Header Ads
Showing 27001 words to 30000 words out of 57539 words

Chapter 10 - KADDARAR SAFWAN Book one 1 by khadeejerh Ishaq.txt

Ads the beginning of article before Image

19 Jun 2024

556

Ads at the middle of Article

shagwaɓa, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mai ba,
"Ki tafi da wayar a haka idan kinje ki bawa Hindatu" "to" kawai tace sannan ta miƙe ta nufi ɗakin nasu, a zuciyar ta ta na mamakin wannan abun haka.


Da sallama ta shiga ɗakin suna zaune suna hira har da Teemah don tazo part ɗin nasu "Hajiya Safnah ai yanzu nake shirin zuwa ɗakin naki don naji ki shiru, gashi an faɗa min gogan namu har waya ya siya miki ma a kawo mana mu ɗan dangwala" duk surutun da Teemah take yi bata lura da alamar da Safnah take yi mata ba se da ta kai aya.


"Safnah Teemah ce ke magana ko?"
"Ehh" ta faɗa tare da ƙarasawa wajen Hindatu ta miƙa mata wayar, "me ya faru?" Hindatu ta tambaya bayan ta ƙarɓi wayar, kafin ta bata amsa taji Muryar yaya Abdul yana faɗin "Hindu ki faɗawa Teemah idan na dawo se ta ɗanɗana kuɗar ta" Dariya Hindatu ta sheƙe dashi tare da cewa "yaya Abdul ya kwana biyu 2" jin ta ambaci yaya Abdul yasa Meenal matsowa kusa da ita banda Teemah da ta saki baki ya kasa rufuwa.


"Ba wani kwana biyu 2, bayan tunda na tafi ba wanda ya kira ni a cikin ku, se A'isha, wannan ya nuna baku damu dani ba ma"


"Haba yaya Abdul wallahi mun damu da kai kawai an samu akasi ne ba mu kira ba, amma kayi hakuri" cewar Meenal, Hindatu ta ɗora da cewa "yaya kayi hakuri bamu so mu takura maka ne gara kayi aikin ka"


"To naji nagode, amma meyasa kuke barin Safnah ita ɗaya a ɗaki?" Kallon Safnah tayi da ta tafi duniyar tunani ma sannan tace "yaya kasan halinta har yau ta kasa sakewa damu"


"Kuma muma muna so muga muna hira da ita sosai amma bata shiga lamarin mu" Meenal ta faɗa.


"To naji dai nace ta daina zaman ɗaki ita kaɗai, idan ta zauna ma ku rinƙa bin ta tunda nasan baza tace ku fita ba"


"To yaya za'a kiyaye" cewar Hindatu
"Ba Teemah wayar" ya faɗa,
"Gashi Teemah" Hindatu ta faɗa tare da bata wayar ba musu ta ƙarɓa ta kara a kunne tare da cewa "Allah ya taimaki babban yaya kwata-kwata da fatan kana lafiya" "ban sani ba, ke wai yaushe zaki yi hankali ne Teemah, baza ki nutsu ba ko?" "Yaya kayi hakuri"
"Shikenan kema har da ke ko nema na baku yi ko se ƴaruwa ta kawai"


"To afuwan babban yaya"


"To bata wayar ta kar ki mata latse-latse naji kina faɗin zaki yi, ko kar ki mata wani ɓarnar"


"Su yaya Abdul manya kasan nima wayar nan dai ina da ita, base kunyi min gori ba"


Ɗif! Taji ya yanke wayar, ita ma sauke wayar tayi tana dariya tace "Kai!, Allah ya bar mana yaya Abdul namu"
"Ameen" duka suka amsa.
"Wai wasu sharuɗa naji yana gindaya muku ne?" Cewar Teemah tana ta latse-latse a wayar Safnah don har yanzu yana wajen ta.
"Bafa wani sharaɗi bane kawai cewa yayi mu daina barin Safnah ita ɗaya" cewar Meenal"ikon Allah abu ya kan-kama haka akayi!" Cewar Teemah tana zare idanu waje "ke dai kina da matsala wallahi" Hindatu tace, ko bi ta kanta Teemah bata yi ba sema cewa Safnah tayi "La! Ashe kin buɗe facebook da WhatsApp shine ko kiyi adding ɗin mu, ko number mu ma baki dashi" Murmushi Safnah tayi sannan tace "kuyi hakuri ƴanuwana jiya na buɗe kuma bansan sunan da kuke using ba a facebook, ki saka min number ki da na sauran harda na A'isha ma"
"To ko ke fa!,
"Kai Teemah ba dama, inaji yaya Abdul na miki gargaɗi kar ki mata latse-latse a waya, amma se da kika yi, shima ai yasan hali ne" cewar Hindatu.
"To ai mara gaskiya shi yake gudun ayi mai bincike a waya wallahi" cewar Teemah tare da ba Safnah wayan ta, bayan ta saka mata number, sannan tayi searching sunan su a facebook ta tura friend request.


Hira suka cigaba da yi se bayan isha'i sannan Teemah ta koma part ɗin su bayan ta cika cikin ta.


ZARIA


Safwan bashi ya farka ba se ƙarfe 9:00 na safe, da sauri ya tashi ya shiga bayi yayi wanka tare da yin alwala, wata jallabiya fara ya saka sannan ya shinfiɗa darduma ya gabatar da sallar asuba ɗin shi, sannan yayi istigifari tare da addu'o'in Allah ya shirye shi.




Bayan ya idar ne ya nufi sif ɗin shi, ƙananun kaya ya fito da su Baƙar wando da jar riga ya saka, sunyi bala'in yi masa kyau, agogo ya ɗaura wa hannun shi tare da ɗaukan wani glass baƙi ya kwama wa fuskar shi, sannan ya ɗauki makullin shi, wanda yake haɗe da na mota da na ɗakin shi ya fita.





??????????????????
_*????‍♂️ƘADDARAR SAFWAN????‍♂️*_
??????????????????
_*By*_
_*Khadeejerh Ishaq*_
*{Oum Ayshat}*
_*Jakadiyar Dashen??Allah*_




°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*DASHEN??AIIAH*
*WRITER'S??ASSOCIATION*
```Ƙungiyace ta jajirtattu kuma tsayayyun marubuta masu aiki da basira da hikima da fikirar da Allah yabasu, wajen kawo muku litattafai masu ilimantar daku da wa'azantar daku da faɗakar daku da kuma koyar daku darussa kala-kala dan gane da rayuwar duniya data lahira ma gaba ɗaya, da kuma nishaɗantar daku Masoyan mu```
_*ALLAH SHINE GATAN MU*_
_*AL'ƘALAMI✍??YAFI TAKOBI??️*_
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
_*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*_


*PAGE*_21&22
A falo ya samu Daddyn shi da Anty suna hira, zama yayi shima tare da gaishe su,


"Babana ina zuwa haka, ko zaka wajen ƴartawa ne" Daddy yace


"A'a Daddy ni daga nan Kano na nufa na fito na faɗa maka ne dama"


"Kano kuma?" Daddy ya tambaya da alamar mamaki.


"Ehh Daddy kasan munyi hutu, kuma na daɗe ban je ba"


"To Allah ya dawo da kai lafiya, kwana nawa zaka yi ne"


"Daddy gobe zan dawo ma"


"To Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya my son"


"Ameen Daddy" yace tare da miƙewa ya fita, kai tsaye wajen da motocin shi suke ya nufa wata jar mota ya shiga ya tayar tare da nufan gate ɗin gidan.




Katsina
Bara mu waiwaya gidan su yaya Abdul


Bayan tafiyar Abdul Hajiya Safiya ta bawa yarinyar ta Hafsat wayar ta don ta kira Dadyn ta, ta faɗa mai, aiko ƙarya da gaskiya ta haɗa ta faɗa mai.


Ko minti10 ba'ayi ba ya iso gidan, nan da nan aka kira Doctor ya duba ta, ya tabbatar musu ta sami tsagewar ƙashi, ran Daddy ya matuƙar ɓaci sosai, hakan yasa shi yi ma Abdul faɗa tare da cewa ya koma wajen aikin shi.


Sai da ya samu Baba Bashir (Baban su Teemah) yayi mai magana ya faɗa mai abinda ke faruwa, shine ya samu Baba Babba ya bashi hakuri sannan ya yarda ya dawo idan sun samu hutu, da yace kar ya sake ya dawo.


Hajiya Safiya kuwa wani tsanar Abdul ne ya ƙara shiga ranta haɗe da shakkar sa, don duk abinda take yi mai tana shakkar sa sosai.




Yau Safnah suka je suka ƙarɓo ɗinkin ta sunyi kyau sosai, kuma ɗinkin zamani akayi mata, kaya ne masu yawan gaske don ba'a gama ɗinkawa ba ma.






Ƙarfe 1:00 Safwan ya isa Kano wata anguwa da ake kira Tarauni, dai-dai wani haɗaɗɗen gida ya tsaya horn ya danna, buɗe mai ƙatoton gate ɗin akayi.


Danna hancin motar yayi zuwa cikin gidan, kai tsaye wajen da aka tanada don aje motoci ya nufa ya ajiye nashi motar sannan ya nufi cikin ƙofar falon.


Da sallama ya shiga, ba kowa a falon se wata dattijuwar mata, cikin fara'a ta amsa sallamar.


Har ƙasa ya duka ya gaishe da ita, cikin fara'a ta amsa tare da cewa "Muhammadu yau kai ne a garin namu"


"Ehh kaka ina Momyna"


"Sannu mai gidana wato baka yi kewar matar taka ba, se Momyn ka ko?, Ko da ka manta da ni tunda naji ance auren ka ma ya kusa"


Dariya yayi tare da cewa "Haba kakana kinsan kina raina, daga ke ba wata"


"Yayi kyau, Momyn ka tana nan a waje baku haɗu ba"


"A'a Kaka, ban ganta ba ta fita ne?"


"A'a tana cikin gidan nan tayi baƙo ne" wani irin bugu zuciyar Safwan tayi, miƙewa yayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi waje.


Be hango momyn nashi ba, hakan yasa shi zuwa wajen mai gadi ya tambaye shi ina momyn shi, wata mota mai gadi ya nuna mai tare da cewa "tana cikin waccan motar"


"Nagode"kawai Safwan yace sannan ya nufi motar.


Glass ɗin motar a rufe yake hakan yasa shi yin knocking, buɗe glass ɗin akayi, wata farar mata ce kyakkyawa fuskar ta ɗauke da murmushi tace "my son yaushe ka zo"
Shi ko Safwan mutumin da yake cikin motar ya kurawa ido, fari ne sosai kuma ze iya girman Dadyn shi, a zuciyar shi yace "momy ko me ta gani a jikin wannan, dame yafi Daddyna don Allah"


"Kai Safwan wannan Wani abu ne ka ƙurawa mutum ido ko gaisuwa babu?"


Maganar Momyn shi ta dawo da shi daga tunanin da yake yi don da ƙarfi tayi mai maganar.


"Ina wuni" Safwan ya faɗa bayan ya tattara nutsuwar sa.


"Lafiya lau, ya hanya" mutumin ya faɗa da murmushi ɗauke a fuskar shi.


Safwan be saurari wani magana ba ya koma ciki, be samu kaka a falo ba hakan yasa ya nufi wani ɗaki wanda ya kasance na autan su momyn shi ne mai suna Mubarak, sa'an Safwan ne suna mutunci sosai.


Ya same shi zaune a falo yana kallo, gaiswa suka yi sannan yace "Mubarak wai waye suke zance da Momy a waje,


"Alhaji Umar ne, shine wanda zai auri Anty, saura 3week ma"


Jiri ne ya kwashi Safwan, ba shiri ya zauna a kujerar da yake dafe da ita, cikin tsantsar mamaki yace
"Mubarak dama da gaske ne Momyna zata auri wani"


Cikin halin ko in kula Mubarak yace "Ehh mana"


Tashi Safwan yayi ya fita, falo ya dawo ya samu Kakan nashi na zaune, shima zama yayi, yana zama momyn shi ta shigo da sallama.


Kaka ce ta amsa sallamar don Safwan ko sallamar be amsa ba, waje ta samu ta zauna, tare da cewa.


"Safwan yaushe ka zama haka, kana gani na da baƙo baka gaishe dashi ba, amma ka ƙura mai ido, waye yace ma kazo wajen?"


"Momy ba kiyi farin ciki da zuwa na ba kenan, har kike min faɗa don na kasa hakuri naje na gan ki"


"A'a ya za'ayi nace banyi farin ciki da zuwan ka ba, kasan kai ne ɗa guda ɗaya da Allah ya bani"


"Shikenan Momy, amma ban ji daɗi ba da baza ki dawo garemu ba, Momy ina matuƙar buƙatar ki a kusa dani"


"Safwan nida zuwa Zaria se bikin ka in sha Allah, ya Safnah kuwa?"


Wani iri Safwan yake ji, yayi takaicin zuwa Kano ma da yayi yau ɗin nan,


"Momy Safnah bata nan tana garin su"


"Ayya! Allah ya dawo da ita lafiya"


"Ameen"
Kawai Safwan yace


"Mai gidana ko abinci baka ci bafa ga abincin can a dining"


"Na ƙoshi" Safwan yace.


Momy kuwa miƙewa tayi ta nufi ɗakin ta,


Kallo Safwan ya bita dashi, kafin ya tashi shima ya koma ɗakin Mubarak domin yin Sallah, don yanzu kusan 2:30 ma.


Falo ya dawo bayan yayi sallar sunyi hira da Mubarak, ba kowa a falon hakan yasa shi nufar ɗakin Momyn shi.




Kwalliya ya samu tana yi, don har ta sake wanka ma, amsa sallamar da yayi tayi, waje ya samu ya zauna tare da cewa "Momyna zaki fita ne?"


"Ehh Safwan zan je anguwa ne"


"Zan raka ki" Murmushi Momy tayi tare da cewa "Safwan kenan, kana mayar da kan ka yaro, da girman ka yanzu zan tafi da kai anguwa?"


Murmushi yayi sannan yace
"Momy driving ɗinki fa zanyi"
"A'a Safwan ka tafi ɗakin Kaka yanzu zan dawo nima, yaushe zaka koma Zaria?"


Tashi Safwan yayi ya fita ba tare da yace komai ba.


Kai tsaye tsakar gidan ya nufa wajen da yayi perking motar shi, shiga yayi tare da kunnawa ya bar gidan a guje.




KATSINA


Safnah ne tare da Hindatu a kicin sun dage se aiki suke, don girkin tarar ya Abdul suke yi, don yana hanya yau, musamman ya kira Safnah ya faɗa mata ta shirya mai girki gashi da abokin shi zasu zo shi ɗan Kaduna ne, tunda Abdul ya tafi kusan-kullum se ya kira Safnah sun gaisa, abun har haushi yake bawa Safnah, don bata son yawan surutu.




**********
Safwan kai tsaye Zaria ya nufa don idan ya cigaba da zama a Kano lallai zuciyar shi zata iya tarwatsewa.


Ƙarfe 5:30 ya iso Zaria, a matuƙar gajiye ga baƙin ciki da takaici, perking motar shi yayi ya nufi cikin gidan.


Da sallama ya shiga falon ganin Daddyn shi a falon,
"Sannu da gida Daddy" ya faɗa yana nufar kwanar ɗakin shi,


"Safwan!" Daddyn shi ya kira shi, Safwan na shirin shan-kwanar ɗakin yaji kiran Daddyn nashi, yaji haushi sosai na kiran don baya so Daddyn shi ya gane halin da yake ciki.


"Safwan ya na ganka yau, kai da kace se gobe zaka dawo"


"Ehh Daddy na canza shawara ne"


"Ok, wai baka ga munyi baƙuwa bane?"


"Ehh, Daddy waye?"


"Ƴa ta Salmah mana"
"Salmah!" Ya faɗa a zuciyar shi,


"Gata can a dining".


Duban shi ya kai zuwa dining ɗin, Salmah ya gani fuskar ta ɗauke da murmushi, takaici ne ya cika shi, hanyar ɗakin shi ya nufa ba tare da ya sake kallon ta ba.


Yana shiga ɗakin ya faɗa kan kujera dafe da kan shi, da yake mai bala'in ciwo.


A falo kuwa Daddy ne yake cewa Salma "Salmah se kinyi haƙuri sosai da Safwan, domin wani irin mutum ne me yuwan sha'ani"


"Bakomai Daddy Insha Allah zanyi haƙuri"
"Yawwa ƴar albarka, yanzu kije ki same shi ku gaisa se ki fito driver ya kai ki gida"


"To Daddy" Salmah ta faɗa tana miƙewa da sauri don tayi kewar Sweet ɗin nata don anyi hutun school"


Murɗa kofar tayi taji ta a buɗe, da sallama ta shiga ɗakin, can ta hango shi a kujerar idon shi a rufe, kusa da kujerar ta ƙarasa,


"Yaya Safwan!, Yaya Safwan!" Ta kira sunan shi, be amsa ba kuma be ɗago ba.


"Yaya Safwannn!!!" Ta faɗa da ɗan ƙarfin ta,
Cikin zafin nama ya miƙe tsaye, Ba zato ba tsammani taji ya yarfa mata wani kyakkyawan mari,


Wani razanannen ihu ta saki tayi tagal-tagal zata faɗi, cikin zafin nama ya taro ta don akan kwalba zata faɗi wurgi ya ƙara yi da ita wajen ƙofar ɗakin,


"Uban waye ya baki damar shigo min ɗaki?, har kina min ihu a kai, ke daƙiƙiyar ina ce?"


Salmah miƙewa tayi fa karkaɗe jikin ta, tare da share hawayen da suka wanke mata fuska sannan tace "Yaya Safwan da'ace zan iya cire soyayyar ka a cikin zuciya ta da tuni na cire, domin kaso wanda baya son ka babbar wahala ce, a kullum ina roƙon Allah ya yaye min soyayyar ka duk da anyi mana baiko, amma a kullum kamar ana ƙaramin son ka ne, Ya Safwan miye laifina don zuciyata ta kamu da ƙaunar ka, don Allah ka agaza min ka furta min kalaman so, zuciyata zata yi sanyi, ko so ɗaya ne kace kana so na mana"


Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, Jikin Safwan yayi sanyi sosai, don se yanzu ya dawo hayyacin shi.


Wajen da take ya ƙarasa tare da cewa
"Kiyi hakuri Salmah ina cikin wani hali ne, ki share hawayen nan kar Daddy ya gani don Allah"


"To yaya Safwan, amma me yake damunka ne?"


"Ba abun da ya shafe ki bane, ki tafi gida za muyi waya anjima"


"Ka tabbatar?, Haka kake cewa nayi ta kira baka ɗauka ba kuma"


"A'a ni zan kira ki da kai na ma" fara'a ne ya wanzu a fuskar ta Murmushi tayi tare da cewa "to se anjima" sannan ta buɗe ƙofar ta fita,


Tsaki Safwan yayi sannan ya nufi Bedroom ɗin shi domin yin Sallar la'asar da ta riske shi a hanya.




Yana shiga wayar shi ta ɗauki ƙara alamar shigowar kira, da sauri ya duba don ganin me kiran nashi.


MY MOMCY
Sunan da ya gani kenan, cigaba da tafiya yayi bayan ya saka wayar a aljihun shi, kira ne ya sake shigowa bayan waccan ya yanke, ciro wayar yayi ya ɗauka tare da kara wa a kunnen shi "Safwan ina ka shiga ne kasa hankalin mu ya tashi"


"Momy na taho gida ne"


"Wani gidan?"


"Momy ina Zaria, na dawo tun ɗazu ma"


"Har kake faɗa min kana Zaria, ba sallama ba komai, se dai na neme ka na rasa ko?, hakan ka kyauta kenan Safwan!?"


"Haba Momy kiyi hakuri"


"Shikenan ka kyauta" tana kaiwa nan ta kashe wayar.


Safwan cilli yayi da wayar kan a kan gadon shi, sannan ya nufi toilet ɗin.


Minti10 yayi cikakku sannan ya fito ɗaure da tawul, gaban miron da yake ɗakin yaje, mai kawai ya shafa a jikin shi se ya fesa turare sannan ya zura wata baƙar jallabiya, darduma ya shinfiɗa tare da tayar da sallah.




*****KATSINA*****


Se wajen ƙarfe 2:00 sannan suka gama girkin, a mutuƙar gajiye Safnah ta nufi ɗakin ta domin yin wanka, itama Meenal ɗakin su ta nufa, Hindu kuwa tana part ɗin su Teemah.


Safnah tana shiga ɗaki ta zube akan kujera don ji take kamar kanta ze tsage tsabar ciwo da yake mata, bata yi aune ba bacci mai nauyi ya ɗauke ta.




Se wajen ƙarfe 3:15 sannan Meenal ta shigo tashin ta.


Miƙa Safnah tayi tare da miƙewa ido ta tsurawa Meenal ta kasa magana ma.
"Ki zo yaya Abdul yana kira"


"Har ya iso ne?" "Ehh tun ɗazu ma".


"Don Allah ki jira ni, wanka zanyi tun ɗazu bacci ya kwashe ni, bari nayi shaf-shaf"


"To yi sauri". Meenal ta faɗa tana zama a kujerar da yake falon.




Cikin mintuna15 Safnah ta fito sanye da doguwar riga Blue colour yayi mata kyau sosai se wani hula da ta ɗaura pink colour mai kamar na sanyi amma kuma shara-shara ne, ko hoda bata shafa ba se man baki da ta saka fuskar ta se tayi fresh sosai.


Jerowa suka yi suka fito, can ta hango yaya Abdul ɗin su biyu ne a dining ɗin, basu gan su ba, kasancewar sun juya musu baya ne.


Da sallama suka ƙarasa wajen, amsawa sukayi
"Ina wuni yaya Abdul" Safnah ta faɗa
"Lafiya lau Safnah" juyawa tayi ta gaishe da ɗayan kyakkyawan saurayi ne sosai gashi fari kamar Balarabe, cikin shi da Abdul bansan waye gwanin kyau ba.


"Safnah tun ɗazu na iso na tambaya aka ce kina bacci"


Safnah bata ce komai se sunkuyar da kai ƙasa tayi, don wata irin kunya take ji kamar ta nutse ga kallon da abokin yaya Abdul yake mata, bata son kallo ko kaɗan.


"Safnah wannan shine

Ads At the End of Article

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
Footer Ads