Showing 21001 words to 24000 words out of 57539 words
Chapter 8 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
yace "Hello Kamal ka na ina ne?" "Ina gida ya aka yi?" "yau ba wani labari ne?", "Kamar wanne?" "ka ji d'an rainin wayo wani labari na ke tambayar ka" "ok yau kam akwai wani chasu da aka shirya 'karfe hud'u4:00 ne ma" agogon hannun shi ya duba ya ga 'karfe 3:00 yace "saura awa d'aya kenan" "Ehh" cewar Kamal "to zan shirya ka zo gida ka d'auke ni" "to", Kamal yace cikin farin ciki sosai, sannan su ka yi Sallama wanka Safwan yayi sannan ya yi Sallah da 'kyar don kan shi bala'in ciwo yake mi shi ga tunani da ya addabi zuciyar sa ji yake kamar ze bar duniya ne.
Ƙarfe hud'u 4:00 Kamal ya zo ya d'auke shi ko 'kara lokaci be yi ba, kai tsaye club d'in su ka nufa, dondazon maza da mata ne aciki su na ra'kashewa, wa su Hausawa ne wa su kuma yare, wasu 'ya'yan musulmai ne, abun ba kyau ga ni sunyi wata kalar shiga, zama Safwan ya yi, 'yan wajen na gani shi su ka d'au ihu bosss d'aga mu su hannu kawai ya yi kafin kace me aka cika mai gaba da kayan ciye-ciye ga kwalaben giya, kud'i ma su yawa ya bawa Kamal, ya cire na shi sannan ya ba su raguwar, ya shiga filin rawa shi ko Safwan giyar ya bud'e, wata zuciyar ta na fad'in mai ka da ya sha, ba shi da wata mafita da ya wuce ya sha d'aga kwalban ya yi ya fara sha, tun da ya sa abaki be cire ba se kwalbar ya ajiye, ya shanye!, wani ya 'kara d'auka shi ma ya shanye, se da ya sha uku gyatsa ya yi kafin kace me ya fara fita hayyacin shi mi'kewa ya yi yana layi ya nufi wajen rawar, rawar shima ya yi sosai ganin haka yasa na fito don d'auko muku sauran labarin.
Safnah ita kad'ai a gidan har se kusan magrib sannan su Meenal su ka dawo, ta yi musu sannu da zuwa sannan su ka shiga su ka yi wanka, falo su ka dawo su ka sameta, zama su kayi Hindatu tace "wallahi yunwa nake ji sosai gashi nasan ba abinci ko?", "Akwai raguwar doya da na dafa d'azu, yau me aikin ma bata zo ba" cewar Safnah, "Ehh ai dama yau bata zuwa weekend", tashi ta yi ta zubo doyar da miya su ka zauna su ka ci ita da Meenal don Safnah a koshe ta ke, sun gama ci su ka mayar da kwanonin sannan Su ka zauna hira su na kallon pictures d'in biki, knocking su ka ji daga kofar falon na su Meenal ta tashi don bud'ewa ta na bud'ewa wa za ta gani "ya Abdul!" ta fad'a tare da rungume shi tana Hindatu ga ya Abdul ita ma da gudu ta zo tare da rungume shi ta na fad'in yaushe ka zo ya Abdul, "d'azu" kawai yace tare da jan jikin shi ya nufi falo, zama ya yi kallon Safnah da ke zaune ya yi yace "ke ba ki iya gaisuwa ba ne?", shiru ta yi bata ce komai ba, "Yaya ina tsarabar mu?" "ta na d'akina" "yawwa ka huta ka d'auko mana" "wa yace miki na ga ji tun Misalin 11:00 na sauka a Katsina, ba ku gida kun je yawo" "yaya biki ne fa mun so ma mu kai amarya amma ya majid ya wani zuwa d'aukan mu", "ai da kun kuskura kun kai Bayan magrib, da da kai na zan zo kuma jiki ze fad'a", "ai ba ayi haka ba ma yaya" cewar Meenal don tasan karon ba dad'i "yaushe Safnah ta zo?" ya tambaye su, "yau satin ta d'aya" Hindatu ta fad'a, "ai Dad ya fad'a min sun d'auko ta, gobe da safe ku shirya akwai in da zamu dukan ku, har ke Safnah" "to" kawai Safnah tace, "bari na koma d'aki akwai abun da zan yi" "to yaya", "Safnah ki dafa min wani abu simple ki kawo min" "to" Safnah tace d'akin shi ya nu fa, Hindatu ne ta kalli Safnah tace, "ke ki ka yi mai girki da rana ko?", "Ehh", cewar, Safnah, dariya ta yi tace "kin zama me mai girki kenan don ya Abdul in dai ki ka mai abu ya ji dad'i to shikenan su nan ki soory, tun da na gyara mai d'aki ya yi mai kyau to kullum ni ke gyara mai har ya koma", "ki tashi muje na ta ya ki" cewar Meenal, kicin d'in su ka nufa, chips na Dankalin turawa, da kwai ta yi mai, se ta had'a mai black tea, falo su ka fito Meenal rike da flat d'in chips d'in Safnah kuma ta rike kofin tea d'in, d'akin su ka nufa har da Hindatu, sanye ya ke cikin jallabiya ba'ki da alama wanka ya yi, ya na zaune bisa kujerar d'akin ya d'aura system akan cinyar shi, da Sallama su ka shigo d'akin ajiye, system d'in ya yi ya mi'ke zuwa center table d'in da su ka aje mai abincin, "sannu da 'ko'kari" ya furta bayan ya bud'e flat d'in, "to yaya se da safe" "to ku shirya da wuri" "to yaya" Hindatu ta fad'a lokacin da ta kai kofa don su sun fita ma, jawo 'kofar ta yi, d'akin su suka nufa, kwanciya su ka yi bayan sun yi sallar isha'i don sun gaji sosai.
Taku har kullum
Khadeejerh Ishaq ✍️ ce
More comment
More typing
??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*17&18
Washegari
Bayan sun tashi sun yi wanka su ka nufi kicin don had'a breakfast, nan da nan su ka gama su ka je su ka gaishe da kaka su ka kai mata nata, sannan su ka kaiwa ya Abdul sannan su ka ci na su,
Bayan sun gama ne su ka je suka yi wanka, riga da sket su ka sa ka su ka d'auki gyale, su ka fito falo, ya Abdul su ka tarar a falon sanye yake cikin shadda golden yellow se 'kyalli ya ke, yayi masifar kyau, kallon su yayi yace "ina zuwa haka?" shiru su ka yi su na kallon shi don daga jin maganar sun san ya shirya tafiya ne,
"ku koma ku saka hijab" to su ka ce su ka nufi d'akin don sa ko hijab, fitowa su ka yi bayan sun zumbulo hijaban, "Ko ku fa!? Har kun fi kyau, Meenal je ki ce fatima ta fito, sa'adatu ma ki ce ta fito ku yi sauri ku zo tare"
"to yaya"
tace sannan ta nufi part d'in su Teemah, afalo ta tarar da ita, sanye da gyale da alama ma Part d'in su zata nufa, "to sannu Hajiya Teemah gara ma ki koma ki cire gyaken nan don yaya Abdul na kira", cikin zaro idanu tace "dagaske?"
"To tsaya nan" ta faɗa tare da yin gaba zuwa part ɗin su Sa'adatu, ita ma cikin sauri ta fito sanye da hijabin ta Teemah ma hijabin ta koma ta sako sannan suka nufo part ɗin su.
Lokacin da suka fito sun samu Hindatu da Safnah tsaye a bakin motar Abdul yayin da shi yake ciki yana ganin ƙarasowar su hakan yasa ya kunna mota Hindatu da Safnah ne suka shiga mazaunin dake tsakiya, yayin da Sa'adatu, Meenal da Teemah suka shiga baya kasancewar motar me sashi uku ne harda na direba, "waye direban ku?" suka jiyo Abdul na faɗa, "Safnah ki koma gaba" cewar Hindatu, Ba tayi musu ba ta koma gaban yayin da Teemah kuma ta dawo ya kasance mutu biyu-biyu ne, jan motar yayi ya bar gidan don tun-tuni ma an buɗe mishi ƙofar gidan.
Kai tsaye wani haɗɗen wajen shopping ya kai su, wajen ya haɗu sosai zuwa wajen ma se wanda ya amsa sunan shi mai kuɗi, cikin sauri su Meenal suka fita suka nufi ciki, Safnah ne kawai ta rage don ta ji motar a rufe yasa key, gashi ta kasa yi mai magana ya buɗe mata, "ki je ki ɗauki kaya da yawa don nasan baki taho da kayan ki ba, duk abun da kike so ki ɗauka", ta jiyo muryar ya Abdul yana faɗa, kallo ta bishi dashi bayan ya gama maganar ne ya cilla mata key ɗin motar ɗauka tayi tare da buɗewa, bayan ta fita ne ta ziro hannu ta ajiye key ɗin tare da kama hanya, koda ta shiga su Hindatu har an fara jidan kaya don sun kusa cika Basket ma, zuwa tayi ta ɗauki basket ta fara ɗaukan kaya ita ma.
Ta daɗe tana ɗiba amma bata wani tara kaya da yawa ba hakan yasa Teemah taya ta, lokacin Abdul ya shigo, bin kayan da Safnah ta ɗiba yayi da ido sannan shima ya ɗauki basket ya nufi can wani waje yayi nisa da su, a tunanin su kayan shi ze ɗibo shima, se suka ganshi da kayan mata tun daga kan atamfofi Shadda, materials, turaruka, kayan kwalliya da sauran su, "kun gama ɗiban kayan?" Ya jefa musu tambayar, "Ehh" "to muje" yace yana yin gaba mai turo mai kaya na binshi a baya, wajen biyan kuɗi suka zo, koda akayi total kuɗin su wajen 1.5m ba tare da wani jinkiri ba, Abdul ya miƙa Atm card ɗin shi don cire kuɗin.
Sai da suka samu wasu suka kwasan musu kayan har zuwa motar su duk girman but ɗin motar seda ta cika dam harda wasu kayan a wajen da suke zaune.
Kai tsaye gidan su ya nufa da su gidan Baba babba kenan tun jiya da ya dawo be zo ba se yau don gaishe da matar baban shi Hajiya Safiya wanda suke cewa (anty) don mahaifiyar Abdul ta rasu tun lokacin da ta haifi ƙanwar shi mai suna A'isha gashi yanzu tana da shekara18 ne duk sa'annin su Hindatu ne kuma ƙawar su ce.
Hajiya Safiya ta kasance masifffiyar mata ce ta ƙarshe kamar mijin ta don wani abun ma da Baba babba ke yi ana zargin da saka hannun ta, tsantsar kiyayya take nuna wa Abdul da ƙanwar shi A'isha, su biyu mahaifiyar su ta haifa, hakan yasa Abdul ma barin gidan ya koma can, don Abdul mutum ne me wasa da dariya da hakuri kuma duk da kasancewar shi Soja, amma wani lokacin akwai saurin fushi ga zuciya, hakan yasa yayi nisa da Hajiya Safiya don indai yana gidan yana kallon ta to ba zaman lafiya.
Koda ya iso gidan perking yayi su Hindatu ne suka fita suka nufi cikin gidan shi kuma yana cikin motar don shi kamar ɗabi'ar shi ce, idan yayi perking mota baze fito ba se yayi wasu ƴan mintuna.
Da sallama suka shiga dakin Hajiya Safiya na zaune ta amsa ba-yabo-ba-fallasa ƙarasawa suka yi tare da gaishe da ita, ciki-ciki ta amsa musu guri suka samu suka zauna, jiki a sanyaya don basu ga fuskar hira ba.
"Momy A'isha tana nan?"
Cewa Teemah don Teemah ba ruwan ta bata shakkar uban kowa bata tsoro kuma jajitacciya ce sosai, ba kamar sauran ba, don ko wani waje ne zasu je kowa na tsoron tambaya Teemah ce mai tambaya musu, don ko ƙofar gida zasu fita se sun tambayi ɗaya daga cikin Babannin nasu.
"Ehh tana ɗakin ta" Hajiya Safiya ta faɗa rai a haɗe tashi suka yi suka nufi ɗakin nata, suna shiga Abdul ya shigo falo.
"Ina wuni Anty" ya faɗa, wata uwar harara ta wurga mai tare cewa "da ban wuni ba zaka ganni ne?, Tun yaushe ka shigo garin nan amma kafi ƙarfin ka shigo ka gaishe ni saboda ni ba Uwar ka bace ko?, ka kyauta bara Uban naka ya shigo naji ko shi yace kar kazo ka gaishe ni, don shi dai nasan kun haɗu a babban gida".
Tunda ta fara masifar Abdul yake binta da kallo har ta gama waje ya samu ya zauna, ba tare da yace mata komai ba, wata yarinya ce ta shigo falon itama mai kimanin shekaru 16, yarinyar Hajiya Safiya ce itace babbar yarinyar ta se maza huɗu.
Waje ta samu ta zauna, "ke baki iya gaisuwa bane?" Cewar Abdul "Ehh fa bata iya ba ka koya mata ne?" Hajiya Safiya ta mayar mai da amsa, ita kuwa yarinyar hararar shi ma tayi haɗe da murguɗa mai baki, aiko nan da nan ya hassala cikin zafin Nama ya taso ƙyakykyawan mari ya ɗauke ta da shi wanda se da taga taurari, sannan yace "naga take-taken ki baki da kunya ko wallahi se na gyara miki zama, har ni zaki yi ma wannan kallo?" Ita kuwa Hajiya Safiya tasowa tayi ta nufo shi hakan yasa shi tsayawa kallon ta, ta ƙarasowa ta ɗaga hannu da niyar ta mare shi, beyi ƙoƙarin yin komi ba seda ya bari hannun ta ya kusa kaiwa fuskar shi, cikin zafin nama, ya ɗago hannun shi ya daki hannun ta, wani azababban ihu ta kurma don duka sosai yayi wa hannun nata ihu take riƙe da hannu, da sauri yarinyar nata da ake kira da Hafsat ta ƙaraso ta riƙe momin nata.
Da sallama su Hindatu suka shiga ɗakin A'isha ai da gudu ta taso ta rungume su, tana murnar ganin ƴan uwan nata nan da nan aka buɗe shafin hira, Hindatu ce tace "Indo baza ki rinƙa ganin mu a gidan ku ba kinsan Boss tana nan ke ki rinƙa ƙoƙarin tambayar Baba Salihu ki zo mana" "Hindatu kenan baza ki gane bane, kona tambaya base Anty ta yarda ba" "hakane kuma amma da nice a gidan nan se na gyara wa matan nan zama wallahi" cewar Teemah "Hm baki da hankali ma, to Baba Salihu ze barki ki taɓa mai mata ne" cewar Meenal.
Suna can suna hirar su basu san me yake faruwa ba a falon.
Abdul ɗakin A'isha ya nufa don kiran su Teemah su tafi, be ko kula da halin da Hajiya Safiya ta shiga ba don ni a tunani na ma ta samu karaya a hannun nan.
Cikin zafin nama ya buɗe ɗakin don ranshi ya ɓaci sosai"ku taso mu tafi" su kan su sun razana da jin muryar shi, da sauri suka miƙe suka yi waje da sauri A'isha ta ƙaraso ta rungume yayan nata "A'isha zan wuce anjima zamu yi waya" kafin tayi wani maganar har yayi nisa.
Su Hindatu a falo suka samu su Hajiya Safiya a ƙasa riƙe da hannu ko ba'a faɗa musu ba sun san aikin Yaya Abdul ne, tunda suka ga ranshi a ɓace fita suka yi suna kunshe dariyar su, seda suka shiga mota sannan suka samu damar yi, amma banda Safnah don ita kamar gangar jikin ta ne a tare da su, amma zuciyar ta na wani wajen, suna cikin dariyar Abdul ya same su hakan yasa su yin shiru, shiga yayi ya ja motar da matuƙar gudu sosai se da suka razana.
"Yaya Abdul zaka kashe mu ne?" Cewar Teemah, wani irin birki yaja kiiiiiiiiiit! Kake ji, tuni ƴaƴan cikin su suka kaɗa a tunanin su gun Teemah ze zo.
Buɗe ƙofar motar yayi cikin zafin nama tare da rufe ta, wajen wani mota da ta perker yanzu ya nufa, kafin ya ƙarasa aka buɗe ƙofar wani kyakkyawan saurayi ne ya fito daga motar wanda kusan sa'anni ne da Abdul ɗin.
"Yaya Sadiq!" Hindatu ta furta cikin tsantsar murna da farin ciki, "yaushe ya dawo ne?" Cewar Meenal "wallahi ban sani ba" Hindatu ta bata amsa.
A can waje kuwa bansan me Abdul ya faɗa wa wannan matashin ba, kawai gani nayi ya shiga motar shi shi kuma ya nufo motar da su Hindatu su ke buɗewa yayi ya shiga tare da zama.
Gaishe da shi su kayi ya amsa cikin fara'a sosai.
"Ya Sadiq yaushe ka dawo?" Cewar Hindatu.
"Yau kwana biyu" ya faɗa yana Murmushi,
"Shine baka zo wajen mu ba ko, nasan yanzu ma, yaya Abdul ne ya kira ka"
"Ehh yace nazo na mayar da ku gida akwai wajen da zai je ne"
"Ai gara don kar ya kashe mu da sauran kwanan mu" Cewar Teemah
Dariya suka yi dukan su, Ya Sadiq ne yace "kun yi bakuwa ne?"
"A'a Safnah ce fa, baka gane ta ba?"
"Oho! Dama itace?, Ance min dama ta dawo ai ban san ta ba wallahi"
"To gata yanzu ka ganta ai" Cewar Sa'adatu don na lura itama kamar bata cika son magana ba sosai.
Ƙarfe3:15 suka dawo gida kowa ya kwashi kayan shi ya mayar sif ya adana shi, ita kuwa Safnah wanda ta ɗibo itama ta kwasa ta ajiye akan gado,
"To sauran wa kika bar ma wa" Meenal ta faɗa tana kwasan raguwar nata"ba na yaya Abdul bane?" Safnah ta tambaya
"A'a naki ne Safnah" Hindatu ta faɗa
"Amma ai sunyi yawa sosai"
"Kin ga Malama ki kwashi kaya naki ne, sutura ai baya yawa" Meenal ta faɗa.
Su Teemah tun ɗazu sun kwashi na su sun nufi part ɗin su, taya ta kwasa suka yi suka shigan mata da shi don kayan da yawa.
Bayan sun gama komai sunyi sallah sunyi wanka suka fito falo don cin abinci kasancewar tun ɗazu mai aikin ta gama girka musu, zama suka yi suka cika cikin su sosai.
Yaya Abdul kuwa tunda ya hau mota ya tafi be dawo gidan ba se wajen 6:00 na yamma hannun shi ɗauke da leda ya shigo, kai tsaye ɗakin shi ya nufa don watsa ruwa.
Su Hindatu na zaune a falon ɗakin su suna chat don kowa da wayar ta, yayin da Safnah ke zaune tana karanta wani Novels da ta ɗauko a ɗakin Teemah, don Teemah shugaba ce ta karanta Hausa Novels.
Kira ne ya shigo wayar Meenal, ɗagawa tayi ta kara a kunne tare da cewa "Hello yaya Abdul" "daga can ɓangaren yace "kun koma lafiya?" "Ehh yaya Abdul"