Showing 30001 words to 33000 words out of 57539 words
Chapter 11 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt
Umar (Faruq) kuma babban Abokina ne, kuma aminina ne shi, ɗazu baki nan na gabatarwa su Hindatu shi"
Safnah bata ce komai ba har yanzu, neman hanyar guduwa ma take yi.
"Safnah ki same ni a ɗaki zanje nayi Sallah don naji ana kira" cewar Meenal tana yin gaba.
"A'a muje kawai nima banyi ba ai" Safnah tace tare da bin bayan Meenal.
"Kai Abokina ƙannen naka har guda nawa ne, naga basu ƙarewa" cewar Faruq.
"Kai! Ai a ƙannena baka ga komai ba ma"
"Lallai ne babban yaya, ni kuma kaga Ƙanwa ta guda ɗaya ce Ummu Salma, ina son ta Sosai, amma kasan menene aboki?"
"A'a se ka faɗa"
"Wallahi ƙanwar ka ta tafi dani sosai"
"Wacce kenan?"
"Wannan da naji ka kira Safnah"
"Lallai yaro to wannan anyi mata miji da kake gani"
"Kasan yadda zaka yi, ya haƙura ya barmin ita kawai"
"Lallai ma to an kusa bikin ma"
"Gaskiya a fasa wallahi" dukan wasa Abdul ya kaiwa Faruq tare da cewa"ɗan rainin wayo matar tawa ne kake so"
Dariya sosai Faruq yayi sannan yace "dai-dai ma kenan tunda kaine Seka haƙura ka barmin"
Dariya Abdul yayi tare da cewa"gaskiya fa ka haƙura domin wannan bazan iya barin maka ita ba, kayi biyayya na baka wata ƙanwar tawa dai"
"Yawwa babban yaya wacce a ciki?"
"Biyun nan da ka gani Hindatu da Meenal suna da wanda suke so, wata ce anjima zaka ganta"
"To shikenan muje muyi sallah nazo na ƙara abincin nan don yayi min daɗi sosai"
"Girkin ƙanwata ce"
"Ƙarya haramun fa"
Faruq ya faɗa, lokacin har sun kai ƙofar fita falon.
Basu suka dawo gidan ba se ƙarfe 5:15 lokacin su Safnah duka suna falo suna kallo, ƙarasawa sukayi suka zauna, hira suka cigaba da yi.
Abdul ne ya matso saitin kunnen Faruq tare da cewa "Mallam ka daina kallon min mata fa, kar kaji naushi yanzunnan"
Dariya Faruq yayi tare da cewa "ayi min afuwa Oga" shi da ƙarfi ya faɗa, saɓanin Abdul da yayi mai raɗa, hankalin shi yana kan Safnah yana lura da halin da take ciki kamar bata da lafiya gashi taƙi sakewa sosai yau.
"Hindatu ki je ki kira min Teemah, ku taho tare yanzu fa"
"To" Hindatu tace tare da miƙewa ta nufi hanya"
"Yaya yaushe zaka koma ne?" Cewar Meenal.
"Ai se nayi one month kafin na koma"
"Kai naji daɗi sosai amma"
"Abba ya faɗa muku za'a yi baikon ku keda Hindatu a cikin wannan satin?"
Rufe fuska Meenal tayi, tare da gyaɗa kai alamar Ehh,
"To yayi kyau se a cigaba da karatu idan an shiga ɗaki ko"
"Insha Allah Yaya, Teemah kuma tace se ta fara karatu kafin nan"
"Ki ƙyale ta, tana da taurin kai ne Fatima amma Abba yace duk tare za'a yi nan da two months2"
Dafe ƙirji Meenal tayi tare da cewa "yaya two months2 fa, ai yayi kaɗan wallahi".
Dariya sosai Abdul yayi sannan yace "lallai ai kuwa Baba babba har ya saka ranar ma"
"Ka ga kana da bukukuwa da yawa, ƙanne har nawa, kasan bikin Salmah na saura One month1 shima" cewar Faruq
"Kai! Haba ashe biki ya matso"
"Ehh mana"
Dai-dai lokacin su Teemah da Hindatu suka shigo, da sallama.
Amsa musu sallamar suka yi, cikin falon suka ƙaraso, Hindatu ta zauna a inda take, ita kuma Teemah can kusa da yaya Abdul ta nufa cikin fara'a take cewa
"Babban yaya kenan, kace har ka iso, to ya hanya kuma ya aiki"
"Lafiya lau" Abdul yace.
"To naji kira ne, ance kuma idan kaji kira samu ne, tsarabar tawa ce aka kawo?"
"Ehh! Amma baza ki iya zama bane kika tsaya min a kai kamar sanda"
"Allah ya huci zuciyar babban yaya"
Ta faɗa tana yin baya don zama, cikin rashin sani ta zauna a kan Safnah wanda yanzu jikin nata yayi tsanani sosai don ji take kamar kanta ze rabe gida biyu, ƴar ƙaramar ƙara ta saki a wahalce.
Dasauri Yaya Abdul ya tashi ya nufo wajen ai kafin ya kawo Teemah ta ruga da gudu tabi hanyar kofa.
Muryar shi ta jiyo yana cewa "Teemah idan kika kuskura kika bar falon nan se kin ɗanɗana kuɗar ki wallahi".
Cak! Teemah ta tsaya don tasan karon ba daɗi.
Safnah kuwa har hawaye sun fara bin fuskar ta,
"Sannu Safnah bata ji miki ciwo ba ko?"
Gyaɗa kai Safnah tayi, daƙyar tace "zanje nasha ruwa"
"Hindu ɗibo mata ruwa tasha"
"A'a yaya bari naje" ta faɗa tare da miƙewa cikin sauri har tana haɗa hanya.
Sum-Sum Teemah ta fara tahowa don dawowa, har gurin Ya Abdul ta nufa ta duƙa a gaban shi tare da kama kunne tace "yaya Abdul kayi hakuri wallahi ba da sani na ba na zauna a kanta ba, Allah kuwa"
"Zamu haɗu ai jeki zauna" waje ta samu ta zauna tana dariya ƙasa-ƙasa, bata san Abdul yana kallon ta ba, har da ɗagawa Meenal gira.
Faruq kuwa ya zama kamar kurma se ido ba baki, Teemah kawai yake kallo, Abdul ne ya ɗan taɓa shi ya waigo, da ido yayi mai alama da ya tashi su shiga ciki.
Tare suka miƙe suka nufi ɗakin Abdul ɗin.
"Ya! Abokina ya ka ganta ne" cewar Abdul yana tura ƙofar.
"Kai! Masha Allah wallahi nayi mata in sha Allah tayi sosai, kasan miye ma?"
"A'a se ka faɗa"
"Wallahi tafi ɗayar nan ma kyau, gata da baki, ni nafi son me baki ma wallahi ba kamar ɗayar ba"
"Ai kai kace, amma ni nafi son natsatstsiyar yarinya mai hankali"
"Au kana nufin matar tawa ba nitsatstsiya bace kenan"
"Kaji wani magana, a ina ta zama Matar taka, kayi biyayya yaro ka samu Teemah, kasan a hannuna komai yake"
"To naji babban yaya, yanzu ya za'ayi kenan"
"Daɗi na da kai naci da ƙosawa, ka jira zanyi magana da ita"
"Matsalata da kai nuƙu-nuƙu da jan magana tayi tsayi, ni ason raina yanzu kawai ka sameta"
"Kai dai ka bari gobe in sha Allah zan haɗa ka da ita"
"To naji"
"Taso mu koma falon"
Cewar Abdul, tashi sukayi don dawowa falon.
Suna nan zaune a wajen da suka bar su, suna hira, amma Safnah bata dawo ba.
"Ina Safnah?" Abdul ya tambaya don be ganta awajen ba.
"Bata dawo ba fa" cewar Hindatu.
"Jeki ki kira min ita"
"To" Hindatu tace tare da miƙewa ta nufi ɗakin Safnah.
Safnah kuwa tunda ta bar wajen daƙyar ta ƙaraso ƙofar ɗakinta ma, tana zuwa kuwa jiri ya ɗibeta ta faɗi a kofar, kuka ta saki don ita kaɗai tasan abunda take ji a jikinta, tafi mintuna goma10 a ƙofar kafin daƙyar ta yunƙura ta tashi ta shiga ciki, tana shiga a kujerar falon ma ta zauna, zuciyar ta na wani irin bugu da ƙarfi ga wani tari da ya kamata lokaci guda daƙyar ta miƙe don zuwa ta ɗauko ruwa a firij ɗin dake ɗakin, kafin ta ƙarasa wajen ta zube ƙasa sumammiya.
Hindatu na buɗe ɗakin idon ta ya sauka akan Safnah da take ƙasa kamar gawa, da gudu ta ƙarasa wajen, jijjigata ta shiga yi, amma bata ko motsi, cikin tashin hankali ta juya da gudu zuwa falon.
Suna zaune a falon har yanzu, suna ganin Hindatu a guje duka suka miƙe tsaye.
"Meya faru Hindatu" Cewar Abdul,
"Yaya Safnah ta.....!ta.......!"
"Ta mene!?"
Be tsaya jin me zata ce ba yayi gaba duka suka bishi a baya.
"Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un" Abdul ya furta lokacin da ya hango Safnah yashe a ƙasa, dai-dai lokacin su Meenal da Faruq suka ƙaraso, tashin hankali sosai suka shiga suma.
"Hindatu ku kama ta ku fito da ita waje, Bara na ɗauko mota" Abdul ya faɗa tare da juyawa da sauri ya nufi waje Faruq ma bin shi yayi.
Su uku suka kama Safnah zuwa wajen da motar yake, suna fitowa suka shiga don Abdul ma har ya kunna motar sun shiga, hanyar gate ya nufa da gudun gaske.
??????????????????
_*????♂️ƘADDARAR SAFWAN????♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_
*PAGE*_23&24
*****Zaria*****
Shirye-shirye sosai Daddyn Safwan yake na biki, ana ta gyaran gidan da zasu zauna a unguwar su gidan yake ya haɗu sosai, yanzu ana maganar lefe ne da za'a haɗo nan da sati ɗaya, don yanzu bikin saura sati Uku ne.
Shi ko mai gayya mai aiki Safwan ko a jikin shi, don gani yake kamar wasa ne ma wannan auren ba gaskiya bane.
Gidan su Salmah ma shiri ake sosai kasancewar ta ƴa ɗaya tilo mace, kuma ga kuɗi da suke da shi.
*****KATSINA*****
Emergency room aka wuce da Safnah lokacin da suka isa asibitin, kowa ka gani hankalin shi a tashe, Abdul har ya kira Baba Babba da Baba Bashir suna asibitin suma.
Har yanzu ba'a buɗe ɗakin da aka shiga da Safnah ba, duk suna zaune suna jira yayin da Abdul zama ya gagare shi, se yawo yake don yafi kowa damuwa.
Kusan awa ɗaya1 sannan aka buɗe ɗakin, doctor Nurses suka fito, kai tsaye wajen da suke zaune Dotor ɗin ya nufa.
"Waye mahaifi ko mijin mara lafiya ya biyo ni" cewar likitan yana yin gaba.
Baba Bashir ne ya tashi ya bishi, mintuna biyu2 bayan shigar shi ya fito ya dawo ya zauna.
Abdul yana so ya tambayi Baba Bashir me yake damunta amma ya kasa, gashi yana son sani, wata shawara ce ta zo mai, ƙarasowa yayi wajen da suke yace "Baba an rubuta magunguna ne"
"Ehh Abdul ga takardan nan ka je ka siyo"
"To" Abdul yace tare da ƙarɓar takardan ya nufi ciki.
Kai tsaye ofishin likitan ya shiga da sallamar shi, amsawa likitan yayi tare da yi mai alama da ya zauna.
Zama yayi akan kujerar da take kallon likitan sannan yace
."Doctor dama akan mara lafiyar da muka kawo ne, don Allah menene yake damunta?"
Ido likitan ya tsira mai na wasu sakonnin sannan yace,
"Ai na riga nayi bayani ma wanda ya fita, ba shine mahaifinta ba?"
"Ehh shine, amma ni yayanta ne ni, kaga ko ina da hakki na sanin me yake damunta
"Ok ƙanwarka jininta ya na gaf da hawa ne sanadiyyar damuwa da take fama dashi, wanda ya haddasa mata barazanar kamuwa da wannan ciwon, kuma idan ba'a ɗauki mataki ba, abun ze cigaba ne har zuwa inda bamu fata, amma idan ta cigaba da shan magungunan da aka rubuta mata zata samu sauƙi sosai.
Gumi ne ya ƙaryowa Abdul sosai najin abinda Doctor yace, ya za'ayi ace yarinya kamar Safnah ta gamu da hawan jini.
"To Doctor mun gode in sha Allah za'a kiyaye shan magungunan da aka rubuta, Mungode" ya faɗa tare da miƙewa ya nufi waje.
Lokacin da ya fito ya samu su Baba na shirin fita har da Faruq, kasancewar kiran sallar Magriba da ake yi, shima bin su yayi don zuwa yin nashi sallar shima.
Bayan sun idar su Baba gida suke wuce yayin da Abdul da Faruq suka dawo ɗakin da aka kwantar da Safnah.
"Har yanzu bata farfaɗo ba" Abdul ya faɗa yana kallon Teemah da ta tsura mai idanu.
"Ehh yaya shiru wallahi har yanzu"
Hindatu ta bashi amsa
"Yaya ashe Umma ce zata kwana da ita, ta kira ni tace min tana hanya ma" cewar Teemah
"Ehh ni na kira ta!, Ku gida zamu wuce da ku, se ku bar ɗaya ta taya Umma kwana"
Yana rufe baki kuwa suka ji sallamar Umma (Mahaifiyar Teemah) gaishe da ita su kayi duka, amma banda Faruq kasancewar baya ɗakin.
"Ya jikin nata ne Abdul?" Umma ta faɗa fuskarta ɗauke da tsantsar tausayin Safnah.
"To Umma gata nan dai!, Da sauƙi za'a ce"
"Subhanallahi! Allah ya bata lafiya"
"Ameen" Duka suka amsa dashi.
Mintuna talatin30 da zuwan Umma suka kama hanya don tafiya gida, lokacin ma kusan ƙarfe 9:12 ne, Hindatu aka bari don taya Umma kwana yayin da suka kamo hanyar gida.
Lokacin da suka iso gida 9:30 kowa part ɗin su ya nufa, Teemah taso ta taya Meenal kwana kasancewar Hindu abokiyar ta ta tana asibiti.
Meenal kuwa ɗakin Kaka ta nufa don bazata iya kwana ita kaɗai ba, ba abokin hira.
"Faruq ina cikin tsantsar damuwa da halin da Safnah take ciki, ina jin yau daƙyar idan zan iya bacci!" Cewar Abdul dake kwance a 3siter da take falon ɗakinshi.
Gyara zama Faruq yayi tare da kallon abokin nashi yace "lallai ne abokina ka kamu sosai, amma ina mamakin wannan abu haka, kace Safnah ba a gidan nan ta taso ba, hasalima bata daɗe da dawowa gidan nan ba!"
"Faruq kenan!, Baka san so ba, tunda kai ko budurwar ma baka da ita, amma wallahi tun ranar da na fara ɗaura idanuna akan Safnah Bayan dowawar ta matsanancin son ta ya shiga cikin rai na, a da na ɗauka wasa ne, amma yanzu na tabbatar in dai ba Safnah rayuwata tana cikin wani hali"
"To Allah ya kyauta!, Amma kuma kace min Safnah bata san cewa kana son ta ba, to baka gani hakan matsala ce!, Duba da kace min duk aure za a musu kaga Safnah na iya bayyana wani ba kai ba, to ƙaddara ma bata da wanda take so, kai kace auren haɗi za'ayi idan mutum be fito da wanda ze aura ba!"
Miƙewa Abdul yayi da sauri sakamakon wani tunani da yazo mai, ya tuna wayar da su kayi da Sadiq jiya yake faɗa mai ya samu matar aure a cikin Familyn su.
Da sauri Abdul ya jawo wayar shi, Number Sadiq ya lalubo tare da danna mai kira.
Gaf da wayar zata yanke Sadiq ya ɗaga "Assalamu alaikum babban yaya" Sadiq ya faɗa daga can bangaren
"Sadiq jiya muna waya baka faɗa min wacce yarinya bace kake so ba"
Dariya Sadiq yayi daga can sannan yace
"Akan wannan ka kira ni babban yaya!"
"Sadiq bana son wasa fa tambayar ka nayi"
"Saurin me kake yi, zan gabatar da ita ma kowa ranar Family meeting kasan ya kusa"
"A'a ni yanzu nake son ji!"
"To shikenan ka canka, wacece tafi kowa kyau a cikin matan Familyn mu"
Yanke wayar Abdul yayi zuciyar shi na dukan tara-tara, yasan halin Sadiq tunda ya mayar da maganar wasa ba
ze faɗa mai ba.
"Lafiya Abokina" Faruq ya faɗa ganin yanayin da abokin nashi yake ciki.
Labarin yadda suka yi da Sadiq ya bashi ya ƙara mai da cewa "yace wacce tafi kyau a Familyn mu"
Da sauri Faruq ya miƙe tare da cewa "kar dai ace Teemahna! Don wallahi tafi kowa kyau duk da ban ga sauran ba"
Duk da halin da Abdul yake ciki se da yayi dariya sosai, bayan ya tsaya da dariyar ne yace
"Lallai aboki ka faɗa da yawa, kaima kenan yau fa kuka haɗu amma har kake jin tsoron rasa ta!, To ni kuma nace mene?"
"To Allah ya kyauta!, Abin yi dai Shine kafin na wuce muje mu samu Sadiq, bayan ya bayyana mana ba ita bace, se na samu gimbiyar tawa, don da dukkan alamu idan na tsaya jiran ka zan rasa Teemah, tunda kaima naga baka ƙarfafa taka soyayyar ba, bare nawa" Faruq ya ƙarasa maganar yana yin dariya.
Shima Abdul dariyar yake yi, haka suka cigaba da hirar su cikin nishaɗi, don idan suna tare koda ɗaya yana cikin damuwa, ɗayan ze yi ƙoƙarin mantar da ɗaya damuwarsa.
Washe gari
Tunda su Abdul suka tashi sallar asuba ya je ɗakin Kaka ya faɗa wa Meenal ta haɗa mu su abun break fast na asibitin, domin zuwa ƙarfe 7:00 su ke son komawa asibitin.
Zuwa 7:00 suka fito se da suka karya sannan suka fito suka nufi asibitin.
Zuwa ƙarfe 7:25 suka isa asibitin, kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Safnah suka nufa da sallamar su.
Kai tsaye idanun Abdul suka sauka kan Safnah da Umma ke bata Tea a baki, farin ciki ne ya luluɓe shi, da sauri ya ƙarasa tare da gaishe da Umma, Faruq ma gaishe ta yayi.
"Umma ashe ta farka!"
"Ehh Abdul!, Tun jiya ma, kun fita ba daɗewa ta tashi"
"Safnah ya jiki?" Faruq ya faɗa
"Da sauƙi, ina kwanan ku ya Abdul"
Safnah ta faɗa da Muryar ta can ciki, irin ta mara lafiya.
"Lafiya lau Safnah ya jikin naki?"
"Yayi sauƙi"
"Umma ga break fast nan, a ina kuka samu kayan Tea"
"Sadiq ya kawo, tun jiya ma!"
Gaban Abdul ne yayi mummunan faɗuwa, kar dai ace tunanin da yake ya zama gaskiya.
Muryar Umma ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, ji yayi tana faɗin
"Lokacin da ta farka se tace yunwa take ji, gashi bamu taho da abinci ba, se Hindu ta kira shi ta faɗa mai saboda shine yafi kusa da asibitin, ga kuma dare yayi lokacin"
Abdul ya ɗan samu natsuwa kaɗan "amma ya zama dole naga Sadiq yau" ya faɗa a zuciyar shi.
*****ZARIA*****
Safwan ne shi da Kamal da kuma Daddyn shi suna magana akan bikin shi da yake saura kwana 18 yau.
"Daddy nifa bana son ayi wani Event a bikin nan bayan walima" cewar Safwan
"To shikenan tunda haka kace, amma son samu ne ace anyi, nasan can gidan su yarinyar baza a rasa shiryawa ba"
"Daddy kar ka bi maganar Safwan!, Ya za'ayi ace biki Kamar na Safwan a garin nan ayi shi hakanan ba komai, ai wannan ze iya taɓa darajarmu' cewar Kamal
"To Kamal naji naka kaima, ku zauna kuyi shawara duk halin da ake ciki dai kuyi min waya se na turo muku da kuɗin da ze ishe ku, don zuwa jibi in sha Allah nake son wucewa, ina jin kuma zan kai ana saura kwana uku biki kafin na dawo"
"To Daddy mun gode" cewar Kamal.
Tashi suka yi suka nufi ɗakin Safwan don yin shiri don yau ma akwai wajen da za su je, shine ma makasudin zuwan Kamal gidan.
*****KATSINA*****
Su Abdul na zaune a asibitin, dangi ne ke ta zuwa gaishe da Safnah, don da yawa basu ji ba se yau, iyayen su da yara duka sun zo sun gaishe da ita, mutum ɗaya ne bata zo ba, Antyn su Abdul (matar Baba Salihu) don ba ko ina take zuwa ba.
Abdul ganin mutanen da suka zo yasa su fita kai tsaye gidan su Sadiq suka nufa shi da Faruq.
Ba kowa a gidan se Sadiq ɗin don yaran na makaranta momy kuma ta na asibiti wajen.
Da sallama suka shiga ɗakin Sadiq ɗin yana zaune gaban system ɗin shi, rufe system ɗin yayi tare da amsa sallamar su fuskar shi ɗauke da Murmushi.
"Ɗan rai nin wayo, se yawo da hankali kake min, to