Showing 57001 words to 57539 words out of 57539 words
Chapter 20 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
na ƙarewa gidan kallo don iya haɗuwa gidan ya haɗu na ƙarshe.
"Safnah!"
Safnah ta ji an kira sunan ta, gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa don duk duniya ta yi imani mutum ɗaya ne mai wannan Muryar wato Safwan.
Ƙasa juyowa ta yi don kafafunta da su ka yi mata nauyi, amma ta na jiyo takun tafiyar shi alamun ya nufo wajen da take.
"Safnah ashe ke ce!, Ba gizo idanuwana su ke min ba, Allah na gode maka!" Safwan ya faɗa fuskar shi ɗauke da tsantsar farin ciki.
Dakyar Safnah ta daidaita nutsuwarta ta ɗago ta kalle shi, tare da ƙaƙalo murmushin da za'a iya kiran shi da yaƙe ne, ta ce "Ehh Safwan, ya kwana biyu 2"
"Lafiya lau, ina ki ka shige ne ko nema na ba ki yi, ba kira ba chat kin sani cikin damuwa!, Kuma me ya kawo ki gidan nan?"
"Safwan ashe ba ka manta da ni ba kenan har ka ke tunani na da damuwa akan tafiya ta?"
"Haba Safnah ya zan yi na manta da ke!'
"Ok!, Na zo bikin Salmah ne dama!"
"Salmah kuma?, Miye haɗin ki da ita?"
Murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo Safnah ta yi sannan ta daure ta ce "Lefi ne don na zo bikinta?, Kuma na ga ai bikin ka ne kai ma!"
"Safnah ki bar wannan magana ki ɗauƙi auren nan a matsayin ba aure ba, saboda ba son rai na aka yi shi ba!" Safwan ya faɗa fuskar shi ɗauke da damuwa.
"Safwan kenan! Ban san meyasa ka ke faɗa min haka ba, kamar bansan soyayyar da ta ke tsakanin ku ba tun a School"
"A'a Safnah wallahi ban taɓa jin son Salmah a rai na ba ko kaɗan!"
"To shikenan!, Ba damuwata ba ce hakan, ni se dai na ce Allah ya ba ku zaman lafiya!"
"Safnah ni kuma damuwata ce hakan!, Saboda Safnah ke ce zaɓina, da ke na ke son na ƙare rayuwata!"
"Ban fahimci mai ka ke faɗa ba Safwan!, Ka fahimtar da ni!"
"Safnah yau ba wani ɓoye-ɓoye don na gaji da dakon son ki da ya ke wahalar da ni, Safnah ina son ki! Ina son ki!! Ina son ki Safnah tun da daɗewa, kuma ke ma na san ki na so na!, Ki daure ki faɗa min haka ko na ji sauƙi a rai na!" Safwan ya faɗa cikin rawar murya kamar mai shirin yin kuka.
Ita kuwa Safnah kuka ta fashe da shi mai tsuma zuciya, don zuciyarta ta tsinke, cikin kukan Safnah ta ce "Safwan ba kalmar da na daɗe ina jira ta fito daga bakin ka irin wannan, amma ba ka faɗa min ba!, Safwan nima Ina son ka! Matuƙar so!"
Kafin wani ya sake yin magana su ka ji motsin mutum a bayan su, tare da karar faɗin abu.
Da sauri su ka juyo a tare, Abdul su ka gani tsaye idanun shi sun kaɗa sun yi jazur, fuskar shi a matuƙar ɗaure kai za ka ce be taɓa dariya ba a rayuwar shi, in da su ke ya nufo a matukar fusace.
Zan tsaya anan don ni kai na Abdul ya ba ni tsoro har ta kai alƙalamin rubutu na ya faɗi, amma idan tsoron ya gushe zan ɗauko alƙalamin nawa domin na sanar da ku yadda za ta kasance.
Ku kasance da ni har kullum
Khadeejerh Ishaq ce ✍️