Header Ads
Showing 45001 words to 48000 words out of 57539 words

Chapter 16 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

561

Ads at the middle of Article

itama ta na part ɗin na su.


"Ehh in sha Allah!, Gobe nake son tafiya"


"Amma mu gaskiya se ranar bikin za muje don wallahi kunya ma nake ji, kuma gashi sun damu da na zo, don Salmah kullum se ta kira ni, wai mu taho tare da kai, har an fara Event"


"A'a ba zaki je gobe ba!, Se jibi, jibin ma se anyi sallar azahar za ku fita inda zaku isa da yamma ko ma da dare"


"To yaya Allah ya kai mu" Hindu ta faɗa.


Hira su ka cigaba da yi abun su gwanin burgewa.




Bari mu waiwayi mutanen Zaria kuma don jin irin wainar ta ake toyawa.




*****ZARIA*****


Safwan ne zaune a babban falon su, misalin ƙarfe 12:00 na rana, Daddyn na shi ma, saukar shi kenan a garin yau, don dama yace se bikin two ko three days sannan ze dawo, yau kuma bikin saura kwana uku 3 ne.


Tarin kayan lefen da Daddyn shi ya ƙaro suke kallo, don ya ninka wanda Antyn ta haɗo, sau biyu ma, a fili Antyn ta nuna jin daɗinta da kayan da ya ƙaro amma a cikin ranta baƙin ciki ne fal!.


"Safwan ka koma ka duba gidan kuwa? Ka tabbatar sun gama komai?" Daddyn Safwan ya faɗa.


"Ehh Daddy an gama komai tun last week ma"


"To Masha Allah!, Anjima ku na da Event da zaku gabatar ko?"


"Ehh Daddy!, Amma ni ban so suka shirya wannan abubuwan ba, ga na can gidan, ga kuma na su Kamal"


"Haba Safwan ya ka ke wannan maganar ne?"


"To Daddy ayi haƙuri"


"Ok, gobe za'a kai lefe fa" Daddy ya faɗa yana kallon Antyn.


Murmushin yaƙe ta yi tare da ce wa "to Allah ya nuna mana goben lafiya"


"Ameen!" Daddy ya amsa dashi.


Shi ko Safwan fita yayi ya bar gidan ma gaba ɗaya.


Gidan su Kamal ya nufa, don daga can yake son shiryawa su tafi Event ɗin da za'a yi a gidan su Salmah, daga nan kuma su wuce wanda su ka shirya na dare.


Ayi min afuwa zan tsaya anan, sannan ina baran addu'o'in ku saboda ba na jin daɗi, shiyasa kuka ji ne shiru, yau ma na dage ne nayi typing ɗin.
Nagode.


Comment ɗin ku shine ƙarfin gwiwar mu.




??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*_35&36


*****Washegari*****




*****ZARIA*****


Kamar yadda Daddy ya faɗa hakan ce ta kasance, misalin ƙarfe 3:30 na rana aka kai lefen Gidan su Salmah, yau ta kasance Laraba, saura kwana biyu 2 bikin, don ranar juma'a ne bikin zai kasance.


Gidan su Safwan har mutane sun ɗan fara zuwa, amma ƴanuwa Daddyn shi ne kawai, a ɓangaren Momyn shi kuwa babu wanda ya zo, ko da mutum ɗaya, Momyn shi ma fushi take yi da shi, saboda be je bikinta ba, tun lokacin da yaje ya dawo ba tare da saninta ba be sake zuwa gidan ba.






A ɓangaren gidan su amarya kuwa, cike yake da jama'a ƴan uwa da abokan arziƙi, se hada-hadan biki ake yi, tun ana saura sati ɗaya biki ake Event, Momy da Daddy shiri su ka yi wa bikin sosai, saboda bikin tilon Ƴarsu ne.




Safwan kuwa tunda su ka fara Event sau uku ya taɓa zuwa, don wasu ma ba'a buƙatar shi a wurin na iya dangin amarya.






*****KATSINA*****


Abdul yau yake shirin zuwa Zaria saboda bikin ya kasance jibi ne, misalin ƙarfe 12:00 ya gama shirin shi tsaf, yana zaune a dining table yana cin daddaɗan girkin da ya saka Safnah ta yi mai, gefen shi kuwa Safnah ce da Meenal, suma abincin su ke ci, Hindu ta na ɗaki ta na bacci don bata jin daɗi sosai.


"Safnah ina abinda nace ki ɗauko min?" Abdul ya faɗa yana kallon Safnah.


Kallon shi Safnah ta yi ba tare da tace mai komai ba, don se yanzu ma ta tuna yace ta bashi hotonta.


"Kin manta ko?" Ta ji muryar shi yana faɗa.


Gyaɗa mai kai ta yi alamar "Ehh"


"To je ki ɗauko min, yanzu kafin na wuce"


"To" ta ce tare da miƙewa ta nufi ɗakinta.


Zama ta yi a bakin gado tana tunanin ta zo da hoto ma kuwa garin nan, ƴar ƙaramar jakar da tazo da ita ta ɗauko ta fara dubawa, ta samu hoto guda ɗaya, amma kuma hoton be yi kyau ba kuma baza ta iya bashi ba, ajiye wa ta yi tare da fitowa ta dawo wajen.


Lokacin da ta dawo ba ta samu Meenal a falon ba, da alama ta shiga ɗakinsu ne.


"Ya na ga hannun ki babu komai?" Abdul ya faɗa tun kafin ta ƙaraso wajen shi.


"To yaya hotuna na suna Zaria ai ban zo da su ba!" Safnah ta faɗa tare da zaunawa a wajen da ta tashi.


"Ok, to ba ni wayar ki" ba musu Safnah ta miƙa mai wayar.


Kai tsaye Gallary ya nufa na wayar yayi sa'a kuwa akwai hotuna da Safnah ta yi, kuma duka ranar Family meeting ɗin su ne su ka yi da su Hindu a part ɗin su Teemah.


Hotunan sun yi kyau sosai da sosai, murmushi ne ɗauke a fuskar Abdul na ganin hotunan masoyiyar tashi, WhatsApp na wayar Safnah ya shiga tare da yin mark ɗin hotunan ya tura ta number shi, sannan ya kashe mata Data ya miƙa mata wayarta.


Ƙarɓa Safnah ta yi ba tare da ta ce komai ba.


Miƙewa Abdul yayi tare da cewa "kin san menene Safnah?"


"A'a yaya se ka faɗa"


"Wallahi ji nake yi kamar na tafi da ke, saboda zan yi kewar ki sosai iya na yau kaɗai"


Safnah bata ce komai ba se murmushi ta yi, don bata san me za ta ce ba.


"Amma zan yi hakuri har gobe" Abdul ya faɗa tareda nufar ɗakin shi.


Mintuna biyu2 da shigar shi ya fito ɗauke da jakar shi, wanda zai tafi da ita.


Safnah ta na tsaye a wajen da ya bar ta, ƙarasawa yayi tareda ce wa "Safnah kira su Meenal mu yi sallama na wuce rana ta na ƙara yi"


"To yaya" Safnah ta faɗa tare da nufar ɗakin na su.


Shi kuwa juyawa yayi ya nufi ɗakin kaka.


Da sallama ya shiga ɗakin, a zaune ya sameta ta na cin abinci wanda mai aiki ta kawo mata tun ɗazu.


Amsa sallamar ta yi tare da cewa "Kaka na zo miki sallama ne zan wuce"


"To Abdul-jabbar a gaishe da su Faruqu da iyayen na shi.


"To kaka za su ji, gobe su Hindu za su taho su ma"


"To Allah ya kai mu"


"Ameen" Abdul yace tare da fita daga ɗakin.


A falon ya samu su Meenal ɗin har da Hindu don ta ji sauƙi sosai, har wajen motar shi su ka raka shi, ya shiga tare da barin gidan.




A maimakon su koma part ɗin su se kawai su ka nufi na su Teemah.


A falo su ka samu Umman Teemah gaishe da ita su kayi sannan su ka nufi ɗakin Teemah.


A falon ɗakin na ta su ka same ta ta na waya.


"To Sarkin waya!, Kullum ki na maƙale da waya kamar mayya, Allah ya shirye ki dai" Meenal ta faɗa.


Da gudu Teemah ta tashi ta nufi uwarɗakar ɗakin nata, don tasan ba za su bar ta ta yi wayar cikin nutsuwa ba, ta na shiga kuwa ta dannawa ƙofar key.


"To fa!, Allah ya kyauta" Hindu ta faɗa ganin abinda Teemah ta yi.




Zama su ka yi su ka cigaba da hirar su.


Bayan mintuna 2 Teemah ta fito ta na faɗin "Allah ya shirye ku, baku san idan mutum yana waya ku yi shiru ba se kun yi mai wannan surutan na ku na banza"


"To Inna ayi hakuri ko!" Meenal ta faɗa


"HM, ku-ku-ka sani dai" Teemah ta faɗa.


"Ke fa ƴar rainin wayo ce wallahi, ke akwai wanda ma ya kai ki yin haka, se dai kice Allah ya shirye ki" Hindatu ta faɗa.


"Ni dai yau ba najin surutu ku kyaleni kawai"


"Kai! Ku bata hannu Teemah ta fara hankali wallahi, gara ai ki yi hankali saboda gidan wani zaki" Meenal ta faɗa.


"Kai bana son iskanci fa!, Yau abun naku kai na ya dawo, wannan ta ce waccen ta ce, to wallahi za mu hau sama mu sauko!"


"To fa!, Baza a hau ba ma bare a sauko" Hindu ta faɗa ta na dariya, ita kuwa Teemah haɗa rai ta yi sosai.


"Don Allah ku bar wannan zancen haka, kar ya zama faɗa fa" Safnah ta faɗa.


"To Anty babba ta yi magana se ku bar surutun haka nan" Meenal ta faɗa.


"Ai ko yaya Abdul ɗin ne yayi ya bari" Teemah ta faɗa.


"Yau da dukkan alamu Teemah ran ki a ɓace yake waye ya taɓa min ke ne? Haba amarya wajen Faruq bada kanki a sare!" Meenal ta faɗa cikin sigar wasa.




Murmushi Teemaah ta yi tare da cewa "wallahi rai na fes!, Ba damuwar komai"


"To shine ki ke wani cin magani"


Dariya Teemah ta yi tare da cewa "ai ku ne idan ba na fito mu ku a mutum ba ba za mu tafi dai-dai ba, da Momyn Faruq fa mu ke waya amma kuna ta min wasu maganganu"


"To Allah ya huci zuciyar ki" Hindu ta faɗa.


Hira su ka cigaba da yi abun su, har bayan la'asar sannan su ka dawo part ɗin su domin ɗaura girkin dare.




*****ZARIA*****


Anty ne zaune ita da kawu a falon na su gefe kuma Kaka ne kwance, kallo ɗaya zaka yi mata kasan ta na jin jiki sosai.


"Abban Khalil yanzu haka za mu zura mata ido ka ga fa jikin nata kullum ƙaruwa yake yi" Anty ta faɗa fuskarta ɗauke da tsantsar tausayin halin da kaka take ciki.




"To ya za'a yi!, Duk abinda ya kamata ayi mata anyi kuma typhoid ne kawai da maleria ko a asibiti na bar ta iya abinda za'a mata kenan, magani ne, se kuma ruwan da ake saka mata"




"To Allah ya bata lafiya!"


"Ameen! Shine abin cewa" Kawu ya faɗa.


"Amma Abban Khalil ya kamata fa mu waiwayi Safnah, ka ga fa yau wata uku kenan da tafiyar ta, ba mu ƙara jin ɗuriyarta ba, gashi ba number ta bare mu kira mu ji, kuma ka ga yanayin jikin kaka ya kamata ace ta zo ta duba ta"


Tunda ta fara maganar kallon ta Kawu kawai ya ke yi se da ta gama sannan yace


"To yanzu ya ki ke so ayi?"




"Yana wajen ka ai!, Kamar yadda su ke da iko da Safnah kai ma kana da iko da ita, ya kamata ace ta dinga zuwa idan buƙatar hakan ya ta so, kuma akwai muhimman kayan ta a ɗakinta musamman ma na karatu, ya kamata ta zo ta ɗiba ko mu kai mata"


"To shikenan zan kira Baban na su" Kawu yace tare da wasu tunane-tunane a cikin zuciyar shi.


"To shikenan, na san ba ta san da bikin Safwan ba ma da za ta yi ƙoƙari ta zo"


"Ni ba na son ma ta sani, saboda ba amfanin hakan, ina son su rabu gaba ɗaya ne, kar komai ya ƙara shiga tsakanin su" Kawu ya faɗa.


Hira su ka cigaba da yi kusan duk akalar hirar ta su ya karkata ne a kan Safnah.


Har cikin ran Anty ta na son Safnah ta dawo, domin sun yi sabo sosai, ta so ace aure ne kawai ze raba su da Safnah, Kawu shi ma ya so hakan amma na dole ya hakura.




*****KATSINA*****


*****Washegari*****
Safnan tunda ta tashi gabanta ya ke faɗuwa, ta rasa dalilin hakan, a wani ɓangaren na zuciyarta kuma cike take da farin cikin zuwa Zaria da za su yi don tasan dole ta je gidan Anty kuma za ta haɗu da masoyinta Safwan.






Misalin ƙarfe 12:00 na rana Sadiq ya shigo gidan na su tare da cewa su shirya yanzu za su wuce don Abdul ya kira shi yace yazo ya ɗauko su yanzu.


Ba ɓata lokaci su ka fara shiri dama sunyi wanka kayan da za su tafi da shi ne kawai suka tsaya kimtsawa, shi kuma Sadiq kai tsaye part ɗin su Sa'adatu ya nufa domin zantawa da sahibar shi, don tun kafin ya taho ya faɗa mata ta shirya, har kayanta ta haɗa zuwan shi kawai take jira dama.




Se misalin ƙarfe 1:00 sannan su ka bar gidan, kai tsaye gidan su Abdul su ka nufa domin ɗaukar A'isha, sun sameta ta shirya tsaf, ba tareda ɓata lokaci ba su ka ɗauki hanyar Zaria.


To se in ce mu ku a sauka lafiya.




****ZARIA*****
Gidan su Safwan se cika yake da jama'a ƴanuwan Daddy da kuma ƴanuwan Anty, musamman ma yau da ya kasance gobe ne za'a ɗaura aure.




Duk wannan shagalin da ake yi Mommyn Safwan ba ta zo ba har yau, kuma ba wanda ya bi ta kanta ma, ciki kuwa har da Daddy, Safwan kuwa ko kaɗan be ji daɗin hakan ba, kuma be kira Momyn na shi ba, rabon da su yi waya ma tun ana saura sati biyu biki.




*****JUSHI*****


Abdul ne shi da Faruq zaune a ɗakin da ya kasance na Faruq ɗin ne su na hutawa, don sun gaji sosai tun safe ba su samu hutu ba se awannin da su ka wuce.


"Ka kira ka ji su na ina ne?" Faruq ya faɗa.


"Ba zan kira ba, ka jira har lokacin da za su zo, kai ka cika ƙosawa wallahi"


"Yayi kyau!, Kasan zan iya kiran Teemah ta faɗa min ai"


"Ok kira ta, idan ta san garin kenan"


Murmushi Faruq yayi tare da ɗaukar wayar shi, number Teemah ya kira, yayi sa'a kuwa bugu ɗaya ta ɗaga, "Assalamu alaikum!" ya faɗa.


"Wa-alaiku-mussalam!, Ya hanya?"


"Alhamdulillah!" Teemah ta faɗa.


"Ku na ina ne?"


"Kasan ai ban san garin ba"


"To ki tambayi Sadiq mana"


"Yace mun wuce Kaduna tun ɗazu" Teemah ta faɗa bayan ta tambayi Sadiq ɗin.


"Ok, se kun ƙaraso" Faruq ya faɗa tare da yanke wayar, sannan ya dubi Abdul yace "sun kusa isowa fa!"


"Ok Allah ya kawo su lafiya" Abdul yace.


Kafin su ƙara wani magana su ka jiyo ana bugun ƙofar falon, Abdul ne ya tashi ya ya nufi ƙofar domin buɗewa.


Salmah ne tsaye a bakin ƙofar lokacin da ya buɗe, Masha Allah! Ta haɗu sosai simple makeup ne a fuskar ta, ta saka kayan Fulani kasancewar yau za su yi funali day, kayan sun amshi jikinta sosai.


"Amarya da kanta ne ashe, kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa!" Abdul ya faɗa.


Murmushi Salmah ta yi tare da cewa "Nagode yaya Abdul"


Shigowa ɗakin ta yi tare da cewa "yaya faruq Daddy yace ka zo"


"To, ba ku fara ba ne?" "Ehh yaya se anyi Sallar la'asar, kuma gashi ma be zo ba"


Duba wayar shi yayi ya ga ƙarfe 3:45, sannan yace "to Allah ya kawo shi"


"Yaya na ji shiru ne ba su iso ba"


"Yanzu na kira sun kusa isowa"


Murmushi Salmah ta yi, sannan tace "to Allah ya kawo su lafiya"


"Ameen" su ka amsa.


Ta na rufe baki aka yi sallama a ƙofar ɗakin, wata ce wacce za suyi sa'a da Salmah ƴar ƙanwar Momyn su ce, Farida sunan ta.


Ƙarasowa ta yi tare da yi wa su Faruq sannu sannan ta ce "Salmah Momy na kiran ki!"


"To" Salmah tace tare da nufar ƙofar fita, Farida ta mara mata baya.


Su Faruq ma miƙewa su ka yi don amsa kiran Daddy.


**********


Safwan ne kwance a bedroom ɗin shi, gefen shi kuma Kamal ne, yayin da falon ɗakin shi ke cike da abokan su, duk sun shirya Safwan kawai su ke jira don zuwa gidan su Salmah.




"Safwan wai ka san ƙarfe nawa yanzu kuwa?" Kamal ya faɗa


"Na fi ka sani tunda ka ga da agogo a hannu na, kuma ni ba makaho ba ne"


"To Allah ya huci zuciyarka, ai ban ce kai makaho ba ne dama"


"Ka ji da shi dai!" Safwan ya faɗa tare da miƙewa ya nufi bayin ɗakin nashi.


"ka jira ni a waje zan yi wanka" Safwan ya faɗa lokacin da ya kai ƙofar bayin, ba tare da ɓata lokaci ba Kamal ya tashi ya fita.


Mintuna 15 Safwan ya ɗauka a bayin kafin ya fito, mayuka ya shafe jikin shi da su da turaruka kafin ya buɗe sif ɗin shi, kayan da aka ɗinka mu su musamman na Fulani day ya ɗauko ya saka, sunyi bala'in yi mishi kyau, se ya zama kamar bashi ba, Wayar shi ya ɗauka tareda mukullin shi ya fita.


Su na falon kamar yadda ya bar su harda Kamal "mu je" kawai yace mu su, miƙewa su ka yi gaba ɗaya, su Goma ne har da Safwan da Kamal su ka nufi waje, Safwan rufe ɗakin shi yayi tare da nufar babban falon na su.


Mutane ne sosai a falon su na ta hada-hadan bikin, gaishe da su Safwan yayi kafin daga bisani idon shi ya sauka a kan fuskar Momyn shi, Murmushi ne ya faɗaɗa a fuskar shi, da sauri ya ƙarasa tare da ce wa "Momy yaushe ki ka zo?"


Murmushi ita ma ta yi sannan ta ce "Safwan ɓan daɗe sosai ba, Masha Allah ka ga yadda ka yi kyau! Se kace Fulanin gaske!"


"To Momy ai Fulanin ne"


Hira su ka ɗan taɓa da Momyn na shi, kafin ta ce mai "Safwan ka tafi lokaci yana ƙurewa" tashi yayi ya nufi waje don su Kamal tun ɗazu su ke jiran shi a wajen, ka na ganin Safwan za ka ga fuskar shi ɗauke ta farin ciki, wanda ya daɗe be yi kamar shi ba, dama tsakanin uwa da ɗa Allah ne kawai ya sani.


Yana fitowa motar shi ya shiga, sauran kuma su na ɗayan motar har da Kamal, kai tsaye gidan su Salmah su ka nufa.






**********


Misalin ƙarfe 4:5 su Safnah su ka iso gidan su Salmah, tunda suka shigo gidan bugun zuciyarta ya ƙaru.


Perking Sadiq yayi sannan su ka fito daga motar, Farida ce ta zo ta tarbe su, kasancewar Salmah ta na can ana sake mata kwalliya don Safwan ya kirata ya faɗa

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads