Header Ads
Showing 18001 words to 21000 words out of 57539 words

Chapter 7 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

555

Ads at the middle of Article

ya kira Salmah akaro na farko da ya ta'ba kiran ta, ta yi mai kwatance.
Kafin ya iso ta yi wankan ta ta yi kwalliya sosai ta had'u don Salma ba mummuna ba ce, d'akin momin ta ta nufa da murna tace "momi yana hanya", "to Allah ya kawo shi lafiya, amna Salmah son da kike yi wa yaron nan na sha fad'a miki ki rage don be miki rabin shi amma bakijin magana", "momi kar ki 'bata min rai don Allah ki barni kawai", horn su ka jiyo a bakin kofa Salmah ta zaci shine se da ta le'ka ta window ta ga Daddyn ta ne, shigowa ya yi yace "'yar Baba irin wannan wanka haka ina zuwa?" murmushi ta yi tare da sunkuyar da kai momi ne tace "za ta yi ba'ko ne" "kai! Mamana ki ce suruki na ne zai zo", Dariya Sàlmah ta yi sannan ta nufi d'akin ta, Horn su ka 'kara ji wanda Salmah ta san shine don ta ga kiran shi, da sauri ta fita don taro shi.




'Dakin ba'ki aka kai shi, Safwan se kallon gidan yake ya had'u sosai se dai su zo kai d'aya ma da nasu wajen had'uwa, zama yayi ta jere mai abinci kala-kala da drinks, bud'e d'aya ya yi ya d'auki cokali ya d'iba yakai bakin shi, kallon Salmah ya yi yace "waye ya yi girkin nan?" "Ma su aiki ne" "What! Ke miye àmfanin ki baza ki girka min ba se ma su aiki to bazan ci ba kuma yunwa naje ji", jawo lemon yayi ya bud'e ya fara sha tare da snak, don Safwan ba ya wa sa da cikin shi, ita kuwa ta na zaune ta na kallon shi, har ya gama yace "to ga ni na zo gidan ku ko?", "Ehh nagode sosai, mu je ka gaida momi na to", "ok".


Fitowa su ka yi har falon momi na Zaune akan kujera ya durkusa ya gaishe ta momi ne tace "ya hanya?" "Alhamdulillah!" "Madallah!", dai-dai nan kuma Daddyn ta ya fito 'karasowa ya yi yana murmushi yace "mamana ke da surukin nawa ne?", Safwan tun kan ya d'ago ya gane mai muryar nan tabbas kuma ya na d'agowa ya tabbatar shine, "Sannu Daddy ina wuni?", "lafiya lau" cewar Dad ya na zama tare da cewa "Muhammad dama kai ne?", Murmushi Safwan ya yi yace "Ehh Daddy ni ne" "gaskiya wannan abu ya yi min ya Daddyn ka shi ma ya dawo hutu ko?" "Ehh yana nan" "to ka gaishe shi kafin muyi waya" "to ze ji" cewar Safwan yana mi'kewa ya mu su sallama tare da fita Salmah ma mi'kewa ta yi ta bishi har wajen motar shi Sallama su ka yi ta koma cikin gidan.


Zama ta zo ta yi kusa da Dad tace "Dad dama kasan Safwan ne?" "Sosai ma kuwa Baban shi abokina ne kuma abokin kasuwanci na ne", dad'i sosai Salmah ta ji momi murmushi ta yi tace "ya aka yi ko bansan shi ba?" "kuma tun muna wancan gidan yana zuwa wataran da Dad shi amma be kai haka ba, yanzu zan samu Daddyn shi mu tsaida magana", "to Allah ya tabbatar da alkhairi" momi tace ta na barin falon ya yin da Salmah ta rungume Daddyn ta "ina son ka Dad", "ba ki da kunya ko mamana?" ta shi ta yi ta shiga d'akin ta da gudu.


Safwan ko abun ya bashi mamaki ashe Salmah 'yar aminin Daddyn shi ne, ai ko abun nan ba ze bari Dad shi ya ji ba ko kad'an, haka ya yi ta tunani har ya dawo gida agajiye sosai, ya so kuma ya biya gidan su Safnah a ba shi adireshi don yana son zuwa Katsina ne don ba ze iya jiran dawowar Safnah ba, lokacin da ya isa gida ana kiran sallar magrib ne hakan ya sa yana yin perking ya fito ya nufi masallaci, acan ma ya samu Dad shi, har se da akayi isha'i sannan su ka dawo gida, abinci su ka ci sannan Safwan ya wuce d'akin shi ya cigaba da tunani, Kiran Kamal ya gani, ya shigo wayar shi d'au ka yayi yace "Hello Kamal", dagacan Kamal yace "boss ya kake?" "Lafiya lau" "kwana biyu ba na ganin ka a club me yasa?" "kai dai bari kawai!, ina cikin matsanancin damuwa!" "me ya faru?" "Ba abun da ma be faru ba!, kasan Besty na ta bar garin nan kuma baza ta dawo ba?", "ina ta je?" cewar Kamal ko ajikin shi dad'i ma ya ji don ya na da sanin Safnah ke hana Safwan zuwa club da sauran su, "Katsina ta je" "to miye na damuwa ba ga Salmah ba yarinyar nan ta na son ka sosai amma Safnah kai ka ke son ta"


"waye ya gaya maka Safnah bata so na?


"Se an fad'a, da ta na son ka ai zata fad'a maka, ka ganni nan bazan auri wacce nake so bata so na ba se dai na auri wacce ta ke so na sosai wallahi za ka ji dad'i",


"Dalla mallam kauce!, da irin wannan tunani na ku da na bi ya sa gashi ina shirin rasa Safnah, don haka ko yau da zanga Safnah zan furta mata ina son ta",


Dariya Kamal ya yi yace "lallai boss ka shiga hannu!" "Bana son iskancin banza!, me ye ma na kira na ne to?", "Babu!, na kira na gaishe ka ne", "to nagode" sannan su ka yi sallama, kwanciya ya yi amma sam baccin ya 'ki zuwa, tunani ya dinga yi har bacci ya yi gaba da shi.


Anty ne zaune da yaran ta da Daddyn su ana cin abinci ana hira, Afrah ne tace "momi yaushe Anty Safnah za ta dawo?" Kallon Dad su ta yi kafin tace "ki tambayi Dad ku", "Dad yaushe za ta dawo?" "Bazata dawo ba ta tafi garin su, amma idan ku na karatu sosai zan kai ku wajen ta", tsalle su ka yi su na murna sosai, Khalid ne yace "momi ranar da ki ka tafi anguwa ki ka bar wayan ki anty Safnah ta kira na yi miki save d'in number ma", "Dagaske?" Cewar anty ta na d'auko wayar ta Daddyn su ne ya 'kar'bi wayar yace "dare ya yi baza ki kira ta ba", "Dad khalid jiya Safwan yazo wai na ba shi adireshin ta a katsina, ko number ta" "kar ki sa ke ki bashi, kinsan halin Safwan ze je, kuma kinsan irin gidan su don haka kibar shi kawai tun da mutunci su ke yi, shikenan tunda ta tafi abar shi haka", "to ai dama bansan ma gidan ba", cewar Anty, kawu ya 'kara da cewa "ko number kar ki bashi nasan ma ba number ta ba ne", "to" Anty tace sannan su ka cigaba da Hirar su ci ke da kewar Safnah.


Safwan bacci ya sha sosai don be yi bacci ba se wajen 'karfe uku3, hakan yasa shi makara gashi yau za su fara exam cikin sauri-sauri ya shirya ya nufi makarantar ko karatun Jarabawar be samu sukunin yi ba, shi da ba ya wasa da karatu.


Lolacin da ya isa har sun fara jarabawar, da sauri ya yi perking ya fito, lecturer ne yace "Safwan ya aka yi ka yi late?" "wallahi na makara ne!" "to shiga" cewar malamin, jarabawa ta d'auki zafi se fafatawa ake yi yayin da Safwan ya ji saukin ta sosai don shi ya fara gamawa, duk da sun riga shi farawa.


KATSINA
Yau satin Safnah d'aya a Katsina ya yin da ji take kamar a 'kaya ta ke, gashi yau ta tashi cikin ba'kin ciki sosai don tasan su na can su na jarabawa amma banda ita ta kira number maryam ba ta shiga ta kira Anty shi ma haka, na Safwan kuma bata sani ba, hakan ya sa abun ya mata yawa ta na zaune ita kad'ai a falo don su meenal sun je bikin wata 'kawar su tun 'karfe 10:00 majid ya zo ya kai su don aminiyar su ce sosai su ne manyan 'kawaye, Safnah tace bazata ba don bata son yawo sosai, wanka ta yi ta shirya cikin wata doguwar riga yayi bala'in mata kyau, wani hula ta sa ka mai kama da na sanyi amma mai kyau ne sosai, duk cikin kayan Meenal ne, zama ta yi a falo se tunane- tunane ta ke yi mi'kewa ta yi ta nufi gerden d'in gidan don ta gaji da zama a wajen gashi idan ta je d'akin kaka surutu za ta yi ta sata, yana ta baya ne garden d'in ta 'barayin part d'in su Teemah, tafiya take yi a wajen ba kowa kuma ba motsin komai se kukan tsuntsaye, swimming pool ta hanga a zuciyar ta tace da ta iya da ta shiga, wajen da aka kewaye da shuke+2 ta shiga ayaba ta ciro da mangoro ta zo ta samu wani waje ta zauna ayaban ta 'bare ta gutsira ta fara taunawa, ya nuna sosai ya yi za'ki, ajiye wa ta yi a gefe, tunani ta koma yi duk akan karatun ta ga kuma Safwan da take masifar tunanin sa tasan yana nan da Salmah ya manta da ita wasu zafafan hawaye ne su ka zubo mata, kuka ta fara yi don Safnah ba ta raina abun kuka bare kuma abun ya samu, kuka ta ke a hankali sautin kukan ta ke fita yayin da hawaye ke bin fuskar ta.


Cak! ta tsaya da kukan ta jin kamar tsayuwar mutum a bayan ta, tsorata ta yi don tasan ba kowa a gidan se kaka kuma kaka tasan bazata fito ba, a hankali ta fara juyowa, kafar mutum ta gani sanye cikin Kwanbos sama take yi da kanta a hankali takalmin ya kusa gwiwar shi mi'kewa tsaye ta yi zunbur ganin kayan soja, ido biyu su ka yi da shi, dogo ne sosai kuma kyakykyawan saurayi kaman shuwa, shima kallon ta ya yi azuciyar shi ya furta "tabarakallahu ahsanal khali'kin", jikin Safnah ne ya fara rawa don ta na bala'in tsoron soja a rayuwar ta da sauri ta yi hanya za ta gudu cikin zafin nama ya ri'ko hannun ta, kallon shi ta yi tace "don Allah ka yi hakuri" hankicif ya ciro a aljihun shi ya mi'ka mata, tare da cewa "ki goge hawayen fuskar ki" hannunta na rawa ta 'kar'ba ta goge, "me ya same ki? kika zo nan kina kukà tun d'azu nake wajen ina jinki", Safnah rasa mai zata yi tayi se gir-girza kai take yi, ya fahimci tsoron shi take hakan yasa ya sake ta tare da cewa "ke ce Safnah?" d'aga mai kai ta yi, yace "ina su Hindatu?", "sunje biki" ta fad'a "waye ya kai su?" ya sake jefo mata tambayar, "ya majid ne", "to ke me ki ke yi anan ko kukan ne ki ka zo nan yi", "a'a" "to muje" ya fad'a tare da nuna mata hanyan part d'in su, tafiya take yana binta a baya, hànyar d'akin su ta nufa, "ke!" taji yace tsayawa ta yi ba tare da ta juyo ba don tsoron shi take ji, "d'akin kaka" kawai yace mata juyawa ta yi ta nufi d'akin da sauri ta shiga tare da sallama kaka da ke zaune ta amsa tare da cewa "Safnah baki je bikin ba?" "Ehh kaka ba najin dad'i ne" "to Allah ya kawo sau'ki" "Ameen" Safnah tace, shigowa yayi da sallama murmushi yayi tare da cewa "'yar tsohuwa mun same ku lafiya", "lafiya lau mai gida saukan yaushe?", "yau d'in nan ko gida banje ba nayo nan" "to ka kyauta 'kannen naka sun tafi biki se wannan" murmushi ya yi yace "wannan da bata sanni ba, can naganta a gerden", "ikon Allah Safnah baki san Abduljabbar d'in ba?" d'aga kai ta yi alamar Ehh, "ba ki ji su Hindatu na maganar shi ba, shima anan part d'in yake"


"Ni yaya Abdul kawai na sa ni su na magana", "gidan ku!, wannan ba shi ne Abdul d'in ba", cewar kaka sunkuyar da kai ta yi tsabar kunya, don tabbas sun mata bayanin Ya Abdul kuma sun ce mata soja ne, amma kaka ne da tace mata Abduljabbar bata gane ba Shiyasa.


"Baban ka ya matsa se ta dawo don bata san 'yan uwa ba, wa su ba su san ta ba, amma tun da ta dawo ai zata san su ahankali" murmushi Ya Abdul ya yi sannan yace "kaka bara naje na yi wanka na huta na gaji sosai", "ai da gajiya d'an nan dole ka gaji" murmushi ya yi sannan ya fita, tare da ce wa Safnah "zo muje" tasowa ta yi ta biyo shi, "je kicin ki zibo min abinci", "to" tace sannan ta bi hanyar kicin ɗin, tunda ta zo gidan bata ta'ba zuwa ba se yau, yana da girma sosai ga kaya cike a ciki har da wasu d'akuna aciki duba inda tasan ana aje abincin ta yi amma bata ga komai ba, fitowa ta yi ta tarar da shi zaune a kan kujerar falo, "Ba abinci" tace mai, "to ke baki iya abincin ba ne?", "na iya" "to kije ki min zanyi wanka na dawo" "to" tace sannan ta nufi kicin d'in, ta rasa mai zata dafa mai gashi bata ga komai ba, bud'e d'aya daga cikin d'akunan ta yi, kayan abinci ta gani sosai tun daga kan buhunan shinkafa, kwalayen taliya, na macaroni, na cus-cus da su semonvita, kaya ne sosai komai akwai shi, rufe wa tayi ta bud'e d'ayan d'akin shi kuma Dankali da su doya da kires na kwai, da su kwalayen maggi ne har ta gaji da irgawa, doya ta d'auko, tare da d'ibo kayan miya, da komai da zata bu'kata ta fito fridje d'in da ke kicin d'in ta bud'e kifi da nama ne aciki se su tomatos da peppe da sauran su, doya ta dafa mai da miya yaji nama sosai sannan ta had'a mai juice na karas, dining ta zo ta jere mai sannan ta juya zata nufi d'akin su, "Safnah!" taji ya kwala mata kira juyowa ta yi ya fito daga d'akin sanye cikin wa su 'kananan kayan jar riga ne da ba'kin wando, wandon ba dogo ba ne amma ya wuce gwiwar shi hakan ya bata damar ganin gashin 'kafar shi, ba'ki sid'if, sosai ya kwanta luf a farar fatar kafar shi, "kin gama?" taji muryar shi yana fad'i d'aga mai kai ta yi, "ke wai baki magana ne kike d'aga kai kamar 'kadangaruwa", dariya maganar ta bata dariya ne ya su'buce mata, wanda tundà ta zo gidan bata yi ba kallon ta ya tsaya yi yadda dariya ke bala'in mata kyau sosai ga dimful d'inta ya lotsa, "d'azu kukan me ki ke yi?" kallon shi ta yi, tace "kai na ke ciwo", "to se baza ki fad'a ba ki ke yi ma mutane kuka", shiru ta yi dining d'in ya nufa tare da bud'e kulan da ta saka doya, sannan ya bud'e na miyar, 'kamshi ne ya bugi hancin shi zama yayi ya ja filet d'in ya zuba tare da saka miyar ya fara ci dad'i sosai girkin ya yi mai 'karawa ya yi bayan ya cinye, kad'an ya rage.




Safnah tunda ya nufi dining ita kuma ta yi d'akin su don bacci take ji agogo ta duba ta ga kusan 'karfe2:30, Sallah ta fara yi sannan ta yi wanka, sif d'in Meenal ta bud'e ta d'akko wani riga da siket, ta saka sannan ta fito bata ga Abdul ba dad'i ta ji sosai don shima ta lura akwai surutu sosai, dining ta nufa kulolin ta bud'e ta ga saura kad'an dauka ta yi ta mayar kicin ta tattara wajen sannan ta dawo ta zauna, kallo ta saka don rage lokacin don kewa ya ishe ta ga ba wayan ta.


ZARIA


Safwan yana gama jarabawa ya fito ya samu waje ya zauna, Salmah ya hango ta nufo inda yake kallon ta yake yi har ta iso, sallama ta yi ya amsa sannan tace "zan iya zama?", "Ehh" kawai yace mata waje ta samu ta zauna "Ya gajiyan jiya" shiru yayi mata, ta 'kara cewa "momi tace na gaishe ka da gajiya" "to, dama Wannan ne Daddyn ki?" "Ehh, ya fad'a min Daddy abokin shi ne" hira ta dinga jan shi da shi idan ta yi sa'a yace mata Ehh, ko a'a, har su ka gama jarabawa aka tashe su, Motar shi ya shiga kai tsaye gidan su Safnah ya nufa don Anty ta yi mai adireshin gidan su Safnah, Anty ta shaida mai bata san gidan ba don bata ta'ba zuwa ba ko Dad khalil ma be sani ba haka Safwan ya taho be wani gamsu ba ya za'ace wai ba su sani ba yana jin kunyar anty ne da yace "ta fad'a mai gaskiya", haka ya kamo hanya jiki ba kwari, Perking motar shi yayi a inda ya saba ajiyewa, falon su ya nufa da sallama, Dad shi ya gani yayi ba'ko Gaishe su yayi se da ya juyo kafin ya gane ashe Baban Salmah ne, gaban shi ya yi mummunar fad'uwa, "Safwan!" Yaji Dad shi na kira, dawowa yayi ya zauna a kusa da shi dafa kan shi ya yi yace "Yau karo na farko ka sani farin ciki mara adadi Safwan ashe 'yar aminina kake so, gaskiya na yi matu'kar farin ciki zumuncin mu ze 'kara 'karfi, zan so wannan had'i sosai Safwan dama muna so muyi magana ne a tsayar da rana", Safwan da tun da Dadyn shi ya fara magana ya ke had'a zufa kamar yana gidan buredi, ya ma rasa me zai ce gashi baze iya kallon idon Dad shi yace baya son Salmah ba, ga Dadyn ta a wajen shiru yayi Dadyn shi ne yace "Safwan yaushe kake gani za'a sa ranar tun da duk a shirye mu ke karatu ne kawai ko da aure za'ayi", da'kyar ya iya bud'e baki yace "Daddy duk san da ka saka" "to Safwan Allah ya maka albarka" Dad Salmah yace, sannan ya tashi da'kyar ya iya zuwa d'akin shi saboda tsabar takaiki da 'bacin rai ya rasa mai ke mai dad'i a duniya ya rasa me ze yi ma, number Kamal ya lalubo kira d'aya ya d'aga, ya

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads