Meenal da kuma Safnah Teemah ta koma part ɗin su tun bayan sun gama girkin bayan ta ɗiɓi nata a wani kula, kaka kuma sun kai mata nata, don a ɗakinta take ci, wataran ne take fitowa falo.
Bayan sun gama cin abincin ne suka nufi ɗaki don gabatar da sallar isha'i da aka fara kira.
Zaune su ke suna hira, bayan idar da sallar ta su.
Wayar Safnah ce ta ɗauki ƙara alamar shigowar kira, ko da ta duba yaya Abdul ne, dama tsammanin kiran shi take don tun ƙarfe 5:30 ya kira ta ya faɗa mata ya fita ta ajiye mai abincin, idan ya dawo ze kira ta.
Ɗaga wayar ta yi tare da ƙarawa a kunne "Assalamu alaikum" ta ji ya faɗa, amsa mai sallamar ta yi, kafin ya ƙara cewa "ina jiran ki a falo!"
"To" kawai tace, sannan ya yanke wayar.
"Ku zo muje falo don Allah!" Safnah ta faɗa tare da kallon su Meenal.
"Lallai ma! Ki na so yaya Abdul ya ji haushi mu ne!, Ke kaɗai yace kuma baki san me zaku tattauna ba, kila ma sirri ne!" Cewar Meenal
"A'a wallahi ba wani sirri, kawai abinci zan saka mai na dawo"
"Ok mu je!" Hindu ta ce.
Miƙewa su ka yi tare da nufar ƙofar fita.
A kujerar falon su ka hangi yaya Abdul ɗin, ƙarasawa su kayi amma ban da Safnah da ta nufi kicin.
Mintuna 2 se ga ta ɗauke da babban faranti wanda ta jero mai abincin da kuma drinks da ta haɗa mai.
"Sannu da aiki Safnah!" Abdul ya faɗa lokacin da ya ke ƙoƙarin buɗe kular abincin.
Zama ita ma tayi a kujerar da Hindu ta zauna.
Abdul kuwa ba tare da ɓata lokaci ba ya fara cin abincin shi, don yunwa ya ke ji sosai, rabon da ya ci abinci tun da safe shima tea ne kawai ya sha.
Yana cikin cin abincin ne wayar shi ta fara ringing, ko da ya duba, Faruq ya gani hakan yasa shi miƙewa da sauri ya nufi hanyar ɗakin shi.
Sai da ya shiga sannan ya ɗaga kiran lokacin ma kiran farko ya yanke wani ne ya sake shigowa.
"Assalamu alaikum babban yaya ya kake?" Faruq ya faɗa daga can ɓangaren.
"Wa-alaiku-mussalam lafiya lau Alhamdulillah ya Momy?"
"Lafiyan ta lau"
"To yayi baka tambaye ni ya Teemah ba?"
Dariya Faruq yayi tare da ce wa "ai yanzu ko kai wallahi na fi ka sanin lafiyar Teemah!"
"Haka zaka ce ko? To ni da muke gida ɗaya ai dole na fi ka sani"
"Hmm ba zaka gane ba!, Mu bar maganar kawa, gobe fa su Daddy su na nan zuwa fa?"
"To Sarkin azarɓaɓi!, Se ka bari ka ga zuwan na su ai"
"Hmm ka bari kawai!, Baka san yadda na ƙosa a mallaka min Teemah ba, gani nake kamar har yanzu akwai wanda ze kwace min ita"
"Haba dai! Baka da matsala abokina, ka ƙaddara ka samu Teemah, ka manta nace na baka ita ne?"
"To Baba!" Faruq ya faɗa cikin sigar wasa.
"Faɗa da babban baƙi!, Kasan ance babban yaya uba!"
Dariya Faruq yayi sannan yace "Allah ya biya babban yaya!"
"Kai Mallam ka dame ni da surutu abinci nake ci wallahi"
"To shikenan!, Se anjima ma yi waya"
"Ok, Bye!" Abdul ya ce tare da fitowa waje.
Zama yayi ya cigaba da cin abincin shi, su na falo kamar yadda ya tafi ya bar su, ba ya son yin waya a gaban su, don kar su raina shi, musamman idan da faruq ne.
"Alhamdulillah!" Abdul ya furta, lokacin da ya kammala cin abincin na shi, kallon su yayi tare da ce wa "kun yiwa Faruq alƙawarin zuwa bikin ƙanwar shi ko, to gashi bikin ya gabato saura kwana goma 10 yau.
"Yeah! Yaya Abdul wallahi na ƙosa na je Zaria" Meenal ta faɗa.
"Ni ma wallahi na ƙosa mu je!" Hindu ma ta faɗa.
Safnah kuwa ido ta bi su da shi jin an ambaci Zaria.
"To shikenan, ni zan tafi rana ita yau, ana saura kwana biyu 2 biki, ku kuma ranar biki Sadiq ze kawo ku"
"Haba yaya ina laifi mu tafi tare, ana jibi bikin!" Meenal ta faɗa, sannan Hindu ta ƙara da cewe
"Ai kuwa dai yaya, mu ya kamata mu fara zuwa, Maza ai nasu ɗaurin aure ne kawai a biki"
Murmushi Abdul yayi tare da ce wa "yawwa se ku je gidan mutane ku tare ko? Har kwana uku3, kuma kunsan gidan surukan Teemah ne ko?"
"Ehh yaya! Ita Teemah se ta tafi ranar bikin"
"Tare za ku tafi!, Ranar bikin"
"To shikenan yaya!" Hindu ta faɗa.
"Safnah wai ke kurma ne ko?" Abdul ya faɗa yana kallon Safnah da tun ɗazu take bin su da idanu.
Murmushi ta yi tare da ce wa "ai duk abinda zan ce sun faɗa yaya"
"Au kema ki na bin na su ku tafi ana jibi bikin kenan?"
Murmushi Safnah ta yi tare da ɗaga kai alamar"Ehh"
Abdul ma murmushin yayi tare da ce wa "to shikenan za ku tafi ana gobe bikin!"
"Yawwa yaya!" Su ka faɗa har su na haɗa baki.
Hira su ka cigaba da yi, bayan sun gama kuma su ka hau kallo, ba su su ka kwanta ba, se ƙarfe 10:30.
*****WASHEGARI*****
Shirye-shiryen sa ranar su Abdul da Teemah ake yi, da sauran matasan gidan gaba ɗaya.
Iyayen Faruq sun zo, har an tsayar da magana wata uku3, duka rana ɗaya aka saka.
Misalin ƙarfe 3:00 iyayen Faruq su ka nufi Zaria, bayan sun gaisa da Teemah ta ga soyayya sosai a wajen su, kuma su ma sun ji daɗin ganin gidan da da yaron na su ya nemi aure, don sun san gidan mutumci ne.
Abdul yana cikin tsantsar farin ciki sosai mara musaltuwa, na baiko da akayi mai da Safnah, shi a son ran shi ma wata biyu ya so a saka, a haɗa da na su Hindu, don shi wata biyu aka saka, amma shi ma an ƙara, yanzu an dawo da su ɗaya.
Safnah ta ci kuka lokacin da ta ji wai har da ita aka saka ranar, zama ta yi a ɗakinta tun bayan tafiyarsu, ta ci kuka har ta gode Allah.
Misalin ƙarfe 5:30 kiran Abdul ya shigo wayanta, ko da ta ɗaga cewa yayi ta same shi a falo.
Miƙewa ta yi bayan ta goge ƙwallar da ta zubo mata.
A kujerar falon ta same shi, shi kaɗai ne a falon, gaishe da shi ta yi, don wunin yau gaba ɗaya ba su haɗu da shi ba.
"Safnah ɗago ki kalleni!" Ya faɗa ganin tunda ta zo kanta a ƙasa ya ke.
Ɗagowa ta yi ta kalle shi "me yasa idanun ki, su ka yi ja?, Kin yi kuka ko?"
Kai ta gyaɗa mai alamar "a'a"
"Kai ki min ƙarya Safnah, kukan me ki ka yi?"
Kuka ne ya taho ma Safnah, cikin kukan ta ce "to ba kai ba ne!"
Cikin tashin hankali Abdul yace "Subhanallahi! Safnah, me na yi miki?"
Shiru ta yi bata bashi amsa ba, se sheshsheƙar kuka take.
"Safnan ki yi magana mana!, Don Allah bana son wannan kukan kiyi shiru!"
Ganin ya shiga tashin hankali yasa Safnah cewa "to ba kai ne, kace a mana baiko yanzu ba!"
Shiru Abdul yayi yana kallon ta daga bisani yace "Safnah ba ni na ce ba, su Baba ne, ko baki ga duka aka saka ranar ba, har da Teemah fa!"
Shiru ta yi ba ta yi magana ba, Abdul ne ya sake ce wa "na ce ki yi shiru, ko dai ba ki so na ne Safnah?"
Ɗaga kai ta yi alamar "Ehh!"
"Ba na son wasa Safnah, kar ki sa hankalina ya tashi!"
"To ni ai Soja ne ba na so" Safnah ta faɗa cikin shagwaɓa.
"A shirye nake da na ajiye aikin indai baki so Safnah"
Ɗago kai ta yi ta kura mai ido na wasu ƴan sakonni, kuma ta ga alamar da gaske yake yi, canza akalar maganar ta yi da cewa
"A'a yaya ban ce ka ajiye aikin ka ba, wasa nake maka, amma kuma gaskiyar ranar da aka saka ta yi kaɗan, shekara ɗaya1 ya kamata a saka"
Murmushi Abdul yayi tare da ce wa "to ki samu su Baba ki faɗa mu su"
"Ai bazan iya ba ne, amma nasan kai za ka iya, kuma za su fi jin maganar ka ma"
Murmushi Abdul yayi tare da ce wa"to shikenan!, Zan faɗa mu su" ya faɗi hakane don tabar maganar don baya son ganin damuwarta ko kaɗan.
"To se aje ayi min girki ko Madam, zan je gidan su Sadiq na dawo"
"To zan yi" kawai Safnah tace, tare da miƙewa ta nufi ɗakinta.
"Safnah!" Ta ji yaya Abdul ya faɗa, juyowa ta yi "na yi mantuwa gashi!" Ya faɗa tareda miƙa mata wata baƙar leda babba cike da kaya.
"Menene yaya?" Safnah ta faɗa lokacin da ta ƙarɓi ledar.
"Alawa ne da cimgum na saka ranar mu"
Gaban Safnah se da ya faɗi, dakewa ta yi tare da cewa "to ni waye na sani anan da zan bashi, dama dai a Zaria ne"
"Ehh ki je dashi naki ne!" Juyawa ta yi amma ba haka taso ba, taso yace ta je Zaria ne ta raba mu su, amma ta kudirinta a ranta se ta tambaye shi za ta Zaria.
*****BAYAN SATI ƊAYA 1*****
Abdul zaune da ƴan ƙannen na shi suna hira, don indai ya samu hutu haka mai ɗan yawa ta dawo ba aikin da yake yi se ziyara da kuma hira da ƴan ƙannen na shi.
"Yaya wai gobe ne zaka tafi ko?" Teemah ta tambaya, don