Showing 6001 words to 9000 words out of 57539 words
Chapter 3 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
Jss3 kasancewar kawun ta yasan wacece Safnah akwai son karatu kuma malamin abokin shi ne kuma yana fad'a mai 'ko'karin Safnah, shiyasa ya yarda aka mata jumping d'in.
Ajin su Safwan aka kaita, Su ka dinga raina ta don ganin ta 'yar 'karama, yanzu ta shiga shekara na sha 14 ma, har da Safwan shi ma yana mamakin ganin ta a ajin, duk da akwai yara a ajin amma manyan sun fi yawa.
A layin gaba Safnah ta zauna ku sa da wata maryam, har zuwa mallam ya shigo (malamin English), hakan ya sa Safnah ciro littafin English d'in ta, tambaya malamin ya yi wanda al'adar shi ce idan ya shigo sai ya tambayi abun da akayi a ajin baya, kafin ya yi musu sabo, ai ko kowa shiru ya yi aka rasa mai bada amsa, can Safwan ya mi'ke ya fad'a malamin yace ka kusa dai amma akwai gyara, waye ze gyara mishi, Safnah da tun d'azu ta ke son fad'a amma kuma se ta ji kunyar mi'kewa take yi, d'aga hannu ta yi tace "sir",
"yes" tashi ta yi ta fad'i malamin ya sa aka tafa mata sannan yace "ke sabuwar zuwa ce ko?", "Ehh!" Safnah tace, yace "ya yi kyau", sannan ya cigaba da tambaya komai ya tambaya se Safnah ta d'aga hannu sosai ta burge 'yan ajin da su na mata kallon rainin wayo yanzu kuma kowa se ya dawo dama za su yi kawance.
Ko da malamin math ma ya shigo anan su ka sha mamaki don Safnah akwai math, solving d'in da aka musu jiya malamin yace ayi mai kowa ya kasa, sai Safnah ce ta fito ta Solver gyaran d'aya kawai malamin ya yi mata.
Ko da su ka fito break Safnah ita da maryam su ka fito su ka samu guri su ka zauna yayin da Safwan hankalin shi na kan Safnah, haka kawai ya ke jin dad'in kallon ta don Safnah kyakykyawa ce ta 'karshe ita ba fara ba ce sosai amma kuma Ta na da tsantsar kyau sosai. har su ka koma aji.
'Karfe biyu2 aka tashe su gida, Safnah su ka jero da Maryam don zuwa yanzu sun saba sosai da ma Safnah haka ta ke akwai saurin sabo amma idan mutum ya sakin mata fuska, har su ka fito bakin gate Safwan ne ya fito a dalleliyar motar shi ya wuce ta gaban su saura kad'an ma ya taka Safnah, abun ya ba Safnah haushi, maryam ta kalla tace
"waye wannan",
murmushi maryam ta yi tace
"ba ki gan shi a class d'in mu ba, Safwan su nan shi d'an mai kud'i ne sosai, a unguwar ku ma ai yake, ba kin ce Samaru ki ke ba",
"Ehh"
Safnah ta ce
"to ya akayi baki san shi ba?",
"Shikenan dai amma haka yake saura kad'an fa ya taka ni,
"ki yi hakuri ba halin shi ba ne ina jin be lura ba ne", shiru kawai Safnah ta yi,
yayan Maryam ne ya zo d'aukan ta, hakan ya sa su ka yi sallama ita kuma Safnah Napep ta tare ta shiga.
_??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE**BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*_9&10
Washe gari Safwan ya samu maryam yace "don Allah ina son 'kawance da sabuwar zuwan nan, ya za'ayi?" Murmushi maryam ta yi sannan tace "to zan mata magana"
"wani irin magana kuma!, kar yarinya ta raina ni kawai dai kisan yadda za kiyi amma kar tasan ni nace ina son kawance da ita",
"ok, zan gani" tace afili
a zuciya kuwa dariya ta ke yi ta na mamakin son girma irin na Safwan da kuma rashin son raini don baya d'aukan rai ni ko kad'an.
Safnah ce zaune ita da Maryam a wani ɗan dakali suna hira, kallon Maryam Safnah ta yi tare da cewa "maryam wancan shine wanda ya ku sa ta ka ni jiya ko?" ta ƙarasa tana nuna wajen da Safwan ke zaune shi da Kamal suna hira.
"Ehh amma ai komai ya wuce be sani ba ne amma yana da kirki sosai", "ok" kawai Safnah tace sannan Maryam tace ta rakata koyan karatu, ba musu Safnah ta miƙe domin raka ta.
Kai tsaye wajen Safwan ta nufa Safnah na biye da ita, waje Maryam ta samu ta zauna, kusa da shi tace "Safwan don Allah math d'in jiya, zaka nunamin" murmushi Safwan ya yi yace, "ki ce kin zo tsokana ta dai maryam, ga ki ga caculator a kusa ki ka zo nan", dariya ta yi tace "waye caculator" "gata nan New comer d'in nan", Dariya Safnah ta yi wai caculator, Sannan tace "ni computer ce ba caculator ba ka ji ko", dariya Safwan yayi sannan yace "ke babbab ce fa", "ko!" Safnah ta ce, yace "Ehh mana" "to yayi kyau", zama su ka yi su ka sha karatu nan da nan su ka saba da Safwan kuma ta yarda jiya be ganta ba ne don da ta zata wulakanci ne na masu kud'i amma Safwan ba ruwan shi.
Yau sati d'aya da canzawa Safnah aji yayin da wata irin shakuwa ce ta shigà tsakanin Safwan da Safnah wanda duk dad'ewar da su ka yi da maryam ba su yi irin ta ba, kowa ma kallon soyayya ya ke musu.
Safnah yau ta na dawowa gida ta ci abinci ta zauna ta fara ba anty labarin Safwan, anty tace "ai d'an gidan Alhaji muhammad ne, yànà zuwa gidan nan ma kwana2 ne ma na daina ganin shi, Dadyn khalil ai Likitan gidan su ne ya na duba dad shi", mamaki sosai Safnah ta yi a she ma anty ta san shi.
Anty ne tace "Safnah miye tsakanin ki da shi?", "anty bakomai kawai abota ne", "Safnah abota da namiji!, amma kinsan Safwan kuwa?, Safwan mutumin kirki ne kafin ya 'bata halin shi da shaye-shaye tun bayan rabuwar momin shi da Dad shi, bayan shaye-shaye da zuwa club kuma bai da wani abu, amma kuma kinsan d'an shaye-shaye ba abun da baze iya yi ba", ita dai Safnah shiru ta yi don sosai abun ya bata mamaki, duk da ƙarancin shekarun ta amma Safnah yarinya ce mai hankali da hangen nesa,yanzu take shekara na 14 amma a yanayin girman jikin ta zaka ce ma ta wuce haka don tana da tsayi ga jiki, jikin ta ya yi sanyi sosai har su ka gama hirar da anty bata sake yin kwakwkwaran magana ba.
Washe gari kuwa Safnah ko da taje school Safwan be zo ba ta tambayi Maryam tace mata wallahi bata san me ya hana shi zuwa ba, "gashi bani da number shi", cewar Maryam
Wajen kamal ta nufa tace "don Allah number Safwan na ke nema" murmushi ya yi sannan ya bata number kasancewar Maryam tana da waya amma don karatu aka siya mata, kira ta gwada yi taji ya shiga sannan tace "na gode" ta tafi
Kira ta 'kara yi amma ba'a d'auka ba, Safnah ce ta ƙarɓi wayar ta ƙara kira tare da ƙarawa a kunne, gaf da wayar zata tsinke aka d'aga sallama ta yi, da'kyar ta ji ya amsa sallamar, sannan ya fara fad'in wa... wa... wa...ye......ne... ? Zama Safnah ta yi kan wani dutse ba ta ma san ta zauna ba kasa magana ma ta yi shi ko Safwan be fasa surutan da ya ke yi ba hawaye ne su ka zubo wa Safnah a ido yayin da ko kasa kashe wayar ta yi shima be kashe ba har tsawon mintina5 sanna ta yanke wayar ta miƙawa Maryam ta tashi na nufi Class gaba d'aya ma bata gane karatun da akayi ba don tunanin da ya yi mata yawa.
Ko da Safnah ta koma gida 'karyar ciwon kai ta yi wa anty don ta kasa gane kan ta.
Washe gari ko da ta je makaranta a can ta sa mu Safwan, har ya je, yana hangota kuwa ya taso yana kwala mata kira Safnah banza ta yi da shi don haushin shi ma take ji yau, gudu yayi har ya kamota yace "haba Besty ina magana kin kyale ni", ko kallon shi bata yi ba ta yi gaba, be hakura ba binta ya cigaba da yi, har su ka iso wajan zaman su, su maryam duk suna wajen 'karasawa ta yi ta zauna kusa da maryam, zagayowa Safwan ya yi yace
"Safnah kin 'ki fad'a min laifin da na miki kinsan bazan iya jure fushin ki ba besty na mutanen da su ke wajen ne su ka kwashe da dariya, wasu har da shewa ma, kallon su Safwan ya yi sannan ya musu alama da su bar wajen.
Cikin minti1 Safnah ta ga ba kowa kallon shi ta yi tace "Safwan jiya meyasa baka zo school ba" shiru ya yi sannan yace "banajin dad'i ne"
Murmushin takaici Safnah ta yi sannan tace "Safwan jiya fa na kira ka, da safen, Safwan dama abun da aka fad'a min gaskiya ne Safwan kana shan giya", Idon ta taf da ƙwalla take maganar,
Hankalin Safwan yayi matu'kar tashi ganin hawaye a fuskar ta Hakuri ya shiga bata cikin kukan Safnah ta ke cewa "Safwan wannan fa halin an ce min da baka yi yanzu me yasa ka d"aura wa kan ka?, Kasan ubangijin mu ya hana fa kai ba jahili ba ne Safwan meyasa ka ke wannan abun Safwan.
Safwan ya ma rasa me zece mata don zuciyar shi ta yi mai zafi sosai, shi kan shi besan ya aka yi ya zama d'an giya ba, duk da momin shi na mai fad'a da wa'azi sosai idan yaje mata ziyara amma yau ne karo na farko da ya ji tunanin daina sha ya zo mishi, hakuri ya bata sosai, Safnah tace.
"Ni ka daina bani hakuri shawara ce kawai na baka, mi'kewa ta yi zata tafi.
"Safnah!"
ya kira sunan ta bata juyo ba amma ta tsaya cak, yace
"Nagode Allah da yasa ki ka san ba hali na ba ne amma!, amma ina bu'katar addu'an ki domin ni kai na ba'a son rai na na ke sha ba Safnah wataran idan ban sha ba jina nake kamar zan mutu, kaɗaici yayi wa rayuwa ta mamaya, Daddy na da nake matuƙar so baya nan ya zaɓi kasuwanci da zama a nan, momy na rabin raina bata tare dani se nayi dogon tafiya zan je wajen ta, kuma tace na daina yawan zuwa wajen ta, Anty (matar Daddy na) ba ta da maƙiyi da ya wuce ni, to ya zanyi kullum se dai, na je makaranta idan na dawo, ina zaune a ɗaki ko na fito kofar gida yin Ball, ba wanda za bani shawara yace yi wannan ko bar wannan, duk abinda naga dama shi nake yi".
se lokacin Safnah ta juyo ta kalle shi idanun shi sunyi jajur tace "Safwan na fahimci damuwar ka amma yaƙi zaka yi da zuciyar ka na ganin ka daina sannan ka dage da Addu'a da karatun Al-qurani, ina maka kyakykyawan zato",
Tana fad'in haka ta wuce aji, ta dad'e da shiga amma Safwan be shigo ba yana waje, mi'kewa ta yi ta nemi Izinin fita ta fito waje yana inda ta bar shi ya kifa kan shi, "Safwan!" ta fad'a be d'ago ba 'kara kiran shi ta yi se lokacin ya d'ago ya kalle ta tace
"an fara karatu baza ka shiga class ba ne"
"Ehh" yace mata, "meyasa?" "Ko na shiga Bazan iya karatu ba Safnah kai na ke ciwo", "to shikenan" Safnah tace, Sannan yace "ki kira Kamal ya kai ni gida"
"to" tace sannan ta juya cike da tausayin shi, ta nufi class d'in lokacin ma ba malami a ciki ya fita, Kamal ta kira ya kama shi ya saka shi a mota su ka nufi gidan su, cikin minti10 su ka isa gidan ko da su ka shiga falon Anty na zaune Mansur na gefen ta suna kallo Kamal ne ya shigo da sallama, Ko amsawa bata yi ba tace
"to ɗan giyan ne aka dawo da shi ya bugu ko?, kai! Allah ya wadaran naka ya lalace wallahi"
Kamal da yasan hali ko kallon ta be yi ba ma ya raka shi d'aki, kwanciya Safwan ya yi sannan yace "Kamal ka koma school ka kulan min da Besty na Don Allah"
"ok", yace sannan ya fita Ko da ya fito mansur ne kawai a falo, yace "yaya Kamal yayana bashi da lafiya ne?" "Ehh" kawai Kamal yace, "jikin nashi da sauƙi?" "da sau'ki" Kamal yace mai sannan ya wuce.
Safnah ko da aka ta fi da Safwan Ba malamin da ya sa ke shigowa kasancewar ma an kusa ta shi, ta na zaune tana tunani, har aka ta shi ta nufi gida cike da addu'ar Allah ya ba shi lafiya.
Washe gari ko da Safnah ta zo Makaranta acan ta Samu Safwan domin ya iya sammako Idan yaga dama, 'karasawa ta yi ta mai ya jiki yace "yayi, sau'ki gani ma kina kallo na", "Allah ya 'kara lafiya", nan dai su ka sha Hirar su sosai.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yayin da Safnah yanzu tana da shekara Goma
Sha biyar16 Safwan kuma yana da 24ya bata shekara takwas8 kenan yayinda, suna Ss3 sun kusa ma fita don har sun fara shirin graduation.
Yayin da Muguwar shakuwa had'e da soyayya ta shiga tsakanin su a cewa ta da sauran mutane amma su sun ce sam ba soyayya ba ce ba kawai Abota ce, haka dai kowa ya kyale su akan abota ce.
Tsarkakakkiyar tarayya suke yi tsakanin su don Safwan ko hannun Safnah be ta'ba ri'kewa ba, sa'banin wasu ko a school d'in na su ma, abun se dai Allah ya kyauta.
Safwan yana zuwa gidan su Safnah har d'akin anty kasancewar tun kafin Safnah ma ta zo yana zuwa don Kawun Safnah Likitan Baban shi ne da sauran gidan su ma, za su sha fira sosai, kasancewar Anty da Kawu sun san halin Safwan shiyasa su ka 'kyale Safnah da shi.
Da taimakon Safnah kuma duk shaye-shayen da Safwan ya ke yi ya dai na shi se wanda ba'a rasa ba a'boye don Idan ta sani akwai damuwa.
Bayan sun gama karatun su ne kuma Kawu yasa Safnah a A B U don ta 'kara karatu yayin da a wannan lokacin ne dangin Mahaifin ta su ka matsa lallai ya ba su 'yar su za su mata aure tunda shi ya barta ta na zaune haka nan ya ba su hakuri ya samu Safnah yace ta fito da miji domin ga abun da Baban ta yace, duk da yasan shima Safnah bata kula samari idan ba Safwan ba, Safnah tace mai bata da saurayi ita karatu za ta yi, "to" kawai Kawu yace ya kyale ta amma a zuciyar shi ya na mamakin Yaran nan, don ya yi ma Safwan magana ma yace mai ai ba soyayya su ke ba, haka dai Kawu ya share maganar.
Washe gari su ka had'u a school kamar kullum su na zaune su na hirar su, Safwan ne ya kalli Safnah yace "Safnah ki na so na!?", sosai Safnah ta yi mamakin tambayar a zuciyar ta tace "lallai ma yaron nan wato baze ce ya na so na ba se dai ya tambaye ni Ina son shi",
"kinyi shiru", maganar shi ta da wo da ita,
"a'a" tace mai, dariya ya yi yace "na zaci ke ki ka fad'a wa Kawu ki na so na", "Allah ya sawwa'ke me zan yi da kai d'an yaron ka da kai duka fa shekara takwas ka ba ni", dariya Safwan ya yi yace "lallai ma ni ne yaron to ki bari ki ga matata wallahi se kin rai na kan ki",
"oho dai mu gani a 'kasa, Dady ma baze maka aure yanzu ba ma", "haka ki ke ga ni, to ki dai na wannan tunanin don ko yau nace ma Dady na fito da mata se ya yi min aure", dariya Safnah ta yi tace "yayi kyau mu 'yan shan biki ne dai" haka su kayi ta hirar su.
Dad Safwan ya so ya kai shi England domin yayi karatu amma yace shi A B U kawai ya ke so don baze iya nisa ya bar Safnan ba, haka Dad shi ya yi hakuri ya kai shi A B U kuma yayi ma abokin shi da ke koyarwa acan magana yace yasa mai Ido sosai akan shi duk abun da yake ya na Idon shi, don har ya fad'a wa Dad shi maganar Safnah, sosai Dad shi ya ji dad'i.
Bayan su Safnah sunyi graduation sunyi hutu hakan yasa suka tafi Kano don gaishe da kakan su tsohuwa mai ran ƙarfe, duka suka tafi har da Kawu, suka yi kwana biyu shi da Anty sannan su ka dawo su ka bar yaran sai sunyi wata ɗaya kafin su dawo, don sun samu hutu mai yawa.
Kakan su taji daɗin zuwan su don sun ɗebe mata kewa sosai, Safwan kuwa Kullum se sunyi waya don yanzu tana da ƴar ƙaramar waya a hannun ta, Safwan yana so ya siya mata babban waya amma taƙi yarda, don Kawun ta yace se ta shiga babban makaranta ze siya mata.
Yau ma kamar kullum Safnah na kwance a gadon da ya kasance nata ne tunda tazo Kano, waya ne a maƙale a kunnen ta suna magana da Safwan.
"Kina ganin wasa ne ko, wallahi gobe ina nan zuwa Kano, se dai idan baki so mu haɗu ba, ki ka ƙi yi min kwatancen gidan" cewar Safwan
Dariya sosai Safnah ta yi sannan tace "zaka zo gurin momy kenan" "A'a ni wajen ki zan zo momy na bata son naje wurin ta ma" cikin shagwaɓa yayi maganar hakan